Showing 171001 words to 174000 words out of 216282 words

Chapter 58 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ta mik'e ta k'arasa wajan sa tace, "Dr ya jikin nata?." Likitan ya kalli Daddy ya kalli Mum d'in sannan yace, "Ta haihu." Da mamaki Mum ta kalli Daddy shima ya kalle ta ta dawo da kallon ta ga likitan tace, "Kamar ya ta haihu? Yi min bayani ban gane ba."

Dr yace, "Eh ta haihu, ta haifi yaro namiji d'an wata bakwai wanda ake kira bakwaini." Daddy yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "Haihuwa Dr?."
"Eh yallabai, tsoro da firgici da tashin hankalin da take a ciki ne ya jawo haihuwar da gaggawa, inda ace cikin k'arami ne bai zama mutum ba da zai zube ne sabida ta firgita sosai."

Mum tace, "Yanzu ya jikin nata ita?." Dr yace, "gaskiya jikin ta babu dad'i, jinin ta ya hau sosai ga kuma haihuwa ga zuciyar ta da take bugawa very fast har yanzu unconsciously take. Babyn kuma yana inda aka tanada domin cigaba da rainon sa."

Baya Mum tayi ta zauna a wannan lokacin Eman tazo wajan ganin yanayin da Mum take ciki ya skaa ta rik'e ta tana fad'in, "Mum meye faru da Jiddan?." Zama tayi kusa da ita Daddy ma ya zauna ya kalli Mum yace, "Ki sanar dani abinda ya firgita Jidda haka dan nasan kuna tare, sannan ya banga mijin ta ko wani nata a nan ba sai ke kad'ai?. Ba taro aka kira ku a gidan sarki ba?."

Kuka Mum take yi sosai babu alamun zata tsayar dashi balle kuma ta iya masa magana ganin hakan sai ya tashi ya fita daga asibitin ma gabad'aya ya barsu a wajan dan firgice shima yake jin ance tsoro ya saka ta haihu. Duk yadda Eman taso rarrshin Mum abin yaci tura kuka take kamar wacce aka yiwa rasuwa itama sai ta fara kukan duk da bata san abinda ya faru ba amma kukan Mum d'in ya sakata kuka dan tasan akwai wani abun a k'asa.

*&&*

? ? ? ? ? Kuka Suhaima take yi sosai ganin Mama a kwance ko motsin kirki batayi an saka mata abinda zai taimaka mata wajan yin numfashi amma duk da haka numfashin baya fita yadda ya kamata a kirjin ta yake tsayawa baya sauka ciki.

Tana zaune a kan kujerar kusa da gadon Maman tayi pillow da gadon tana cigaba da zubar da hawaye. "Yaya Hydar, Yaya Aliyu meyasa kukayi abinda kuka yi? Meyasa baku duba halin da Mama dani kaina zan shiga ba kuka zab'i son zuciyar ku akan farin cikin Mama?. Allah sarki Yaya Asad ya zaiji? Duk qaunar da yake yiwa Yaya Hydar amma da abinda zai saka masa kenan?. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta fad'a a bayyane tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya bata tab'a shiga kwatankwacin rud'ani kamar wannan ba.

Tun daga bakin k'ofar ake jin sautin kukan Suhaima Dr Yasir ya shigo da sauri yana kallon ta murya can k'asa yace, "Suhaima please ki daina wannan kukan baki ga a gaban patient kike bane ba? In kika tashe ta fa?."

Maimakon tayi shiru sai ta nuna masa Mama tana kuka tace, "Mama ce fa a kwance a haka, kalli Mamana ita kad'ai ba Yaya Hydar babu Yaya Aliyu babu Yaya Asad a tare da ita. Ya Mama zataji in ta farka ta ganta ita kad'ai babu su a tare da ita?. Bazan iya yin shiru ba ka barni nayi kukana bazan iya daina kuka ba."

Ganin yadda take maganar kamar bata cikin hankalin ta hakan ya saka shi fita da sauri suka shigo da nurses mata guda biyu aka d'auke Suhaima daga wajan suka fita da ita zuwa wani d'akin daban aka yi mata allurar bacci suka saka mata ruwa dan itama tana buk'atar magani.

