Showing 3001 words to 6000 words out of 216282 words

Chapter 2 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

yafe mana dan Allah kuyi mana rai, wallahi zaman gidan yari babu dad'i dan Allah ku tallafa mana daga yau baza mu sake irin wannan kuskuren ba" D'aya ya fad'a yana kallon su kamar zai zubar da hawaye.

D'an sandan yace, "yi mana shiru; k'aramin yaro ne kai ko kuma baka da hankali da za'a saka ka wannan d'anyen aikin kayi? Zaku girbe abinda kuka shuka gobe za'a tura case d'in ku kotu zaku gane baku da wayo, ku tashi muje" ya fad'a da tsaya ba shiri suka tashi suka tasa su a gaba suka fita.

Sai a sannan Asad ya lumshe idanun sa ya bud'e yace, "Mama za'a a kaita asibiti." Umma tace, "Bama buk'ata na fad'a muku, abinda muke so a gare ka dan girman Allah ka janye maganar auren Rauda tunda ba itace mace ta farko a duniya ba. ban san dalilin ka na cewa zaka aure ta ba amma ni jiki na yana bani akwai dalilin ka nayin hakan domin ruwa ba sa'an kwando bane. In kana so za'a iya kawo maka mata d'ari koda dga k'asar larabawa ne in badan kana da wata manufa ba meyasa zakace sai ita?. Tunda ka furta maganar nan muke ganin tashin hankalin da bamu tab'a gani ba tunda muke har ya kawo da neman rayuwar ta akan abinda bata furta ta amince bama, dan ni nasan a akan ka akazo kashe ta in kuma tace ta amince kenan a ranar sai an k'ona ta da ranta kenan. Ina rok'on ka dan Allah ku janye maganar nan a bar Rauda ta huta da ranta da kuma lafiyar ta, bana son rasa ta dan Allah ka janye maganar nan a bar mu ji da talaucin mu" Umma ta fad'a tana hawaye tana kallon Asad.

Nan take jikin Asad yayi mugun sanyi ya kalli Hydar shima ya kalle shi kafin suyi magana Baba yace, "Me kike cewa haka? Kin manta k'addara ne ko kin manta hukuncin Allah akan bayin sa?." Umma ta kalli Baba tace, "nidai a bar maganar kawai tunda ai ba ita kad'ai ce mace ba. Baka nan mahaifiyar sa tazo in kaji irin maganar da ta fad'a da ikirarin da tayi akan abinda zata yiwa Rauda in ta auri d'anta baza kayi sha'awar aura masa kazar gidan nan ba balle kuma ita. Kud'i ko mulki baya gaban mu mutunci da zaman lafiya muke nema, zamu rike kan mu suma su rik'e kansu kafin aje ko ina gashi an fara turowa a kashe ta, kisa fa kamar a film!, maganin kada ayi kada a fara gwara kowa yayi hak'uri daman daidai ruwa daidai tsaki" ta fad'a tana kallon Baba tana zubar hawaye har lokacin.

Hydar yace, "kiyi hak'uri Mama hakan bazai sake faruwa ba in sha Allah; ba'a kyauta muku ba na sani, badan Allah ya kawo mu ba da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, amma ki tuna duk abinda ya faru da Rauda Allah ya rubuta zai faru da ita tun kafin tazo duniya babu wanda zai hana faruwar sa, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai samu Rauda in sha Allah." Inna tace, "Gwara dai a bar maganar kar muma a biyo ta kanmu nan gaba, tunda gashi har suka shigo cikin gidan bamu sani ba, in ma gidan ne ba'a so mu zauna sai mu tattara kayan mu mu tafi daman ba namu bane aro aka bamu."

