Showing 93001 words to 96000 words out of 216282 words

Chapter 32 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

mata ba tun farko, bata so akayi auren tayi biyayya ta amincewa abinda na zab'a mata ga kuma abinda ya faru na kuma d'ora mata alhakin hakan."
"Ai babu komai kamar yadda kace k'addara ce babu wanda yake kauce mata duk inda kake sai ta bika ta same ka, mun karb'e ta hannu biyu in sha Allah nan gaba zamu ga alkhairin hakan. Ni sai nake ganin ko na tura ta gidan Yaya Bilki tayi iddar ta a can?."
"Da idda a kanta ne?" Baba ya fad'a yana kallon ta da mamaki.

Umma ta d'aga kai tace, "Akwai idda tun dawowar ta na fahimci hakan a tare da ita, ni burina ma Allah yasa ba ciki dan bana so wata alaqa ta sake had'a mu kar nan gaba suzo suce abinda ta haifa ba nasa bane, shiyasa na k'agu naga ta gama iddar hankalina zai fi kwanciya."

Murmushi Baba kawai yayi kafin yace, "basai taje ko ina ba ki barta tayi iddar a nan babu wanda k'addara ta wuce fad'awa kansa." Umma tace, "haka ne. Allah yasa mu dace." Baba ya amsa da amin bata jima sosai ta sakko k'asa.

*&&&*


? ? ? ? ? Washe gari su Asad suka tafi Madina aka kai Abba asibiti nan da nan aka karb'e shi aka fara k'ok'arin gano kan matsalar a sannan Asad ya bar Hydar da Uncle a wajan sa shi ya tafi hotel ya shirya cikin farar jallabiya ya saka huta fara k'arama a ciki ya d'ora hirami fari ya saka bak'ar alkyabba kamar yadda labarawan suke yi. Sak ya fito a balaraben Saudia ba b'ata lokaci mota tazo ta d'auke zuwa taron da aka gayyace shi.

Bai dawo da wuri ba dan an tattauna abubuwa da dama ciki harda son da suke ya dawo Madina da zaka amma ya nuna hakan bazai yu ba, maimakon ya koma hotel sai ya nufi asibitin wajan su Abba. Kamar can a ranar dai ba'a ce ga abinda yake damun Abba ba Asad yace bazai koma ba ya zauna nan suka wuce ziyarar Rauda.

Kwanan su biyu a madina amma shiru ba'a samu wani cigaba ba anyi iyakacin binciken da ya kamata amma ba'a ga wani ciwo ba dukkan su hankalin su ya tashi sosai. Asad yana zaune bayan an gama yi musu bayani ya dafe kansa ya kalli Hydar yace, "Hydar bazan bar Abba a nan ba zamu koma Nigeria dashi." Hydar yace, "Amma ranka ya dad'e da ka barshi a nan zai fi samu kula a akan can."

Uncle ma yace, "Nima a gani na ranka ya dad'e gwara zaman nan d'in zai fi samu kulawa akan can, amma hukuncin daka yanke shine daidai."
Asad ya shafa fuska sa kana yace, "muje dashi can" yana fad'a ya mik'e dukkan su babu wanda ya isa ya musa washe gashi jirgi ya d'auko su zuwa Nigeria.

A katafaran b'angaren da aka gina mai kyau da tsari aka sauke Abba kafin la'asar an had'a duk abinda Abba zai buk'ata a cikin gidan an fara bashi kulawa a cikin gidan. Asad yana zaune a falo bayan an gama kula da mai martaba Mama da Hajiya da Ammi suka shigo da sallama. Mik'ewa yayi yana amsawa suka shiga inda mai martaba yake bai bi bayan su ba Jim kad'an suka fito Hajiya tace, "Amma sai nake gani zaman sa a can zaifi samun kula a akan nan."

Asad yayi shiru bai amsa ba Ammi tace, "Gwara nan d'in yafi samun addu'a." Nan ma dai baiyi ba suka fita aka bar shi da Mama ta kalle shi tace, "meyasa bakayi shawara dani ba ka tawo dashi nan?." Ya d'aga ido ya kalle ta sai ya sunkuyar da kai tace, "dakai nake magana? meyasa?."