*&&&*
? ? ? ??
? ? ? ? ? Ciwon kai mai tsakani ya saka Rauda a gaba tunda suka koma gida ko buWe ido bata son yi sabida yadda kan yake mata mugun ciwo ga zuciyar ta da take bugawa tunda take a duniya bata tab'a jin tashin hankali kamar wanda take ciki ba, ji take zuciyar ta na fizga sabida bala'in rud'ani jikinta har rawa yake yi.

Umma da take zaune a gefen ta a zaune ita kuma ta jingina da kujera ta rik'e kai da hannu biyu tana kallon sama. Umma tace, "Sannu Rauda, kodai muje asibiti wannan ciwon kan bana k'are bane ba." Kai ta girgiza alamun a'a Umma tayi shiru tana girgiza kai in ta tuna irin abubuwan da suka ji sai taji amana ta k'are a duniya kowa ma ba abin yarda bane.

Umma ta kalle ta tace, "Gwara muje asibitin kar kiyi b'ari, dan abinda kike ji a zuciyar ki a yanzu tsaf zai iya sakawa cikin jikin ki ya zube." Lumshe ido Rauda tayi ta d'ago kai ta kalli Umma ta mayar da idon ta ta kulle. Umma ta mik'e tsaye ta mik'ar da ita itama tace, "Muje ki kwanta ko zaki samu sauk'in abinda kike ji."

D'aki Umma ta kai Rauda ta kwantar da ita ta bata magani tasha ta zauna a gefen ta har sai da bacci ya d'auke ta sannan ta fito ta k'yale ta. Baba bai dawo ba sai magriba har lokacin Rauda bacci take yi kai tsaye b'angaren Umman ya nufo yana zuwa ya same ta ta idar da sallah tana lazimi a kan kujera ita kad'ai Ummulkhairi da Khalil suna wajan Innan su.

Da sallama ya shigo ta amsa tana sauke numfashi ya k'araso ya zauna yace, "Ya jikin Raudan?." Umma tace, "bacci take har yanzu, dak'yar baccin ya d'auke ta shiyasa ko sallah ban tashe ta ba." Baba ya girgiz kansa yace, "Ai gwara ta samu baccin, irin wannan tashin hankalin sai ya saka zuciyar ka ta buga."
Umma tace, "ita da take da k'aramin ciki ma sai ya zube, wacce ya girma ta fad'i tana zubar da jini ina ga wacce bai girma ba?" Ta fad'a tana tagumi domin abubuwan da suka faru ganin su take kamar almara.

Baba ya girgiza kansa yace, "Wato Binta tunda Allah ya kawo ni duniya ban tab'a jin tashin hankali kamar wanda naji yau ba, ace wanda kuke ciki d'aya uwa d'aya kuma uba d'aya sune suke k'okarin ganin bayan ka akan abinda ba kaine ka bawa kanka ba?. Ke duniya ina zaki je damu? Amana tayi k'aranci kowa ba abin yarda bane ba."

Umma ta girgiza kai tace, "Har yanzu nutsuwa ta tak'i dawowa jikina, kaina jinsa nake a cushe bana fahimtar komai wallahi. D'an uwa na jini uwa d'aya uba d'aya amma akan mulki ya nemi salwantar da jinin sa? Meye abin so a mulkin?." Baba yace, "Baki san dad'in mulki bane shiyasa kike fad'ar haka, duk wani mai mulki da ya lashi zumar sa baya so ya daina lasar ta har abada, shiyasa hankalin su yake tashi in suka rasa kujerar su wasu kiga kamar ma zasuyi hauka. Mulki babu abinda baya sakawa ayi dan a d'auki rai a neman mulki abu ne mai sauk'i."

Umma tace, "Ni kuwa nasan abu ne mai sauk'i tunda gashi naji da kunne na. Babu wanda ya bami tausayi sai Asad d'in da mahaifin sa, duk irin abubuwan da mahaifiyar sa tayi mana amma wallahi sai nake jin zuciyata tana tausaya mata dan Allah kad'ai yasan halin da take ciki a yanzu. Y'ay'anta da take alfahari take tutiya ace d'aya ne kawai mai amfani a cikin su? Muguntar wannan tana wane ta wannan, kowa a cikin su burin sa ya kawar da d'an uwan sa?."