Asad ya dafe kansa yace, "kuyi hak'uri dan Allah duka" ya furta a sanyaye domin jikin sa ya gama yin sanyi gabad'aya. Rahma tace, "Kayi hak'uri mudai a bar maganar auren kawai tunda abin yazo da neman rayuwar Anty Rauda akan auren da in tayi ba rahama za'ayi mata ba, gwara ayi hak'uri a huta domin rai yafi komai a duniyar nan." Asad zaiyi magana Umma tace, "Dan Allah kayi hak'uri a hak'ura kawai maganar nan ta k'are a daren nan dukkan mu mu huta, mun gode da alkhairin ka a gare mu; k'afarta ta ma a barta a haka tunda tana tafiya mun gode Allah wasu ma yanke k'afar ake gabad'aya, gidan nan kuma zamu tashi mu koma namu tunda abin yazo da haka."

Asad yace, "Shikenan Mama karki damu. Amma ku zauna nan har a gama aikin gidan, lafiyar ta kuma za'a cigaba da nema mata kamar yadda aka fara" ya furta cikin muryar sa ta koda yaushe da take a raunane amma ta lokacin har ta ninka na baya. Hydar yace, "kuyi zaman ku a nan babu wanda zai kuma takura muku, sannan in zaku kulle k'ofar gidan nan a dinga duba ko ina sabida wad'annan sun shigo ne kafin a kulle gidan dasu aka kulle, za kuma ayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata. Zamu kawo security da zasu dinga kula da lafiyar ku in sha Allah."

Baba yace, "babu komai Hydar mun gode Allah ya saka da alkhairi, muje na raka ku." ya fad'a yana yin gaba Hydar ya tsaya yace, "Tana buk'atar ganin likita." Umma tace, "mun yafe dan Allah kuje kawai." Baba yayi gaba suka biyo shi a baya dan babu yadda zasuyi.

A jikin mota suka tsaya Baba ya kalli Asad yace, "kayi hak'uri da abinda suka ce ransu ne a b'ace da kuma tsoro kaga hakan bata tab'a faruwa damu ba, a film ma muke ganin ana zuwa gidan mutane kisa bamu tab'a gani a gaske ba balle mu kawo hakan zai zo kanmu." Hydar yace, "Suna da gaskiya ba'a kyauta ba gabad'aya an kuma aikata babban laifi amma zamuyi maganin abun in sha Allah. Ka koma gida dare yanayi" ya fad'a yana bud'e tasa motar ya shiga Baba ya juya ya koma gida ya kulle gidan.


Asad ya kasa motsin kirki ya hard'e hannayen sa k'irjin sa ya sunkuyar dakai yana kallon k'asa jikin sa yana ji kamar ana zare masa duk wani kuzarin da yake tare dashi, numfashi ya fesar ya kalli gidan ya lumshe ido yaso ya ganta ko zaiji dad'in zuciyar sa amma mutanen gidan basu bashi had'in kan faruwar hakan ba, baki ya jige ya mik'e daga jikin motar ya shiga mota yaja ya bar k'ofar gidan jikin sa a mace sosai.

A falon ya sake tarar dasu Baba ya kalle su yace, "kuje ku kwanta mana kowa ya kwantar da hankalin sa komai ya wuce." Umma ta shiga d'akin da Rauda take Baba yabi bayan ta suma duka suka shigo suka ganta a zaune har lokacin bata dawo daidai ba sai tari take idon ta yayi ja sosai.

Umma ta k'arasa ta zauna kusa da ita tace, "Ya jikin naki Rauda? Ya kike jin wuyan naki?." Rauda tana rik'e da wuyan ta har lokacin idanun ta ruwa yake yi ta kasa cewa komai.
Baba yace, "Ki barta ta huta dan Allah." Umma tace, "ta yaya zan iya tafiya na barta bayan ga halin da take ciki? Bazan je ba gaskiya a nan zan kwana kusa da ita."

