Showing 51001 words to 54000 words out of 216282 words

Chapter 18 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

yana tattare rigar jikin ta. Motsawa tayi zata hana ya sake matse ta sosai a haka ya zare rigar ya saka hannun sa a bayan ta ya b'alle hook d'in brezia ta ta cire ta baya.

Bai juyo da ita ba ya sake matse ta sosai a jikin sa yana sauke numfashi a hankali hannun sa na fatar bayan ta ya rik'e ta gam kamar za'a kwance masa ita. Bata kuma yun?urin kwace kanta ba tayi lup a cikin sa tana jin yana yawo da hannun sa jikinta.

A hankali take jin saukar numfashin sa alamun yayi bacci ta kalli fuskar sa ta tabbatar yayi baccin sai taji ya bata tausayi a zuciyar ta domin bata gane abinda ya jefa shi a cikin wannan yanayin ba lokaci d'aya. So take ta tashi amma ya hana hakan har lokacin tana rik'e a jikin sa kuma bacci yake yi a haka sai ta mayar da kanta ta kwanta a k'irjin sa itama baccin ya d'auke ta.

? ? ? Sun jima suna bacci sai da akayi la'asar ta riga shi tashi ta samu ta zare jikinta bata tsaya mayar da rigar mata ta fita bata son ya farka ya ganta. Wanka tayi ta shirya cikin riga da wando wanda basu kamata sosai ba ta saka dogon hijjabi tayi sallar la'asar bayan ta idar tayi azkar. Yunwa take ji sosai hakan ya saka ta fito falon nan ta same shi ya fito amma kafin su kai ga had'uwa ya fita. Tasan abincin ya tafi d'aukowa ta koma ta zauna sai kuma ta tashi ta had'a tea tana sha domin yunwar ta d'an kwanta kafin ya dawo.

? ? ?? Door bell taji an danna tayi k'ara kamar baza ta tashi ba sai kuma ta tashi ta k'arasa ta bud'e tayi karo da kyakykyawar balarabiya hannun ta da tray tayi mata murmushi itama ta mayar mata da martani kafin ta mik'a mata tray ta karb'a ta koma itama ta shiga ciki ta tura k'ofar da k'afa ta k'arasa ta ajjiye akan table ta bud'e ta fara ci daman yunwa take ji sosai. Taci ta k'oshi tasha magani sai ta tuna da abinda Muhibba ta fad'a ya fad'o mata a zuciyar ta, tsaki taja tana so ta kawar da tunanin amma ta kasa maganar yawo take mata a kanta gashi daman kuma abinda yake zuciyar ta kenan.

Tana wannan tunanin taji kiran magriba ta tashi tayi sallah ta karanta suratul waqi'a kana ta tashi ta shiga d'akinta tana kallon k'atuwar tagar glass d'in dake d'akin, 'Rauda akwai dalilin da Asad ya saka ya aure ki, babu soyayyar da zata saka ya bar mahaifiyar sa sabida ke sai dai in akwai wani abun a k'asa, to meye shi?' Numfashi ta fesar ta kama k'ugu tana kallon tagar zuciyarta ta cigaba da bata labari, 'wata?ila wani aikin asirin za'ayi dake shiyasa aka auro ki bayan haka baki da wani amfani a wajan sa. Amma kin manta kalaman da ya fad'a miki lokacin da ya karb'i budurcin ki?.'

A bayyane tace, "Wannan dad'in baki ne kawai amma tabbas akwai wani abun a k'asa." Ranta taji gabad'aya ya b'aci damuwa ta mamaye mata zuciya tana nan tsaye har akayi i'sha ta bar wajan tayi sallah tare da shafa'i da wutur ta kuma tashi ta koma bakin tagar ta tana kallo tana tunanin mafita da inda zata nemo gaskiyar dalilin kawo ta k'asar matsayin matar sa.

? ? ? ? Ta baya taji ya rungume ta ya d'ora kansa a wuyan ta yana kallon tagar shima ba tare da yayi magana ba ta daure bata kalle shi ba ta cigaba da kallon tagar ta domin bata so zuciyarta kamu da soyayyar sa kar hakan ya zama mata babbar illa nan gaba, "kinyi kyau!." Yarrrrr taji a jikin ta kasancewar a kunnen ta ya fad'a ta sauke numfashi ta lumshe idanun ta sai ga hawaye suna sakko mata daga idanun ta.

Kallon ta yayi ya sake ta ya dawo yana fuskar ta ya rik'e fuskarta ta saukar da kai k'asa tana kuka ya d'ago da fuskar ta sai ta kulle idanun ta hawayen na cigaba da zuba taji ya saka hannu yana share mata hawayen amma baice komai ba. Kallon ta kawai yake yi zuciyar sa na bugawa da sauri ko kad'an baya so yaga tana kuka amma ya lura dabi'ar da ta d'auko yanzu kenan ko dan taga baya so ne oho.

