Showing 78001 words to 81000 words out of 216282 words

Chapter 27 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

taji yace, "Na ganta."

Daga can b'angaren Mama tace, "Yauwa nayi mamaki da kace bata k'araso ba, dan Allah Asad karka bani kunya kaga dai itace zab'ina abinda nake so kuma kana so kayi k'okarin ganin ka sauke hakkin ta da yake kanka, kar ka duba baka sonta ka duba ni ka kuma duba hakki ka tuna kai yanzu babban mutum ne lokacin da zaka fara tara y'ay'a yayi.

? ?? Da hannu ya nuna mata hanya ta rab'a shi ta shiga tana kallon sa da murmushi, baima kula tana murmushi ba tunanin sa ya tafi ga ciwon da ya same shi a Egypt wanda tun lokacin har kawo yau bazai iya d'aukar nauyin ko wacce mace ba bai kuma mayar da hankali sosai akan neman magani ba tunda suka baro can gashi ba jimawa yayi ba aka yi wannan auren, jin bai baice komai ba Mama ta kuma cewa, "Ina fatan babu wata matsalar dai ko?."
"Babu" ya furta a kasalance domin bazai iya furta mata abinda yake damun sa ba gwara yayi shiru da bakin sa kawai tunda mai martaba baya nan ya yiwa kansa magani a hankali.

? ? ?? "Ka tabbatar babu matsala Asad?." Ya sauke numfashi yace, "Babu Mama." Yana jin sautin murmushin ta tace, "Allah ya tashe mu lafiya, karka manta kasha maganin dana baka na tsari ne suna da mahimmaci sosai domin Abie kafin ya rasu duka su yake sha."
"In sha Allah. A huta lafiya" daga haka ta datse kiran ya sauke wayar daga kunnen sa yana kallon sa.

? ? ?? Jimm yayi yana kallon k'aton mudubin da yake facing d'insa ya sauke numfashi ya juyo sai ya tsaya cak yana binta da kallon mamaki, ta cire alkyabbar ta ajjiye a gefe daga ita sai rigar bacci bak'a wacce iyakarta guiwa tabi jikinta sosai kana ganin komai na jikinta. D'auke idanun sa yayi daga kanta yaja k'aramin tsaki Allah ya sani ya tsani mace mara kamun kai irin ta in ya tuno yadda suke cafkewa da Aliyu sai yaji takaici ya cika masa zuciyar sa.

Wajan madubi ya nufa ya ajjiye wayar sa ya k'araso inda take ya wuce ta ya shiga band'aki khamshin turaren ta gabad'aya ta dagula masa lissafi, tsigar jikin sa tana tashi kansa na sarawa zuciyar sa na bugawa sabida d'akin da yake ji a cikin ta. Bai jima ba ya fito fuskar sa da ruwa da alama alwala yayi ya kalle ta sai yaga tana murmushi tana kallon sa ya sake kallon ta shi abinda yake nufi taje tayi alwala ita kuma ta d'auka burge shi tayi.

"Barka da dare" ta fad'a cikin murya mai sanyi. Wuce ta yayi jin tama raina masa hankali tun d'azu bata gaishe shi ba sai yanzu zata wani ce barka da dare, a dak'ile yace, "Barka" daga nan yaja bakin sa yayi shiru bai kuma ce mata komai ba. Ganin zata b'ata masa lokaci baiyi sallar i'sha ba ya saka shi tsayawa a kan sallaya yana niyar tayar da iqama sai yaji tace, "Bara nayi alwala nazo muyi banyi sallar i'sha ba."

Tana fad'a ta shiga band'akin ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba badan mahimmacin Jam'i ba babu abinda zai saka ya tsaya ta, jim kad'an ta fito ta saka alkyabbar da ta cire mayafin da ta yafa ta kuma yafawa suka tayar da sallah. Sun jima a tsaye yana karatu a bayyane tun tana daurewa har ta k'osa ta fara yamutsa fuska, dak'yar ta kai i'sha d'in nan kafin ya sake mik'ewa dan ta burge shi ta tashi itama taga sunyi raka'a biyu amma ita ba'a jima sosai ba yayi sallama.