Baba yace, "Hydar d'in shine abin mamaki, ki tuna yadda yake shigewa Asad d'in gaba a akan komai hatta auren sa da Rauda shine ya assa shi ashe yana da manufar yin hakan badan Allah ya aikata ba. Yafi kowa bani mamaki ya kuma fi kowa bani tsoro, domin kaji tsoron maqiyin ka mai fuska biyu gwar wanda zai nuna maka kai tsaye baya sonka da wanda zai dinga yi maka kwantan b'auna."

Umma tace, "Shi mai martaban ya zaiji?. K'anin sa uwa d'aya uba d'aya, matar sa kuma uwar gidan sa, ga ita kanta babar Asad d'in, ga y'ay'an sa guda biyu. In ba namijin gaske mai dakakkiyar zuciya ba sai ya yanke jiki ya fad'i ya had'u da lalurar shanyewar b'arin jiki. Ace duk wanda ya aikata maka sharri jinin kane da matan ka?."

Baba yace, "Allah baya cutar da bawa akan laifin da bai aikata ba, duk wanda ya kasance mai yawan addu'a da neman zab'in Allah Allah bazai barshi da kansa ba sai ya shiga cikin lamarin sa. Yanzu ki duba shi Wazirin cikin lokaci kad'an Allah ya nuna masa sakayya babu b'ata lokaci y'ay'an sa biyu sun rasu a lokaci d'aya. Ni na d'auka ma yara ne fa ashe dukkan su babu wanda bai kai munzalin aure ba babu kamar namijin ma da ya girma sosai. Abin mamaki da d'aure kai turaren da aka bashi da nufin kashe Asad da baban sa suka d'auka sukayi amfani dashi su suka mutu. Dan Allah in baka ji tsoron Allah a lamarin nan ba tsoron me zaka ji?. In bakayi imani da Allah ba dawa zakayi imani?. Kai Allah kasa mufi k'arfin zuciyar mu."

Umma girgiza kai kawai take yi cikin rud'ani zuciyar ta ta karye tace, "Kaji tsoron wanda aka zalunta in Allah ya tashi saka masa, yanzu kalli cikin lokaci kad'an Allah ya nuna masa bai isa yayi abinda bai nufa ba. Ita kuma uwar gidan garin son a kashe wani kaso kashe ta in mai hankali ce iya wannan ya isheta ishara, kalli ita mahaifiyar tasu duk alfaharin da take dasu da nuna talaka ba komai bane sai gashi alfarmar talakan taci kuma y'ay'an nata guda ukun d'aya ne kawai mai amfani a ciki. Shi Aliyun da ake nufin kashe d'an uwan sa dashi har ana so a saka shi hauka sai gashi......." umma bata k'arasa ba sai tace, "Kai Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya hayyu ya qayyum ka saka mufi k'arfin zuciyar mu, ka tsare mu ka kare mu a duk inda muke kasa mu rinyaji zuciyar mu ba ita ta rinjaye mu ba" Umma ta fad'a tana d'aga hannun ta sama.

Baba ya amsa da amin sukayi shiru dukkan su kafin Baba yace, "Ni daman nasan babu ta yadda za'ayi Asad ya rsntse yace bashi ya saki Rauda ba akan k'arya, ashe duka aikin d'an uwan sane." Umma bata ce komai ba girgiza kai kawai take yi kafin ta sauke numfashi tace, "Duka haka Allah ya nufa ya kuma k'addara, shekara har ta kusa zagowa da bikin sai yanzu ake samun sassauci a lamarin auren nasu. Ni wallahi yanzu abin yafi na baya bani tsoro, kaga Hydar d'in nan gani nake kamar bazai bar Rauda ba dan babu alamun nadama fa a tare dashi."

