Showing 54001 words to 57000 words out of 216282 words

Chapter 19 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc



"Jikin ki akwai zafi" ya furta yana kallonta. Jikinta har rawa yake a hankali tace, "Nasha magani." Shiru yayi baiyi magana ba sai kallon ta da yake yi yana jin kamar ya mayar da ita jikin sa ya huta da kewar ta da yake ji a ko wanne lokaci a zuciyar sa. In akace zai so mace kamar yadda yake sonta zai karyata faruwar hakan amma da yake Allah shine mai tsara komai sai gashi yana jin sonta fiye da komai a duniya. A kan kujerar ya ajjiye ta ya mik'e ya k'arasa inda butar shayi take ya kunna nan da nan tayi zafi ya had'a tea a kofi ya dawo inda take ya zauna ya mik'a mata yace, "take it."

Kunyar sa take ji ba kad'an ba hakan ya saka ta mik'a hannu zata karb'a shi ya d'auka ta rik'e sai ya saki sai kuwa ya d'an zuba a yatsan ta ta yarfe hannu shayin ya zube a wajan, "wayyo Allah" ta fad'a tana yarfe hannun ta yayi saurin karb'ar hannun nata ya saka yatsan a bakin sa kamar alawa. Shiru tayi tana kallon sa shima ita yake kallo kafin ya zame shi daga bakin sa ya kalli yatsan nata sai kuma ya saki hannun nata ya tashi ya shiga d'aki.

Jim kad'an ya dawo da wani cream dogo a hannun sa ya bud'e ya shafa a yatsan nata ya kalle ta yace, "Sannu, ko muje asibiti?." Kai ta d'aga zai kuma tashi ta rik'o shi tace, "Bana jin zan iya shan tea ka barshi kaima baka da lafiya." Bai fasa tashin ba ya k'arasa fridge ya d'auko lafiyayyen yogurt mara sanyi sosai ya k'araso kusa da ita ya zauna ya bud'e ya nufi bakin ta dashi. Ba yadda ta iya haka ta bud'e baki ya zuba mata ta shanye ya sake bata ta sake shanyewa a haka sai da yaga ta sha da d'an yawa sannan ya k'yale ta ya d'auko magani ya bata tasha ya sake tab'a wuyan ta yaji har lokacin da zafi.

"Jikin ki akwai zafi still, meyasa bakya son ganin Dr?."
"Ai naji sauk'i bana son fita ne yanzu."

Da kafad'ar sa ta tayar da kai shi kuma ya rik'e hannunta, babu mai magana a cikin su kowa yayi shiru tana kwance a jikin sa yaji saukar numfashin ta alamun tayi bacci ya kalle ta yayi mata kiss a goshi ya tashi ya d'auke ta ya kaita d'akin sa ya kwantar a kan gado ya zauna gefen ta yana shafa goshin ta a hankali cikin k'auna da soyayyar ta mai tarin yawa.

*&&&*

? ? ? ? ?? "Mai martaba sarki mai murabus ne babu lafiya, yanzu haka ance jikin sa ko motsi bayayi yana kwance kamar gawa" hadimai suke suna tafiya suna tattauna maganar cikin jimami. A wannan lokacin Hankalin Hydar a tashe yake sosai sai shige da fice yake so yake private get d'in Asad da za'a d'auke shi a kaishi Germany ya zama ready domin yanayin jikin sa ya gigita shi.

Dukkan iyalan sa suna zagaye dashi har y'ay'an sa mata da suke gidajen mazajen su sun hallara suna zaune an saka shi a tsakiya kowa yayi shiru ana yi masa tofi masu kuka suna kuka masu jimami suna jimami.? Fari siririn mutum ne zaune kusa dashi sanye da lab court kana ganin sa zaka fahimci likita ne sabida yadda yake yake ta had'a magani da allura yana yi masa ko za'a samu ya motsa amma abin yaci tura sai idanu kawai da yake bin mutanen d'akin dashi.