Shiru babu mai magana ita binsa take da kallo kawai dan Allah ya sani tana sonsa yana kuma burge ta sosai musamman bakin sa tana ji kamar ta kamo shi ta tsotse bakin sa. kallon yaji yayi yawa a jikin sa ya d'ago ya kalle ta sai ya nuna mata leda da hannun sa kafin ya mik'e tsam ya fita ya bar mata d'akin. Jawo ledar tayi ta bud'e sai taja tsaki ganin abinda yake cikita ture ita ba kaza take son ci ba shi take buk'ata kawai ba wani abun ba.

? ? ?? Gajiya tayi da zaman ta tashi ta zare alkyabbar ta zauna a gefen gado tana jiran ya shigo amma shiru babu alamun sa ta kasa daurewa ta tashi ta fita ta bud'e d'aya k'ofar ta ganshi a zaune yana duba littafi, k'arasawa tayi kusa dashi ta zura hannayen ta a kafad'ar sa cikin shagwab'a tace, "kazo mu kwanta." Rutse ido yayi ya cize bakin sa ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani iri a jikin sa.

Dumin lips d'inta yaji a cheek d'insa a daidai kunnen sa tace, "Come on my king." Bai bari ta fahimci ya shiga yanayi mara dad'i ba ya d'auke hannun ta daga kafad'ar ta ta matso kusa dashi tace, "My king pls." Shiru yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya cigaba da duba littafin hannun sa turaren jikin ta gabad'aya ya hautsina masa lissafi.
"I'm coming" ya furta cikin muryar sa mai sanyi ba tare da ya kalle ta ba, bubbuga k'afa ta fara tana turo baki gaba tace, "Please ka tashi muje tare tsoro nake ji na kwanta ni kad'ai."

? ? ?? Shiru yayi ya cigaba da abinda yake yi ganin yayi mata banza ya saka tace, "zanje ka tawo yanzu dan Allah." Bai bata amsa ba ta fita ya kifa kansa a kan littafin yana jan numfashi dak'yar yana k'ok'arin daidaita kansa.

Bai jima a haka ba ya d'ago kansa ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya fita daga d'akin. Kallon d'akin da take yake yi yana tunani a zuciyar sa domin bai san me zai mata ba in ya shiga, ya fahimci abinda take nema gashi shi kuma bashi da abinda take so d'in babu amfanin shiga hakan ya saka shi sauka k'asa ba tare da ya shiga ba.
?? Jidda tunda taji sa shiru kawai taja tsaki ranta a b'ace ta kwanta zuciyar ta na rawa sabida b'acin rai a haka bacci ya d'auke ta.

*&&&*
? ? ? ?? Aliyu yana tsaye yana kurb'ar lemo a glass cup yana kallon taga wayar? sa tayi k'ara ya duba ganin mai kiran ya saka shi ya d'auka daga can b'angaren akace, "Ranka ya dad'e an aiwatar da komai kamar yadda kace, na zuba maganin kuma tabbas ya tsallaka a d'azu."
Aliyu yace, "zaka ga alert yanzu, ka tuna in naji maganar a bakin wani....." bai k'arasa ba mutumin yace, "baza ka barni ba."
"Good" yana fad'ar ya yanke wayar yana murmushi.

? ? ? "Asad lokaci yazo, lokacin ka ya fara nawa kuma ya kusa fara aiki, nan bada jimawa ba labari zai sha banban da wanda aka saba ji a ko yaushe. Lokaci Asad" ya fad'a yana murmushi ya kurb'i lemon nasa. Wayar sace tayi k'ara ya duba ganin mai kiran ya saka shi ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Allah yaja da ran yarima akwai matsala a binciken mu na d'azu na kira ka ban samu ba sai yanzu."

? ? ?? "Meye matsalar?."
"Yarinyar da Asad ya saki akwai yuwar dawowar ta masarauta kuma matuk'ar ta dawo komai ya lalace."
"Ta yaya zata dawo?."
"Shine abinda ban sani ba, amma binciken mu ya tabbatar min da akwai yuwar dawowar ta, cikin kashi d'ari akwai tabbacin kashi saba'in na dawowar ta dole a d'auki mataki."