Kansa ya dafe kad'an kafin yace, "Please Mama" yana fad'a ya hau sama ba tare da yace komai ba domin haushin su dukkan su yake ji ya barta a wajan a tsaye a tana kallon sa. Mamaki ya kusa saka Mama ta zube a k'asa a wajan ta bishi da kallo cikin tsantsar tashin hankali amma sanin babu abinda zatayi ya saka ta fita zuciyar ta cike da tashin hankalin da bata san dalilin sa ba.


Bayan wasu kwanaki.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*054.*

? ? ? ?? Waya ce a hannun Mama tana juya ta kana kallon yanayin ta kasan tana cikin tunani domin fuskar ta ta bayyana hakan kallo d'aya zakayi mata ka fahimci akwai damuwa mai tarin yawa a tare da ita duk da tana k'ok'arin b'oyewa. Sake kallon fuskar wayar tayi ta danna video call ta kira Aliyu, ba jimawa aka d'auka fuskar sa ta bayyana a kai ta kalle shi tace, "Aliyu kana wacce k'asa ne?." Aliyu da yake zaune ya kalle ta yace, "Bahrain."
"Yaushe zaka dawo ne? Wannan wanne irin zama kake yi a wata k'asar bayan kasan ina buk'atar ka nan." Yace, "Mama zan dawo akwai abinda nake yi a nan d'in ne amma dana gama zan dawo nima nafi so na dawo nan d'in akwai dalilin zaman nan d'in." Yana bata amsa ta yanke kiran ta cillar da wayar a kan kujera ta dafe kai da duka hannayen ta.

"Asslamu alaikum" Hydar ya fad'a a sanyaye yana shigowa falon ya zauna a kusa da ita. A ciki ta amsa ya kalle ta yace, "Akwai damuwa a tare da mahaifiyata, ko zan iya sanin dalilin zuwan ta?." Ta furzar da iska ta jima a haka bata bashi amsa ba kafin ta d'ago tace, "Hydar Asad! Ya canja yanzu gabad'aya kamar bashi ba." Hydar ya girgiza kai yace, "Allah yaja da ran Mamana akwai wani abu da ya aikata ne?."

? ? ?? "Meye ma bai aikata ba Hydar? Asad yanzu baya shawara dani yake aiwatar da komai sai dai naji labari a bakin Sadiya ko Jidda, Sadiya da Jidda sai sun fara jin abu kafin ni naji meyasa yake neman canjawa lokaci d'aya?." Hydar ya girgiza kai yace, "Allah ya wuci zuciyar ki; kinfi kowa sanin halin Asad kece kika haife shi kika kuma raine shi kinfi kowa sanin halin sa a kan kowa a duniyar nan. Duk yadda akayi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yana da dalilin aikata abinda yake yi."

"Dalilin sa na banza da wofi, duk yadda kake tunanin Asad a baya yanzu ba haka yake ba. Wacece Sadiya da zata riga ni sanin wani abu daya shafe shi?."
"Allah ya wuci zuciyar ki, zan same shi da kaina nayi masa magana a kai in ma akwai wani abun da yake damun sa zan ji."
"Jeka maza yanzu, yamma ce yana b'angaren sa."
"A tashi lafiya" ya fad'a cikin girmamawa yana tafi ya fita direct ya wuce b'angaren Asad.

? ? ? ? Asad yana zaune hannun sa rik'e da waya yana dannawa Jidda ta fito daga d'akin sa sanye cikin riga da siket y'an kanti kanta babu d'ankwali tayi kyau sosai tana zuwa ta yiwa kanta mazauni a cinyar sa ta kwace wayar a hannun sa ta ajjiye a gefe ta had'a goshin su waje d'aya tana kallon idanun sa. Shima kallon nata yake yi kamar yadda take kallon sa; shidai kawai yasan zuciyar sa tana sonta a wannan lokacin amma bai san yaushe hakan ya samo asali ba.

