Showing 21001 words to 24000 words out of 216282 words

Chapter 8 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

akan keken suka shiga ciki har lokacin kallon asibitin take ganin sa hawa-hawa. Labarawa, turawa, Chinese, Japanese sune kawai suke kai kawo a cikin reception na asibitin wanda kallon sa ya kusa saka Rauda rud'ewa sabida ba komai ta gani a zahiri ba.

Wajan eveletor suka k'arasa taga ya danna ya bud'e suka shiga ya kulle ya danna hawa na biyu ba jimawa suka je ya sake bud'ewa suka fita yana gaba tana bin sa a baya. A bakin wani office suka tsaya ya danna door bell d'in jiki ta bada sauti daga ciki suka ji an bada ikon shigowa ya tura k'ofar ya shiga ya bud'e mata ta shigo sannan ya rufe.

Balaraben likitan yana ganin sa ya mik'e tsaye da mamaki da farin ciki ya tawo ya rungume shi yana murmushi shima Asad d'in murmushin yayi suka gaisa likitan cikin harshen larabci yace, "Sheikh Asad daman da gaske zaka zo d'in?." Asad ya murmusa ya shafa gashin fuskar sa cikin larabci shima yace, "gani kana gani." Likitan yace, "gaskiya nayi farin cikin ganin ka sosai dan uwana, zauna mana" ya fad'a yana nuna masa wajan zama da farin ciki a fuskar sa shima haka.

Asad ya zauna ya saci kallon Rauda da gefen ido yaga duk ta rud'e sai ya d'auke kansa daga kallon ta ya kalli Dr Asif yaga ya tashi ya bud'e fridge yana d'auko ruwa da lemo da kayan motsa baki ya dawo ya ajjiyewa Asad a gaban sa yana ta murmushi har lokacin shi kuma Asad fuskar sa dai kadaran kadahan, "Bismillah" ya furta yana kallon Asad bai yi magana ba ya d'aga masa kai kawai sai yayi dariya yace, "Har yanzu kana nan da rashin son maganar ka kenan?." Murmushi kawai yayi bai amsa ba.

Asad ya d'auki dabino d'aya yaci dan kar yaji babu dad'i ya bashi abu bai ci ba sannan ya nuna masa Rauda dake zaune yace, "ga patient d'in da mukayi magana dakai." Asif ya kalle ta ya kalle shi yace, "Ya sunan ta?." Asad ya kalle ta kana tace, "Rauda." Sai da gaban ta ya fad'i rana ta biyu kenan da taji ya ambaci sunan ta sai taji wani iri musamman yadda yake fitar da harafin R d'in kamar a bakin sa aka halicci harafin, ta kalli likitan dan ba larabci take ji ba ta dai d'an fahimtar abu kad'an irin dai na islamiyya dake koyawa.

Dr Asif ya jawo computer gaban sa yana danne-danne kafin ya juyo ya kalli Asad yace, "bata iya tafiya ne?." Asad ya d'aga masa kai alamun eh ya d'aga kai ya danna wani abu a kusa dashi sai ga nurses mata guda biyu kyawawa sun shigo cikin uniform d'in su.

Da harshen su yayi musu bayani da aje da Rauda ayi bincike k'afar ta, ba musu suka kalli Rauda d'aya daga ciki tace, "Muje" cikin harshen larabci ta fad'a kuma kalmar daman ba wani wahala ne da ita ba Rauda taji me tace sai ta danna madannin tafiya suka fita suna rik'e da keken ya bisu da kallo a zuciyar sa yana tunanin da wanne harshe zata yi musu magana in sun tambaye ta?.

Kawai sai yaji bai gamsu ba ya kalli Dr Asif yace, "Zan bi bayan su" yana fad'a ya mik'e Dr Asif d'in ma ya biyo shi suka fito suka bi bayan su. D'aki aka shiga da ita babba mai d'auke da injina da na'uroro kala-kala suka kunna wata na'ura suka k'araso kusa da Rauda ita duk tsoro take ji ganin injinan harrrrr a idanun ta sai taji ta tsorata. Kan gado suka nuna mata alamun ta kwanta sai taji bazata iya ba sabida tsoron da take ciki ganin hakan ya k'araso kusa da ita ya kalli fuskar ta da take a kwab'e kamar zatayi kuka yace, "Relax."

