Showing 102001 words to 105000 words out of 216282 words

Chapter 35 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

su tsohuwar matar ka zaka saka aje a rushe musu gida? Duk kyautatawar da suka yi maka da abinda zaka saka musu kenan?."

Asad ya sauke numfashi kamar bazai yi magana ba ya kalle shi yace, "Ina matsayin shugaba a gare ka zaka zo kana yi min ihu a kaina dan kaga ina k'yale?." Sai ya cize baki ya girgiza kansa kana ya kuma cewa, "Bana son su, bana qaunar ahlin su yarinyar gabad'aya sai me?."
"Ka kyauta, kayi abinda kake so akwai limit d'in da za'a zo in akace kayi baza kayi ba." ya fad'a rai a b'ace yana kallon Asad da shima shi yake kallo cikin mamakin da ya kasa barin sa. Tashi Asad yayi ya shiga ciki ya bar Hydar a tsaye yana kallon sa har ya b'ace ya girgiza kai ya fito.

? ? ? ? ? B'angaren Baba lokacin da ya shiga gida a babban falo ya samu matan sa sai Rauda da Rahma k'ananun sun tafi makaranta yanayin da ya shiga ya saka suka bishi da kallo har ya zauna ya cire hular kansa ya dafe kansa, Umma tace, "Malam lafiya?." Baba yayi kalle su kafin yace, "Wanne gida kuke ganin zamu samu haya daga yau zuwa gobe?."? Rauda tace, "Kenan sai mun tashin? Nifa bazan bari hakan ta faru ba wallahi zan iya shiga gidan rediyo akan maganar nan."

Baba yace, "Dakata malama! Babu yadda zamuyi tashin ya zama dole dan yanzu ma daga gaban mai martaban nake amma nayi dana sanin zuwa tunda nake ban tab'a jin to tozarcin da ya tab'a min zuciya kamar wannan ba." Umma ta girgiza kai tace, "bai saurare ka ba kenan?." Baba yace, "Yace iya abinda zasu iya kenan, a tak'aice dai sai an rushe badan Anas bama ai da ba wannan zancen ake yi ba."

Rauda ta zabura ta mik'e tace, "Akan wanne dalili wai za'a rushe mana gida? Me muka aikata?. Wallahi bazai yu ba dan kawai a tozarta mu kawai sai ace za'a rushe gida? Daman can ai ba mu muka ce su gyara gidan haka ba; sune sukayi niya da ra'ayi, fili namu ne dan haka basu isa suce zasu rushe mana gida ba wallahi. Ina zuwa" ta fad'a tana niyar fita Baba yace, "Kee Rauda, dawo nan." Ba musu ta dawo ta zauna Baba ya kalle ta yace, "Kome ya faru nine na jawo Rauda, na nuna musu ina son dukiyar su a kanki shiyasa suke yi mana duk abinda suka ga dama, kar naji kinje gidan wata radio akan wannan ku fara had'a kayan su zamu tattara mu bar gidan kar a wula?anta mu."

? ? Rahma tace, "Amma Baba Anty Rauda tana da gaskiya banga dalilin....." baba ya dakatar da ita yace, "Rahma ya isa haka, kuyi abinda nace kawai" yana fad'a ya mik'e ya fita ya hau saman sa jikin sa a salub'e.

Rauda ta runtse idanun sa sabuwar tsanar Asad take ji tana zaga ko ina na jikinta fiye da wacce take ji a baya, da ace tana da dama sai tayi masa abinda bai tab'a tunani ba a yanzun ma kuma bazata fasa ba sai ta nuna masa daidai take dashi.

Umma tace, "Abin mamakin in dai ba shirin to tozarta mu akayi ba ina masarauta ina hurumin rushe gidajen mutane?." Inna tace, "Abinda na gani kenan, sai dai in anso a wula?anta mune kawai." Rahma tace, "In Allah ya amince baza mu wulak'anta ba sai dai yaga wula?anci akan sa." Rauda ta furzar da iska tana jin wani iri a jikinta gani take kamar ko meye ya faru itace ta jawo, jin dad'in tama dasu Walida suka tafi da bata san yadda zatayi ba kunya ba.