Ya kalli Inna da Rahma yace, "kuje ku kwanta dare yayi, ke Ummulkhairi kema kwanta gobe kina da makaranta." Juyawa sukayi suka fita Ummulkhairi ta kwanta Umma na zaune kusa da Rauda da take sauke numfashi tace, "Sannu Rauda, Allah ya bi miki hakkin ki. Abinda muke gani a film shine yau yazo har gidan mu, Allah ya kare gaba." Baba yace, "ki ta magana kamar wata wacce bata san k'addara ba, a gaban yaran nan kike dinga wasu maganganu marasa dad'i duk d'awainiyar da suke damu baki gani ba."
"Ina ruwana da wata d'awainiyar da suke damu? Ni na rok'e su nace kuzo kuyi d'awainiya damu ko su suka saka kansu?. Daman d'awainiya da Rauda a ka'ida a kansu yake tunda sune suka buge ta har ta samu matsalar k'afa, hakkin sune su kula da lafiyar ta har ta samu sauk'i. In sun ga dama su daina d'awainiyar da ita sai me su suka jiyo."
"To duk bak'in cikin ki dai sai Rauda ta shiga gidan sarauta da izinin Allah."

Baki sake Umma take kallon sa cikin mamaki tace, "Au wai duk abinda ya faru kaii baka cire rai da auran Rauda da yaron nan ba? Har gida fa aka aiko a kashe ta ko minti biyar ba'a yi ba duk baka gani ba idanun ka ya rufe akan kud'i?." Baba yace, "Kina da tabbacin sune suka aiko?."
"In ba su bane su waye?."
"Nida ke bamu da masaniya a kai dan haka baza mu yanke hukunci ba."
"Baza ka yanke ba dai Malam; amma su kansu sun san daga gidan su aka aiko a kashe ta, yaje can ya nemi wata ya aura amma ba Rauda ba in Allah ya amince."

Baba baice mata komai ya fita daga d'akin itama ba tace ba tana ta kallon Rauda da take a firgice har lokacin bata dawo daidai ba.

B'angaren Asad a sanyaye yake jan motar kamar baya son tafiyar har ya isa gida lokacin k'arshe sha biyu na dare ta kusa ya faka motar direct ya wuce apartment d'in Mama duk da dare yayi.? Bai same ta a falo ba ya wuce k'aramin falo ya ganta a zaune tana kad'a k'afa hankalin ta na kan agogo da alama akwai abinda take jira. motsin da taji ya saka ta juyo tana kallon sa har ya k'araso sai ga Hydar a bayan sa ta bisu da kallo har suka k'araso. Idanun sa a raunace ya zube a k'asa ya kalle ta yace, "Mama meyasa? Kisa fa Mama!" Ya fad'a yana kallon ta.
Gaban ta ya fad'i jin abinda ya ambata ta bisu da kallo tace, "ban gane kisa ba?." Hydar yace, "kashe Rauda da aka saka ayi na tabbatar kuma da sanin Mama Mum ta aika ayi."

Mik'ewa tsaye tayi tana binsu da kallo tace, "an kashe ta d'in ne?." Hydar ya kalli Asad ya kalle ta yace, "Yanzu da gaske da saka hannun Mahaifiyar mu a cikin wannan aikin?."
"Na fad'a masa na tsane ta bana sonta zan iya yin komai wajan ganin na raba su, meyasa yak'i ji ya nace sai ita?."
"Kisa fa Mama!."
"Bama ita kad'ai ba kaf dangin ta zan iya sakawa a kashe matuk'ar Asad bai fita daga sabgar ta ba, bana sonta bana k'aunar ta."

Asad ya kalle ta yace, "Da an kashe ta fa?."
"Dana kashe banza da wofi dan basu da abinda zasu d'auki fansar abinda nayi musu" ta fad'a tana kallon sa.
"Allah fa?" Hydar ya fad'a yana kallon ta ransa a b'ace amma bashi da ikon bayyanawa.