Aliyu yace, "Me kayi game da hakan?."
Yace, "na fara aikin da zan saka ya manta da ita da dangin ta baki d'aya na sanar dakai ne sabida gudun matsala in akwai abinda zakayi a naka b'angaren sai a had'a k'arfi da k'arfe." Aliyu yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "ayi abinda ya dace nima zan san abinda zanyi" ya fad'a yana datse kiran wayar yana kallon tagar d'akin cikin sabon tunani.

Murmushi yayi samo mafitar da yayi a zuciyar sa ya cize baki yana girgiza kai cikin gamsuwa da shawarar da zuciyar sa ta bashi yace, "Asaddddd!" Sai ya yi y'ar k'aramar dariya yana sake taune lab'b'an sa zuciyar sa cike da mugayen abubuwa wanda ya tsara domin kuwa kashe Rauda shine abinda ya fara zuwa zuciyar sa.



*Akwai kura.*


FitattuBiyar
Nana Haleema.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*050.*

? ? ? ? ?? A zaune take a gefen gado ta shirya cikin doguwar riga ta lace tayi mata kyau sosai fuskar ta a cushe babu walwala hannun ta rik'e da waya a kunne tana magana, yadda take maganar zaka gane da wacce take yi daga can b'angaren akace, "Ke Jidda bana son k'arya fa." Jidda tace, "Wallahi Mum da gaske nake; ni tunani nake ma anya za'ayi abin arzuk'i da mutumin nan?."

Mum tace, "To meya faru haka? Nifa bana so a d'auki lokaci mai tsaho bai mayar dake cikakkiyar matar sa ba dan in hakan ta kasance akwai matsala wallahi."
"Hmmmm ban san meye ba."
"Amma mu bashi lokaci dan jiya ta wuce ai akwai yau ki san yadda zakayi ki tabbatar wani abun ya shiga tsakanin ki dashi kafin kwanaki bakwai d'in nan su wuce, suna da matuk'ar mahimmaci a zaman auren ki dashi bana so a samu matsala Jidda."

? ? ?? "To ni Mum ya zanyi? In bai neme ni bafa?." A fusace tace, "ke baza ki neme shi ba? Ai naga igiyoyi uku ne na auren sa a kanki kina da hakki a kansa, kin san kalar bak'ar wahalar da nasha kafin a samu azo wannan ranar?. Cikon burina kuma shine kasancewar ki cikakkiyar matar sa." Jidda tace, "Na fad'a miki abinda ya faru ma fa jiya Mum in ta sake faruwa fa me zan masa?."

Mum tayi shiru tana tunani kafin tace, "Barni dashi ni nasan abinda zanyi amma duk da haka kiyi iya bakin k'okarin ki wajan ganin an wuce wajan matsala ce bana so Jidda." Jidda tace, "Zanyi." Mum tace, "ya dai kamata. Ga Eman nan ta tawo zata kawo miki magunguna da zaki sha ki shafa kiyi wanka dasu, ko wanne an rubuta yadda za'ayi amfani dashi a jiki ki karanta dakyau nasan halin ki bakya nutsuwa wani lokacin akan wannan maganin ki nutsu ki karanta sai kiyi amfani dashi."

Jidda tace, "Mum duka maganin nan na meye kike d'ura min?." Mum tace, "baki da hankali, a kaf duniya ina d'aya daga cikin wanda suka san halin uwar mijin ki zatayi k'ok'arin ganin ta mallake ki a yanzu sai abinda tace zakiyi ni kuma badan haka na bari kika shiga gidan nan ba dan a nuna mata akwai iyakar ta ne, shiyasa nake dafa ki yadda ya kamata ta yadda komai zata turo miki bazai same ki ba." Jidda tace, "Ina so nima yadda yake fizge-fizgen nan yana k'in yi min magana nan gaba ya dawo sai abinda nace zaiyi."

Mum tace, "to ki nutsu kiyi abinda duk na fad'a miki, babar sa tana da mugun wayo sosai da iya bakinta zata mallake ki sai kinyi takatsantsan." Jidda tace, "Toh Mum zanyi." Bud'e k'ofa akayi hakan ya saka ta kalli wacce ta shigo tayi murmushi kafin suyi sallama da Mum ta kalle ta tace, "Suhaima." Itama kallon ta take tace, "Amarya."

