Showing 108001 words to 111000 words out of 216282 words

Chapter 37 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

kenan aka shigo b'angaren ko basu juya ba sun san wacece dan babu wanda zai shigo wajan daga su sai ita sai maganar ta maqale ya fasa Mama ta kalle ta ta ga ta d'aure fuska ta kalli Asad tace, "Wacece ni a wajan ka?." Yayi shiru na d'an lokaci kafin yace, "Mahaifiyata" yadda ya furta sai da suka kalle shi duka domin a sanyaye yayi maganar sosai.

Mama ta sauke numfashi tace, "Na isa dakai kamar lokacin baya Asad?." Ya girgiza kai yace, "Matsayin mahaifiyata baya tab'a canjawa." Ta kalle shi ta kalli Jidda tace, "Nasan kai shugaba ne koyi ya kamata mutanen cikin gidan nan dana waje suyi dakai akan komai, amma dole ce ta saka zan saka ka aikata abinda zan fad'a domin zama da ita ba alkhairi bane a rayuwar ka, ban damu da maganar mutane ba indai zaka zamu lafiya shine burina. Dan haka Ina baka umarnin ka saki wannan yanzun nan!" Ta fad'a yana nuna masa Jidda da yatsan sa.

Juyawa yayi ya kalli Jidda suka had'a ido yaga tana murmushi ya dawo da kallon sa ga Mama ya sake kallon Jidda sai ya kasa cewa komai ya sauke kansa k'asa zuciyar sa tana bashi umarnin aikata abinda Mama tace amma harshen sa da gangar jikin sa sun k'i bayar da wannan damar. Mama ta kuma cewa, "mahaifiyar ka nake shiyasa nace ka sake ta nasan baka tab'a tsallake umarni na a ko yaushe. Ina so ka sake tabbatar mata da na isa da kai yanzun nan ba anjima ba ka sake ta Asad."

Kai ya saukar k'asa sosai ya sauke numfashi zuciyar sa naso ta furta amma maganar tak'i zuwa harshen sa, dak'yar ya iya tattaro abinda yake bakin sa yace, "Allah ya wuci zuciyar Mama na, bazan iya sakin ta ba!."
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*059.*

? ? ? ? ?? Yadda Mama ta k'ame 'kam tana kallon sa da alamun mamaki a tare da ita mai had'e da tsoro da firgitarwa da tashin hankali had'i da rud'ani take kallon sa, tashin hankalin da ya shiga jikinta har a kan fuskar ta ya bayyana k'arara ta kasa furta komai sai kallo da take binsa dashi shi kuma kansa yana k'asa baice komai ba. Bakin ta har rawa yake yi tace, "Asad....!."
"I'm sorry Mama ina so na aikata abinda kika ce amma bazan iya ba, ina neman izinin tafiya" ya furta a sanyaye bai jira ta bashi umarnin ba ya juya ya hau sama ta bishi da kallo jiri yana d'aukar ta.

Baya tayi zata fad'i Suhaima tayi hanzarin rik'e ta shi kansa Hydar ya daskare a wajan kallon inda Asad yabi kawai yake yi hankalin sa a tashe tsoro ya mamaye masa zuciyar sa, murmushi Jidda take yi daga gefe kafin ta k'araso inda Mama take tace, "Har abada bazai tab'a iya sakina ba, zai iya rabuwa da dukkan ku amma bazai iya rabuwa dani ba, In ma tunanin da kike kenan is better ki ajjiye shi sabida bazai tab'a faruwa ba ko yanzu ko nan gaba. Zaku iya tafiya zanje wajan mijina na taimaka masa yayi wanka ya huta."

Mama idanun ta a lumshe yake bata iya magana ba Suhaima zatayi magana Hydar ya hanata dan baiga amfanin maganar ba suka rik'e Mama suka fita sabida mutane ma ta k'ofar baya suka bi zuwa b'angaren Mama dan har lokacin suna rik'e da ita jiri take yi.Kafin su isa zazzaSi ya lullub'e Mama suna ajjiye ta falo Hydar ya kira Dr ya sanar dashi emergency yake son zuwan sa.


