Showing 66001 words to 69000 words out of 216282 words

Chapter 23 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

bud'e ya fito yana kallon gidan sai yake ji ya zamar masa bak'o kamar ba'a nan aka haife shi ba. Ciki suka nufa Asad yayi hanyar da zata kai shi apartment d'in su ta kalle shi ta cigaba da tafiya, yasan ma'anar kallon ko bata ce ba yabi bayan ta a gajiye.

Tana shiga apartment d'in ta aka fara kawo gaisuwa amma babu wanda take kulawa har taje k'aramin falon ta wanda ba kowa yake zuwa ba ta zauna a kan kujera ya zauna a k'asa Suhaima ta wuce d'akin ta, kallon sa tayi tace, "Ban amince da d'akin ka na da ba dan haka zaka zauna a nan kafin a kammala komai ka koma b'angaren ka, aiki yayi nisa ko nace an gama ma." Shiru yayi baiyi magana ba tace, "ko baka ji bane?."
"Naji. Ina neman izini zanje can d'in na d'auko abinda zanyi amfani dashi."
"Ban amince ba ka fara hutawa kaje anjima, tashi ka shiga d'akin da Hydar ya kwanta." Bai musa ba ya tashi ya shiga tare da kullo k'ofa.

? ? ? B'angaren Fulani Hajiya tana zaune labarin dawowar Asad yazo kunnen ta bata nuna komai ba sai da ta shiga d'akin ta ta zauna a gefen gado tayi dariya tace, "ita a ganin ta dawo dashi d'in da tayi shine mafita a gare ta?, bata san lokacin mune zai fara ba" ta fad'a da farin ciki tana d'aukar waya ta danna kira.

Daga can b'angaren aka d'auka tace, "Albishir babba na kira na sanar dakai, Asad dai yau ya dawo gidan nan." Yace, "wasa kike ko gaske? Kin ganni kin saka na tashi zaune ban shirya ba."
"Da gaske nake wallahi ai ko mintina biyar basuyi da shigowa gidan nan ba. Na fad'a maka daman duk yadda Rabi'atu zatayi sai tayi wajan ganin ta dawo da Asad gidan nan tunda har aka furta maganar mulki wallahi sai ta dawo dashi shiyasa nake zargin ta a ciwon Takawa."

"Meyasa kike zargin ta?."
"Sabida shine kawai zai hanata dawo da Asad a kaf duniyar nan shine kawai zai dakatar da ita, inda yana nan da bata isa taje ta tawo dashi ba ya sanar da ita sai da izinin sa zai dawo. Daren ranar da zai kwanta ciwo itace ta shiga wajan sa ta kuma jima kafin ta fito."
"In ma dai itace ko ba ita bace mu hakan yayi mana daidai domin daman jiran dawowar Asad muke kuma ya dawo, da zarar an tamk'a masa mulki a hannun sa a wannan lokacin zamu fara gabatar da aikin mu."

? ? "Haka ne. Ka sanar da master duk abinda yake faruwa a sake nutsawa a cigaba da aiki."
"Wannan ko baki fad'a bama sai anyi" ya fad'a yana yanke wayar tabi wayar da kallo zuciyar ta cike da farin ciki burin su ya kusa cika.

? ? ? ? Asad bai fito ba sai bayan la'asar ya samu kiran sabon sarki baiyi k'asa a guiwa ba ya garzaya wajan sa domin amsa kira. Da girmawawa ya nemi izinin shiga wajan sa aka bashi dama yayi sallama ya amsa tare da fad'in, "Shigo mana Asad." Asad ya shiga ya zauna a k'asa yace, "barka da hutawa." Yayi murmushi ya shafa kansa yace, "barkan ka dai Asad. Ya hanya? Ina fatan an dawo lafiya."