Bayan ya kammala ya kalle su yace, "I'm sorry to say, na kasa gane abinda yake damun sa tafiya Germany d'in kamar yadda Hydar ya fad'a is better." Mai martaba sarki mai rik'on kwarya yace, "Dr jiya fa lafiya lau yake meya same shi da sauri haka?." Dr yace, "Allah ya taimaki sarki bana ce ba, kuma ita k'addara tana samun mutum ne a ko wanne lokaci koda bai shirya ba."

Cikin gamsuwa yace, "Haka ne. Allah ya bashi lafiya." Dukkan su suka amsa da amin Hydar ya shigo yace, "Komai ya zama ready zamu iya tafiya yanzu." Mai martaba sarki mai rik'on kwarya yace, "Hydar dani ya kamata ayi tafiyar nan."
"A'a Ranka ya dad'e, in hakan ta faru bamu ciki masa burin sa na k'in son a bar masarauta babu shugaba ba. Ayi hak'uri mu fara yin gaba daga baya sai a samu damar zuwa."

Ya girgiza kai alamun haka ne waziri zaiyi magana hydar ya riga shi yace, "Nida shi kawai zamu tafi a yanzu, Mama ko Hajiya ko Ammi inda wanda wacce zata biyo bayan shi sai tazo daga baya, yanzu kam emergency muke son tafiyar" ya fad'a yana d'aure fuskar sa dan baya so ma ya bawa Waziri damar ganin dariyar sa balle yace masa zaije.

K'arasawa wajan sa Hydar yayi yace, "Na shigo da mota nan mu fita dashi." Duka a tare suka mik'e da Hydar da sabon sarki da Dr suka d'auke shi aka fita dashi aka saka shi a mota. Hydar ne ya kuma dawowa ya shiga cikin d'akin sa Jim kad'an ya dawo da k'aramar jaka a hannun sa key d'in motar ya fad'i ya juya zai d'auka suka had'a ido da Mama.

Irin kallon da tayi masa ya saka shi ya gano mai take nufi ta tashi ta fita daga falon ya fita shima ya saka jakar a bayan motar kasancewar doguwa ce a baya aka kwantar da mai martaba yabi bayan Mama da sauri, a k'aramin falon ta na biyu ya same ta ya shiga da sauri yace, "Mama sauri nake yi." Tace, "nasan saurin kake yi ai, tambayar ka zanyi ka kuma bani amsa kayi min k'arya Allah ya isa ban yafe maka ba Hydar."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mama me yayi zafi haka?" Ya fad'a a rud'e yana kallon ta taja tsaki tace, "kadai ji me nace ai."
Jikin sa yayi sanyi yace, "in sha Allah bazan fad'i k'arya ba."
"A wanne gari Asad yake a Egypt?." Gaban sa ya fad'i jin tambayar da tayi masa ya kalle ta yaga sai kallon sa take yi ko wanne yanayi nasa tana karanta ya sunkuyar da kai tace, "kayi min k'arya wallahi ban yafe maka ba Hydar. Nasan kasan komai raina min hankali kawai kake yi."

Hydar yace, "dan Allah Mamana ta daina fad'ar haka a akan d'anta."
"To fad'a min" ta fad'a tana kallon sa idanun ta a waje. Hydar ya sauke numfashi cikin rashin abinyi yace, "Cairo."
"Wanne hotel ko wanne estate?." Hydar yaji kamar ya kurma ihu ya shafa kansa kafin ya kalle ta yace, "Four Seasons hotel."

