Showing 141001 words to 144000 words out of 216282 words

Chapter 48 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

Ya maimaita a fili yana kallon su har sukayi masa nisa bai d'auke idanun sa daga kansu ba, ransa yaji yayi mugun b'aci nan take abinda ya fito yi a sirrance ya fita daga ransa ya ya d'aga bak'in glass d'in motar yadda duk nacin ka baza ka gane waye a ciki ba ya juya motar ya bar unguwar yana ji zuciyar sa na tafasa gabad'aya komai ya tsaya masa jin kalmar duka bayan ance tana da ciki kuma.

? ? ?? Bayan sun koma aka yiwa Umma allura aka bata magani sai tayi bacci itama Raudan suka lallab'a ta Allah ya taimaka tayi baccin gidan ya zama shiru babu wanda yake magana kowa da nasa tunanin a zuciyar sa.

? Sai yamma Rauda ta farka jikinta yayi mata tsami ta tashi zaune babu kowa a d'akin ta kalli fuskar ta a mudubin d'akin fuskar ta ta kumbura sosai ga jini a idanun ta ya taru sabida marin da tasha a hannun Baba. Sakkowa tayi daga kan gadon amma sai ta kasa tsayuwa sabida k'afar ta bazata iya d'aukar ta ba tayi saurin dafa bango tana tafiya kanta ko d'ankwali zuwa d'akin Umma.

A falo ta tarar dasu har Umma suna zaune a gefen ta suna ta bata hak'uri suka hango Rauda tana tafiya tana layi kamar zata kifa, fuskar ta da suka a kunbure shine ya sake karya musu zuciya ta k'araso gaban Umma ta zube maganar ta bata fita sosai tace, "Umma dan Allah ki...." Umma ta runtse idanunta tace, "Ki tashi ki bani waje Rauda wallahil azim bana son ganin ki, bana son kallon fuskar ki ki tashi kafin na saka k'afa nayi ball dake a wajan nan." Yayar mu ta taso ta d'aga Rauda daga wajan tace, "Koma ki huta ranta a b'ace yake sosai bazata saurare ki ba."

Shigar da ita tayi d'aki ta zaunar da ita ta zauna itama a gefen ta tace, "Rauda waye ya miki ciki? Anas ne kowa?." Sai kawai ta kuma fashewa da kuka ta kifa kanta a kafad'ar Yayar mu tana kuka sosai ita kuma tana bubbuga bayanta a hankali tausayin ta na sake shiga jikinta dan su kam sun yadda da ita tunanin su fyad'e akayi mata ba yin kanta bane.

? ? ? ? Yaya Nafisa ta shigo da abinci da shayi mai zafi ta zauna tace, "Rauda karb'i shayi kisha sai kici abinci." Kai take girgizawa tace, "bazan iya sha ba, bazan iya ba. Dan Allah ku fad'awa Baba ya kashe ni bana son rayuwata nima."

Duk sai jikin su ya kuma yin sanyi suka dinga rarrashin ta amma baya aiki dan batayi shiru ba kuma bata ci komai ba. Wanka suka saka tayi da ruwa mai zafi sanda ta fito sai da suka tsorata da shatin bulalar jikinta duk bata da hasken fata amma fatar tayi ja sosai duk ta tashi wani wajan ya fashe.

Kaya ta saka tayi sallar la'asar a zaune bayan ta idar ta d'ora hannun ta akan cikinta tunawa da tana da ciki sai taji kamar ta had'd'iye zuciya ta mutu da bak'in cikin da take ji a ranta har gwara ma ace ta mutu ta huta kawai. Basu barta ita kad'ai ba dan zuciya zata iya d'aukar ta yiwa kanta illah.

Har magriba babu wacce ta tafi a cikin su bayan anyi sallah ne su Baba da Kawu Badamasi suka shigo aka kira kowa aka bada umarnin fito da Rauda. Suna rik'e da ita aka zaunar da ita a k'asa suma duk suna k'asa iyayen ne kawai a kan kujera. Kawu Badamasi yace, "Haba Adamu, wannan wanne irin hukunci ka yiwa wannan yarinyar? Kalli fuskar ta da idon ta yadda ya koma."

