Showing 75001 words to 78000 words out of 216282 words

Chapter 26 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

mahaifina ya tafiyar dashi badan mun fishi k'warewa ba sai dan zamanatar da namu da zamuyi cikin ilimin addini dana zamani. Ina yiwa kowa fatan alkhairi da fatan komawa gida lafiya, ina rok'on Allah ya k'arawa mahaifina lafiya ya tashi kafad'un sa nan kusa, ya bamu ikon farawa lafiya ya bamu ikon gamawa lafiya, ya bamu ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu."

Addu'a yayi da larabci yana yi yana tsayawa sabida yanayin amma sai ka d'auka wani sabon style d'in ne hakan sai ya sake burge mutane musmaman yadda yake magana da ilimi a cikin ta.

Tambari aka buga sai da gaban kowa ya fad'i shamakin Katagum wanda ya kasance kowa yaushe yana gefe ya matso da sauri aka k'arasa aka gyara masa wajan zama ya zauna bayan an kare zaman nasa.

? ?? Jijiyoyin kansa ya rik'e domin harbawa suke sabida ciwo gabad'aya ya gaji ya galabaita jira yake kawai a tashi kowa ya watse ga sallar la'asar a kansa baiyi ba. Ba jimawa mai girma gwamna yayi jawabi kafin a watse a tafi raka mai martaba sarki Asad cikin gidan sa.

Gudu ake a kan titi ana jiniya mutane da yawa sun fito kallo ana d'aga masa hannu duk sai yake jin wani iri sabuwar k'asaita tana shiga ilahriin jikin sa, a haka aka isa gidan sarauta ya shiga ta k'ofar da mahaifin sa ya shiga yana tafiya ana kirari ana takawa a hankali cikin rashin kuzari.


Kida ake a gidan ana wasa da dawaki ana busa jama'a sun cika sosai na cikin gidan da wajan gidan. B'angaren Mamaa aka fara raka shi Mama tana zaune ita da y'an uwanta da k'awayen ta jakadiya ta shiga tana gud'a tana fad'in, "Ga farin wata nan ya tawo ya haske ilahirin duhun da ya mamaye gidan nan, ga bangon sikari nan ga fari ka zak'i, yadda yake fari fari haka zuciyar sa take fara tass, ga inuwar bishiya nan mai kud'i ya zauna talaka ya zauna. Allah yaja da zamanin Sarki jikin sarki, Allah ya k'arasawa sarki lafiya da nisan kwana. Shigo lafiya Angon Fulani Jidda....."

? ?? Duka mutanen Falon sun tashi banda Mama da take jin kanta a sama kamar zai???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? fashe Asad ya shigo falon yana kallonta ta saki Murmushi ya k'arasa kusa da ita ya tsuguna a k'asa ta d'ora hannunta a kansa tace, "Allah ya yiwa rayuwa albarka, Yadda ka fara lafiya yau Allah yasa ka gama mulkin ka lafiya."

? ?? "Amin, Allah yaja da ranki ya baki tsahon kwanan ganin mulkin jinin ki" dogarai suka fad'a cikin d'aga murya. Mama tace, "ka gaji kaje ka huta." Kai ya girgiza domin bazai iya magana ba ya mik'e sai a lokacin ya kalli matan falon yaga dukkan su sun zube a k'asa kowa da farin ciki a kan fuskar sa.

Fita sukayi daga b'angaren ana ta kid'a ana busa ana ta tambari an saka masa lema a sama yana takawa mata suna gud'a da addu'a ana ta d'aukar sa hoto shi kuma yana dogara doguwar sanda mai cike da ado yana takawa a hankali yana kallon kowa d'aya bayan d'aya, aka raka shi har inda ya kasance b'angaren sa kafin kowa ya watse ya barshi shi kad'ai domin ya huta dan bazai iya zaman fada ba.