*&&*

? ? ? ? B'angaren Mama kwana d'aya ta rame sabida ciwon kan da ta kwana ta tashi dashi babban tashin hankalin ta kuma rashin kiran wayar da Mum bata yi mata ba har lokacin, duk ta damu hankalin ta ya tashi matuk'a kana kallon yanayin ta zaka fahimci hakan. Tana zaune dafe da kanta Suhaima na zaune a k'asan ta tana matsa mata k'afafun ta suka ji sallamar Mum tare da shigowa. Mama ta kalle ta Mum ta k'araso tana fad'in, "Tuba nake ranki ya dad'e,? Allah ya wuci zuciyar ki" ta fad'a tana k'araso ta zauna a kan carpet.

Mama ta saki kanta ta kalle ta tace, "tun jiya nake kiran ki baki d'auka ba kuma baki kira ni ba." Mum tace, "Shiyasa nace tuba nake ranki ya dad'e." Mama ta kalli Suhaima tace, "Jeki." Ba musu ta tashi ta basu waje Mama ta kalli Mum tace, "akwai abinda yake faruwa a gidan nan kin sani?."

Mum da alamun mamaki tace, "kamar me kenan ranki ya dad'e?."? Mama tayi tari kad'an kana tace, "Ki fad'a min gaskiya mai kuka yiwa Asad keda y'ar ki Jidda?." Mum ta zaro idanu tare da dafe k'irji tace, "kamar ya me muka yi masa ranki ya dad'e? Me kuwa muka yi masa?." Mama ta jingina da kujera tace, "Don't pretend like baki san komai baSadiya, kin san abinda nake nufi. Wanne malami kika samu ya mallake min d'ana haka?."

Mum ta rausayar da kai tace, "Haba ranki ya dad'e wanne irin mallaka ana zaune lafiya? Ni ban yiwa Asad komai ba." Mama tayi mata kallon kin raina min hankali sannan tace, "Sadiya kin san karrr nake kallon ki, ki fito ki fad'a min abinda kika yiwa Asad tun muna shaida juna nida ke."

Mum tayi murmushi ta gyara zama tace, "Irin malaman da kika samu suka mallake miki mijin ki da kuma y'ay'an ki, irin malaman da kika samu suka mayar da mijin ki tamkar gawa, irin malaman da kika samu aka mayar dake tauraruwa a wajan mijin ki wajan su nima naje." Gaban Mama yayi mugun fad'uwa tabi Mum da kallon mamaki tace, "Sadiya! Me kike cewa ne?."

Mum tayi dariya ta tashi daga kan carpet ta dawo kan kujera ta d'ora k'afa kan d'aya tana kad'awa tace, "Abinda kika ji shi nace. An fad'a miki zan bar Jidda ta shigo gidan nan ba tare da na shirya ba duk da nasan halin ki? Kar ki manta nice fa Sadiya wacce kike fad'awa zaki mallake masarautar nan ko shi sarkin sai abinda kika ce masa, to kin fad'a min wannan ni da yake doluwa ce mara wayo sai na zuba idanu y'ata ta zama bora duk da kasancewar ta matar sarki?. Keda kike uwar sa ace kece zaki san komai kafin ita? Impossible kema kin san bazai yuwa ba ai Rabi" ta fad'a cikin murmushi tana kallon Mama.

Mama ta kasa magana sai kallo da take binta dashi cikin tashin hankalim da ya bayyana a tare da ita tace, "Sadiya....!." Tayi farr da ido tace, "Na'am Rabi'atu. Kinyi saurin karaya bayan yanzu aka fara wasan ai, yadda kike tunanin mallake komai ni sai na riga ki mallakar sa, yadda kike juya kowa nima sai y'ata ta juya ki kina ji kina gani d'anki sai yafi k'arfin ganin ki."

