Showing 96001 words to 99000 words out of 216282 words

Chapter 33 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

dashi balle kee y'ar talakawa jinin talakawa wacce bata da tarbiyya." Jidda ta murmusa ta kalli hadimar tace, "kinji me nace miki ai ko?."

Ta girgiza kai alamun eh da hannu ta bata umarnin ta bata waje ta fita jiki na rawa Suhaima taja dogon tsaki ta fita ta barta a zaune zuciyar ta na fasa sabida b'acin rai.
Murmushi tayi tana kallon inda Suhaima tabi tana wasa da hannun ta tace, "zaku d'and'ana kud'ar ku badai yanzu Asad din a hannuna yake ba....? Hmmmmmm muje zuwa" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki tana jin izza a zuciyar ta da gangar jikin ta.

? ? ? ?? Yarda Suhaima ta shiga d'akin Mama a firgice ya saka Mama tashi tsaye Hydar yana rik'e da ita tace, "Me tace miki Suhaima?." Suhaima tace, "Ki gafarce ni Mama amma Jidda ta wuce tunanin ki, kallon idanuna tayi ta kira hadimar ta take sanar da ita koda kece kika je kar a barki ki shiga matuk'ar ba ita ta bada umarnin hakan ba."

"K'arya take! Wacece ita waye ubanta a garin nan? Yaushe ta shigo gidan nan har da take da bakin furtawa wannan mummanar kalma akan Mama..?" Hydar ya fad'a a fusace cikin b'acin rai yana kallon Suhaima kamar zai dake ta.

Mama da take jin kanta yana juyawa tace, "yi a hankali Hydar bana so mutanen gidan nan su san abinda yake faruwa, ku barni da ita in anyi i'sha kuzo muje wajan Asad d'in dukkan mu koma meye yake faruwa zan gani zan kuma yi maganin abin a yau d'in nan, bazan bari abun yayi nisa ba dan ni zata cutar."

Hydar yana rik'e da ita ta zauna ya kalli Suhaima yace, "Zo ki rik'e ta." Ba musu Suhaima ta zauna kusa da Mama ta rik'e ta ita kuma ta dafe kanta da yake mata ciwo zuciyar ta na harbawa da sauri tashin hankali na sake mamaye zuciyar ta.
Kiran sallar magriba ya saka Mama ta tashi Suhaima ma ta fita zuwa nata d'akin domin yin sallah.

? ? ? ? Fulani Hajiya na zaune cikin mayan y'ay'an ta mata su kad'ai ne a zaune bayan su babu kowa tattaunawa babbar cikin su wacce ake kira da Fulani Babba ta kalli Hajiya tace, "Hajiya mai martaba k'anina yana gari kuwa?." Ta tab'e baki tace, "Yana nan yayi wahalar gani yanzu gabad'aya halayyar sa ta canja kamar bashi ba." Wacce take binta biyun Fulani Jamila tace, "Haka Khaleesat take fad'a min gabad'aya yanzu an rasa gane kansa, daman ya za'ayi a barshi lafiya yayi sarauta..? Ba babar sace ta nace ba ai yanzu sai ta zuba ruwa a k'asa tasha."

Fulani Babba tace, "Me ya same shi? D'azu da na shiga duba jikin Abba na d'auka zan ganshi wajan sai ban ganshi ba sai Hydar dalilin hakan ya saka na d'auka baya k'asar." Hajiya tace, "Ai bashi da wannan lokacin a yanzu, in ba Jidda matar saba bana tunanin ko ita Rabi'atu yana saurara, gabad'aya ya canja daga Asad ya koma wani daban."

Fulani Babba tace, "Ya kamata kuwa a tashi tsaye a kansa domin in ba haka ba sunan gidan mu zai lalace, in ya lalace ba iya shi ya lalacewa ba harda mu."
"Ina ruwan ki ya lalace d'in mana kece kika lalace? Ba babar sace take son hakan ba....? ai ga mulkin nan sai tayi abinda take so."
"Allah yaja da ran Hajiya ai d'an uwana ne, kuma shugaban wannan gari yadda ake yabon sadaka da kyautar sa ga talakawa in muka bari hakan ta cigaba da tafiya ba iya shi ba har mu sai abin ya tab'a."