*The beginning.......*


FitattuBiyar
Nana haleema
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*049.*

? ? ? ?? "Rauda! Rauda!! Rauda!!." Daga can cikin d'aki tace, "Na'am! Baba gani nan." Jim kad'an ta fito daga d'akin hannun ta rik'e da d'ankwali ta fito inda Baba yake tsaye tace, "Baba gani" ta fad'a tana d'aura d'ankwalin. Ya nuna mata waje yace, "Zauna" ya fad'a yana zama shima ta zauna a kan carpet tana kallon sa yace, "Ashe yau aka nad'a mijin ki ya koma sarkin katagum amma shine koda wasa baki fad'a min ba?."

Gabanta ya fad'i har sai da ta dafe k'irjin ta ta d'ago ta kalle shi zatayi magana yace, "Wannan ai wula?anci ne kin san da abu baki sanar damu ba ai ko Allah ya sanya alkhairi maje muyi masa ko bamu muje wajan nad'in ayi damu." Yadda yake magana da fad'a ya saka ta had'd'iye abinda yazo harshen ta Umma da take zaune tace, "Ke kin san za'ayi sarautar ne?." Kai ta girgiza alamun a'a ta mayar da kanta k'asa bata ce komai ba.

? ? ? "K'arya kike, ta yaya za'ayi masa sarauta matsayin ki na matar sa baki sani ba?, nafa san take-taken ki tun farkon auren nan ba so kike ba keda uwar ki da take goya miki baya shiyasa tunda kika dawo kike neman hanyar da zaki bi ki datse igiyar auren tunda kin samu abinda kike so k'afa ta warke ko?. Rauda tayi shiru bata ce komai ba Baba ya kuma fad'in, "Ta yaya zaki ce baki sani ba banda rainin hankali...? ko kuma kishin ya k'ara aure kike yi shine ya mayar dake haka?."

Lumshe idanun ta tayi ta bud'e su bata da abinda zata ce Baba ya fahimce ta gwara taja bakin ta tayi shiru a ganinta hakan yafi mata kwanciyar hankali, "ba magana nake miki ba? Kishi kike ko me?" Baba ya sake katse ta a fusace.
"Kayi hak'uri Baba, duka abinda ka fad'a ban san anyi ba, tunda muka dawo yace min a kawo ni gida zaizo nayi hak'uri daga nan ban kuma ganin sa ba."
"Ba kince kuna waya ba?."

? ?? "Eh muna waya Baba amma ba sosai ba" ta fad'a a sanyaye tana mayar da idanun ta k'asa. Baba yaja tsaki yace, "Zamu je muyi masa Allah ya sanya alkhairi matsayin sa na wanda yake auren y'ata." Rauda ta kalli Baba hawaye ya ciko idanun ta tace, "Baba basai kunje ba, da ace yana so kuje da zai sanar dakai."? Umma da take gefe tace, "Abinda na gani kenan nima dai. Bai sanar damu ba kawai sai a d'auki k'afa a bishi ayi masa Allah ya sanya alkhairi?."

? ? ? "Daman ai ke ba son auren kike ba tun farko dole kice haka da yake dukkan ku baku san ya kamata ba, ai ko babu komai tsakanin su ko dan aikin da akayi mata ta samu lafiya aje ayi masa balle matar sace. Dole naje nayi masa fatan alkhairi matsayin sa na sirikina." Rauda ta runtse ido jin kalaman Baba na k'arshe zuciyar ta nayi mata d'aci da mugun ciwo tana bugawa tunawa da abinda ya faru.

Umma taja bakin ta tayi shiru Rauda ta sunkuyar da kai tana wasa da hannun ta Baba yace, "In ma akwai wani abun a ranki kiyi gaggawar kawar dashi, auren ku babu rabuwa in sha Allah dan ya auri wata ba wani abun bane ba itace daman wacce babar sa take so ya aura tun farko, ki kwantar da hankalin ki ki kawar da ko maye a ranki tunda shi yana son ki zance ya k'are. Yauwa dan aure kam babu rabuwa da izinin Allah" yana fad'a ya tashi ya fita Rauda ta bishi da kallo ta sauke ajiyar zuciya.