Murmushi tayi masa shima ya samu kansa da mayar mata da martani khamshin bakin sa ya daki hancin ta ba shiri ta kai bakin ta kusa da nasa ta d'ora a hankali ta fara kissing d'insa slowly, bai hanata ba sai ma taya ta da yake yi hannun ta akan sajen fuskar sa tana shafa gashin tana sake rik'e fuskar tasa sosai. Kusan minti biyu suna a haka kafin ta zame bakin ta a hankali tayi dariya ta kwanta a k'irjin sa tace, "i love you my king."

Idanun sa ya lumshe ya bud'e su a kanta muryar sa can k'asa yace, "Love you too." Wani irin dad'i take ji yana ratsa jijiyoyin jikinta tayi farrr da idanun tana jin kanta a sama in ta tuna Asad da yake fizge-fizgen yanzu shine a hannun ta sai abinda tace masa yake yi.

Zatayi magana wayar sa ta fara yin k'ara, kallon screen d'in tayi taga Hydar yana yawo a kai taja tsaki ta danna ta kashe k'arar tana kallon sa bai hanata ba. Wata wayar ce ta sake shigowa ta sake ganin sunan sane ta d'auka ta saka a kunne Hydar yace, "Assalamu alaika, Ranka ya dad'e in an bani dama ina so na shigo mu tattauna akwai magana mai matuk'ar mahimmaci da zamu yi."

Jidda ta yatsine fuska tace, "Bashi da wannan lokacin, ka jira gobe kwa tattauna a fada." Hydar da mamaki yace, "Jidda ina yake?."
"Kar ka sake kirana Jidda, Fulani shine sunana. Gashi nan muna tare bashi da lokacin kane."
"What! Kin sanar dashi nine nake waya?."
"Shi ya bani na d'auka ai kaga ya fika sanin waye ya kira, kar ka takura mana yanzu please" tana gama fad'a ta yanke kiran ta ajjiye tana kallon sa kamar zai mata magana sai kuma taga ya fasa.

D'aga shi tayi shi kuma ya mik'e ya shiga d'akin da ya kasancewa d'akin karatu, da kallo ta bishi tayi dariya ta shiga d'aki da sauri hannun ta yana rawa ta lalubo waya ta dannawa Mum kira tana d'auka tace, "Mum aiki yana tafiya yadda ya kamata, Asad ya dawo hannuna Mum ko Mama sai yaga dama yake zuwa inda take balle wani Hydar."

Mum tayi dariyar farin ciki tace, "nasan wannan ranar zata zo Jidda na jima ina yi mata shiri mai kyau shiyasa da ta tashi zuwa tazo cikin dad'i da annushuwa. Kice yanzu Rabi ta zama y'ar kallo?."
"Bari kawai Mum, sai fa yaga dama ma zaije wajan ta duk kuma abinda nace ina so shi za'ayi koda ba daidai bane ba kuwa."
"Kar dai kiyi sake ina fad'a miki nasan babar sa sarai ta wuce tunanin ki. Babban burina ki samu ciki yanzu yadda zamu yak'e ta da makamai masu tarwatsa duniya."

Jidda ta zauna a gefen gado tace, "An kusa samu Mum." Mum tayi siririyar dariya tace, "Dana fi kowa farin ciki in hakan ta kasance, akwai tarin abubuwa dana shirya Jidda yanzu baki fara ganin komai ba ki d'auka ba'a fara komai na." Jidda zatayi magana Mum tace, "Ina zuwa Daddyn ku nayi min waya" tana fad'a Jidda ta yanke kiran tana murmushi burinta guda d'aya tal a duniya daman ta mallaki Asad kuma ta mallaka sai yadda tayi dashi ko Mama bata kulawa balle wasu kuma.

? ? ? Gaban tane ya fad'i tunawa da wani abu da ta binne tsoro ya fara shigar ta sai tayi saurin kawar da tuannin a bayyne tace, "Ta yaya zan bayyana?. Har abada bazai tab'a bayyana ba in sha Allah tunda ai Aliyun baya nan na tabbata bazai tab'a dawowa ba har abada."

? ?? Hydar jikin sa a matuk'ar sanyaye yake tafiya ana gaishe shi ma bai san ana yi ba ya wuce b'angaren da Abba yake ya samu d'akin daga shi sai Uncle a zaune likita yana yi masa allura an samu idanun sa suna bud'ewa cikin kwanakin kana fahimtar yayi bacci ko idanun sa biyu.