"Alhamdulillah" ya furta a tak'aice ba tare da ya kalle shi ba. Yace, "Maman ka taje ta tawo mana dakai mun huta jira." Murmushi kad'an Asad yayi har lokacin ciwon zuciyar sa bai warke ba yana daurewa ne kawai.
"Naji dad'in dawowar ka kaga yanzu sai a saka ranar da za'ayi bikin baka karaga ka hau mulki ni kuma nabi bayan yayana naga ya jikin sa yake." Asad yace, "Allah ya taimake ka ina neman alfarmar a jinkirta komai naje naga jikin sa na dawo."
"A'a Asad, mulki akwai dad'i akwai wahala iya kwanakin nan da nayi akan kujerar mulki ni kad'ai nasan abinda na tarar a cikin sa. Jiran dawawar ka ya saka aka bani to ka dawo yanzu kuma zan baka, juma'a mai zuwa in sha Allah za'a yi bikin nad'i da kuma bikin auren ka da wacce mahaifiyar ka saka aka nemo maka auren ta komai ya dawo hannun ka a huta."

Bashi da bakin magana yayi shiru yana ji kamar ya kurma ihu sabida takaici mai martaba ganin haka ya saka yace, "kada ka damu fa zaka iya mulki fiye da wanda mahaifin ka yayi, hak'uri zaka k'aro dan zama shugaba ba abu bane mai sauk'i, ka k'aro juriya ka k'aro addu'a da nutsuwa. Sai wannan rashin maganar taka kayi k'okarin ganin ka d'an canja kodan sabida talakawan ka."

Asad yace, "Zanyi kokarin hakan in sha Allah." Yayi murmushi ya kuma shafa kansa yace, "Allah ya bada ikon hakan. Kaje zan sanar da mutane ranar juma'a in sha Allah zaka mallaki kujerar mulkin garin katagum. Daman an sanar da governor yana jiran ka dawo ne ayi komai a gama." Asad yace, "Godiya nake, a huta lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita ya d'an tsaya ya dafe kansa sabida ciwon da yake masa kafin ya cigaba da tafiya.

Babu wajan wacce bai shiga sun gaisa ba a iyayen nasa yaga k'annen sa maza da mata sannan ya nufi apartment d'in su dan akwai abinda yake so ya duba, da sallama ya shiga falon sai kuma yaja ya tsaya yana yamutsa fuska sabida warin sigarin da yaji falon yanayi. Gabad'aya falon a hargitse kamar ba'a rayuwa a ciki ya ga ragoye-ragoyen sigari ga tokar ta ga kwalbar giya da aka sha aka rage.

Ya rasa ranar da Aliyu zaiyi hankali a rayuwar sa ya d'auki sab'on Allah ba komai ba ya mayar dashi ado in baka yi ma baya abota dakai gani yake kamar ba mutum bane ba, sanin mahaifin su baya nan Mama ma bata nan shine yake yin abinda yake so babu wanda zai hana shi. Tsaki Asad yayi cikin jin haushi da takaici ya wuce zuwa d'akin sa ya zaro makullin a aljihu ya bud'e d'akin ya shiga.

Yana nan yadda ya barshi sai dai yayi k'ura ya tura k'ofar ya kulle ya k'arasa d'akin karatun sa ya shiga, ya jima a ciki har yamma tayi sosai sannan ya fito ya kulle d'akin zai bar falon kenan yaji maganar Aliyu yana cewa, "A'a yaushe ka dawo deaf?." Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya k'araso gaban sa yana kallon sa ya d'aga masa gira yace, "Mama taje ta tawo dakai kenan" sai yayi y'ar dariya kana yace, "ni daman nasan Mama bazata tab'a barin ka ba sai ta dawo dakai. To ya matar taka tana nan ko ta raba ku?."

Asad bin sa yake da kallo babu ta inda ya barshi a kammani sak kamar su iri d'aya ce musamman yanzu da yake magana a tausashe sai ka rantse Asad din ne yake magana, halayya ce kawai ta banbanta dan in Aliyu ya shiga waje yayi shiru baya magana tsaf za'a d'auka shine sabida tsantsar kamar da suke da juna. Asad yace, "Yaushe zaka daina wannan halayen naka?." Aliyu yayi dariya yana nad'e hannun rigar sa yace, "Our uztaz? kar ka damu na kusa saura kad'an jira nake na zama shugaba sai na ajjiye."
"In ka mutu fa.?." Aliyu ya wara idanu sai kuma ya juya idanun kamar yadda Asad yake yi kana yace, "mutuwa ai ba yanzu ba Asad, akwai burikan da nake gab da cimmawa dan haka bazan mutu yanzu ba."