Shiru tayi Hydar zai kuma magana Asad ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kafin yayi magana ta riga shi tace, "Asad bana sonta, bana qaunar ta Asad, baka tab'a yi min musu akan komai nace bana so kana bari amma a kanta kake musu dani har kake cemin kai ita kake so. Ya kake so nayi Asad? Bana sonta bana k'aunar ta ko kad'an bana so ta rabe ka, Jidda nake so ka aura ba ita ba" ta fad'a da zallar b'acin rai tana kallon sa

Asad yayi shiru yana kallon ta kafin ya sauke numfashi yace, "Mamana tana so na rabu da ita?." D'ago kai tayi ta kalle shi ta k'araso kusa dashi ta rik'e hannun sa tace, "Shine farin cikina, shine kwanciyar hankali na da nata kwanciyar hankalin." Asad ya numfasa yace, "Shikenan Mama, Zan rabu da ita amma ina neman alfarma guda d'aya." Mama ta fad'ad'a murmushi ta goge idanun ta da sukayi ja tana kallon sa tace, "Fad'i ko meye zan amince maka indai zaka rabu da ita."
"Zan yi sabida Mamana kawai. Ina so Mama ta barni na cigaba da samar mata da lafiya komai zan mata na taimako kar tace komai akai; ni kuma zan cire ta a raina zan auri Jidda zab'in mahaifiyata" ya k'arasa fad'a yana kallon ta kafin ya sunkuyar da kanta.

Da sauri tayi hugging d'in sa cikin jin dad'i tace, "Na amince Asad, na amince, Allah ya maka albarka." Numfashi ya sauke ya kalli Hydar da yake gefen sa yace, "Amin Mamana, zan iya hak'ura da komai akan farin cikin mahaifiyata." Ta bar jikin sa tana murmushi tana kallon sa sai ya murmusa kad'an yace, "Lokacin Hutum mama ne ko zata iya hutawa?" ya fad'a yana kallon ta fuska a sake.

Kai ta girgiza ta juya tana tafiya kafin ta juyo ta kalle shi tace, "Kar ka canja abinda kace Asad, nasan ka baka sab'a alqawari ka tabbatar da maganar ka." Kai ya girgiza mata alamun to kafin ta shiga ciki shi kuma ya mik'e ya wuce ya bar Hydar a tsaye kafin ya biyo bayan sa.

Gidan tsitt sai sautin tsuntsaye da yake tashi a gidan da motsin dokuna da kukan dawisu suka wuce zuwa apartment d'in su, a bud'e suka same shi hakan ya tabbatar musu da Aliyu yana nan basu bi ta kansa ba Asad ya shiga d'aki Hydar yabi bayan sa yace, "Me ka aikata?." Ya juyo ya kalle shi amma bai tanka masa ba Hydar yace, "meyasa kace ka barta Asad? Ka manta itace wacce kake so kake burin aure meyasa zaka ce ka fasa?. Indai zaka biyewa Mama baza ka tab'a samun abinda kake so ba a duniya."
"Hydar ban tab'a ce maka ina so na aure ta ba, then zan iya barin kome nake so akan Mama u know dis."

Hydar zaiyi magana yace, "Hydar zan barta kodan ta tsira da rayuwar ta akan ina sonta bazan bari ta rasa rayuwarta sabida ni ba,kana jin mai Mama tace a kanta why zan saka rayuwar ta cikin hatsari sabida ni?, indai da gaske ina sonta Hydar barin ta shine abinda yafi min alkhairi" ya fad'a yana jawo drawer ya d'auko passports d'insu Rauda yace, "Please a siyo min ticket ina so ayi mata aikin nan immediately" yana fad'a ya shiga toilet bai kuma kallon Hydar ba.

Hydar ya fita jikin sa a sanyaye yana girgiza kai domin yasan daman Mama zata iya galaaba akan Asad amma ya kuma ci alwashin matuk'ar yana raye Asad bazai rasa Rauda ba sai ya mallake ta tunda yana sonta.


Asad kuwa bayan ya kwanta duk sai yaji ya kasa nutsuwa maganar Umman Rauda da maganar Mama nayi masa yawo a cikin kansa sun hana shi sukuni gabad'aya, bai tabbatar haka yake son Rauda ba sai? a lokacin da ya furta zai barta nan yake jin wani abu na tasowa daga zuciyar sa yana taruwa a idanun sa da tsakiyar kansa ya cure waje d'aya.