Likitan ya fita Hydar ya zauna ya kalli Abba da shima shi yake kallo sai ya sunkuyar da kai yace, "Uncle me yake damun Asad ne?." Uncle yace, "kaima ka kaga canje-canjen dana gani kenan ko?." Hydar ya sauke numfashi yace, "yau ni mai martaba ya saka Fulani ta d'auki waya tana cewa bashi da lokaci na....?, ni Hydar fa Uncle? Ashe akwai ranar da zaice bashi da lokacin Hydar Uncle?."

Uncle ya murmusa yace, "Itace babbar matsalar sa Hydar, matar sa kamar ta juyar masa da hankali komai nasa ya canja hatta yawan karatu da zikirin da yake yi ya daina sai yaga dama. In tak'aice maka labari sai mai martaba yaje wani taro ba tare dana sani ba sometimes sai ya d'auki Suhail bai d'auke ni ba. Ba k'aramin abu tayi masa ba shiyasa da ya tashi kama shi bai masa kamu ta sauk'i ba."

Hydar ya girgiza kai cikin damuwa mai tsanani yace, "Tabbas Uncle Jidda itace matsalar Asad nima nayi tunanin hakan domin itace take sake assasa komai, Duk qaunar Asad da Mama baya zuwa inda take sai yaga dama. Hmmm Dole mu taya shi da addu'a kafin abun yazo yafi k'arfin mu."

Murmushi sukaga Abba yayi a karo na farko tunda ya kwanta ciwo dukkanin su suka k'arasa inda yake da farin ciki Hydar yace, "Uncle murmushi naga yayi ko idanuna ne?." Yace, "Nima na gani ba kai kad'ai ba, Alhamdulillah lafiya tana samuwa tunda muka dawo Nigeria."

"Gaskiya na jima banga abinda ya faranta min rai kamarwannan cigaban da aka samu ba, Alhamdulillah." Kallon su suka ga yanayi suma shi suke kallo sai kuma suka ga ya lumshe idanun sa hakan ya saka suka bashi waje kar suje hayaniya ce tayi masa yawa.

Hydar wajan Mama ta wuce ya same ta a d'akin ta ita da Suhaima suna tattauna batun canjin da Asad ya samu ya shiga da sallama tun kafin ya k'araso ta tashi tace, "Ya kuka yi dashi?."

Hydar ya sunkuyar da kansa kana yace, "Ki gafarce ni Mama, matar mai martaba Fulani ta d'auki wayar sa tace bashi da lokacin da zai saurare mu gabad'ayan mu, maganar da nake yi yanzu ban ganshi ba shima bai ganni ba." Mama ta dafe kai tana fad'in, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, me yake shirin faruwa dani ne haka?." Ta fad'a kamar zata fad'i Suhaima tayi saurin tare ta tana fad'in, "Mama!."

Zaunar da ita sukayi ita da Hydar suka tsuguna a kusa da ita Hydar yace, "Allah ya sanyaya miki zuciya Mama, ina mai baki hak'uri a madadin sa in sha Allah komai zai dawo yadda kike so amma sai mun dage da addu'a sosai domin lamarin nasa ba mai sauk'i bane." Suhaima tace, "ita wacece da zata ce baza ka ganshi ba? Yaushe ta shigo gidan da zata fara yi mana mulkin mallaka....? Ina zuwa" tana fad'a ta tashi a fusace ta fita daga d'akin ta nufi b'angaren Jidda a zafafe.

? ? ? A bakin babban falon ta tarar da dogarai maza guda biyu tana isowa suka bata waje suna zubewa a k'asa bata kula su ba ta shiga babban falon ganin bata nan ta nufi na biyun, jakadiyar ta da wata baiwa sukayi saurin tare hanyar suka ce, "Allah ya wuci zuciyar Fulani ina mai baki hak'uri sanar dake cewa Zakanyar mai martaba tace kar mu bar kowa ya shiga ba tare da izini ba."
Da matuk'ar mamaki Suhaima ta girgiza kai a bayyane tace, "Zakanya!." D'aya ta duk'a tace, "kwarai da gaske ranki ya dad'e."