Shiru yayi suma kowa yayi shiru Kawu Badamasi ya kalle ta yace, "Rauda!." Ta d'ago a hankali ta kalle shi yace, "Subahanallah haka idon naki jini ya taru? Gaskiya baka kyauta ba duka ba hukunci bane." Shiru aka kuma yi ba'a amsa ba yace, "Rauda tsakanin ki da Allah cikin waye a jikin ki?, kinga maganar bikin akeyi ga wannan abin da ya taso a yanzu babu maganar aure dan ba'a aure da ciki. Cikin waye a jikin ki."

Shiru tayi ta kasa magana sai kuka Kawu Mansur yace, "ba kuka akace kiyi mana ba, tambaya ce guda d'aya kawai ki bamu amsa." Nan ma shiru batayi magana ba Baba ya fusata yace, "Kun gani ko? Bata jin ko wanne yare sai duka ku barni na b'alla ta in yaso sai tayi bayani." Kawu Mansur yace, "Dan Allah ka sakawa zuciyar ka salama, ka barmu zamu tambaye ta da kanmu."

"Rauda ke muke saurare cikin waye a jikin ki?." Nan ma shiru ba amsa sai kuka Kawu Badamasi? ya kuma cewa, "Ko shi Anas d'in ne yayi miki?." Ta girgiza kai alamun a'a tana kuka Baba ya fusata ya mik'e ya k'arasa inda take ya d'aga hannu zai dake ta yaji ance, "Dan Allah Baba ka bar dukan ta haka!." Cak ya tsaya jin muryar wanda ya sani a kwanakin baya bai sauke hannun ba ya juyo yana kallon inda yaji maganar kowa ya zubawa k'ofar ido ana kallon wanda yake tsaye cikin zallar al'ajabi da tsoro da kuma mamaki...........
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*069.*

? ? ? ?? A tsaye yake cak fuskar sa a bayyane duk da babu annuri a cikinta amma tayi haske sai shek'e take yi idanun sa akan inda Baba yake yana shirin dukan Rauda nan kawai yake kallo dan tunanin sa a wajan yake. sanye yake da manyan kaya na sakarai daga kallon aikin jikin su basai an fad'a ba kasan ba k'aramin mutum bane zaiyi wannan shigar sai wanda ya amsa suna basarake kuma mai abin hannu.

Kansa yayi nadin buzaye ya zagaye fuskar sa da hirami kalar kayan jikin sa takalmin k'afar sa irin aikin jikin kayan sa ne yana tsaye cak cikin nustuwa da ta game ko ina na jikin sa yana kallon su.

Dukkan su mik'ewa tsaye sukayi Baba ya juyo da sauri ya k'araso wajan yana jinjina yace, "Allah yaja zamanin mai martaba barka da zuwa, bismillah" ya fad'a yana bashi hanya alamun ya wuce shi kuwa Rauda kawai yake kallo dan yanayin ta ya bashi tsoro. "Barka da zuwa ranka ya dad'e" Kawu Badamasi ya fad'a yana kallon sa cikin girmamawa suke maganar.

Sai a sannan ya d'auke idon sa daga kanta ya murmusa kad'an Baba yace, "Ranka ya dad'e tsayuwa ba taka bace, ayi mana alfarma a zauna dan Allah." Ba musu ya taka har tsakiyar falon da takalmi a k'afar sa gujerar da ta kasance babba a ciki ya zauna, Baba zai zauna a k'asa yace, "Dan Allah Baba" ya fad'a yana nuna masa kan kujerar kusa dashi alamun ya zauna. Baba yace, "Wane mutum" ya fad'a yana zama a k'asa duk kowa ya zauna a kasa sai ahi kad'ai ne a akan kujera.

? ? ? ?? "Barka da zuwa ranka ya dad'e, da fatan mai martaba yazo lafiya?." Shiru ya d'an yi kafin yace, "Alhamdulillah, fatan bamu zo a lokacin da bai kamata ba."
"Ko wanne lokaci mai martaba yaso ziyara daidai ne a wajan mu, mai martaba ya ziyarce ka ma ai babban abin alfahari ne a gare mu baki d'aya" Kawu Mansur ya fad'a da girmamawa shima.