? ? ?? Y'ar dariya Jidda tayi Suhaima tace, "In kin gama wayar Mama tana neman ki a apartment d'inta." Jidda tace, "na gama muje." Tare suka fito daga falon suka fito daga b'angaren ta jakadiyar ta tabi bayan ta da sauri duk inda ta gifta ana zubewa ana gaishe su hakan ya k'arawa Jidda girman kai take jin kamar ita kad'ai ce mace ma a duniya.

? ? ? ?? A falo suka samu Mama tana zaune tana waya da Hydar akan jikin mai martaba suna k'arasa shigowa ta kashe wayar tana bin Jidda da kallon k'urilla tana son ta gano wani abu a tare da ita, a k'asa Jidda ta zauna tace, "Barka da Safiya Mama." Mama tayi murmushi tace, "Barkan ki dai Daughter, ya kwanan bak'unta? Duk da gidan ba bak'on ki bane amma mijin naki bak'on kine." Murmushi tayi kad'an kana tace, "Alhamdulillah."
"To yayi kyau. Kinga masu yi miki hidima na tura miki ko?."
"Eh Mama, na gansu har mun gaisa."
"Sunyi miki ko a canja?."
"Sunyi Mama ba laifi." Mama bata ce komai ba tayi shiru ranta ya b'aci domin kuwa ta fahimci babu abinda ya had'a Jidda da Asad a daren jiya.

? ? ?? "Asslamu alaikum" Eman ta fad'a tana shigowa falon. Suka amsa a tare Eman ta k'araso ta zauna a k'asa ta gaida Mama ta amsa fuska a sake tana tambayar ta gajiyar biki. Ta kalli Jiddan tace, "ku koma can sai kuyi hirar." Daman haka suke so suka mik'e suka fita suka koma b'angaren Jiddan.
Suna fita ta d'auki waya ta kira number Asad amma bai d'auka ba sai ta share bata kuma kiran sa ba tana jiran ya kira ta taji dalilin da ya saka baiyi abinda tace masa ba.

? ?? Shi kuwa Asad da ciwon kai ya tashi mai zafi bayan yayi mafarki da Rauda tana kuka sosai tana bazata yafe masa ba tuna mafarkin shine yake sake yautsina masa lissafi hakan ya saka shi zama waje d'aya ba tare da yaje ko ina ba. Yana zaune yake jin k'arar wayar sa bai samu ya d'auka ba dan bata kusa dashi hakan ya saka bai san wanda yake kira ba gabad'aya baya tare da nutsuwar sa. Sake kiran wayar da akayi ya saka shi ya mik'e dakyar ya k'arasa inda wayar take ya d'auka nan yayi karo da sunan Uncle Mubarak yana yawo a kan screen d'in nasa.

? ? ? D'auka yayi ya k'arasa ya zauna a akan kujera ya saka a kunne yace, "Barka da safiya Uncle." Yace, "Barka da safiya Ranka ya dad'e." Asad ya yamutsa fuska shi sam baya so yaji suna yi masa irin haka dan yana sarki ai gaba suke dashi kuma iyayen sane bai kamata su dinga girmama shi haka ba duk sai yaji wani iri, wannan dalilin yana d'aya daga cikin abinda ya saka ya tsani mulki.

? ? ?? "Uncle zamu iya magana dakai?." Daga can b'angaren yace, "Ina sauraro."
"Uncle please ko zaka shigo cikin gida?."
"Umarni za'a bayar aikin na cikawa, gani nan ranka ya dad'e." Asad ya sauke wayar ya kalli missed call yaga sunan Mama ya danna kira ya saka a kunne ta d'auka da sallama kafin yace wani abun tace, "Asad akwai damuwar data hana ka kasancewa da matar ka jiya?."

_Hasbunallahu wani'imal wakil_ ya furta a zuciyar sa jin tambayar da take yi masa ya lumshe idanun sa ya bud'e baiyi magana ba tace, "Ba magana nake maka ba? Ko baka ji bane?."
"Tuba nake Mama."
"Fad'a min dalilin hakan."
"Maamaaaa" yaja sunan ta sosai sai kuma yayi shiru tace, "Amma kace min babu matsala a daren jiya ko? Wula?anci ne ya saka ka aikata hakan kome?."