Ta girgiza kai tace, "Four Seasons hotel...!? Hotel mai tsada kuka sauki y'ar talakawa wacce bata tab'a kwana a a.c ba sai da kuka basu gida. Room number fa?." Hydar yace, "Special room 012." Kai ta girgiza tana kallon sa ganin hakan ya saka shi niyar fita ta dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Ka sake ka kira Asad ka sanar dashi ka fad'a min inda yake ban yafe maka ba, kuma kar ka saka ran zan yafe maka har a tashi duniya." Jikin sa ya sake yin sanyi ya tsaya cak bai juyo ba yana jin kamar yayi kuka domin yasan tabbas akwai abinda zai faru gashi baya son abinda zai raba d'anuwan sa da abinda yake so, ga kuma abinda Mama tace, ya juyo yace, "Allah ya wuci zuciyar Mama, ina rok'on Mama da tayi min afuwa a zuciyarta bani da laifin komai. Na wuce Germany ina neman albarka Mama" ya fad'a yana ya fita da sauri.

Numfashi ta fesar tayi murmushi tace, "Suhaima!" Ta fad'a da d'an k'arfi. Suhaima da ta shigo lokacin cikin jimamin jikin mahaifinta tace, "Na'am Mama."
"Kina da visa Egypt?."
"Eh ina da ita, amma ina jin saura baifi sati biyu tayi expire ba."
"Ki nema mana ticket nida ke na zuwa Cairo, in zai yu jirgin yau nake so da daddare in babu kuma na sassafe zakiyi booking."

Suhaima ta bita da kallo tace, "To, amma Mama me zamu je yi can?." Ta kalle ta tace, "kiyi abinda nace malama, in baza kije ba ki nema min ni kad'ai ba lallai sai dake ba." Suhaima ganin ta fusata ya saka tace, "Allah ya wuci zuciyar Mama zanyi, wanne hotel zanyi booking?."
Da hannu tayi mata alamar ko wanne Suhaima ta wuce ta shiga ciki zuciyar ta cike da tunanin abinda zai kai su Cairo.

Mama ta sauke numfashi tana hasasho abinda zai faru a can domin tasha alwashin sai ta raba Asad da Rauda koda zata dawo babu rai, daman Mai martaba ne yayi mata katanga da hakan yanzu kuma katangar ta rushe zatayi duk abinda take so ba tare da sanin sa ba tunda ba lafiya yake da ita ba, tayi murmushi tace, "Gani nan zuwa Asad!!!."

? ? ?? *&&&*

Bayan Rauda ta farka taji dad'in jikinta sosai tayi sallah ta sake yin wanka ta fito falo bata ganshi ba amma akwai abinci ta zauna taci bayan ta ta kalli wani k'aton mudubi da yake falon, tashi tsaye tayi tana kallon kanta sanye take cikin doguwar riga mai fad'i ta saka hular ta tana kallon kanta. Ita kanta burge kanta take yi domin kuwa ita kanta tasan tayi kyau fatar ta ta murje sai shek'i take ga kib'a da tayi duk wata komad'a nama ya cike shi duk da dai daman bata da rama. Murmushi tayi tunawa da abinda ya faru sau biyu tsakanin ta da Asad sai ta saka hannu ta kulle fuskar ta tana murmushi shima da yake bayan ta murmushin yayi dan ya tabbata abinda ya tuna itama shi ta tuna.

Shi kam baiga bak'i da munin da Mama take maimaitawa a kanta musamman da yaga fatar jikinta har tafi fuskar ta haske, kyaun ta yake gani shi kam fiye da komai baya ganin muni ko bak'i a tare da ita.

? ?? A hankali ya tako inda take har lokacin hannun ta na kan fuskar ta ya k'araso ya zura hannayen sa ya rik'e shafaffen cikin ta ya had'e bayan ta da jikin sa ya rugume ta tsam ta baya ya d'ora kansa a kafad'ar ta yana kallon ta mudubin har lokacin fuskar sa da murmushi har hakoran sa suna waje. Cak yaga ta tsaya tana bud'e idanun ta a hankali suna had'a ido tayi saurin kulle idanun ta ya yiwa kunnen ta kiss taji sautin sa har kwakwalwar ta.