Duk suna zaune kusa da ita ba jimawa yazo Hydar ya bada damar shigowar sa ya shigo ya fara auna BP Mama, sai da ya kammala ya bata magani ya kalli Hydar yace, "Ranka ya dad'e jinin Fulani ya hau sosai fiye da tunanin ka, inda akwai abinda yake damunta ayi gaggawar ganin ta rage damuwar ta in ba haka ba akwai matsala gaskiya."

Sallama sukayi da Hydar bayan ya bata magani ya tafi ya dawo kusa da ita yace, "Mamana muje d'aki ki huta." Taimaka mata sukayi ta tashi zuwa d'aki ta kwanta a gefen gado idanun ta rufe sai a lokacin suka lura kuka ma Maman take yi. Basu iya cewa komai ba ta kwanta suka kullo mata d'akin ko wanne jikin sa a sanyaye.

Hydar ya kalli Suhaima yace, "Wanne mataki kike ganin zamu d'auka akan Jidda?." Suhaima tace, "wanne mataki kenan Yaya Hydar? Mama fa ita take son Jidda ita ta saka ya aure ta ta raba shi da wacce yake so, ni daman wallahi sau da yawa na kanyi tunanin kamar akwai wata manufar da Mum take zaune da Mama a lokacin dana fad'a mata bazata amince ba sai dai ma raina ya b'aci. Yanzu kuma sun fito da asalin kalar su, waccen matar tasa yana sonta haka Mama ta raba su yanzu kuma gashi tana so ya rabu da wacce baya so yace bazai ba."


"Kinga Suhaima wannan ya wuce, meye mafita yanzu da zamu taimaka masa?."
"Addu'a mana, asiri suka yi masa wallahi dan in ba asiri ba banga abinda zai raba Mama dashi ba. Sai dai mu taya ta fad'awa Allah ya kawo sanadin raba su dan in ka lura yanzu ibadar sa ta ragu."

Hydar yayi shiru yana saukar da numfashi yace, "Zan sanar da abokan sa na Madina su taya shi Addu'a nima zan nemo maganin da za'a dinga bashi ba ko Allah zai taimake mu ya warke, matsalar kuma in an nemo ma basha zaiyi ba." Suhaima tace, "in muna Addu'a zai sha wata rana ai. Kawai dai mu dage da addu'a in ba haka ba wallahi sai gidan nan ya gagari Mama zama wata rana, ka duba har jinin ta ya hau in aka cigaba ban san me zai faru da Mama ba." Hydar ya girgiza kai ya fita ya bar Suhaima a wajan.

*&&&*

? ? ? ?? "Mum kin san bata jima da fita ba na fito nazo nan wai ya sake ni." Mum tace, "What! Ya sake ki?."
"Wallahi Mum, kuma yau yadda yayi mata magana cikin biyayya yayi mata ni na fara jin tsoro wallahi kar wata rana tayi galaba a kansa fa."

Mum tace, "kice sai an sake nemo mafita kenan, in aka cigaba da haka wata rana zatayi nasara. Ta bazama nema masa magani yau ma daga Kano ta dawo wajan malaman su nacan akan matsalar in muka bari ana haka tabbas wata rana namu zai karye. Dole a samo mafita."
Jidda tace, "abinda ya kamata ayi kenan Mum dan ni na tsorata wallahi, yadda yayi mata magana a sanyaye ya bani tsoro. wacce mafita za'a samu?."
Mum tayi shiru tana kallon wani wajan daban zuciyar ta na kawo mata wani abun kafin tace, "Kashe ta za'ayi Jidda!."

A firgice Jidda ta mik'e tsaye idanun ta a waje tace, "Mum kisa?." Mum ta kalle ta tace, "dallah malama zauna kar ki tara min jama'a" ta fad'a tana jan hannun Jiddan ta zauna har lokacin idanun ta a waje Mum tace, "Nutsu."? Jidda ta had'd'iye yawu cikin tsoro tana kallon ta Mum tace, "Dan nace a kashe ta kika wani firgita kamar nace ke za'a kashe?, in tana duniya wallahi wata rana sai ta raba ku dashi. Kar kiga shi shugaba ne a tsarin gidan sarauta sarki baya saki ke bama sarki ba ko wanda suke a k'asan sarki basa saki to wallahi sai ta nemo hanyar da zata raba ku, shu'uma ce duk yadda kike tunanin ta ta wuce haka."