? ? ? Had'a ido sukayi da Umma tayi saurin d'auke kanta itama Umma ta d'auke kai Rauda ta tashi ta shiga d'aki jiki a sanyaye Umma ta bita da kallo tana k'iyasta kishin auren sane ya mayar da ita haka. Baba ne ya kuma shigowa yana fad'in, "Ku gyara Anas zai shigo ku gaisa." Umma ta mik'e ta d'auko mayafi ta yafa Baba yace, "Kira Rauda su gaisa" yana fad'a ya fita Umma ta shiga d'akin Rauda wacce jin motsi ya saka ta saurin goge idanun ta ta fara neman kaya kamar daman can abinda take yi kenan.

Umma ta kalle ta tace, "ki ta b'oye damuwar ki a ranki Rauda ke zata dama bani ba, ke zata zamarwa ciwo a zuciyar ki bani ba, bazan kuma tambayar ki ba na gaji da k'aryar babu komai d'in da kike fad'a min bayan a bayyane ba haka bane ba. Ki sako hijjabi Anas zai shigo zaku gaisa" tana fad'a ta fita Rauda jikin ta yayi bala'in sanyi zuciyar ta ta karye hawaye suka cigaba da zuba, Umma ce abokiyar shawarar ta a ko yaushe amma yanzu ta kasa fad'a mata damuwar ta sai take jin nauyi a zuciyar ta, hannu ta saka ta share idanun nata sannan ta sako hijjabi ta fito gaban ta yana tsananta fad'uwa.

? ? ? Da Umma ta tarar suna? gaisawa ya tsuguna har k'asa yana murmushin da ya saba koda yaushe ta k'araso wajan kanta a k'asa, Umma tana murmushi ta kalle ta tace, "K'araso mana ku gaisa, Anas ga Rauda ta dawo." A tare k'irjin su ya buga duka su biyun ya d'ago idanun sa ya kalle ta a lokacin itama ta kalle shi sai ya saki murmushi tayi saurin kawar da idanun ta jin yadda k'irjin ta yake bugu kamar ana doka ganga.

? ? ? ?? "Ma sha Allah Rauda an samu lafiya" ya furta a nutse yana murmushi har lokacin yana kallon ta. Dak'yar ta iya furta, "Ina wuni."
"Lafiya lau Rauda, ya k'arfin jikin?."
"Alhamdulillah."
"Ma sha Allah. Allah ya k'ara lafiya."
"Amin na gode. Allah ya k'ara hak'uri ya jikan wanda suka rasu." Sai da ya murmusa kad'an kana yace, "Amin ya rabbil alamin, na gode" ya mayar da kallon sa ga Umma yace, "Umma zan koma."

Umma tace, "To Anas na gode sosai Allah a yiwa rayuwa Albarka."
"Amin Umma, sai anjima."
"Ka gaida mutanen gidan" ya amsa da zasu ji ya fita ba tare da ya sake kallon Rauda ba. Yana fita Rauda ta zauna a akan kujera ta d'ora hannu a kanta ta rasa abinda yake mata dad'i komai sake lalace mata yake a zuciyar ta. Umma ta kalleta ta kawar da kanta bata ce komai ba sai ma tashi da tayi ta bar mata wajan dan tayi alqawarin bazata sake tambayar ta damuwar ta ba, tunda ta zab'i ta b'oye tai ta b'oyewa ba ruwan wani.

? ? ?? *&&&*

Asad tunda aka raka shi b'angaren sa ya kasa kwanciya ma balle ya iya yin bacci yana zaune a kan kujera yana k'arewa d'akin kallo yana jinsa kamar a mafarki abin yake faruwa.?? Numfashi ya fesar ya d'auki wayar sa ya danna number Hydar bata jima tana ringing ba ya d'auka daga can b'angaren yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, Allah ya k'arawa sarki lafiya da nisan kwana, Allah ya karya mak'iyan ka ubangiji yasa kaga bayan su badai suga bayan ka ba. Ranka ya dad'e mai martaba sarkin Katagum da kewaye."

K'aramin tsaki Asad yayi jin dogon surutun da Hydar ya cika masa kunne dasu yace, "Ya jikin Abba?." Hydar ya sake cewa, "Allah ya taimaki mai martaba jiki gashi dai bama ce ba dan har yanzu babu cigaba, a taya mu da addu'a Allah ya kawo d'auki da gaggawa." Asad yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "zan zo nan da bada jimawa ba."
"Allah ya kawo ku lafiya, ya tsare hanya."
"Amin."