Ya lura ta fara sonsa kamar yadda yake sonta hakan ya saka yake jin farin ciki fiye da baya ya kalle ta yaga tana murmushi amma idanun ta a rufe. Juyo da ita yayi ta koma ta juyawa mudubin baya shine yake kallon madubin ya rugume ta very tight yana ji kamar wani ne zaizo ya raba su a lokacin. Sun jima a haka babu wanda yake yiwa wani magana kafin ya sassauta rik'on da yayi mata ya d'ago da fuskar ta yaga har lokacin idanun ta a rufe yake ya yiwa idanun nata kiss ya kai bakin sa daidai kunnen ta yace, "I'm in love with you Love."

Yarrrrr taji gashin jikin ta yana tashi ta sake kwantar da kanta a k'irjin sa ta rik'e shi da hannayen ta da suke bayan sa shima ya rik'e ta kafin ya sake ta ya kalli doguwar rigar jikin ta yaga tayi mata kyau sosai ta haska ta kasancewar kalar ta jah ce sai khamshin humra take mai dad'i, mayafin doguwar rigar ya gani a gefe ya d'auka ya yafa mata ya rik'o hannun ta yaja ta sai yaga ta turje ta d'an kulle idanun ta alamun akwai abinda yake mata ciwo.

K'are mata kallo yake yi tun daga sama har k'asa ya fahimci dalilin tsayarwa ta sai yace, "Ohh sorry, amma sai munje kinga dr." Rik'e hannun nata ya kuma yi a hankali suka fita daga d'akin ya kulle suka shiga elevator suka sauka, sai a nan ta tabbatar da ana rana a garin ganin rana ta kwalle sosai suka shiga mota yaja suka tafi.

? ? ? Asibiti suka fara zuwa badan taso ba aka bata magani suka sake fitowa suka shiga motar. Kasuwa ya kai ta suka shiga ya kalle ta yace, "ki d'auki abinda kike so, then kiyi tsaraba." Murmushi tayi ta fara d'aukar dogayen riguna da riga da siket dana riga da wando dan iya zaman ta a k'asar tana jin dad'in saka su.

Kad'an yaga ta d'iba ya kalle ta yayi mata alama da ta k'ara ai kuwa ta cigaba da d'iban abinda take so tana d'aukar su Umma ta cika basket taf bayan ta gama suka k'arasa ya biya kud'in aka cika musu manyan ledoji guda uku aka kai musu har mota suka shiga suka tafi.

Gani yayi tana ta farin ciki sai kawai ya canja hanya suka wuce wajan wasan yara, sai da sukayi sallah sannan suka shiga nan Rauda ta dinga karo da y'ay'an larbaawa suna ta wasa tayi murmushi tana kallon wajan, ticket ya siya musu na lilo mai kyau wanda yake lulawa har sararin samaniya suka hau ganin yadda yake gudu a sama ta kwanta a jikin sa tana chukikwye masa riga daman shi haka yake so ya rik'e abar sa suna juyawa a sama. Ji take kamar kanta yana juyawa kasancewar karon farkon ta kenan suna sauka sai da ya rik'e ta dan kamar zata fad'i ya zaunar da ita tasha ruwa.

? ? ? ? Suna barin wajan suka wuce wani lafiyayyen garden da masoya suke zuwa; suna shiga taga wasu shuke-shuke ga fitila a ko ina mata da miji suna zazaaune ko wanne da kalar soyayyar da yake nunawa matar sa, kallon sa tayi suka had'a ido tace, "wajan yayi kyau." Murmushi yayi mata ta zauna akan grass carpet ya zauna shima sai ta zame ta kwanta a cinyar sa ganin duk haka larabawan sukayi a wajan.