Jidda fuskar ta har lokacin da tsoro tace, "Duk da haka Mum kisa fa?, kisa sai kace cinnaka ko kiyashi? Nidai a bar maganar kisa Mum."
"Mtsww sai kiyi ai, ke za'a taimakawa fa in aka barta da rai billahillazi sai kinzo kina kuka da idanun ki nan gaba domin ta wuce inda kike tunani, gwara mu yiwa tufkar hanci yadda zaki mulki gidan san ranki kiyi abinda kika ga dama in kuma ganin bakya son hakan fine Jidda daman ai ke za'a taimaka." Jidda ta rausayar da kai tace, "Yadda kika ce Mum, kawai ina jin tsoro ne." Mum tayi murmushi tace, "kar komai ya baki tsoro ni nasan yadda zanyi, ki bani nan da wasu kwanaki zanyi maganin ta."

Jidda ta juyar da kai zuciyar ta gabad'aya a cushe haka kawai take ji bata so a kashe Mama amma bazata nunawa Mum ba dan duk abinda take yi dan ita take yi in ta nuna mata bata so bazata ji dad'i ba amma bata son aje ga kisa. Ta jima suna hira a gida har Daddy ya dawo suka gaisa sannan drivern ta da jakadiyar ta suka kwashe ta aka koma gida.

*&&&*

? ? ? ?? Waziri ne a zaune malami a gaban sa su uku ne a zaune a falon shi da malamin sai Suhail malamin ya kalli Waziri yace, "Ranka ya dad'e in ba'a gaggawa ba komai zai iya canja salo ya zama dole ayi abinda ya kamata." Waziri ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya yace, "Za'a yi cikin kwanakin nan kuwa in sha Allah." Sallama sukayi malamin ya tafi falon ya rage dashi sai Suhail ya kalli Suhail yace, "Meye shawarar ka?."

Suhail yace, "ta yadda za'a raba shi da mulkin shine aiki." Waziri ya sauke numfashi yace, "kawo shawara dai."? Ya gyara zama yace, "a ganina shi shugaba ne kuma wanda ake yiwa kallon mai addini da sanin ya kamata, me zai hana mu samu baiwa mace a had'a baki da ita a biya ta kud'ad'e masu yawa a kuma ja mata kunne matuk'ar nan gaba ta furta abinda ya faru sai an kashe ta."

Ya gyara zama yace, "Me za'ayi kenan?." Suhail yace, "Sharrin alfasha!." Waziri ya zubawa Suhail ido shima shi yake kallo kafin ya sauke kansa yace, "duk k'imar mutum alfasha tana zubar dashi, duk mulkin mutum alfasha tana sakawa a ganshi tamkar bawa, duk kud'in mutum alfasha tana sakawa a ganshi kamar talakan da bashi da cin yau bare na gobe. Duk yadda ka kai da ilimin ka da addinin ka indai alfasha ta shigo ciki ko kai kad'ai ne malamin da jama'a suke sauraron wa'azin su daga rana sun daina domin zasu ga abinda kake tsoratar dasu da kar su kusance shi kai kana kusantar sa. Sharrin Alfasha shine zai tarwatsa Asad ta k'arfi sai an sauke shi daga wannan karagar."

Waziri ya girgiza kai cike da gamsuwa da maganar sa zuciyar sa cike da tsantsar farin ciki yace, "Na jima banji maganar data kwantar min da hankali kamar wannan ba Suhail. Kana da hangen nesa da sanin ya kamata kayi tunani mai kyau Suhail shawarar ka tayi dari bisa dari babu kuskure a cikinta, tabbas wannan shine zai tarwatsa sarki da dangin sa." Suhail ya murmusa ya shafa kansa yace, "Godiya nake ranka ya dad'e."
"Tashi kaje zan neme ka anjima."
"A tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya fita ya bar mahaifin nasa a zaune.

Yana fita wayar sa tayi k'ara kamar jira ake ya fita ya duba ganin number da yake jira ya saka shi ya d'auka yace, "Kamar kin san jiran kiran ki nake yi master." Tace, "akwai update ne?."
"Sosai ma kuwa."
"Ina jin ka."
"Maganar raba Mai martaba da kujerar sa ce an samo mafitar da zai barta koda baya so."
"Meye ita?."