Asad ya kalle shi jin abinda yace kamar ran nasa a hannun sa yake sai ya girgiza kai zai wuce Aliyu yace, "Na manta congratulations zaka zama shugaban mu nan da wasu kwanaki kafin a shiga season two." Asad ya tsaya sai ya juyo ya kalle shi Aliyu yayi murmushi ya shafa kai yace, "kayi hak'uri d'an karamin tunani ne irin nawa." Asad yace, "meyasa baka bi Hydar wajan Abba ba?." Aliyu yace, "sabida ina da abu mai mahimmaci wanda yafi wancan."

Kallon mamakin da yaga Asad yanayi masa ne ya bashi dariya yayi y'ar k'aramar dariya yace, "Kar ka damu wannan ba komai bane. Nace saki nawa ta saka ka yiwa abar son naka?. Naga ma duk ka rame baka nustuwar ka da alama duk soyayyar tata ce ko?." Asad bai kula shi ba ya fita ya k'yale shi a zuciyar sa yana tabbatarwa shaye-shayen da yake yi ya fara tab'a masa kwakwalwa.

Aliyu ya bishi da kallo yayi murmushi yace, "Yanzu aka fara wasan Asad mu zuba mu gani aga nida kai waye zai hau karagar mulki, nidai bazan bar maka ba Mama kuma nasan bazata bar min ba amma dai zamu gani da alama a wannan season d'in za'ayi kashe-kashe" ya fad'a yana zaro waya a aljihu ya buda ya mayar ya fita.

B'angaren Mama tana zaune bayan ta tashi daga baccin gajiya suna waya da Hydar Mum ta shigo ta zauna a kan carpet jikin ta nata tashi khamshin turare tana kallon Mama har ta gama wayar ta kalli Mum tace, "Wani lokacin wayar ki bata da amfani Sadiya." Mum ta duk'a tanayi mata jinjina tace, "tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar gimbiya fulani yar sarki jikar sarki matar sarki kuma babar sarki."

Mama tayi murmushi tace, "Labari na kira ki zan baki daman tun ina can Cairo d'in." Mum ta zaro ido waje tace, "Har anje kenan ranki ya dad'e?."
"Gani ma na dawo, na kuma tawo da d'ana." Farin ciki ya bayyana akan fuskar Mum ta gyara zama tace, "Ranki ya dad'e wannan ai labari ne mai dad'in ji, Allah yasa dai ta sakar masa kurwa asirin ya karye."

Mama tace, "to gashi nan dai har yanzu bai dawo daidai ba har a asibiti ya kwanta a can jinin sa ya hau amma na haramta masa sake waiwayar inda take nasan kuma bazai yi ba."
"Dakyau Fulani, shiyasa nake fad'awa Jidda a koda yaushe samun irin ki a mata wallahi yana da wahala, Allah yayi miki baiwar kwakwalwa kina fahimtar komai yadda ya kamata." Mama bata amsa ba sai murmushi da tayi tana jin kanta a sama Mum ta kuma cewa, "An rabu dai ko?."

"An rabu da k'aya, na saka ya sake ta yayi saki d'aya da yake nasan babu idda a kanta ban damu ba." Mum ta fad'ada murmushin ta cikin jin dad'i kana tace, "Alhamdulillah, addu'ar mu bata fad'i k'asa a banza ba. Amma fa duk da haka ranki ya dad'e kada muyi sake muyi masa abinda zai tsane ta har abada da ita da dangin ta kar wata rana labari ya sake dawowa baya."

Mama ta girgiza kai tace, "Maganar ki gaskiya ce, Malam Audu baya iya komai ne yanzu ki duba aikin da muka bashi akan kashe ta har hijjabi muka samo amma nice nayi aikin shi baiyi komai ba." Mum tace, "Ranki ya dad'e bashi da lafiya sosai, jiya naje wajan sa akan aikin na samu sai jiya ya fara fitowa ma sabida ciwon da yayi kwana biyu ko waje baya zuwa. Amma yanzu zance kar ya aiwatar da kisa yayi amfani da hijjabin nata ya saka masa tsanar ta data dangin sa mai muni ma, yadda ko ya ganta a hanya zai bi ta kanta da mota ya wuce hkan zai fi yi mata d'aci a zuciyar ta."