Kwarjinin sa ya cika falon haka khamshin sa gabad'aya matan tunda suka gaisa sun kasa cewa komai har basa son dagowa ma su kalle shi sabida kwarjinin da yake musu kallon sama sai ka shirya balle magana. Shiru ya ratsa falon shi ya rasa me zaice nauyi yake ji a zuciyar sa ya kasa furta komai su kuma jiran yayi masa suke yi.

Dak'yar ya iya had'a kalmar yace, "Ina neman afuwar ku dukka akan abubuwan da suka faru a baya, ina fatan za'a yafe ni." Baba yace, "Mai martaba da kansa yake neman afuwar mu? Mu su waye da har mai martaba guda zai mana laifi..? Allah yaja da ranka ai mu bamu isa mu rik'e mai martaba a zuciyar mu ba duk abinda ya faru mun d'auka k'addara ce kuma ta riga fata." Ya girgiza kai yana cize bakin sa yana kallon mutanen falon duka fuskokin su babu annuri ga Umma a zaune kamar mara lafiya sai yaji jikin sa ya sake jin sanyi.

Ya d'an jima kafin ya kuma cewa, "Baba ina neman alfarma a wajan ka." Baba ya gigice ya gyara zama yace, "Allah ya kara maka lafiya ai umarni kawai za'a bani amma ina mai martaba ina neman alfarma a waje na."
"Akwai ambulance a waje ina so za'a kaita asibiti" ya fad'a a sanyaye ba tare da ya kalli Baban ko ita Raudan ba.

Baba yace, "Umarni ne ba alfarma ba, duk abinda mai martaba yace an gama." Asad yayi shiru ya d'auki waya yana dannawa jim kad'an sai ga nurses guda biyu mata sun shigo falon suka zube a gaban sa suka ce, "Mun amsa kira ranka ya dad'e." Da hannu ya nuna musu Rauda jiki na rawa suka k'arasa inda take suka duk'a sukace, "Ranki ya dad'e sannu" tare suka kama Rauda suka fita da ita zuwa waje, suka sake dawowa aka rik'e Umma suka sake fita Yaya Ummi da Yaya Fariha suka bisu dan sunji dad'in zuwan da kodan Rauda ta samu kulawa.

Asad yaja numfashi ya lumshe ido ya buWe zuciyar sa na dukan tara tara yace, "Nasan zakuyi mamakin ganina a nan, a fara samar mata lafiya komai zai biyo baya. Alfarma a gare ku gabad'aya dan Allah a bar maganar a nan." Kowa mamaki ya bayyana akan zuciyar sa sai kallon kallo suke yi kowa tunanin sa ta yaya yasan maganar? Kenan daman ita ta kawo shi kome?.

Baba ya gyara zama yace, "Ranka ya dad'e abinda ya faru fa ita Raudan cikin....." da hanzari ya katse Baba yace, "Baba dan Allah wannan kalaman su daina fitowa daga bakin ka." Baba da mamaki yace, "Ranka ya dad'e bikin ta ya kasance saura sati biyu kawai, da wanne ido zan kalli shi wanda zata aura nace masa tayi cikin shege...?."
"Hasbunallahu wani'imal wakil!" ya furta yana dafe kansa ji yake kamar ya toshewa Baba baya son abinda yake furtawa ko kad'an akan cikin da ya kasance na halak wanda aka same shi da aure, ga kuma zancen wani banza da yake masa wanda bazai tab'a mallakar abinda ya mallaka ba har abada shine ya saka shi yin salati ba tare da ya shirya ba.

Jin hakan sai Baba yace, "Tuba nake ranka ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ka, na bar maganar sai ta samu lafiyar kamar yadda aka umarce ni." Kai Asad ya girgiza kai kafin ya kalli sauran ragowar matan yaga biyu sun ragu alamun sun bi su Umma sai ya dawo da kallon sa ga Baba yace, "Zan koma, amma zan dawo" ya fad'a yana mik'ewa tsaye duk sai suka mik'e shima har waje suka raka shi ana godiya ya shiga bayan mota ya sauke glass bayan ya shiga yace, "Baba duka ya k'are dan Allah" ya fad'a a tausahe yana kallon Baba.