Baba yace, "yadda Allah ya kare Asad da mahaifin sa haka Allah zai kare ta, zuciyar ta a wanke take bata tab'a nufar wani da sharri ba Allah bazai bari a cuce ta ba." Umma ta d'aga kai kawai Baba ya tashi ya fita zuwa masallaci dan yaji kiran sallar i'sha itama ta tashi ta tayar da sallah.

Sai bayan ta idar ta duba Rauda ta ganta a zaune da alama ma tayi sallah itama ta koma ta kawo mata abinci da kanta ta tilasta mata taci badan taso ba dan ita har yanzu zuciyar ta bata amince cikin Asad ne a jikin ta ba.

*&&&*

? ? ? ? ? Cikin awa da bai wuce uku ba an chanja komai na b'angaren mai Martaba Asad hatta carpet an cire shi an saka wani dan mahaifin sa yace bai amince da komai na ciki ba. Dukka kayan sawar Asad dana Aliyu an fito dasu daman mai martaba ya bayar da order dinki da alkyabba manya-manya ta Asad duk an kawo an saka ya koma sabo dal.

Yana tsaye a jikin window yana kallon jama'ar gidan da suke ta kai kawo ya sauke numfashi ya juyo yana kallon falon ba komai ne yake fad'o masa ba sai zaman Jidda a cikin sa ita da Yayan sa. Tsaki yaja ya d'auke kansa yana cize baki, "Hydar!" Ya furta a bayyane yana lumshe idanun sa da suka kankance sabida tashin hankali da b'acin rai.

Zuciyar sa bugawa take yi Allah ya sani yana qaunar Hydar da zuciya d'aya duk abin nan da fari baiji son sa ya fita daga zuciyar sa ba saima cutar dashi da son yake so yayi. Barin jikin window d'in yayi ya k'araso cikin falon yana niyar sauka yaga mahaifin sa na yawowa saman.

Dole ya koma da baya ya bashi hanya ya wuce ya zauna ya k'araso ya zauna a k'asan carpet yace, "Barka da zuwa." Mai martaba yace, "Ina kake niyar zuwa haka?." Asad yace, "Zanje wajan Mama ne hankalina yak'i kwanciya ina so na ganta."

"Ban amince da fitar sirrin nan da kake yi ba kayi fitar da ko wanne saraki yake yi." Asad yace, "In Allah ya amince zanyi abinda akace." Mai martaba yace, "Ya batun matar ka Jidda?."

Gaban sa ya fad'i matuk'a ya d'ago yace, "Allah ya k'ara maka lafiya ni ba matata bace ba." Mai martaba yace, "Matar kace Asad, shari'a ta baka d'an cikin ta duk da ba naka bane. Ka tambayi ya lafiyar ta take?."

Asad yace, "Ina neman afuwar ka dan ni gaskiya indai dan igiyar aurena da yake kanta ne na jima da datse ta, na sake ta!" Ya furta a sanyaye yana kallon mahaifin nasa da shima yake kallon sa da nasa mamakin.
"Ka sake ta fa kace Asad? Waye ya fad'a maka shugaba yana saki?. Kaifa sarki ne shugaba ne da zaka daqile yawaitar sakin aure da ake yi amma da kanka kake furta ka sake ta?."

Asad yace, "Allah ya wuci zuciyar mahaifina, bazan iya zama da ita ba mahaifina ya shaida ita d'in fasiqa ce taya zan iya zama da wacce tayi alfasha da auren ta tana sane?. Daman can zab'in Mama ce nayi biyayya ne na aure ta badan ina so ba sai dan gudun b'acin ran Mama, yanzu kuma ga abinda ya biyo baya zama na da ita ya haramta har abada. Batun da da mai martaba yake yi jinin Aliyu jinina ne zan iya rik'e masa y'ay'a d'ari indai akace jinin sane koda ba y'ay'an sunnah bane ba, amma bazan iya zama da ita ba."