Mama tace, "haka yayi ki fad'a masa yadda akayi sai ki sanar dani, a wannan karon kar ya bamu matsala dan Allah."
"Shi d'in banza" ta fad'a tana murmushi. Mama tace, "Ya kamata a fara shiri fa dan nasan bikin nad'in nasa bazai wuce juma'a ba kuma kin san da bikin auren sa za'a had'a a huta, ki fad'a Jidda ta fara shirin zama mata ga sarkin Katagum" ta fad'a tana kallon Mum tana murmushi.

Mum ta sake washe bakin ta tace, "Ai wannan maganar kamar a kunnen ta ranki ya dad'e, za'a sha murna kuwa dan kwana biyu kwana take kuka." Mama tayi dariya kad'an bata ce komai ba Mum tace, "ya tsarin zaman gidan yake a ina zata zauna ranki ya dad'e?." Mama tace, "Zata zauna a apartment d'in kusa dana mai martaba dan aiki ma an gama zance, an gyara inda mai martaba ya tashi itama an gyara mata nata su kawai ake jira su shigo."

Mum tace, "Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Mama tace, "Amin." Daga haka taja bakin ta tayi shiru Mum tayi murmushi a zuciyar ta tana fad'in, _Lokaci yazo Rabi'atu, lokacin da zan kwace duk wata isar da kike ji da ita tazo, lokacin da komai zai dawo hannuna yazo, lokacin da zan zama uwar sarki a madadin ki yazo, lokacin da zan ajjiye ki a gefe ki koma tamkar hoto yazo, lokacin da y'ata zata zamar miki ciwon ido yazo. Asad zai zama tamkar k'aramin yaro ne sai abinda Jidda taso zaiyi, ita zata sarrafa shi yadda take so bazan yi sake ba nafi kowa sanin halin ki sai na tabbatar da y'ata ta zama sama da kowa a masarautar katagum._

Mama ta kalle ta taga tana ta murmushi ita kad'ai tana kuma d'an kad'a kai alamun tunani take yi tace, "tunanin me kike yi?." Ta kalli Mama tace, "tunani nake burin k'awata kuma shugabata ya kusa cika ina tuna irin farin cikin da zakiyi a duk sanda aka d'ora Asad a wannan kujera, tuna zaki farin ciki shine yake bani ninkin farin ciki."

Mama ta murmusa tace, "gab burina yake da cika kam, zan mallaki abinda na jima ina fata, a bayyane Asad zai kasance sarki ne amma a b'oye zan kasance nice nake mulki domin kuwa sai abinda nace yayi sannan zanyi. Lokaci yayi da Rukayya da Sa'adatu zasu san ni ba sa'ar yin su bace."

Kallon ta Mum take yi tana maganar tana bata amsa a zuciyarta tana fad'in, _K'arya kike wallahi kema baya zaki koma duk wannan jin kan naki sai na sauke shi domin komai naki a tafin hannuna yake, sai na nuna miki nima bata wasa bace ba._ A bayyane kuma sai tace, "Haka ne ranki ya dad'e, zamuyi abinda muke za kuma mu bar abinda muke so." Mama tayi dariyar nishad'i tana kallon Mum tana taya ta a zuciyarta tana fad'in, _Anzo wajan Rabi'atu!._


_Fan's nima nace Anzo wajan._=?P? >د?>??[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*047.*

? ? ? ? ? Takawa take a hankali tana k'arewa gidan kallo ganin harda wajan ajjiye mota guda d'aya, dan kyau gidan yayi kyau ta juya tana zagawa tare da d'aga kai tana kallon gidan. Kai ta girgiza gaban ta na tsananta bugawa a bayyane tace, "Ina amfanin wannan hidimar an wulak'anta maka diya?" Ta fad'a tana jan jakar ta zuwa k'ofar da ta gani tana kallon ta.

