Showing 117001 words to 120000 words out of 216282 words

Chapter 40 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

Sadiya, kin yaudare ni kinyi amfani da yarda ta a gare ki kin ci amanata. Jira nake nayi setling komai zan dawo gare ki, sai kin yabawa aya zak'inta keda y'arki. Ta dalilin ki naje neman alfarma wajan k'ananu mutane, kaiiii!" Ta fad'a tana sake dafe kanta ji take kamar zai fashe sabida abinda take ji a cikin sa.

In badan neman taimako ba me zai kaita wajan su? Har su nemi fad'a mata magana sannan kuma suce wai ta dawo da daddare dan kawai sun raina mata hankali. Dogon tsaki taja ta tashi da sauri ta d'auki ruwan sanyi tana sha tana zubawa jikin ta dan ji take tiririn zuciyar ta na tab'a fatar ta.

D'akin da Hydar yake ta shiga ta same shi a yadda yake a kwance kamar gawa ta cize bakin ta tace, "Aliyu shine babba baya nan ko samun sa waya bana yi yanzu, Asad da nake da buri a kansa ya watsar dani an raba mu dashi dani da babu duka d'aya a wajan sa" ta matsa kusa da Hydar ta dafa kansa tace, "Hydar da yake taimaka min a ko wanne lokaci yake k'aunar ganin ya bani farin ciki shima gashi a kwance dashi da gawa duka d'aya.? Gaskiyar Hajiya ne da tace ina amfanin maza ukun da nake tak'ama dasu...? Tabbas babu amfani. Har gwara su masu mata da yawa dan da ace nice da matan dana tura su wani abun nayi wani abun, ko basuyi wani abun ba zasuyi shawara" ta fad'a hawaye na zubo mata daga idanun ta.

"Allah na ro?e ka ka bawa Hydar lafiya, ka dawo min da Aliyu gida ya bar banzayen dabi'un sa yayi hankali, ka karkato da hankali Asad kaina duk abinda aka yi masa ka karya shi ya Allah ka bashi ikon dawowa gare ni. Mijina ka bashi lafiya ka tashi k'afadunsa; tabbas da yana da lafiya abubuwa baza suyi min yawa haka ba, Allah ka dube ni badan halayya ta ba" ta fad'a tana kuka sosai mai tsuma zuciya nan take zazzaSi ya rufar mata ta lallab'a ta fita ta koma d'aki tayi lamo akan gado bata da abokin shawara a kusa balle ta fad'a masa abinda yake zuciyar ta ko zata ji dad'i.

Idanun ta ta d'aga nan tayi k'aro da k'aton hoton su su uku ranar da Asad yayi shagalin nad'in sarautar sa yana tsakiya Hydar yana dama Aliyu yana haggu dukkan su sunyi murmushi ba sunyi bala'in kyau. Murmushin itama take tana hawaye zuciyar ta na azalzalzalar ta akan dole ma ta bazama nemawa y'ay'an ta magani koda zata rasa ranta.

? ? Ana idar da sallar i'sha Mama ta saka Suhaima a gaba sai wajan mota suka shiga aka tayar da motar zuwa gidan su Rauda. Motar na fita daga gate d'in farko kafin yaje na biyun wani dogari da yake tsaye ya d'auki waya ya shiga wani k'aramin d'aki da yake wajan ya danna wayar ya saka a kunne ya d'an yi jimm kafin yace, "Ranki ya dad'e an gama komai, nan da wasu mintina motar bazata sarrafu a hannun ta ba, zata kwace ni ta daki wani abun zasu mutu dukkan su."

Murmushi wacce ake yin wayar da ita tayi tace, "Godiya nake, zaka ga kud'in ka kamar yadda nace maka." Yayi murmushi yace, "Nima godiya nake ranki ya dad'e." Ya yanke wayar yana dariya yace, "Kodan wula?ancin matar nan ai nayi abinda zata mutu, bata d'auki kowa da daraja ba gwara ta mutu ma huta da k'yara da hantara."