Mai martaba da yake jin sa yasan gaskiya yake fad'a masa amma yana gudun zubewar k'imar gidan dan in akaji labarin Asad ya saki Jidda ga d'a kuma sunan gidan da tarihin gidan gabad'aya ya lalace. Duk sanda aka bud'e ido akaga baby Jidda sai Rauda kowa zai ta tunanin inda take k'arshe a fara mumman zato a kan hakan. Yace, "Asad nasan gaskiya kake fad'a, amma ina so ka duba yanayin gidan da kake da kuma matsayin da kake dashi, me mutanen gari dama jama'ar gidan nan da basu san abinda ya faru ba in akace ka saki matar ka bayan tana da cikin ka?." Asad ya kalli mahaifin sa jin ya ambaci ciki sa sai mai martaba yayi murmushi yace, "Nasan ba jinin ka bane amma cikin Aliyu naka ne, abinda yayi ka shine yayi Aliyu. Kowa yasan Jidda matar kace ya kenan in akace yau babu Jidda a gidan sai wata daban me hakan yake nufi?."

Asad yace, "Ban tari numfashin mai martaba ba, amma ina so a duba lamarin wallahi bazan iya zama da ita ba, kuma ni na riga na yanke hukunci gashi na sanar da mahaifina bana tunanin zan iya yin wani hukuncin da ba wannan ba, ina neman afuwar ka akan wannan bazan iya ba wallahi" ya fad'a yana kallon k'asa zuciyar sa na rawa in ya tuna abinda ya faru sai yaji jikin sa kamar ana kwashe masa kuzari sa gabad'aya komai sai ya tsaya masa cak.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*083.*

? ? ? ?? Mai martaba kallon sa yake yi ganin yadda jikin sa yayi sanyi ya sauke numfashi yasan daman abu ne mai wahala amma ya za'ayi dole ayi wani abun dan b'oye wani abun. Yace, "Asad bank'i ta taka ba, amma yanzu ya kenan in mutanen gari suka ji ka rabu da matar ka?." Asad yace, "Allah ya taimaki Abba ni a yanzu ba matata bace, tasan na saketa na fad'a mata baki da baki tun lokacin da take kirana da Aliyu."

Mai martaba yace, "Sai kace min ka gama yanke hukunci ma tuni. Mahaifinta yazo d'azu bayan jana'iza da alama bai san duk abinda yake faruwa ba amma kawun ka yayi masa bayanin komai tashin hankali ya bayyana a tare dashi amma an sanar dashi ya kwantar da hankalin sa komai zaizo da sauk'i, kai kuma gashi yanzu ka lalata komai Asad."

Shiru yayi ya sunkuyar da kansa k'asa Mai martaba ya kuma cewa, "Ya kake so ayi yanzu?."
"Abba in ana so na d'auki abinda zata haifa zan d'auka har abada bazai san bani na haife shi ba, bayan wannan Abba bana tunanin akwai abinda zan iya."
"Yanzu kenan kana so kace ta fita daga cikin gidan nan matsayin ba matar ka ba?, ka tuna fa kowa kallon matar ka yake mata in akace yau bata nan me mutane zasu d'auka? Shugaba mai sakin aure ko kuma me?."

Asad yayi shiru ya kasa bashi amsa Mai martaba yace, "Mahaifinta ya sanar dani tayi haihuwar wata bakwai sabida rud'anin da ta shiga, kaga kenan yanzu auren ku ya k'are; koda yake daman babu idda a kanta." Shiru Asad yayi ya kasa magana kansa yana k'asa.

Mai martaba yace, "Yanzu ya za'ayi da ita Jiddan da mahaifiyar ta?, tayi yun?urin kashe mahaifiyar ka ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, ita kuma Jiddan taso kashe ka kuma taci amana ta kuma aikata alfasha wanda inda za'a yi mata hukuncin addini da za'a jefe tane har sai ranta ya bar jikin ta." Asad ya gyara zama yace, "A ganina bazata amince da hukuncin addini ba, ni a shawarata kawai a k'yaleta yadda Allah yaji da Uncle Abban Suhail suma zai ji dasu."

Abba ya d'aga kai yace, "Hydar fa?." Asad ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya d'ago idon sa ya kalli hasken da yake falon ya sake mayar da kansa k'asa yace, "Ina son Hydar Abba, kaf cikin y'an uwana bani da wanda nake so nake ji dashi kamar Hydar. Zuciyata tana min ciwo in na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login