? ? ? "To ban baki umarnin hakan ba, ki k'yale shi kome yake yi yana sane babu wanda ya kai Asad wayo a gidan nan kawai dan bashi da magana ne." Shiru sukayi dukkan su wayar Hajiya ta d'an yi k'ara kad'an ta duba kana tace, "magriba tayi ku tashi ku tafi gidajen ku." A tare suka duk'a suka ce, "Mun barki lafiya, a tashi lafiya" Suka fad'a suna tashi suka fita falon ya rage saura ita kad'ai ta d'auki wayar ta ta shiga can k'arshen d'akin ta.

Tana shiga d'akin wayar ta sake d'aukar vibration tana d'auka ta saka a kunne tace, "Ina tare da yara ne sai yanzu suka tafi shiyasa ban d'auka ba." Daga can b'angaren yace, "Kiran ki na gani d'azu."
"Kana da labarin yadda abubuwa suke lalacewa a gidan nan kuwa? Daga majiya mai tushe an sanar dani Hydar yaje ganin Asad an hana shi ganin sa."
Dariya yayi irin ta rainin hankali kana yace, "nifa na kwanto kurar ta yaya kike tunanin ban san inda zan kamata ba? Kome yake faruwa a gidan nan na sani kuma ni na saka hakan ya faru. Rabi'atu kad'an ta fara gani sai tayi kuka da idanunta wallahi, sai tayi dana sanin bawa Asad mulki."

Hajiya ta zauna a gefen gado kana tace, "A yanzu ma ta fara d'and'ana kud'ar ta tun ba'a je ko ina ba, amma meyasa yake fifita matar sa a yanzu akan babar sa? Karfa matar ta bamu matsala nan gaba."
"Rabi ta amince da babar yarinyar ko wanne sirrin ta ta sani; ta wannan hanyar tayi amfani da sirrikan ta ta mallakewa y'arta Asad ta yadda sai abinda tace masa zaiyi. Ke banda Asad yana da addu'a da rik'o da salati ai wallahi da yanzu an jima da haukata shi, matsala kuma ko Rabi bata isa ta bamu matsala a yanzu ba balle wata matar Asad."

? ? ? ? "Aliyu fa?." Yayi k'aramar dariya yace, "ke tunda yayi tafiyar nan kin sake jin d'uriyar sa?."
"A'a."
"To ya tafi kenan, Aliyu bazai sake marmarin dawowa Nigeria ba har abada na riga na tura shi bazai dawo ba sai dai in nine naso hakan. Nayi maganin Asad ma balle Aliyu k'aramin alhaki."
"Amma ba haka aka tsara ba, karb'ar mulki a hannun Aliyu sai yafi sauk'i akan karb'a a hannun Asad, da ka bari anyi canjin yadda master ta tsara da yafi a ganina."

? ? ?? "Wannan ma master d'ince ta canja plan d'in kuma hakan shine daidai, barin Aliyu ya hau karaga babbar illa ce domin kin san halin sa yana da bala'in wayo bazai bamu wata damar da zamu tunb'uke shi cikin sauk'i ba. Yanzu kuwa kinga yana wata uwa duniya mun kafe shi a can mu kuma muna nan bai isa yayi wani abun ba tunda baya k'asar ma gabad'aya." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "Haka ne. Har naji dad'i daman babban tashin hankalina Aliyu amma tunda kayi maganin sa zance ya k'are."

"Ai abun ne yazo mana yadda muke so ga mai martaba a kwance ba lafiya, Hydar da Mubarak hankalin su yana kan mai martaba da wannan damar zamuyi amfani mu cimma muradin mu kafin lokaci ya k'ure mana. Nan kusa zaki ji labarin da dole sai an sauke Asad a karagar mulki, badai halayyar sa ta canja ba....hmmmm" ya fad'a cikin zallar mugunta.

Hajiya tayi dariya mai sauti cikin farin ciki tace, "Lokacin yazo ni na matsu nasan wacece master planer." Yayi murmushi yace, "Sab'anin tunanin ki itace Master planer, in kina jin labarin kwantan b'auna ki d'auka master planer itace kwantan b'auna da kanta ba aiki taba. Zan kira ki" yana fad'a yana yanke wayar tabi wayar da kallo.