? ? ?? Su Mama kuwa k'ofar gidan su Rauda suka tsaya daidai lokacin Baba yana niyar shiga ganin mota babba kamar wannan ta tsaya ya saka shi ya tsaya shima dan Umma ta sanar dashi komai yana ganin motar abinda yazo ransa kenan,? Suhaima ce ta bud'e gaban motar ta fito ta zaga ta bud'e maman ta baya ta kalle ta tace, "Mama mun zo." Shiru Mama tayi bata amsa ba Suhaima tace, "Sai da nace Mama ki zauna baki da lafiya amma kika ki."

Mama ta d'an yatsine fuska tace, "Dan Allah jeki kiyi magana dasu ta fito muje." Suhaima ta kulle motar ta kalli cikin gidan taga Baba a tsaye ta k'arasa inda yake tace, "sannu." Yace, "yauwa. Fulanin ce a mota?." Suhaima tace, "eh" ta bashi amsa a tak'aice yace, "to bara na turo Rauda" ya fad'a muryar sa har rawa take ya shiga ciki ita kuma ta tsaya tana jiran sa.

Kamar an cillo shi haka suka ganshi a falon Rauda na raka'ar k'arshe a sallah ya kalli Umma yace, "Ga Fulanin tazo tana waje tana jiran Rauda a mota taje su tafi." Umma ta kalle shi tace, "Shine kake rawar jiki haka Malam? Sallah take yi to." Ya kalli Rauda da take zaman tayya yace, "kiyi ki idar kar ki barsu suna jiran ki." A wannan lokacin Rauda tayi sallama yace, "Maza tashi kije ku tafi ki raka su ki dawo."

Rauda kamar zata yi kuka ta kalli Umma ta dawo da kallon ta ga Baba tace, "Baba yanzu kana goyan bayan na raka su?." Baba yace, "kamar ya ina goyan baya?, zaki tashi kije ko sai nayi ball dake?." Rauda hawaye ya sakko mata ta kalli Umma da take kallon ta itama tace, "Umma bakwa jin tsoro in na bisu su kaini wani wajan da zasu kashe ni? Kun manta matar nan bata sona meyasa zaku ce na bisu?."

Umma zatayi magana Baba yace, "Tashi ki wuce." Babu yadda ta iya tana hawaye ta fita da hijjabin da tayi sallah ta fita zuwa k'ofar gidan Suhaima na ganin ta sai tayi murmushi ta wuce gaban motar ta shiga ta lek'o ta taga tace, "Shigo nan." Rauda jikin ta a sanyaye ta share idanun ta ta isa gaban motar ta shiga suka d'auki hanya.

Tafiya sukayi mai d'an nisa kafin su iso unguwar kasancewar ta shiru babu kowa sai haske wani b'angaren wani b'angaren kuma babu, suna isa k'ofar gidan suka ga akasin haka domin akwai mutane har lokacin ga wajan a cike dam Suhaima ta faka Rauda ta kalle ta tace, "Ina zuwa" ta fad'a tana fita ta shiga cikin gidan.
Jim kad'an ta fito tana fitowa ta k'araso inda suke tace, "Kuzo muje" tana fad'a tayi gaba abinda Mama taji kamar ta jawota ta tsinka mata mari dole suka fito suka bi bayan ta baza kace Mama ta rab'i sarauta ba domin hijjabi ne a jikinta har k'asa.

A k'aramin d'aki suka zauna Rauda tayi shiru kamar babu ita a wajan fuskar ta cike da b'acin rai kana kallon hakan zaka fahimta dan fuskar a d'aure take matuk'a, gyaran muryar Baba ya saka ta kalli k'ofa ya shigo ya zauna a kan kujerar da yake zama yace, "Babata ana ta saka ki aiki ko?." Murmushi tayi mai kama da yake tace, "babu komai ai Baba, bara na shiga ciki" ta fad'a tana tashi ta basu waje domin su tattauna.