Bai san haka yake k'aunar ta ba sai yanzu da ya barta, bai san haka ta mamaye ko ina na jikin sa cikin lokaci kad'an ba sai yanzu da ya furta ya barta bai san soyayyar ta tayi masa mugun kamu ba sai yanzu da ya barta. Ya zama dole ya hak'ura kodan mugun nufin Mama a kanta tsaf zata iya sakawa a kashe ta tunda bata sonta, hak'ura da ita shine yafi masa alkhairi tunda bazai iya jurar ta rasa ranta ba.


Numfashi ya fesar ya juya ya kwanta yana jin zuciyar sa na bugawa ya runtse idanun sa yana jin zafi tun daga cikin kansa har cikin idanun sa yake jin yaji da rad'ad'i na shiga cikin su zuciyar sa kuwa kamar zata fashe a wannan lokacin.
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*028.*

Har safiya Rauda bata dawo daidai ba idanun ta har lokacin akwai ja sosai a idon ta har lokacin wuyan ta ciwo yake mata ga shatar igiya nan a ciki kuma ji take kamar an rik'e mata mak'ogwaro, firgici da tsoro da fargabar jiya bata sake ta ba sukuku take ko magana ta kasa sai binsu da ido kawai da take yi kamar wacce aljanu suka shafa, bata tab'a tunanin tsintar kanta a cikin makamancin wannan yanayi ba shiyasa take yin komai a sanyaye. Dukkun su suna d'akin da take har su Inna an kawo mata shayi mai madara da biredi mai yanka-yanka tana ci a hankali.

Yaya Ummi ce ta shigo da Yaya Shamsiyya da babbar Yayar su wacce suke kira Yayar mu suka shigo a tare kamar gida d'aya suke, Umma ta amsa sallamar ta kalle su tace, "Kamar a gida d'aya kuke?." Dariya Yaya Ummi tayi tace, "a tare duka muka sauka daga mota kamar had'in baki. Ina kwana Inna, Umma ina kwana" ta fad'a a tare tana kallon su. A tare suka amsa suma suka gaishe su kafin Yaya Shamsiyya tace, "ita kuma me ya same ta haka?." Rahma tace, "Bari Yaya Shamsiyya jiya shigowa akayi da daddare za'a kashe ta."

Yayar mu tace, "Kamar ya za'a kashe ta kamar a film?." Rahma tace, "wallahi da gaske muke badan Allah ya tak'aita ba da yanzu sai dai kuzo jana'iza domin har sun shak'e ta; kalli wuyan ta ma zaki ga shatar igiya."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" suka fad'a a tare suna yo inda Rauda take zaune tana shan tea a hankali.
Yaya Shamsiyya tace, "Su waye su d'in to? Me tayi musu? Ya akayi shigo gidan nan?." Umma tace, "turo su akayi su kashe ta tun kafin mu kulle gidan suka shigo aka kulle dasu, badan Allah ya kiyaye ba da yanzu wata k'ila an kaita kushewa."

Yayar mu tace, "To wa Rauda take dashi da zai turo a kashe ta?, bama y'an fashi bane ba kenan turo su akayi kawai dan suga bayan ta, waye ya turo ita da ba y'ar siyasa ba?. Amma dai an kama su ko?." Yaya Ummi tace, "Abinda yake raina kenan; wa Rauda take dashi mak'iyi da zai nemi kashe ta har haka? Me take dashi a duniya?." Umma ta tabe baki tace, "hmmm badai d'an sarkin Katagum ya furta zai aure ta ba; kar ku manta kuma shine mai jiran gado ko yanzu mahaifin sa zai iya murabus ya bashi sarauta shiyasa aka fara neman rayuwar ta sabida kawai ya furta ita yake so."


Yaya Shamsiyya tace, "ikon Allah sai kallo, daga cewa kana so sai a fara yunk'urin kisa? Sai kace wacce d'an sarki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login