Mama binta take kawai da kallo cikin mamaki ta kasa cewa komai dan gani take kamar ba ita ba Mum ganin hakan ya saka tace, "kina ta kallona kamar baki san komai ba, tunanin ki kin amince min na butulce miki ko...? Hhhhhhh Rabi'atu kenan. Kin manta kema mijin ki ya amince miki kuma kika butulce masa har kika kai shi ga kwanciya dashi da gawa banbancin su kawai numfashi ne?. Yanzu aka fara wasan Rabi'atu burin ki na zama cikakkiyar mai iko nima shine burina, y'ata ta zama sama da komai da kowa a gidan nan kuma hakan zata kasance" ta fad'a tana mik'ewa tana kallon Mama.

Mama ta kasa magana sai kallonta kawai da take yi baki a bud'e zuciyar ta na bugawa da gudu sabida tashin hankali kanta har rawa take ji yana yi sabida yadda yake mata mugun ciwo, Mum ta kalle ta tace, "na barki lafiya babar sarki kuma sirikar Jidda, kin kusa yin jika ma domin sirikar ki Jidda tana da juna biyu kin san kin samarwa mijinta maganin da ya samu lafiya yadda zai kasance da matar sa yadda ya kamata dan baki so tayi kuka. Magani yayi aiki kam domin zancen da akeyi yanzu har anyi ciki. Na barki lafiya Rabi na gode da kika yi iya k'okarin ki wajan ganin Jidda ta shigo gidan nan matsayin mata kuma matsayin sirikar ki, sauran aikin nawa ne" tana fad'a ta fita ta bar Mama a zaune kamar an dasa ta a wajan.

? ? ? ? Mama kawai ganin ta tayi a d'aki ba tare da tasan lokacin da taje ba ta zube a kan tiles kawai taji idanun ta na zubar da hawayen bak'in ciki wanda bata shirya musu ba. Tunanin fa daman haka duniya take wanda ka amincewa shine yake k'ok'arin ganin ya cutar dakai....? Me ta yiwa Sadiya haka da ta yanke mata wannan d'anyen hukuncin lokaci d'aya haka. Kuka take yi sosai iyakar iyawar ta kafin wani lokaci zazzaSi ya rufe ta ruf ga ciwon kai mai zafi da suka tarar mata.

Suhaima ce ta shigo ganin halin da take ciki bata yi k'asa a guiwa ba ta kira likita ba jimawa ya k'araso aka yi mata allura aka saka mata ruwa nan da nan bacci ya kwashe ta Suhaima na kusa da ita haka Hydar ma. Bayan tayi bacci likitan ya fita Hydar ya kalle Suhaima yace, "Meya same ta ne lokaci d'aya haka?." Suhaima tace, "Wallahi a nan kawai nazo na ganta a kwance a kan tiles, nasan dai na bar su tare da Mum ban san lokacin da Mum d'in ta tafi ba."

Hydar ya girgiza kai yace, "duk yadda akayi ciwon nata yana da alaqa da zuwan Mum, ki kula da ita ina zuwa" yana fad'a ya fita daga d'akin.

? ? ? ? Mama bata farka ba sai bayan sallar la'asar ta tashi dak'yar har lokacin kanta yana ciwo ta shiga band'aki tayi alwala ta fito tayi sallah bayan ta idar karo na farko cikin addu'ar da take yi taji bakin ta yana furta, "Allah ka bawa mijina lafiya, Allah ka tashi k'afadun sa shine kad'ai zaiyi iya maganin Jidda da babarta, Allah ka dube ni ka fitar dani daga halin da nake ciki" ta fad'a tana kuka sosai ta shafa addu'ar ta tashi da hijjabi a jikinta duk da kanta da yake ciwo hakan bai hanata nufar b'angaren mijin ta ba.

Babu wanda baiyi mamakin ganin ta a b'angaren mai martaba ba dan tunda ya dawo sau d'aya tak taje inda yake amma sai gata da yamma ta shiga ta samu Hydar da Uncle da sauran y'an uwan Abba su uku a ciki, ganinta ya saka suka fita aka barta daga ita sai shi idanun sa a bud'e alamun ba bacci yake ba ta k'arasa kujerar kusa dashi ta zauna ta rik'e hannun sa hawaye yana sakko mata tace, "Mijina sun raba ni da Asad d'ina, sun juyar masa da hankali daga gare ni Sadiya ta cuce ni ita da y'arta. Mamaki nake wai da gaske ne abinda yake faruwa ko mafarki nake? Yau nice aka mallake min yaron dana fi cin buri a kansa?."