"An gama ranka ya dad'e, Allah ya kiyaye hanya." Glass d'in ya d'aga aka ja motar suka bar wajan kowa yabi motar da kallo da mamaki a zuciyar dukkan su. Ciki suka koma Baba ya zauna Kawu Badamasi yace, "Adamu mai martaba da kansa yazo gidan nan ya ceci Rauda daga dukan da kake mata, ya akayi yasan abinda yake faruwa har yazo ya cece ta? Abubuwan da suka faru a baya tsakanin shi da gidan nan ban d'auka zai sake waiwayo ahlin mu gabad'aya. Meyasa yake jin haushi dan kana kiran cikin jikin Rauda na shege?? Anya kuwa ba......" Sai kuma kawu Badamasi yayi shiru yana jijjiga kai jin girman abinda zai fad'a da kamar wuya ya kasance.

Yayar Mu tace, "Abinda ya daure min kai kenan Kawu ya akayi yasan abinda yake faruwa? Bibiyar lamarin gidan nan yake ko me? In bibiya yake akan me to muda ba wata alaqa ce a tsakaninmu dashi ba?. Aure ne ya had'a kuma ya raba meyasa yazo a wannan lokacin har yake neman alfarma a haka duk da tarin matsayin da yake dashi?."

Kawu Mansur yace, "Gashi mun tabbatar da saki a tsakanin su har takardar tana hannun Yaya Adamu dukkan mu munga takardar sakin a lokacin me hakan yake nufi?." Baba ya sauke numfashi yace, "ni nama rasa bakin magana wallahi, amma mu jira ta samu lafiya itace zata warware mana komai. Babban tashin hankalina shine Anas."

"Mu bari zuwa gobe ai komai zai daidaita in yaso sai ayi maganar Anas daga baya." Baba ya kalli Yaya Shamsiyya yace, "Kira Ummi muji a wanne asibitin suke."
"Na kira su bayan fitar ka wai asibitin da Rauda ta kwanta lokacin da akayi mata aikin k'afa suka nufa."
Baba ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokacin kafin yace, "ku tashi ku wuce gida kuma anyi i'sha" ya fad'a suna tashi suka fita domin yin sallah.

? ? ? ? ?? Karb'ar gaggawa aka yiwa Rauda aka kwantar da ita nan da nan aka fara bata kulawa ta musamman wacce zatayi gaggawar taimakawa jikinta wajan dawowa daidai. Umma jinin tane ya hau itama aka saka mata ruwan da bp zaiyi k'asa nan da nan bacci ya kwashe su duka. Yaya fariha ta tafi gida Yaya Ummi ta yiwa mijin ta waya ta sanar dashi zata kwana ya kai y'ay'an ta gidan su wajan Inna.

Asad tun bayan da ya koma guest house shi kad'ai ya zauna ya zuciyar sa cike da tunanin abinda ya faru gabad'aya ya rasa abinda yake damun sa farin ciki yake ji ko akasin sa bai sani ba, waya ya d'auka ya kira Dr Yasir babu b'ata lokaci ya d'auka yace, "Ranka ya dad'e, Allah yaja zamanin ka an gama komai an basu kulawar gaggawa dukkan su sun sami bacci." Shiru yayi bai amsa ba na wani lokaci. Dr Yasir ya fahimci karin bayani yake so hakan ya saka yace, "Allah yaja zamanin mai martaba komai lafiya a b'angaren k'aramar, hatta abinda yake jikinta yana nan lafiya babu abinda ya same shi."