Zaiyi magana yaji tace, "meyasa ka aure ni ka kawo ni nan bayan kasan ni ba sa'ar auren ka bace? Sam ban amince da kana sona ba har kawo yanzu zuciyata tana fad'in min akwai dalilin da ya saka ka aure ni, ka fad'a min meyasa kafin zuciyata ta buga na mutu ka huta" ta fad'a tana sake fashewa da kuka mai sauti. Numfashi ya sake saukewa yana kallon dan bai san me zai kuma ce mata ta amince da sonta yake yi ba wani abu ba, ya fad'a mata abinda ya kamata amma ya lura har yanzu zuciyarta tana rawa akan kalaman sa.

? ? ? ? Zata kuma magana ya toshe mata baki da hannun sa ya girgiza mata kai yana juya kwayar idanun sa a cikin nata ya lumshe ido ya bud'e ya saka d'aya hannun ya jawo ta ya had'a ta da jikin sa sosai har lokacin bai saki bakin ta ba, goshin sa ya had'a da nata goshin ya kulle idanun sa kamar yadda ta kulle nata har lokacin kuka take yi bata daina ba.

Bakin sa ya sanya a cikin nata bayan ya cire hannun sa daga kai ya rik'e kanta da hannu guda yana tsotsar bakin ta cikin k'warewa da son kawar mata da damuwar zuciyar ta. K'okarin kwacewa take yayi mata rik'on da ta kasa ko motsi sai juye-juye take wanda hakan yake k'ara masa jin dad'in abinda yake yi dan hakan da take yi kamar tana taya shi ne. Jikin tane yayi sak ta daina juye-juyen ta tsaya cak tana jin abinda yake yi mata har cikin jikinta.

Babu zato babu tsammani taji ya gama b'alle duka mallaban gaban rigar ta ta bud'e ta gaba ta sake yunk'urin kwacewa ya sake rik'e ta babu yadda ta iya haka ta sake kulle idanun ta tana jin yadda yake mata abinda hankalin ta bazai d'auka ba, k'afar ta bazata iya d'aukar ba a wannan lokacin hakan ya saka k'afar ta fara rawa ta koma jikin sa gabad'aya ya d'auke ta cak ya k'arasa kan gadon ya kwantar da ita yabi bayan ta shima ya kwanta yana cigaba yana yamutsa mata jikin ta.

"Me kike so nace Muwadda? Kina so kiga zuciyata sannan ki amince da ina sonki?" Ya furta a daidai kunnenta amma kuma yak'i bata damar magana. Tayi shiru ta kasa magana sai bugun zuciya da ya addabe ta har kunnen ta take jin bugun ta. "I love you so muchhhhhh!" Yaja kalmar much d'in a kunnen ta daga nan bata sake jin wata magana ba.

*Shud'ewar wasu mintina.*

? ? ? ? Yadda fuskar sa ta jik'e da gumi sai ka d'auka ruwa aka watsa masa rawa jikinsa yake yi hak'oran sa suna had'uwa da juna, gab, gab, gab haka jikin sa yake rawa har gadon amsawa yake sabida jijjigar da yake yi. Kansa sarawa yake yi yana ji kamar zai fashe ya tarwatse kwakwalwarsa ta watse a k'asa, marar sa ciwo take masa wacce bata tab'a yi ba tunda Allah ya kawo shi duniya sai a wannan lokacin ya cure a cikin bargo gumi na zuba a jikin sa kamar ruwa.

Hankalin Rauda in ya kai dubu ya tashi duk da abinda ya faru tsakanin su tana jin zafin jikinta har lokacin kuma babu dad'i kanta ciwo yake amma ta nemi nata ciwon ta rasa ganin yadda yake jijjiga kamar mai manyan aljanu. Tun lafawar komai yanayin sa ya fara canjawa kansa ya fara ciwo haka jikin sa bata yi aune ba ta ganshi a wannan yanayin.

Towel ta shiga band'aki ta d'auko ta d'aura ta haura kan gadon ta zauna ta d'ago kansa ta d'ora a cinyar ta tana kuka tana fad'in, "Asad me ya same ka haka? Meye yake maka ciwo?." Baya iya magana sai rawa da jikinsa yake yi da sauri hankalin ta ya kuma tashi ta fara tofa masa addu'ar da tazo bakin ta a fuskar sa.