Bai motsa ba sai kallonta da yake yi hakan ya saka tace, "Kaina ya kulle na rasa me zanyi ka taimake ni mijina kar kwakwalwa ta ta fashe. Daga jiya zuwa yau na shiga tashin hankali mara iyaka dan Allah ka taimake ni. Allah ya baka lafiya da gaggawa ka taimakawa d'ana ya dawo hankalin sa zasu iya yin komai ganin sun raba shi da duniyar gabad'aya." Kuka take yi sosai a kan hannun sa hawayen ta na tab'a fatar sa sai da tayi mai isar ta sannan ta kalle shi tace, "zan fara nema masa magani ka taya ni fatan Allah yasa na dace."

Ta jima tana kuka kafin ta saki hannun sa ta goge idanun ta ta fita jikinta a sanyaye ta koma b'angaren ta. Da Suhaima suka had'u da Hydar Suhaima tace, "Mama sannu." Kallon ta tayi tace, "Ina key d'in motar ki?." Suhaima tace, "yana d'aki."
"D'auko ki kaini unguwa."
Hydar yace, "Mama ina zaki je baki da lafiya fa?."
"Yanzu zamu dawo Hydar" ta fad'a dafe kanta da har lokacin yake ciwo.

Hydar yace, "to muje na kai ki." Mama tace, "Zamu je da Suhaima" tana fad'a Suhaima ta fito suka fita a babban falo hadiman ta zasu bita ta girgiza musu kai alamun su sha zaman su, ko jakadiya bata d'auka ba ita da Suhaima suka hau mota suka bar gida.

Sunyi tafiya mai nisa suka isa gidan malamin Mama ta bata umarnin ta tsaya ta fita ta shiga ciki tace ta jira ta a ciki, da jama'a sosai ta samu a gidan amma sanin ita wacece yana sallamar ta gaban sa ta shiga ya mik'e yana kawo gaisuwa, zama tayi ta kalle shi tace, "Ya jama'a?."
"Alhamdulillah ranki ya dad'e."
Ta sauke numfashi tace, "babar matsala ce ta kawo ni Malam." Ya gyara zmaa yace, "To ina sauraren ki."

Ta sauke numfashi tace, "dakai na amince nasan baka fitar min da sirrina kana kuma k'okari wajan yi min duk abinda nace ina so. Sadiya wacce muke zuwa tare ta butulce min sun juyarwa da mai martaba kansa gabad'aya baya jin maganar kowa sai tata data matar sa." Malam yace, "Ashsha! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, amma Sadiya tayi butulci ba kad'an ba. Tazo min da maganar kwanaki na amsa mata zanyi amma banyi ba sabida bazan iya cin amanar ki ba."

Mama tace, "Meyasa a lokacin baka sanar dani ba?."
"Kiyi hak'uri ranki ya dad'e naso fad'a miki sai kuma nayi tunanin kar na raba zumuncin ku."
"Yanzu gashi ai komai ya lalace" ta fad'a tana dafe kanta shi kuma ya shiga duba mata abinda yake faruwa. ya jima yana yi kafin ya girgiza kai yace, "Tsakani da Allah ranki ya dad'e bak'in tsafi aka yiwa Mai martaba ba asiri ba, an bashi yaci ya kuma sha anyi amfani da makusantan sa anyi abin cikin sirri ba tare da ya sani. Hak'ik'a tsafin da yake jikin sa ba k'arami bane ba dan zan iya cewa ba'a k'asar nan akayi shi ba."

Mama cikin firgici tace, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" ta fad'a tana dafe kanta da yake juyawa ya kuma cewa, "A halin yanzu yayi sakaci da rok'on Allah kamar baya shiyasa abin yake tasiri a tare dashi, bazan miki k'arya ba karya wannan tsafin na jikin sa ba abu bane mai sauk'i dole sai an had'a k'arfi da k'arfe wajan rok'on Allah, ma'ana sai an samu manyan malaman addini da dama an had'u ana yina addu'a sannan za'a samu nasara."