"Master planer! Wacece ita? A ina take? Ya akayi ya amince da ita.....?." Sanin babu mai bata amsa ya saka ta tashi ta shiga band'aki zuciyar ta cike da farin ciki wani b'angaren babu dad'i.

? ? ? Bayan an idar da sallar i'sha kamar yadda Mama tace ita da Hydar da Suhima suka nufi b'angaren Asad tana gaba suna binta duk inda suka gifta aka zubewa a gaishe su har suka isa b'angaren nasa. Babu wanda zai dakatar da Mama ga shiga b'angaren dole kowa ya bata hanya ko yun?urin hakan ma ba'a yi ba a babban falon k'asa suka zauna Mama ta kalli Hydar tace, "Kira min shi a waya." Kiran wayar da Hydar yayi amma baya d'auka ya kalli Mama yace, "Allah yaja zamanin Mama baya d'auka." Ta kalli saman ta mik'e tace, "muje saman" ta fad'a tana nufar stairs d'in ta fara takawa tana hawa gabanta yana fad'uwa matuk'a amma haka ta d'aurewa zuciyata tana hawa saman.

Ita ta fara shiga falon ta ga Jidda a zaune tana kallon tv hannun ta rik'e da glass cup an zuba nono a ciki tana sha, kawai ganin Mama tayi a kanta ta d'ago ta kalle su ta mayar da hankalin ta kan TV kamar bata gansu ba sai kuma ta d'auki wayar ta tana dannawa. Kallon mamaki Mama take yi mata tace, "Jidda baki ganni bane?." Ta d'ago tare da k'ank'ance idanun ta tace, "Na ganki, jira nake kuyi sallama then sai na yi magana."

Mama ta kalli Hydar suma ita suke kallo ta kalli Jidda tace, "ke duk abinda kike ji dashi ki tabbatar kin ajjiye shi gefe ki san wacce take gaban ki." Wani irin kallo tayi mata akan idon Suhaima hakan ya faru ta zabura tayo inda take tace, "Mama kike yiwa wannan kallon?." Ta kalli Suhaima tace, "Zaki dake ni ne?."
"In na dake ki ya zakayi dani?."
"Wallahi sai kin kwana a cell" ta fad'a tana kurb'ar nono ta ajjige glass cup d'in akan table ta tashi tsaye.

Hydar yace, "Wai jidda me yake damun kine?." Ta kalle shi tace, "tambayi babar ku. Me yake damunta da zata shigo mana har nan babu neman izini balle sallama." Hydar ya zabura kamar zai dake ta Mama ta dakatar dashi ita kuma ta kalle shi tace, "me kake shirin yi?."

Zaiyi magana aka bud'e k'ofar da take falon aka fito duk suka kalli wajan suka had'a ido da Asad da ya fito waya na kunnen sa ganin Mama ya saka shi sauke wayar daga kunnen sa da sauri ya k'araso inda take ya duk'a har k'asa yace, "Barka da dare Mama."

Wani irin sanyi taji a zuciyarta ta lumshe ido ta sauke bayyananiyar ajiyar zuciya ta kalle shi tace, "Asad me yake damun ka kwana biyu?." Kansa ya saukar ya runtse ido yana jin sa wani iri daban yayi shiru bai amsa ba. A kan kujera ta zauna ya zauna a k'asa kusa da ita Hydar da Suhaima duk suka zauna a k'asa sab'anin Jidda da ta hard'e a kan kujera tana kallon su.

Ba ta Jidda take ba dalilin da ya saka batayi mata magana ba tace, "Ina tambayar ka kayi min shiru ka bani amsa." Asad yace, "Mamaaaa...." shiru yayi ya kasa k'arasawa Jidda da take zaune ta fashe da kukan munafurci.