Gani tayi hakan baya aiki ta dire daga kan gadon dirowar da tayi taji ciwo sosai a jikinta ta d'an tsaya tana hawaye kafin ta k'arasa inda alkur'anin ta yake har zata d'auka sai ta tuna daga ita har shi basu da tsarki sai ta fasa ta fita da sauri ba jimawa ta dawo da ruwa a kofi tana tofa ayatul kursi da a'uzubika bi kalmatullayi tammat min sharri ma kalaq.

Sai da tayi k'afa bakwai sannan ta koma inda yake ta fara zuba masa a fuska taga ya zubara kamar mai aljanu ta sake zuba masa taji yaja numfashi amma har lokacin jikin sa rawa yake yi, ta saka masa kofin a baki dan yasha amma yak'i sha ta rasa yadda zatayi dabara ta fad'o mata ta zuba a bakin ta ta zame ta saka bakin ta a cikin nasa tana d'ura masa masa ruwan yana dawowa tak'i cirewa duk da yadda jikin sa yake rawa bai saka ta cire ba sai da taga ya had'd'iye sannan ta k'yale shi ta cigaba da zuba masa tana yin ko wacce addu'a da tazo bakin ta.

A hankali taga rawar jikin da yake na raguwa kafin taga ya daina gabad'aya bacci ya d'auke shi. Ajiyar zuciya tayi har lokacin kansa na cinyar ta ta shafa fuskar sa da duk ta jik'e da ruwa, tuno abinda ya faru take yi yadda komai ya gudana a tsakanin su da yadda yake k'ok'arin furta mata kalma mai dad'i da kuma lokacin da abin ya tsaya can bayan ya janye jikin sa daga nata. Numfashi ta sauke ta kuma kallon sa lokaci d'aya take jin k'aunar sa na shiga cikin zuciyarta da kuma tausayin sa wanda bata san dalilin hakan ba.

Idanunta ta share ta zame kansa daga cinyar ta tana kallon gadon duk a jike amma babu yadda zatayi baza ta iya d'aukar sa ba balle ta d'auke shi daga wajan ta canja masa wani wajan. Tashi tayi tana cize bakin ta domin Allah ya sani tana jin zafi ta rashin lafiyar sane ya saka take daurewa ta shiga band'aki ta gyara kanta sannan ta fito ta saka doguwar riga ta zauna a gefe tana kallon sa kanta nayi mata mugun ciwo.

A gefe ta kwanta tana kallon fuskar sa ta d'ora hannu akan fuskar sa tana shafa fuskar aa hankali har bacci ya kwashe ta.

*&&&*

? ? ? ? ?? Tunda ta shiga take a zaune bata ce komai ba shima kuma baice ba domin in dai batayi magana ba bata isa yayi mata ba, yadda take ji da sarauta haka yake ji shi ya mulki dubban jama'a ita kuwa a k'arkashin sa take. Kusan mintina goma haka kafin ta motsa k'afar ta tace, "Takawa daman magana ce akan dawowar Asad tunda ka bayar da sarautar bai kamata ace anyi sarki biyy a lokaci kad'an ba."

Baice mata komai ba ta sake sauke numfashi tace, "Shine nace mai zai hana ka saka shi ya dawo domin ya karb'i sarautar sa da wuri." Nan ma bai kula ba ta kalle shi taga bama ita yake kallo ba ta sake cewa, "A ganina dawowar sa da wuri shine abinda ya kamata ayi, da ya dawo sai ayi bikin sarautar sa da bikin sa da Jidda." Nan ma baiyi mata magana ba ta kalle shi tace, "Takawa magana nake yi fa." Nan ma bai kula ba ya cigaba da kallon labaran da ake yi.

Kamar ta kurma ihu haka take ji amma ya zatayi ita take nema dole tayi shiru tana kallon sa ta kuma cewa, "Allah ya taimake ka magana nake yi." Sai a sannan ya kalle ta yace, "Ina jinki." Ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido ta sauke kai k'asa tace, "yaushe akayi masa umarnin dawowa?."
"Ba yanzu ba."
"Amma meyasa ranka ya dad'e?."
"Haka nayi niya."

Ta taune bakin ta tace, "Amma Takawa bai kamata ayi hakan ba tunda har ka bayar da kujerar nan me za'a jira kuma?." Ya sake kallon ta yace, "to Rabi'a fad'a min abinda ya kamata sai nayi."
"Allah ya wuci zuciyar ka."
"Mtswww." Sake kallon sa tayi zatayi magana yace, "Ina da iko da Asad kamar ke, ina da ikon na saka shi yayi abinda nake so kamar ke, dan haka ki k'yale ni sai sanda naga dama zai dawo."

Hawaye ya taru a idanun ta tace, "Yanzu fa Asad ko nema na bayayi matar da ka aura masa ta juyar masa da hankali daga kaina gabad'aya, rabon da naji muryar Asad har na manta, wallahi ina so na ganshi kayi min izinin zuwa naje can koda bazan dawo bashi" ta fad'a hawaye yana sakko mata.