? ?? Sun jima sosai har Rauda ta gaji da zaman sai daga baya aka aiko kiran ta alamun sun gama ta shiga d'akin ta samu Baba yana fad'in, "Bazan karb'i komai daga wajan ku ba, banyi dan a biya ni ba kowa yasan dan Allah nake taimakon kowa da aljihuna nake siyan ko wanne magani na kuma bayar kyauta. Nayi miki ne kodan shi shugaban namu na garin nan baza mu so rayuwar da aka jefa shi a ciki ba dole muyi iya bakin k'okarin mu wajan ganin mun taimaka ya dawo hanya ma daidaiciya duk da muma a wajan Allah muke nema." Mama tace, "Mun gode Allah ya saka da alkhairi" karon farko kenan da ta yiwa wata halitta godiya da irin wannan addu'ar.

Baba yace, "babu komai ai yiwa kaine, in kika rik'e abubuwan dana baki da wanda shi za'a bashin nan da wasu kwanaki masu zuwa ko wanne irin tsafi ne zai bar jikin sa in sha Allah amma sai kin dage da addu'a sosai muma kuma zamu taya ki." Mama tace, "Amma dan Allah malam bana so mutane su san da maganar nan, amincewa dakai ya saka na kawo kuka na wajan ka in mutane suka san abinda yake faruwa ban san ya zanyi ba."

Baba yayi murmushi irin na tsoffi yace, "Duk wanda yasan Baba malam yasan baya fidda sirrin wani ga wani, manyan mutane da suka fiki sunzo wajena kuma sun koma lafiya har yanzu babu wanda yasan me ya kawo su. Inda ina fitar da sirrin wani zuwa ga wani da ban kawo yanzu ba, kema da ba'ayi miki kwatance na ba." Mama tayi shiru ya kalli Rauda yace, "Babata kin kyauta abinda kikayi kar kiji a zuciyar ba'a kyauta miki ba abinda kikayi shine daidai. Ita rayuwa haka take akwai lokacin da baka so aikata abu ba In ka aikata sai ya zamar maka alkhairi, ki saka a ranki alkhairin kenan kuma ki taimaki wanda yazo inda kike." ya kalli su Mama yace, "na barku lafiya" ya fad'a yana tashi ya koma ciki suma suks mik'e hannun Mama rik'e da leda mai girma suka fita zuwa wajan mota kamar d'azu suka shiga mota suka d'auki hanya.

? ? ? Tafiya suke yi shiru motar Suhaima ta d'an taka burki taji motar ta tsaya ta cigaba da tafiya ta sake taka burki ya sake tsayawa Mama tacee, "Tsayuwar meye?." Suhaima tace, "Burkin nake ji yana cizewa ne" ta cigaba da tafiya.

K'atuwar mota ce tawo ta gaban su Suhaima tayi gefe mai motar ya danna horn ya gigita Suhaima tana k'okarin taka burki amma abin yaci tura hankalin Mama ya tashi ta kank'ame ledar da Baba malam ya bata tace, "Suhaima ki tsaya mana zaki kashe mu fa." Suhaima hankali tace, "Mama taki tsayawa, tak'i tsayawa wallahi." Motar ce take sake tunkaro su gashi suma tafiya suke babu sitiyarin yak'i juyawa yayi baya. Rauda ganin mutuwa kusa hankalin ta ya tashi tana kuka tace, "Mu fita a haka!."

Kamar jira suke kuwa Mama ta bud'????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
e motar duk da tafiyar da take yi ta fad'a gefe itama Suhaima tayi gefe Rauda ma ta fita ta buge da k'aton dutse a gefe hannun ta ya daki motar da take gudu akan titi ita kad'ai. Garam motar ta daki babbar motar wata motar daga bayan su a guje tayo kansu daidai saitin da Mama take? ba tare da sun farga ba, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mamaaaaaa!" Suhaima ta fad'a da k'arfin gaske cikin ihu tana yin inda Maman take a guje.



*Mama ta ware fa*>?#?>?#?
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*062*

? ? ? ?? Da zafin nama Rauda ta jawo Mama da k'arfin gaske suka fad'i a k'asa motar ta wuce a guje ba tare da ta kalle su bama balle ta bada ha?uri, Suhaima ta k'araso inda suke ta d'ago Mama ta d'ago Raudan ma ta kalle ta tace, "Na gode, badan ke ba da yanzu mota tabi ta kan Mamana" ta juya ta kalli Mama tace, "Mama babu inda yake miki ciwo?." Mama kallon Rauda take yi suka had'a ido Rauda ta d'auke kai domin hannun ta zafi yake mata sosai ga kashin bayan ta da ya bugu fad'owar da tayi daga mota.