Waziri yace, "Sharrin alfasha za'ayi masa, abinda nake nufi a kama shi da mace a d'aki macen ma baiwa." Tayi k'aramar dariya tace, "Sarkin za'a kama da baiwa a d'aki? Kana mantawa da sarki ne fa bafa hakimi ba?." Ta sake yin dariya kafin tace, "sam wannan shawarar batayi ba, babu ta yadda za'ayi sarki guda ace an kama shi da wata yarinya kuma baiwa a d'aki d'aya hankali ma bazai d'auki a wannan ba."

Waziri yace, "Zaiyu mana, ba Zuciya ce fa."
"To ta yaya ta shiga? Meya kaita d'akin sa? Me zata kai masa har d'aki?, daga kanta ya fara?, meyasa a baya ba'a tab'a jin makanancin labarin ba?. Bafa Aliyu bane Asad ne ya kamata ka gane."

Waziri yayi shiru jin yayi shiru ya saka tace, "in zaki yanke hukunci kuyi wanda hankalin mutane bazai kai shiri bane kuyi abu kamar gaske, inda ace Aliyu ne dan munyi masa sharrin nan ba wani abu bane mai wahala kowa kuma zai amince da zai iya aikatawa tunda daman an san dabi'ar sace, amma Asad fa?. Kai koma Aliyun ne sarki ne fa taya zai nemi baiwar sa? In ma neman matan zaiyi ba'a gidan ba sai dai wani wajan daban."

Waziri cikin gamsuwa yace, "Tabbas maganar ki gaskiya ce." Tayi murmushi tace, "tunda lokacin da muke jira yazo zan san abinda za'ayi amma wannan shawarar a ajjiye ta a gefe d'aya ba za'ayi aiki da ita ba kwata-kwata."
"Me za'ayi?."
"Zan sanar dakai in na gama shirya komai."
"Batun yin cikin matar sa fa? Bana so ya ajjiye d'a a duniya domin zai iya zamar mana barazana nan gaba."
"Shida haihuwa har abada, na gama da wannan aikin tun ba yau ba."

Waziri ya sauke numfashi yace, "Zan so ki bayyana min fuskar ki ko sunan ki ni kaina ban sanki ba har gobe." Dariya tayi tace, "nan kusa" tana fad'a ta yanke kiran yabi wayar da kallo zuciyar sa na hasaso masa wacece master planer......?

*&&&*

? ? ? ?? Washe gari

? ? ? ? Da wuri Rauda ta shirya tana jiran su Ramla dan ranar Baba malam ya basu suje su ganshi, k'arfe goma na safe suka bayyana a k'ofar gidan har gida Ramla ta shiga suka fito tare suka shiga mota suka tafi. A mota Rauda tace, "Ina kwana Dr."
"Lafiya lau Rauda, mun fito dake da sassafe." Murmushi tayi kawai bata ce komai tana nuna musu hanya har suka je k'ofar gidan.

K'arewa k'ofar gidan kallo suke yi ganin sa a cike da manyan motoci ga babura Dr ya kalli Rauda yace, "kalli jama'a kamar ana sadaka?." Ramla tace, "abin mamaki ba." Rauda tayi murmushi tace, "Dan ma yau asabar da jiya ne wallahi wajan nan babu waje." Kai ya girgiza suka fito Rauda tace, "shiga ciki zamuyi ai." Cikin gidan suka shiga suna wuce mata a zaune da maza wasu da hijjabi wasu kuma da mayafi wasu kuma da niqab.

? ? ?? A cikin wani d'aki Rauda suka sauka suka zauna sannan ta tashi ta shiga cikin gidan suka gaisa da mutanen ciki ta dawo ta zauna tace musu, "Yanzu zai shigo in sha Allah." Suna zaune kowa yana danna wayar sa babu mai magana a cikin su kusan mintina arba'in a haka kafin suji gyaran murya a bakin k'ofa.