Ya furta a hankali yana rik'o hannun ta ya jingina ta da jikin sa ta runtse idanun ta suka matso da gadon ya kwantar da ita ta rik'e hannun sa gam idanun ta a rufe, k'arar na'urar taji kusa da ita taji an tattare rigar jikin ta an saka na'urar a k'afar ta nan take kasusuwan k'afar ta suka bayyana a jikin wani babban screen dake gaban gadon.

Dr Asif yana kalla suna juya na'urar tana nuno ko ina na k'afar ra har inda matsalar take nan take ya gani ya bada umarnin a cire ta daga ciki har lokacin hannun ta na rik'e dana Asad, kashewa sukayi Dr Asif ya kalle ta yayi murmushi cikin larabci yake ce masa, "Tana da tsoro, amma tana da kyau irin na y'an Nigeria." Asad bai amsa ba ya share shi ya kuma cewa, "y'ar uwar kace? Kuma bakwa kama." Nan ma ya share shi baiyi magana ba ganin hakan sai Asif yaja bakin sa yayi shiru.

Dr Asif ya kuma cewa, "In kun shirya za'a yi mata aikin yanzu ba wani mai wahala bane." Asad ya kalli Rauda da take kwance har lokacin ya sunkuya da kansa daidai kunnen ta yace, "za'a yi aikin yanzu, kar kiji tsoro" abinda yace kenan ya d'ago ya kalli Dr Asif ya d'aga masa kai alamun ayi kawai.

Dr Asif ya kalli nurses d'in ya fad'a musu ayi shirin aiki shima ya fita, uniform suka ajjiyewa Rauda da hula da talamin da duk wanda zai kwanta asibitin yake amfani dashi suka fita suka bata waje dan ta shirya. Jin babu motsi sai ta bud'e idon ta ta kalle shi taga ita yake kallo yayi mata nunu da kayan da ido ta tashi zaune ya saki hannun ta ya fita.

Sun jima basu dawo ba lokacin da suka dawo ta cire kayan ta saka wanda suka bata aka ja gadon zuwa d'akin tiyata yana bin su a baya har cikin d'akin, kallon sa da yaga tana yi sai ya k'arasa kusa da ita ya rik'e hannun ta gam yace, "Kar kiji tsoro." sai ta kulle idon ta akayi mata allura daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.

Cikin lokaci kad'an aka kammala aikin aka fito da ita zuwa d'akin da zata huta har lokacin bacci take a lokacin agogon Cairo karfe hud'u na yamma. Sai da yaga an fito da ita ta kwanta sannan ya samu damar yiwa mahaifinta message ya tura domin bazai iya doguwar magana ba ya fita zuwa masallaci yayi sallah.

Bata san adadin lokacin da ta d'auka a kwance ba ita dai taga ta bud'e idanun tane ta ganta a kwance a kan gado haske ko ga ina kuma babu kowa a d'akin sai k'arar a.c kad'an da yake tashi a ciki. "Sannu Rauda" aka fad'a daga gefen ta ana murmushi ana kallon ta. Gaban Rauda ya fad'i idanun ta suka had'u dana wanda yake mata magana ta ganshi fari tas dashi kana ganin sa kaga balarabe amma taji yana yi mata hausa duk sai ta gigice tana jan ayatul kursiyu a zuciyar ta.

A yanayin fuskar ta ya hango tsoro a ciki sai yayi murmushi yace, "Karki tsorata suna na Dr Khalifa ni bahaushe ne kamar ki." Duk da ta d'an ji dad'i amma bata nuna ba dan ba amincewa tayi da abinda yace ba kawai ita kallon aljani take masa. Murmushi yayi yace, "in kika ji tsoro kina kyau." Asad ta hango ya shigo yana amsa waya ya canja kaya zuwa riga da wando jajaye nasu kauri da tsaho dan rigar irin mai high neck ce kana ganin su kaga kayan sanyi.