Gabad'aya hankalin sa ya koma kanta ya juyo yana kallon ta tace, "Kamar ni Hydar zai ce zai daka, ina matsayin matar ka dan yana k'anin ka sai yace zai dake ni..?. Kenan nan gaba ma bawan gidan nan sai ya d'aga hannu ya dake ni tunda ka nuna musu bani da mahimmaci a wajan ka." Kallon Hydar yayi suka had'a ido ya kalle ta ya sake kallon sa da ido yake masa magana ya fahimta amma sai ya basar kamar bai gani ba domin haushin Asad d'in yake ji ba kad'an ba.

? ? ? ? "Ni zaka kalla Asad ba Hydar ba." Kallon Maman yayi kamar yadda tace zaiyi magana Jidda ta sake katse shi tace, "shikenan ni an wula?anta ni kenan a banza? Ina matsayin matar sarki uwar gidan sa uwar y'ay'an sa wani yayi yunk'urin dukana a zuba masa ido daidai kenan...?." Mama ta fusata tace, "Kee Jidda! Bana son shirmen banza kin san halina, ko Sadiya bata magana in ina magana balle ke."

Jidda tace, "Sai ita tak'i yi amma ni zanyi. My king ko a d'auki mataki akan Hydar ko kuma na bar gidan nan." Asad ya runtse ido ya kalli Hydar yayi shiru baiyi magana ba Mama tace, "Asad wai me yake damun ka? Kayi magana me ta baka kaci ka koma haka..?."
"Abinda kika bawa mai martaba yaci ya koma yadda yake shi na bashi yaci, yadda kika mayar dashi haka nima zan mayar dashi wannan ba damuwar ki bace ba. ku tashi ku fitar min daga b'angaren miji lokaci shiga turaka......" babu zato taji saukar mari a kuncin ta.

Suhaima ce a gabanta ta manta ma a falon wa take da kuma su waye a gabanta jikin tane kawai yake rawa jin yadda take fad'awa Mama maganar da tunda tazo duniya bata tab'a ji an fad'a mata irin ta ba.

Mik'ewa tsaye Asad yayi idanun sa a waje yana kallon Suhaima da take kallon Jidda sai kuma ta kalle shi ta duk'a tace, "ka gafarce ni bazan iya zuba ido ana zagin Mama ba dole na d'auki mataki, nasan kuma mai martaba yana girmama mahaifiyar sa dan na d'auki hukunci akan wacce taci zarafin ta bazai bani laifi ba."

Jidda da take dafe da kunci cikin mamaki dan bata d'auka hakan zai faru ba tace, "Ni kika mara Suhaima? Ina matsayin matar yayan ki, matar sarki, matar shugaban ki sama nake da kowa a gidan nan zaki d'auki hannu ki mare ni. My king kana gani kk?" Ta fad'a tana kallon Asad da yake kallon Suhaima baice komai ba.

"K'asa kike da Mama shiyasa na hukunta ki."
"Ko ita Maman sama nake da ita domin ita ta tako tazo inda nake ba nice nazo inda take ba, babu wanda ya fini a gidan nan koda kuwa itace!."

? ?? Shiru falon yayi ana jiran aga hukuncin da zai yanke dukkan su basuyi tsammani ba suka ga ya tsinkawa Suhaima mari abinda bai tab'a faruwa ba kenan tsahon rayuwar su. Mik'ewa Mama da Hydar sukayi ba shiri Mama ta kallli Hydar shima ya kalle ta suka kalli Suhaima da hawaye yake sakkowa daga idanun ta cikin bak'in ciki da k'unar rai. Hydar ya k'arasa inda yake yace, "Asad kana cikin halin ka? Mama ta zaga fa dan tayi mata hukunci sai ka dake ta?, kenan ka fifita ta akan Mama kenan?" Ya fad'a da alama ya manta matsayin da Asad yake dashi kallon Asad d'in da yake masa.

Asad ya kalle shi yace, "Matata take, kuma sama take da kowa a gidan nan, sau d'aya tak baka tab'a ganin k'annen Abba sun daki Mama ba dan bazan lamunci gani anyi a gaban idanuna na k'yale ba." Hydar da ya zuba masa ido shima shi yake kallo cikin mamaki da tsoro Hydar yake girgiza kai Jidda tace, "wannan hukuncin yayi mata kad'an ina so ka saka ayi hukunci kamar yadda za'a yiwa baiwa in ta aikata kuskure da tayi."