? ? ? Hydar yace, "Ranka ya dad'e mun samu labarin an k'ara aure Allah ya sanya alkhairi ya kawo yara masu albarka." Asad yayi shiru bai amsa ba Hydar yayi murmushi jin bai ce komai ba shima yayi shiru kafin yaji Asad yace, "Call me Asad pls ka daina min wannan dogayen yaren kasan dai ba so nake ba."
"Wane mutum ranka ya dad'e, Ramin kura ai sai y'ay'anta ina ni ina furta wannan babban suna...?."

Shiru Asad yayi na wani lokaci kafin yace, "Hydar still ina ganinta a mafarkina cikin yanayi mara dad'i, ga abinda Mama tace a kanta ban san me ya kamata nayi ba, zuciyata ciwo take." Jin yadda yayi maganar cikin rauni sai Hydar yace, "Ina neman afuwa ranka ya dad'e zanyi magana kamar yadda nake yi da yayana." Sai ya canja murya yace, "kaje ka nemi yafiyar ta Asad, ban san ta yaya kuka rabu ba amma nasan bata hanya mai dad'i Mama ta raba ku ba, babu lallai ma ka kuma yi mata magana bayan kun rabu dan nasan halin Mama bazata bada wata dama da zaku had'u da ita kaga kumaa akwai cutarwa. Yana dakyau kaje ka bata hak'uri in hakan zai yu dan gaskiya ba'ayi mata adalci ba."

Ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru baice komai ba Hydar yace, "nasan it's very difficult kamar ka as emir of Katagum ka bawa wata hak'uri wacce ba matar ka ba but babu yadda ka iya akwai hakkinta da yake bibiyar ka dole ka dinga ganin ta a mafarkin ka domin anyi mata abinda wata?ila ma tana kwance cikin ciwo, zuciyarta tayi rauni over maybe jin maganar rabuwa dakai wani abun ya faru da iyayen ta."
"Ya zanyi Hydar? Mama tace in na sake yin wani abun da ya shafeta bata yafe ba, ta yaya zan iya zuwa wajanta?."

? ? ? ? "In kaje wajan ta neman yafiya ba wani abun bane ba maganar Mama bazata hau kanka ba, da ka zauna da hakkinta fa tana can wata?ila tana cewa bata yafe maka bafa?. Akwai hakkinta a kanka fa dan wallahil azim ba'a kyauta mata ba kaima kuma da laifin ka dole in tace bata yafe ba ya bika." Asad ya sake yin shiru baice komai ba kafin ya sauke wayar daga kunnen sa ya kashe ya lumshe idanun sa yana sauke numfashi. Ya zama dole yaje ta yafe masa komai zai faru sai dai ya faru amma bazai iya zama bai nemi afuwar ta akan abinda ya faru ba duk da shima ba laifin sa bane ba.

? ? ? ? ? Ana idar da sallar magariba kyawawan motoci sama da guda hamshin suna jeru a k'ofar gate d'in masarauta an kawo amaryar mai martaba Jidda gidan ta, tun daga motar da ta fito ake mata tambari ana busa algaita ana kid'a har aka kaita b'angaren Mama. Bata jima sosai a nan ba aka kaita ko wanne b'angaren na matan gidan kafin a wuce da ita b'angaren ta wanda yake kusa dana Asad a ajjiye ta kowa ya tafi ya barta ita kad'ai zuciyar ta fari tassss.

? ? ? ? "Allah yaja zamanin Fulani, Allah yaja zamanin uwar gidan mai martaba. Ina neman izinin shigowa" aka fad'a daga bakin k'ofa Jidda da take zaune ta fuskar ta a bud'e taji izza na shigar ta tayi murmushi tace, "Shigo."
"Godiya nake" ta fad'a tana shigowa ta zube a akan carpet tana yi mata jinjina tace, "Allah ya taimake ki Sunana Hansa'u Jakadiyar mai martaba ana kirana da Jakadiya babba,? Fulani Mama ce ta aiko ni wajan ki."
Kamar baza ta bata amsa ba tayi shiru sai da taga dama sannan tace, "Ina jin ki."