Dr Khalifa ya kalli Asad yace, "Asad da alama wannan sister naka kallon aljani take min dan taji ina hausa" ya fad'a yana murmushi ya k'arasa inda drip stand yake ruwan da yake shiga jikin ta ya tsayar dashi kana yace, "But tana dakyau." Asad baice komai ba ya k'arasa kusa da ita yana kallon k'afar da take cikin wani abu kamar akwati an d'aure ta da farin bandage a mike sanb'al.
"Kina jin ciwo a k'afar taki?" Dr ya fad'a yana kallon ta.

Kai ta girgiza kafin tace, "Akwai ciwon amma ba sosai ba."
"Zai daina shima nan da anjima kad'an zaki daina jin komai." Kai ta d'aga kawai ya juya ya kalli Asad kafin yayi magana aka bud'e k'ofar aka shigo. Kyakykyawar matashiyar budurwa ce d'auke da rigar likitoci ta yafa karamin mayafi a kanta tayi kyau sosai duk da kana kallon ta kasan ba balarabiya bace amma ta had'a jini dasu.

Asad ta kalla cikin mamaki tace, "dana ganka d'azu ban d'auka kaine ba shine nazo da kaina. Ohh Aliyu da gaske kaine?." Kallon ta yake yana so ya tuna inda ya santa amma ya kasa yadai san ya Santa a wani wajan ganin hakan sai ta kama k'ugu tace, "You forgot me right?." Nan ma bai amsa ba sai kallon ta da yake yi tace, "You forgot your school friend Muheeba?." Shiru ya kuma yi alamun yaso dai ya gane ganin hakan sai ta hard'e hannu a k'irji tana kallon sa da wani irin murmushi a fuskar ta kafin tace, "Muheebba!" Ta maimaita a hankali.

Wara ido yayi sai kuma ya tab'e baki tunawa da ya san fuskar ta a wajan Aliyu lokacin da suna makaranta yace, "bani bane." Muhibba tace, "Lallai prince." Khalifa da yake jin su yace, "Dr wa kike nema ne ke?." Tace, "shine fa Prince Aliyu bin Nasir." Khalifa yayi murmushi yace, "Bashi bane wannan triples d'in Aliyu ne Asad."
Wara idanu tayi cikin mamaki tace, "like seriously?."
"Sure."
Dawo da kallon ta tayi ga Asad tana binsa da kallo cikin mamaki da al'ajabi tace, "I see, kasan sai yanzu na gane Khalifa? Cos inda Aliyu ne da yanzu ya bani welcome hug, Wow Allah mai iko babu inda ya bar Aliyu."

Khalifa bai bata amsa ba ta mik'a masa hannu tace, "nice to meet u prince Asad." Kallon hannun nata yayi sannan ya kalle ta sai ya d'auke kai a iya lab'ban sa ya amsa da, "Thanks" yana fad'ar hakan yayo gaban wajan gadon da take kwance ba tare da ya sake kallon ta ba dan Allah ya sani ya tsani mace mara kamun kai da nuna zaqewa a kan namiji da sunan wayewa.


Muhibba kam kallon sa take da mamaki bata tab'a ganin kama irin ta Aliyu da Asad ba duk da Aliyu ya fishi kamar faran-faran musamman ga mata dan da shine yadda suka had'u d'in?nan sai yayi hugging d'in ta amma babu ta inda ya barshi.

Murmushi tayi domin ya burge ta sosai ajin sa ya burge ta matuk'a musamman lokacin da take masa magana yake d'aga girar sa sama yana kallon ta ya k'ayatar da ita har taji bata gaji da kallon sa ba. Khalifa ya kalle shi yace, "Deaf yana da kyau tayi sallah." Asad ya d'aga kansa ya kalle ta ya kalli agogon hannun sa lokacin asuba gab da take da yi amma bai ce komai ba.