Mama so take tace mata ta gode da ceton ranta da tayi amma ta gaza fad'ar hakan sai kallo kawai hannun ta k'amkame da ledar da Baba malam ya bata; ta bar wayar a cikin motar amma bata iya barin ledar ba sabida mahimmacin ta a wajan ta. Kallon motar Mama tayi ta ga gaban motar yayi kwatsa-kwatsa shi kuma mai babbar motar ya gudu ganin basu lura dashi ba.

Suhaima tace, "Mama ina zamu je yanzu? Ban fito da waya ba balle na kira driver yazo ya d'auke mu, taki kin barta a ciki na tabbatar baza ta amfanu ba" ta fad'a tana dafe kanta dan itama ta bugu kanta ciwo yake sosai. Rauda da take hango gidan su tace, "Sai anjiman ku." Ganin ta fara tafiya tana rik'e bayan ta ga hannun da take yarfe shi kana gani kasan yana mata ciwo Suhaima tace, "bai kamata ki tafi ba asibiti ya kamata mu wuce a duba ki." Rauda ta kalle ta tace, "Babu komai" tana fad'ar hakan ta cigaba da tafiya.

"Na gode." Ta tsinci muryar Mama a bayan ta hakan ya saka Rauda tsayawa cak ta juyo yanayin fuskar ta ya nuna tana jin ciwo a jikin ta tace, "Aikin musulmi na gari ceton rai ne ba d'aukar rai ba" tana fad'ar haka tayi gaba abinta ba tare da ta sake kallon su ba sai a lokacin take jin haushin kanta ji take ina ma ta bari motar ta markad'e ta kowa ya huta.

? ? ? ? Mai keke napep Suhaima ta tsayar ta fad'a masa asibitin da zai kai su ta shiga tace, "Mama shigo muje." Mama ta kalle ta ta kalli napep d'in wai yau itace zata shiga keke napep lallai rayuwa ta fara canja mata baya. Babu yadda ta iya haka ta shiga suka tafi wajan Dr Yasir sukayi sa'a yana nan ya duba hannun Mama ya duba na Suhaima ma yaga duka buguwa ce ba ciwo bane ya basu magani da kansa ya d'auko su a mota zuwa gida.

Duk da yanayin da Mama take ciki tana shiga b'angaren ta wajan Hydar ta shiga ta same shi yadda ta? barshi ta d'auko ruwan rubutun da malam yace a gidan shafa masa a fuska da tafin k'afa dana hannu ta shafa tana yi tana cize bakin ta sabida ciwon da jikin ta yake mata. Sai da ta tabbatar tayi komai yadda akace sannan ta shiga d'akin ta tayi wanka da ruwan zafi bayan ta shirya tana zaune a d'aki Suhaima ta shigo da sallama ta amsa ta k'araso ta zauna a k'asan ta tace, "Mama nifa tunani nake kwance min burkin mota akayi, na tura mechanic yaje a d'auke ta ya duba ta a yanzu ya tabbatar da kwance Birkin aka aka juyar da sitiyarin yadda bazai sarrafu ba."

Mama tayi cak ta kalli Suhaima tace, "Kenan so akayi a kashe mu?." Suhaima ta d'aga kai mama ta sauke numfashi ta dafe fuska da duka hannayen ta biyu ita gabad'aya abubuwan nan sun fara fin k'arfin tunanin ta gab kwakwalwar ta take da daina aiki indai aka cigaba da tafiya a haka zuciyar ta ma zata iya bugawa ta mutu kowa ma ya huta Suhaima tace, "Waye zai turo a kashe ki? Su waye meye kuma dalilin su?." Shiru Mama bata amsa ba Suhaima ta kuma cewa, "Badan waccen yarinyar ba da yanzu bak'in labari ya gama karad'e masarautar nan, dole mu sake taka tsan-tsan da kowa Mama, yanzu kinga mu kad'ai ne daga ni sai ke bamu da mai taimaka mana" ta fad'a a sanyaye tana kallon Maman nata.