? ? "Allah yaja zamanin ki an turo ni dan na raka ki turakar mai martaba." Jidda ta k'are mata kallo taga a sa'a jakadiyar zata yi sa'ar Mum in ma bata girme ta ba ta d'auke kai tace, "Wajan mijin nawa ma sai an raka ni?."
"Ranki ya dad'e kin manta matsayin ki a garin nan? Ai dole a samu wanda zasu take miki baya duk inda zaki je dan bamu so ko kud'a ya hau kan fatar ki."

Wani irin dad'i Jidda take ji kafin ta d'aga kanta tace, "Kiyi aikin ki." Yadda ta fad'a cike da k'asaita sai da jakadiya ta kalle ta tana jinjina mulkin da Jidda zata zuba a gida kafin ta taso zuwa inda take ta mik'a mata turare tace, "Ranki ya dad'e tace a baki wannan ki shafa a jikin ki."

Jidda ta karb'a ta bud'e kwalbar ta tsiyaya turaren a hannun ta ta shafa a fatar hannunta da wuyanta da k'afar ta gabad'aya. Jakadiya ta fita jim kad'an ta dawo da alkyabba tace, "Ranki ya dad'e ki saka wannan sai muje." Bata karb'a ba hakan ya sak Jakadiya ta saka mata da kanta tace, "Zamu iya tafiya?."

? ? ? Jidda tayi gaba tana binta a baya tana takawa cikin isa suka fita daga d'akin suka fito falo na biyu suka ratsa suka dawo na farko suka fito harabar b'angaren nata Jakadiya tace, "in babu damuwa ranki ya dad'e akwai hanyar da zamu bi ta nan" ta fad'a tana nuna mata Jidda tabi wajan itama tabi bayan ta.

Babu jimawa suka bayyana a harabar b'angaren mai martaba ba tare da sun fita harabar gidan ba gabad'aya, duk inda suka wuce zubewa ake ana gaishe su Jakadiya ce kawai take amsawa hannun ta rik'e da jasan alkyabbar Jidda gudun kar taja k'asa. A kyayattacen falo suka bayyana wanda yake ta tashin khamshi ga hotunan Asad na d'azu da aka kafa a falon yasha ado da zanen sarauta sai kyalli yake yi ga haske tarrr kamar rana.

? ? ? Falon babba ne iya ganin ka babu abinda babu a cikin sa hakan ya saka Jidda k'are masa kallo cikin burgewa domin ya burge ta matuk'a tana aiyanawa a ranta wani adon sai gidan sarauta. Jakadiya tace, "Allah yaja zamanin ki nan ne iyakata daga nan ba'a bani umarnin sake d'arawa gaba. In kin min izini zan iya juyawa na koma." Jidda ta kalle ta kafin tayi mata alama da hannu da ta tafi ta juya ta fita tana fad'in, "Godiya nake ranki ya dad'e, a tashi lafiya."

Jidda ta kalli steps a can gefen falon kai tsaye ta nufi wajan cikin takun isa ta k'arasa inda steps d'in take tana takawa har ta bayyana a saman ta sake karo da lafiyayyen falo wanda sai ka sauka k'asa zaka shiga cikin sa yayi round sai khamshi yake ga sanyin a.c.

falon har yafi na k'asan kyau da tsari girma na k'asan zai fishi ta da manyan kujeru na alfarma kasancewar sa na saukar bak'i. K'ofa guda d'aya rak ta gani a falon kai tsaye ta nufe ta ta bud'e sai gata a doguwar hanya wacce aka mata ado da fulawa na roba masu wuta da dogon carpet jah a jikin sa an rubuta sunan Asad.

? ? ?? "Woww!" Ta furta a bayyane domin da gaske ya burge ta bada wasa ba. A nan taga k'ofofi sama da guda biyu ta rasa wanne zata shiga a ciki tana wannan tunanin taji an bud'e ta farkon yana fitowa suka had'a ido da ita tana kallon sa yana kallonta, waya ta gani a hannun sa sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login