Muhibba tace, "she's your sister?" Ta fad'a tana kallon Asad ya runtse ido ya bud'e alamun ta dame shi baya son yawan magana amma ta kasa ganewa kafin ya bata amsa Khalifa yace, "Yeah, sister shi ce."
"Woww! Amma basa kama, ya akayi kika bari yayan ki ya fiki kyau haka?. Kalle shi kamar arab in ya shiga cikin larabawan asibitin nan babu wanda zai gane shi" ta fad'a tana kallon sa da murmushi a fuskar ta.

Rauda bata kula ta ba dan haushi ta bata ta lura irin matan nan ne masu shigewa maza ta saci kallon sa taga shima ba ita yake kallo ba, kusa da Khalifa ta k'arasa tace, "Baya magana ne kamar Brother d'insa? Naji kana ce masa deaf kuma naji yayi magana sau d'aya."
"Baya son magana ko kad'an kinji wannan maganar da yayi miki babu lallai ya kuma yi miki wata har ki bar nan gwara ma kiyi shiru" ya fad'a mata a hankali a kunnen ta sai taji ya sake burge ta ta wara idanu tace, "Woww! He impressed me."

Kallon Asad tayi tace, "Lemme help my sister tayi sallah before asuba" ta fad'a tana k'arasowa inda Rauda take tana kallon sa har lokacin. Da hannu Asad ya dakatar da ita alamun ta barshi ya kalli Khalifa shima shi yake kallo kafin Khalifa yace, "Kana kallona kasan ba ko yaushe nake gane me kallon ka yake nufi ba, ka yi magana abeg." Baice komai ba sai ya bar wajan ya fita daga d'akin jim kad'an sai gashi yazo da nurses d'in da alhakin kula da ita yake a wuyan su suna shigowa shi kuma ya juya ya fita.

Dole suma suka fito dan su bar su suyi aikin su suka ganshi zaune akan kujera yana danna wayar sa a nutse bai damu da kowa ana wajan ba, yadda larabawa suke zirga-zirga sai ka d'auka shima balaraben ne hutawa yake yi sabida yadda ya dace da zama balaraben musamman shigar jikin sa da ta sake haska fatar sa. Muhibba ta k'arasa kusa dashi ta zauna a gefen sa tace, "Aliyu abokina ne a school yana ina yanzu? Ko zan iya samun number shi?." In kujerar da suke kai tayi magana tabbas shima yayi bai kalle ta ba wayar kawai yake dannawa.

Zata kuma magana kawai ya mik'e ya bar mata wajan ta bishi da kallo cikin tsantsar burgewa har ya b'acewa ganin ta tayi murmushi tace, "I like his acting" ta fad'a tana murmushi sosai dan ba k'aramin burge ta yayi ba.

A b'angaren Rauda sun bata ruwa tayi alwala a inda take sun nuna mata yadda zatayi sallah tayi duka wanda ake binta ta idar suka kawo mata tea tasha, yadda suke kula da ita baza kace mara lafiya bace abin ya burge ta duk da ta d'auka matsayin Asad shine ya saka suke mata haka dan taga duk sun sanshi bata san haka tsarin asibiti yake hatta na Nigeria kula da mara lafiya a wuyan nurses yake.

Bata jima sosai ba akayi sallar asuba tayi sallah a zaune kamar d'azu bayan ta idar ta kalli gefen ta taga wayar ta ta d'auka ta shiga Islamic app ta fara karatu kamar ko yaushe. Bayan ta gama ta shiga wajan hotunan wayar tana kallon haukan su Khalil a wayar ta tana murmushi tana jin kewar su a zuciyar ta sosai.? Tana cikin farin cikin kallon y'an uwanta ya shigo ya canja kaya cikin suit fara tas tayi masa kyau sosai ya k'araso ya zauna a gefen ta yana kallon fuskar ta da take ta murmushi har lokacin ta kalle shi tace, "Ina kwana."