Sai a sannan ya sauke numfashi ya sauke wayar daga kunne sa ya ajjiye a gefe ya jingina da kujera yayi shiru yana kallon sama. Inda yasan ciki ne zai bayyana a abinda ya faru da bai bar hakan ta kasance ba duk da daman ba'a son ransa ba amma da yayi k'ok'arin rik'e kansa, k'aramin tsaki yaja tunawa da bikinta wai saura kwana sha hud'u a bayyane yace, "Bata da hankali ne." Sai kuma yayi murmushi tunawa da cikin sane fa a jikinta kuma silar sa dole a fasa auren ta da wani duk da ko babu cikin ma sai an fasa tunda matar sace, d'an dukan kansa yayi yana tunanin ta wacce hanya kuma zai bi ya cewa su Baba cikin sane a jikinta?.

Numfashi ya sauke ya kalli wayar sa yaga tana haske ganin mai kiran sai ya d'auka ya saka a kunne, "Okay good" abinda ya furta kenan ya sauke wayar daga kunne ya mik'e tsam ya fita drivern sa yaja suka fita daga gidan gabad'aya.

*&&&*

? ? ? ?? Jidda na zaune a b'angaren sa a falon sa na sa????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  ma duk ranta a b'ace yake hankalin ta kuma a tashe, ganin zaman bazai kai labari ba sai ta mik'e tana ta zagaye har ta fara jiyo takun sa ta juya ta ganshi ya shigo yana waya yana shigowa falon ya sauke wayar daga kunnen sa. Jidda ta matso kusa dashi tace, "My king ina kake zuwa a cikin kwanakin nan kai kad'ai? Ko dogarai baka d'auka fitar sirri kake yi kuma sai dare na kasa fahimta."

Kallonta yayi ya sakko da idanun sa ga cikin ta sai yaji wani iri a zuciyar sa ya d'auke kai baice mata komai ba ya wuceta zuwa d'aki, ta d'aga kafa zata biyo shi ya d'aga mata hannu ya girgiza yatsa d'aya dole taja ta tsaya shi kuma ya wuce zuwa d'akin sa ba tare da ya sake kallon ta ba.

Juyowa tayi ta sakko daga saman a guje ta fita zuwa b'angaren ta aka rufa mata baya masu rik'e alkyabbar ta gudun kar taja k'asa sai gudu suke sabida sauri take yi sosai.

Tana shiga b'angaren ta ta dakatar dasu ta shiga falo na biyu ta tarar da hasken gabad'aya a kashe ta kunna idanun ta ya fad'a cikin na Aliyu da yake a kan kujera yana kad'a k'afar sa, tsoro ya mamaye mata zuciya ta firgita ya kalleta ta k'asan idanu sai yayi murmushi ya mik'e tsaye yace, "Meye shirin ku na gaba akan Mama?." Baya take ja tana girgiza kai tace, "bamu da wani shiri."

Baki ya tab'e ya girgiza kai zuciyar sa nayi masa mugun ciwo yana cize bakin sa ya lumshe idanu ya buWe baice komai ba kawai ya fita ya bar mata falon ma gabad'aya. "Na shiga uku na ni Jidda me na jawowa kaina haka?" Ta fad'a zuciyar ta na bugawa domin ita kad'ai tasan hatsarin kasancewar Aliyu a cikin gidan nan ba k'aramin tashin hankali bane a gare ta.

"Mum!!" Ta furta da k'arfi tana zama jagwab akan kujera ta dafe kanta kawai sai ta fashe da kuka hankalin ta a matuk'ar tashe yake zuciyar ta karkarwa take yi sabida tsoro, kai take girgizawa tace, "dole nayi maganin sa da kaina, dole na kashe Aliyu bazan barshi ya zame min barazana a cikin gidan nan ba, dole naga bayan sa da kaina zan gudanar da wannan aikin" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki tana tunanin irin hanyar da zata bi dan ganin bayan Aliyu.

? ? ? A b'angaren Mama tana zaune tana waya ita kad'ai a bedroom d'inta tana fad'in, "Ina kake zuwa ne Asad? Kwana biyu kana fita babu wanda ya sani ina kake zuwa kai kad'ai?." Shiru tayi alamun yana bata amsa kana tace, "yadai kamata ka cigaba da kulawa bana son wata matsalar ta sake faruwa koda nan gaba."

Shiru tayi kafin ta datse wayar ta sauke numfashi tana jin farin ciki a ranta komai yana tafiya daidai sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login