"Kaina ciwo yake min Mama, Allah ya wuci zuciyar ki bada son raina ba nima." Numfashi ta sauke kafin tace, "Kasha maganin ciwon kan?." Kamar yana gaban ta ya d'aga kai kafin yace, "nasha."
"Allah ya k'ara lafiya. Amma ka tabbatar ka sauke nauyin da yake kanka bana son a sake samun matsala matuk'ar kana son na daina yi maka maganar nan. Ko akwai matsala?." Ya girgiza kai alamun a'a kafin yace, "Babu."
"To kayi abinda nace." Shiru yayi hakan ya saka tace, "Yaushe zaka yi zmaan fada ne?."
"Ranar Monday in Allah ya kaimu."
"To yayi, Allah ya kaimu. Akwai wanda ya kawo maka wani abun ne kaci?."

? ? ? ? ? "A'a." Tace, "to ka nutsu da ka san abinda hannun wanda zaka dinga ci, masu abincin ka na ware su daban na amince dasu baza su cutar dakai ba in kuma matar kace zata dinga yi maka fine." Shiru yayi bai amsa ba jin bai bata amsa ba sai ta tuna yace yana ciwon kai sai ta yanke wayar ya sauke wayar yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudu.

"Ya zanyi da Mama? Ya zanyi da yarinyar nan?" Ya furta a bayyane yana dafe kansa jijiyoyin kan suna harbawa. _Ina buk'atar neman magani_ ya furta a zuciyar sa yana shafa fuskar sa cikin rashin sanin abinda zaiyi.

? ? ? ? Wayar sace tayi k'ara ganin mai kiran sai ya d'auka tare da tashi ya fita daga d'akin ya sauka zuwa falon k'asa ya tarar da Uncle d'in sa a zaune yana ganin sa ya mik'e tsaye Asad ya k'araso ya zauna a akan kujera Uncle zai zauna a k'asa yace, "dan Allah Uncle ka zauna akan kujera, bana jin daWin hakan ko kad'an." Uncle ya zauna akan kujera yana murmushi yace, "to ya za'ayi ranka ya dad'e? Mu talakawan kane dole mu girmama ka yadda ya kamata. Baka ji karin maganar da ake cewa a banza wai talaka ya girmi mai mulki ba?."

Asad yace, "Uncle i need your help." Wambai yace, "wanne irin taimako?."
"Ka kasance a kusa dani ko yaushe Uncle, ban san komai na sarauta ba ina buk'atar ka a tare dani please" ya fad'a yana dafe kansa da suke harba masa sabida ciwo. Uncle yace, "bank'i taka ba zaki, amma ni bani da sha'awar cigaba da mulki gaskiya jira nake litinin tayi ranar da zaka fara zaman fada zanyi resining daga kujera ta zan bi d'an uwana naje naga yanayin jikin sa ko hankalina zai kwanta."

Asad kamar zaiyi kuka yace, "Nima ina so naje jikina yana bani akwai abinda yake faruwa a can d'in, dan na amince da Hydar ne da zan iya cewa bai mayar da hankali wajan nema masa lafiya ba, gangar jikina ne a nan Uncle amma zuciyata tana tare da Abba." Yayi shiru yana had'd'iye yawu na wani lokaci alamun ya gaji da magana Uncle yace, "samu nutsuwa sosai, Sannu."

? ? ? ? Ya cigaba da fad'in, "Ban san komai a nan ba Uncle in ka barni waye zai nuna min yadda abin yake? Ina so ka kasance a side d'ina always please." Uncle ya sauke numfashi yace, "Wannan aikin Uncle d'in kane Yahuza waziri kenan, shine yake da hakkin binka duk inda kake domin a sarautar ma daga sarki sai waziri."
"Ta ya zan iya tafiya dashi Uncle? Kai d'in dai please."
"Ai bazai yu bane Asad, na farko ni na ajjiye sarautar nan, na biyu kuma Yaya Yahuza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login