Mama ta matso kusa dashi cikin sanyin jiki ta juyo dashi da hannunta tana kallon sa shima kirr yana kallon idanun ta tace, "Asad anya kaine?" Ta fad'a tana d'ago kansa tana sake kallon idon sa ta tabbatar shine da gaske ba wani ba tace, "Meya same ka Asad? Wannan canjin daga ina yake haka?" Ta fad'a a tausashe tana kallon sa.
"Mama a gaban ki ta mari Jidda baki hanata ba bayan hakan ba daidai bane" sake kallon sa take jin abinda yace tana girgiza kai.

"Nifa my king kawai su sauka su bar wajan nan bana son ganin su, sannan ka saka a yiwa Suhaima hukunci indai kana sona kana qaunar zama dani!" Jidda ta fad'a tana kuka tana kallon sa suka had'a ido ya kalli Mama ya nuna musu hanya yace, "Mama ko zaku iya sauka?."

"What!" Hydar ya furta yana kallon sa da mamaki jin abinda yacewa Mama idanun sa k'asa kuma kamar koda yaushe. Kafin su gama mamaki suka ji ya kalli Suhaima yace, "Ki tabbatar da sai an miki bulala goma nan gaba in kika sake....." Sai ya dafe kansa kana ya cigaba yace, "zan miki hukuncin da bakiyi tunani ba."

Mama baki bud'e take kallon sa idanun ta sunyi ja sabida tashin hankali da tsoro hadi da al'ajabi da bugawar zuciya tace, "Asad kasan da wanda kake magana kuwa?." Ya runtse idanun sa ya dafe kai yace, "Na sani, na sani Mama! Don Allah ku barni kafin ku haukata ni bana son magana." Hydar ya sake kallon sa yace, "Asad kaine?." Cikin b'acin rai da fusata Asad yace, "Hydar i said out!" Ya fad'a da d'an k'arfi yana nuna musu hanya idanun sa a waje yana dafe kansa jin kamar zai fashe.

Ba shiri Hydar ya kama k'afadun Mama suka wuce Mama na kallon Asad shi kuma idanun sa a kulle hannun sa dafe da kansa suka fara sauka daga steps d'in, "Suhaima ki tabbatar sai kin karb'i hukuncin ki domin bazan yafe miki laifin da kika aikata ba." muryar Jidda ta katse su suka juyo dukkan su suka kalle ta suka cigaba da sauka ko wanne zuciyar sa cike da tashin hankali.


*Boom*=إ?=??=??


FitattuBiyar
Nana haleema
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*056.*

? ? ? ?? Mama bata san sun isa b'angaren ta ba sai gani tayi Hydar ya zaunar da ita a gefen gado ya kawo mata ruwa mai sanyi a kofi ya mik'a mata ba musu ta karb'a ta shanye ko zata daina jin zafin da yake tasowa daga zuciyar ta amma babu canji, cillar da kofin tayi ya tarwatse a wajan ta dafe kanta da hannunta jikin ta yana rawa sosai dan tunda take bata tab'a shiga tashin hankali makamancin wannan ba.

Zabura tayi ta kalli Suhaima tace, "Mik'o min wayata da sauri." Suhaima jikinta duk a mace har lokacin inda Asad ya mare ta zafi yake mata ta mik'a mata wayar hannun Mama na rawa ta kir? number Mum bata d'auka ba ta sake kira ba'a d'auka ba ta cillar da wayar a kan gado tana ji kamar tayi hauka sabida tashin hankalin da take ciki.

Hydar yace, "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalin ki kin sani ba halin Asad bane abinda ya aikata akwai abinda yake faruwa a cikin lamarin nan."
"Abinda yake faruwa ya wuce ta mallake shi?" Suhaima ta bashi amsa daga gefe idanun ta yana cikowa da hawaye.

? ? ? ? Da hannu Mama tayi musu alama da su bar mata d'akin Hydar ya fita Suhaima ta kwashe glass d'in da ya fashe sannan ta fita kowa zuciyar sa babu dad'i akan abinda ya faru. Kamar mahaukaciya haka Mama ta koma so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login