Da sauri suka mik'e dukkan su yana murmushi ya shigo yana fad'in, "Ku zauna mana, Babata zauna." Zama yayi akan wata kujera a d'akin suma suka zauna kafin su gaisa dukkan su ya amsa da murmushi ya kalli Rauda yace, "Babata kinyi min yaji ba'a ganin ki ko kad'an sai kinga dama." Murmushi tayi tace, "Muna gaisawa a waya ai Baba."
"Ni ganin Babata nake so nayi ai ba waya ba, koda yake baki jima da fita daga idda ba ai." Murmushi kawai tayi tace, "Baba ga bak'in da Umma ta fad'a maka zasu zo munzo tare."

Yace, "To ma sha Allah." Rauda ta mik'e tace, "bara na shiga ciki" ta fad'a tana shiga cikin gidan ta barsu dan su sake su fad'a masa matsalar su. Ta jima a ciki suna hira da y'an matan gidan har aka turo kiran ta sannan ta dawo ta shiga da sallama ya kalle ta yace, "Rauda." Ta zauna tare da fad'in, "Na'am Baba."
"Gobe da yamma ko da daddare kizo ki karb'ar musu magani bani dashi a yanzu zuwa da asuba zan samo shi in sha Allah."
"To Baba Allah ya kaimu."
"Amin ya Allah. Kema akwai naki sai ki tafi dashi a goben gabad'aya."
"To Baba."

Baba ya kalle su yace, "Khalifa in sha Allah gobe za'a karb'ar muku maganin da izinin Allah kuma za'a dace, sannan kuma ku bi shawarwarin da na baku in sha Allah za'a dace, a kuma dage da rok'on Allah." A tare suka ce, "Mun gode Allah ya k'ara girma." Baba malam yace, "babu komai, zaku iya tafiya yanzu ina da bak'i."

Dr ya d'auko kud'i masu yawa ya ajjiye masa Baba Malam ya girgiza kai yace, "Bana buk'atar kud'in sadaka daga wajan ku, mahaifiyar Rauda ta sanar dani taimakon da kuka yiwa mata kun cancanci fiye da haka daga wajan iyalan mu. Mu rama alkhairi da alkhairi" ya fad'a yana mik'ewa cikin murmushi fuskar sa sak ta Umma sukayi godiya sosai ya fita.

Cikin gidan Rauda ta shiga tayi musu sallama suka fito suka fita, a k'ofar gidan suka ga dogarai maza guda biyu a bakin wata mota kana ganin motar kasan daga gidan sarauta ta fito yanayin number motar ya nuna hakan suka wuce abin su ba tare da sun kalli wanda yake ciki ba.

A mota suna cikin tafiya Rauda na baya a zaune Ramla tace, "Gaskiya naji dad'i wallahi Rauda, badan ke ba wannan layin ai bamu san lokacin da zamu bar nan ba wata?ila ma layin bazai zo kan mu ba. Allah ya bar zumunci wallahi dan ji nake a jikina kamar har mun samu waraka." Dr yace, "Nima haka, ban tab'a jin wani yak'ini na samun magani kamar wannan ba, kuma ta inda ya burge ni da alkur'ani da hadisi yake amfani baya duba baya tsafi ko wani abun. Gaskiya Rauda kun dace samun babban mutum a dangi kamar sa ma rahama ne."

Murmushi tayi kafin taji yace, "naji yana ce miki Babata sunan maman sane dake?." Rauda tayi dariya tace, "A'a kawai yana fad'a min ne sabida ina kama sosai da babar su Umman shiyasa. Umma tace kamar itace ta haife ni shiyasa yake ce min haka."

Murmushi tayi kawai taji Ramla tace, "gashi duk matsayin ki sai kin bi layi baya tauyewa talakawan da suke zuwa wajan sa hakki akan masu kud'i. Yanzu ka duba motar da muka bari kamar ta gidan sarauta amma layi take bi." Dr yace, "Ai ba ganin Idanun Rauda ba ban tab'a ganin malami kamar sa ba."

Ita dai murmushi kawai take yi Ramla tace, "Sis badan kar kice na cika tambaya ba dana ce daman kin tab'a aure ne?, naji yana miki zancen idda." Rauda ta sauke numfashi tayi shiru tana kallon hanya annurin fuskar ta ya d'auke gabad'aya ganin hakan sai Ramla

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login