K'ofar mai kyau kalar kofi ta tura ta ta shiga a lokacin Sammani yana niyar fitowa, kallon kallo suke yana kallon ta tana kallon sa da murmushi dan taga alamun bai gane ta ba, y'ar dariya tayi cikin k'arfin hali tace, "Sammani ya dai?." Sai kuwa yace, "La wallahi ita, Anty Rauda ta dawo!" Ya koma a guje yana faman kiran Anty Rauda ta dawo. Dariya tayi ta kalli inda ya fito taga tsakar gida ne babba gabad'ayan sa tiles ne a k'asan sa gefe ga matattakalan sama ita duka tiles tabi inda Sammani yabi tana jiyo ihun sa har lokacin.

? ? ? ? "Anty Raudaaaaa!" Aka fad'a da k'arfi lokacin da ta shiga babban falo madaidaici mai kyau mai d'auke da kujeru madaidaita da carpet har da tv bango da a.c da fridge. Ummulkhairi ta gani a guje ta rungume ta tana ihu ta rik'e ta itama tana cewa, "Ke zaki yar dani." Ta d'aga ta tana kallon ta tace, "Anty Rauda kinga yadda kika koma kuwa? Kinyi kyau kinyi kib'a gashi kina tafiya." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta juya ta kalli Khalil da ya shigo shima ya rik'e ta yana ihu tayi dariya tace, "Ina Rahma take?." Ummulkhairi tace, "tana gidan Yaya Ummi, kinga gidan da muka dawo muma mun zama y'an gayu."

Rauda tace, "Ina Umma da Inna suke kun barni Ina ta zuba ban gansu ba" ta fad'a tana yin gaba suka bita a baya Khalil yana jan jakar ta zasu shiga wajan Umma suna ga Inna ta fito daga wata k'ofa tana fad'in, "Ashe da gaske kece Rauda, Tabd'ijam wannan in a hanya na ganki ai bazan gane ki ba." Rauda tayi dariya suka gaisa cikin farin ciki kafin ta shiga wajan Umma.

Ihun su ne ya tashi Umma daga bacci ta fito daga d'aki tana tambayar lafiya taga Rauda na shigo k'aramin falon Umman ta nufe ta da sauri ta fad'a jikinta tana fad'in, "Nayi kewar ki Ummana." Umma da mamaki da farin ciki tace, "Rauda! Saukar yaushe?" Ta fad'a da mamaki da farin ciki tana kallon ta. Rauda ta d'ago daga jikin ta tace, "Umma wallahi nayi kewar ki sosai." Umma tayi dariya tace, "Muma duka munyi kewar ki. Alhamdulillah lafiya ta samu Rauda kece kike tafiya da k'afafun ki?."

? ? ? "Anty Rauda ina tsarabar mu?" Khalil ya katse su ta kalle shi Umma ta riga ta magana tace, "Kwa dai barta ta huta dai tukunna kwa tambayi tsarabar." Rauda tabi falon Umman da kallo ganin sa ba kai girman na farko ba amma mai kyau komai akwai a ciki sa kamar waccan Umma ta kalle ta tayi murmushi tace, "Ki huta duka za'a baki labari, shiga ciki kiyi wanka ki samu ki kwanta duk da tafiyar jirgi gani nake ai ba wata wahala sai dai zuwa nan daga bauchi."

"Ummana Ina Baba?." Umma tace, "Ya fita amma nan da anjima zaki ganshi." Rauda ta shiga d'akin Ummulkhairi ta biyo ta da jaka duk suka mara mata baya gabad'aya dok'in ganinta suke yi gani suke kamar an canja ta. D'akin babba mai d'auke da kayan gado komai akwai harda carpet a tsakiya ga band'aki a ciki ta girgiza kai tace, "Lallai da gaske kike Khairi mun koma y'an gayu" ta fad'a tana shiga band'akin zuciyar a cushe.

Wanka tayi da alwala ta fito har lokacin suna nan tayi dariya ita kanta taji dad'in ganin k'annen nata ta kalli Khairi tace, "Ina kayana na wancan gidan?." Khairi ta mik'e ta bud'e mata wardrobe tace, "gasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login