Bai hana ta ba yana rik'e da hannun ta har wajan ya sunkuya da kansa yayi mata kiss a goshi aka kawo musu abin motsa baki bai sha ba itama haka suna nan zaune a nan sukayi i'sha sannan suka bar wajan. Magana bata had'a su sosai amma zuciyoyin su na amsar sak'on kowa musamman murmushin sa yana sakawa Rauda taji kamar zata fad'i sabida yadda yake ratsa ta.

Katafaran restaurant suka shiga akayi order abinci suka ci shida ita basu jima a nan ba suka wuce home of ice cream, itace kawai tasha shi kam bai sha ba sai da ta shanye suka shiga mota ta sauke numfashi tace, "na gaji na kuma k'oshi." Baice mata komai ba da niyar sa su wuce sharaha amma jin ta gaji sai ya fasa suka d'auki hanyar hotel. Yana ajjiye motar ya saka ma'aikatan yi mata gaba da kayan ta su kuma suna takawa a hankalin hannun su sark'e dana juna ta kalle shi shima ya kalle ta sai ta b'oye fuska yayi murmushi suka shiga elevator.

? ? ? Falon duhu sosai bata tsaya kunna haske ba ta shiga d'aki domin fitsari take ji bayan ta fito daga band'akin ta dawo falon, turus tayi ganin abinda yake falon ya d'auki hankalin ta ya kuma burgeta ta tsaya tana kallon ko ina.

Lafiyayyun flowers ne jajaye da yalaye anyi ado dasu a falon ga balloon a barbaje a k'asa kid'a na tashi kad'an-kad'an irin wanda ake kira slow music sak irin decoration na india, wajan yayi bala'in kyau ta tsaya a tsakiya inda balloon d'in suke tana kalla tana dariya cikin burgewa dan ba gani ta tab'a yi a zahiri ba. K'ananun flowers sune a zube akan carpet d'in da ya mamaye falon ko ina yayi kyau sai khamshi da yake tashi a wajan ga fitilar da take kawowa ta d'auke kalar blue.

_I wanna be in your life until the night is over, I wanna hold you so tight so tight, come in closer, it's been a hell of a ride forever single moment, you were there by my side. Whenever I'm broken u make me feel whole, whenever I'm lonely you're there for my soul, whenever you are girl that's where i call my h??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ome, whenever you doubt it i I'll lettin you know. Woahh girl i want to be dancing with you forever; you see through the storm and take me as I am, Baby it's magic anytime that we're together i make just love you and hold you for my hand, hold you for my hand, my hand, my hand._ wak'ar for my hand kenan ta burna boy itace take tashi a wajan a hankalu cikin dad'in sauraro.

Daidai inda ake ce, 'i wanna hold u so tight, so tight come in closer' daidai wajan Asad yayi holding d'in ta very tight yana jera mata kyakykyawan kiss a wuyan ta wanda ya saka ta kusa zaucewa ta rik'e shi kam a jikin ta. Zuciyar ta bugawa take domin ta fahimci wak'ar sak'o ne yake bata cikin salo na nuna soyayya da kuma sanya nishad'i a zuciya hakan ya saka ta gigicewa ta rike shi sosai shi kuma yana ta mata kiss a duk inda idanun sa yaje.

Cikin k'aramin lokaci dukkan su gangar jikin su da zuciyar su tayi nisa cikin soyayya da k'aunar junan su, shauk'i ne yake d'aukar su dukkan su ta rik'e shi kam shima haka yana yawo da hannun sa a jikin ta. Sakin ta yayi ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta yace, "Ki yarda ko kar ki yarda I love you for the sake of Allah." Yana kallon ta tana kallon sa yake furta mata kalmar da ta saka zuciyar ta jijjiga idanun ta yayi narai-narai kamar zata zubar da hawaye tana kallon sa shima kuma ita yake kallo.

Hannu ta d'aya ya rik'e ya d'auko zobe mai kyau ya kama yatsan ta na kusa da k'aramin ya zura mata shi ya zauna cif a hannunta ya haska fatar hannunta. Kallon zoben take ta kalle shi sai ya d'aga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login