Mama kamar zata zubar da hawaye tace, "Kafin wannan babu abinda za'a iya yi?."
"Akwai ranki ya dad'e, zan bada ruwan rubutun da zai dinga sha amma sai dai a jira a rubuta a wanke a yanzu tunda ban san da zuwan ki ba in sha Allah zai rage wani abun tunda ayar Allah ce."
"Wanne malamai kake ganin za'a samu akan wannan?."

Ya sauke numfashi kana yace, "akwai wani babban malami sai dai ya tsufa sosai a cikin garin nan yake zaune Allah ya yi masa ilihamar iya karya tsafi ko asiri da ayoyin Allah da kuma maganin hausa." Mama ta gyara zama tace, "Ina zan ganshi?."
"Zan bincika ranki ya dad'e in yana nan zan sanar dake sai aje wajan sa."
"Ina jiran ka dan Allah kar kayi wasa."
"In sha Allah ranki ya dad'e. Bara na saka ayi rubutun" ya fad'a yana mik'ewa ya fita.
Ta jima sosai a gidan ta fito da jarkar rubutun tana jiri ta shiga motar Suhaima taja suka koma gida.

*&&&*

? ? ? Baba ne ya lek'a d'akin Umma ya ganta ita da Rauda yace, "kuzo munyi bak'o" yana fad'a ya juya ya fita Umma da Rauda suka fito ko wacce ta saka hijjabi zuwa k'aramin setroom d'in baban. Hydar suka gani a zaune shida Baba ganin su ya saka shi yin murmushi yace, "Mai ciwon k'afa jiki yayi kyau sosai."

D'aure fuska tayi ta zauna sai Umma ce tace, "Wallahi fa, jiki ya jima da warkewa ai." Ya kalli Umma yace, "barka da yamma." Umma tace, "ya mutanen gidan?."
"Alhamdulillah. Rauda ya gida?" Ya fad'a yana kallon ta. Fuska a d'aure tace, "Alhamdulillah."

Hydar ya numfasa yace, "kuyi hak'uri da abinda ya faru d'azu in sha Allah bazan bari hakan ta kasance ba, a tak'aice nayi maganin abun in sha Allah baza su sake zuwa gidan nan da niyar wani abun ba." Baba yace, "to ma sha Allah mun gode sosai. Amma dan Allah meye dalilin sa na sakawa ayi mana wannan wula?ancin?."

Hydar yace, "kuyi hak'uri kawai Baba, gabad'aya ya canja dana je na same shi akan maganar sai yace shi na bar maganar ya tsane ku ne baya son ku baya son dangin ku gabad'aya. Amma......" Rauda ta katse shi da fad'in,? "Amma me? Ka sanar dashi yadda ya tsane mu wallahil azim muma haka muka tsane shi bama son sa bama qaunar wani nasa. Har yana da bakin da zai ce ya tsane mu duk abinda aka yi mana mu bamu ce haka ba sai shii?. To ina so kayi masa albishir muma mun tsane shi dashi da dangin sa gabad'aya, dashi da babu ko nace dashi da banza duka d'aya suke a wajan mu, ka kuma tabbatar ka fad'a masa wallahi bai isa ya wula?anta ahlina na k'yale shi ba sai inda k'arfina ya k'are!" Ta fad'a a fusace tana kallon Hydar shima ita yake kallo da mamakin ta..........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*058.*

? ? ? ? ? Jin yadda tayi maganar a fusace Baba ya kalle ta yace, "Rauda meye haka ne wai?." Shiru tayi tana girgiza kai jin abinda Baba yace Hydar ya cize baki yace, "Babu wanda zaizo ya sake cewa zai rushe gidan nan mun gama magana dasu babu abinda zai faru" ya fad'a yana mik'ewa tsaye Baba ma ya mik'e suka fita tare suna cigaba da tattaunawa.
Da harara tabi bayan sa taja dogon tsaki tace, "Aikin banza aikin wofi." Umma tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta tashi ta shiga ciki ta bar Rauda a wajan tana faman cika da batsewa.

? ? ? ?? Baba ne ya dawo ya same ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login