Da hannu Mama tayi mata alama da ta bata waje ta tashi ta fita Mama ta bud'e fuskar ta tana so ta tuna waye zai bada wannan d'anyen aikin a aikata mata amma kanta ya cushe gabad'aya tama rasa wanda zaizo ranta. _Duk musulmi na gari ceton rai shine aikin sa ba d'aukar rai ba._ kalaman Rauda suka dawo mata zuciyar ta ta daki goshin ta a bayyane tace, "Kaiiii! Meyasa haka yake faruwa dani..?" Ta fad'a tana yin baya ta kwanta a kan gadon tana ji kamar tayi hauka.

Kamar wacce aka yiwa allura sai kuma ta mik'e ta ta d'auki ledar da ta shigo da ita ta fita zuwa b'angaren mai martaba, yana kwance shi kad'ai idanun sa a bud'e da alama ba bacci yake ba ta d'auko maganin da aka bayar nasa tana shafawa masa tana kuka tana fad'in, "Mijina suna so su kashe ni, mijina haukata ni suke so suyi ban san me nayi musu ba. Dan Allah ka tashi ka taimaka min abubuwa sun yi min yawa suna neman fin k'arfin tunani na, kaine garkuwa ta a koda yaushe ka tashi ka taimaki matar ka mai rauni" ta fad'a tana hawaye tana zuba masa ruwan rubutun a bakin sa.
Haka ta dinga soki burutsu a wajan sa kamar kanta ya kwance kafin ta koma b'angaren ta tana ji kamar ta kashe kanta ma kowa ya huta.

? ? ? *&* B'angaren Rauda lokacin da ta shiga gida dukkan su zaman jiran dawowar ta suke yi yadda ta shigo tana d'ingishi hankalin kowa sai ya tashi Umma tayo wajan ta tana fad'in, "Rauda lafiya? Meya same ki?." Rauda ta fara kuka tace, "Umma ba kun amince da ita kun barni mun fita tare ba...? Da yadda kuke zaunen nan sai dai kuji labarin mutuwa ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wani abun ta kuma yi miki? Ba'a son raina kika bita ba bazan ja da umarnin mahaifin ki ba Rauda ba yadda zan iya. Meya same ki?." Baba da ya shigo yace, "meya faru?."? Rauda tace, "Hatsari mukayi."
"Hasbunallahu wani'imal wakil!, hatsari..? A ina?" Umma ta fad'a a gigice tana kallon ta.
"A kan hanyar mu ta dawowa, motar ce tak'i tsayawa sai bud'ewa mukayi tana tafiya muka fita shine na buge da dutse a bayana" ta fad'a tana yamutsa fuska kamar zatayi kuka.

Umma tace, "Wannan mata dai zuwan ta bai tab'a zamar mana alkhairi ba, tunda iyalan ta da ita kanta suka shigo rayuwar mu shikenan komai yake canjawa. Shine kuma suka barki kika tawo ko a kaiki asibiti a duba ki?. Su suna ina?." Rauda tace, "ban sani ba a wajan na barsu kawai nayi tawowa ta. Umma bayana" ta fad'a tana cize bakin ta domin ciwo yake yi mata ba kad'an ba.

Rik'e ta Umma tayi tace, "Malam ya kamata muje asibiti a duba mana ita tunda su da suka fita da ita bata da matsayin da zasu kaita asibiti." Baba yayi shiru kawai baice komai ba dan yasan laifin sane da baice taje ba da hakan bata faru ba. Baba ya fita jim kad'an sai gashi ya dawo yace, "Kuzo muje."

Tare suka fito wanda yake jan napep d'in Baba suka gani suka shiga zuwa asibiti na kusa, kasancewar private ne ba jama'a nan da nan aka dubata aka bata magani nasha dana shafawa dan itama buguwa ce kawai ba wani abun ba, Baba zai biya kuWi kenan sai ga Anas a wajan ya kalli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login