Suhaima tace, "baki gane wacece bane?." Jakadiyar tace, "na gane ki ranki ya dad'e ina bin umarnin shugaba ta ne." Suhaima taja dogon tsaki tace, "in kuna da k'arfin hanani shiga sai na gani" tana fad'a ta zagaye su ta shiga babu yadda zasu yi mata dole suka bita da kallo kawai.

? ? ? ? A falon kuwa Jidda na zaune tana waya cikin nishad'i tana dariya kawai taga Suhaima ta fad'o ta kalle ta ta d'aure fuska ta yanke wayar tace, "Lafiya Suhaima zaki shigo min falo ko sallama babu?."
"Meye matsalar kine da zaki hana Hydar ganin mai martaba?." Jidda tayi y'ar dariya tace, "Sabida ni zakanyar sace." Kallon mamaki take mata hakan ya saka Jidda tace, "Baki gane bane? Shi zaki ni kuma zakanyar sarki, ko waye ko kuma wacece matuk'ar banga damar ya ganshi bazai ganshi ba ciki harda ku ."

"Waye ya baki wannan matsayin?." Jidda ta mik'e tsaye kana tace, "mijina kuma uban yarana, shugaban ki kuma sarkin ki sannan yayan ki." Suhaima ta bita da kallo kafin tace, "ke yanzu har kina da wannan matsayin a wajan a ganin ki?."
"Ai ba a gani na bane ba Suhaima, a bayyane yake in kina musu ki gwada ki gani."
Suhaima tace, "Zanyi kuma baki isa ki hana ni ganin yayana ba dan baki da ko wanne matsayi a wajan sa face wacce Mama ta bashi matsayin ya aura badan yana so ba."

Tayi dariya harda tafa hannu tace, "Zaki ga matsayina da zarar kin gwada hakan kuwa, a nan zaki gane cewa Mama ta bashi ni kuma ya karb'a babu wanda ya isa ya kwace ni."

Suhaima ta harare ta tare da jan tsaki tana girgiza kai cike da jin tsanar Jiddan a zuciyar ta, Jidda kuma ta kira baiwar da tasan tana bakin k'ofa. Da sauri ta shigo jiki na rawa ta zube tace, "Allah yaja zamanin shugabata, Allah ya kare ki Allah ya taimake ki ya rufa miki asiri."
Jidda tace, "ta wacce hanya kika bari Suhaima ta shigo min falo bayan na gargad'e ki game da hakan?."

Jikin ta rawa yake sosai tace, "Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake, kaina bisa wuyana ki gafarce ni. Na sanar da ita umarnin ki tayi watsi dashi ta shigo bazan iya hanata ba." Jidda tace, "Zaki iya rabuwa da aikin kenan."
"Allah ya wuci zuciyar uwar gidan mai martaba, afuwa nake nema a wajan ki ki yafe ni banyi dan na b'ata miki rai ba."

Jidda ta kalli Suhaima da take tsaye tana kallon ta ta kalli baiwar tace, "Daga yau ko Fulani Mama ce tazo indai nace kar a bar kowa kika sake kika bari ta shigo a bakin aikin ki, kuma sai na saka an miki dukan tsiya kin kuma share turke.......!"
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*055.*

? ? ? ?? Ba iya Suhaima kad'ai ba hatta ita kanta hadimar sai da gaban ta ya fad'i ta zaro idanu har tana had'a ido da Jidda ba tare da tasan ta aikata hakan ba sai dan tsabar gigitar da kalaman Jidda suka jefa ta. "Kee! D'auke idanun ki cikin nawa" ta fad'a cikin tsawa ba shiri ta kai idon ta k'asa tana raba ido sabida tsoro jikin ta har rawa yake yi.

Suhaima da ta k'ame a wajan tana kallon Jidda cikin d'ibum mamaki ta tab'e baki tace, "Ko mijin ki bai isa ya hana Mama shigowa nan ba balle ke karan kad'a miya matar cushe, ke bama wannan b'angaren ba ko wanne b'angare na gidan nan babu wanda ya isa ya yiwa Mama iyaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login