Kafin yayi magana tace, "Da sauk'i. " Da mamaki yake kallon ta ta kalle shi tace, "nasan zaka ce ya jikina ne shiyasa na hutar da kai nace da sauk'i." Kyakykyawan murmushi yayi wanda ta jiyo sautin sa a inda take ta sake kallon sa da mamakin abinda ya bashi dariya haka shi kuma yadda tayi saurin amsa abinda bai tambaya ba shine ya bashi dariya wato tasan abinda zai tambaya kenan, sai ta sake burge shi sosai da alama dai tambayar bata mata dad'i shiyasa tayi saurin tare shi.

"Ya kika tashi?" Ya furta in slow voice yana binta da fararen idanun sa masu d'auke da boyayyiyar k'aunar ta wacce shi kad'ai yasan da ita a zuciyar sa. D'ago kai tayi ta kalle shi cikin mamaki suka had'a ido har lokacin fuskar sa da murmushi a kai sai ta sauke kai k'asa tace, "lafiya lau." Murza yatsun hannun sa yayi suka bada sauti ta d'ago ta kalle shi ya nuna mata k'afar ta alamun ya take ji, "babu ciwo" ta fad'a a nutse tana kafe shi da nata idanun a son ranta sai dai ya d'auke nasa ita baza ta d'auke ba amma suna had'a ido sai ta sauke nata k'asa jin wani abu yana shigar ta.

Waya ya d'auko daga aljihun sa yana dannawa ba jimawa ya mik'o mata ta karb'a a hankali dan tsoro take kar wayar ta sub'uce a hannun ta tayi masa asara gata da santsi, fuskar Baba taga ya bayyana akan screen d'in tace, "Lah Baba kaine?." Daga can b'angaren yace, "Nine Rauda, ya jikin naki ance anyi miki aikin?."
Farin ciki ya bayyana a kan fuskar ta tace, "Babu ciwo Baba kamar ba'a yi min komai ba. Ina kwana."
"Lafiya lau Rauda ya zaman misra?."
"Lafiya lau, Ina Ummana?."
"Gata ku gaisa."

Fuskar Umma ta bayyana sanye da hijjabi ta sake fad'ad'a fara'ar ta tace, "Umma na ina kwana." Daga can b'angaren itama da fara'a a tare da ita tace, "lafiya lau Rauda, ya jikin naki?ance har anyi aikin k'afar taki."
"Umma babu ciwo kamar ba'a yi min komai ba. Umma kinga yadda suke kula dani kamar ba mara lafiya ba kamar wata matar shugaban k'asa?, ga asibitin mai kyau Umma kamar ba'a duniya kake ba."
Umma tayi dariya tace, "kedai shirman ki yawa gare shi Rauda, ya mijin naki?."
"Mijina kuma? Au ashe fa ina da miji wallah8 mantawa nake Umma. Yana nan yadda yake Umma ko magana fa baya yi sai yaga dama daga ya jiki sai sannu shikenan, wani lokacin kamar na shak'o wuyan sa haka nake ji, yana da kayan haushi ni mantawa nake miji nane badan kin fad'a ba."

"Lallai baki da hankali Rauda; duk fad'an da nayi miki bai shiga kunnen ki ba." Rauda ta share zancen tace, "Umma ina Ummulkhairi ina Khalil dasu Rahma? Wai Umma yaushe ma Baba yayi babar waya nidai nasan ba'a video call da k'aramar waya sai babba kuma dai nasan Baba bazai fitar da kud'i ya siya ba." Umma tayi dariya tace, "Mijin kine ya bashi kafin ku tafi sabida mu dinga ganin ki kema kina ganin mu."

Rauda tace, "Allah sarki angode Allah ya saka masa da alkhairi."
"Amin. Shiyasa nace ki dinga masa biyayya banda rashin kunya Rauda."
Sai kuma tayi dariya sosai tace, "Daman dai nasan wallahi duk wahala Baba bazai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login