"Ban bada dama ba Rabi'a, indai nine wanda yake auren ki ban baki umarnin barin k'asar nan ba, in kuma kina ganin kin isa bismillah." Mama tace, "nidai gaskiya bazan zuba ido ina ji ina gani a raba ni da d'ana ba, dole naje inda yake."
"Indai ina da rai da lafiya baki isa fita daga Nigeria ba Rabi'a, ke ko garin nan baza ki bari ba sai na bada damar hakan."

Cikin kuka tace, "Shikenan yanzu ka sallamawa wata banza shi ta raba ni dashi ta raba shi da k'asar sa?." Bai amsa mata ba ta mik'e tsaye tana goge idanun ta ta gyara zaman alk'yabbar? tace, "Kayi hak'uri ranka ya dad'e amma sai na dawo da d'ana garin nan, sai ya dawo ya karb'i mulkin sa."
"Kayi duk abinda kika ga dama Rabi'a" abinda ya furta mata kenan ta fita zuciyar ta na sak'a mata hanyar da zata bi wajan ganin tayi abinda take so domin matuk'ar yana raye tabbas bazai bata damar yin abinda take so kamar yadda yace, dole ta d'auki mataki bazata zuba ido wata bak'a mai mummnar fuska ta kwace mata shi ba dole ya dawo ya cika mata burin ta na zama sarki ya kuma auri Jidda........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*042.*

? ? ? ?? Da ciwon kai ya tashi zaune idanun sa har lokacin a kulle ya jingina da fuskar gadon yana sauke numfashi a hankali, ya jima a haka kafin ya bud'e idanun yaga d'akin babu haske ko kad'an ya zura hannu gefen sa ya kunna switch d'in wutar nan take haske ya bayyana a wani sashe na d'akin. Agogo ya fara kalla yaga k'arfe uku da arba'in na dare ya kalli d'akin gabad'aya abinda ya faru yana dawo masa a hankali.

Lokacin da ya gama tuna abinda ya faru sai ya kalli kansa yaga babu riga a jikin sa amma akwai short niker, tunawa yayi da lokacin da abin ya faru ai babu komai a jikin sa ya akayi yaga boxer a jikin sa?. Kansa ya dafe jin yadda ya kuma sarawa har lokacin marar sa a d'aure take ya daure ya tashi tsaye yayi saurin komawa ya zauna jin jiri na neman kayar dashi sai da ya d'an huta sannan ya tashi yana takawa a hankali ya fito zuwa falon, duhu shima falon bai kula da ita a akan kujera ba burinsa yaje ya fara tsarkake kansa ya wuce zuwa d'aki ya shiga tare da kullo k'ofa.

Band'aki ya shiga kai tsaye yana dafe da kansa har lokacin yayi abinda zaiyi a ciki ya fito d'aure da towel a jikin sa yana goge kansa da guda d'aya, shiryawa yayi ya saka doguwar riga mai santsi ya shinfid'a sallaya ya kalli gabas ya tayar da sallah. Ya jima yana sallah har akayi kiran farko na asuba sannan ya zauna yana lazumi yana cin sassuci akan abinda yake ji a jikin sa. Bayan an idar da asuba ya cigaba da lazumin sa yayi azkar kamar yadda ya saba ya d'auki littafan sa yana dubawa duk da baya jin dad'in jikinsa.

Rufe littafin yayi yana kallon wani waje daman yana sake tuno abinda ya faru har ya tsinci kansa a yanayin da bai tab'a shiga ba tunda yazo duniya, "kenan ita ta saka min shortniker?" Ya furta a bayyane yana d'an wara idanun sa yana jin wani iri a jikinsa. "Wanne irin yanayi ne wannan? Meya faru dani?" Ya fad'a yana dafe jijiyoyin kansa da suke sarawa masa ya ajiiye littafin ya tashi ya fito falon. A zaune ya same ta itama tana karatun alkur'ani da ka ba tare da alkur'ani a hannun ta ba tana bin ko wacce aya daki-daki tana lumshe idanun ta alamun karatun yayi mata dad'i.

A kan kujera ya zauna yana kallon ta kafin yaga ta kai k'arshe sura ta bud'e idanun ta ta kalli gefen da yake, had'a ido sukayi taga ya fad'a lokaci guda jijiyoyin kansa a mike har lokacin sai tace, "Ina kwana, ya jikin?" Ta fad'a a tare tana kallon sa.
Da hannu yayi mata alama da tazo inda yake ta mik'e a hankali tana takawa har taje gab dashi juwa ta kwashe ta ta fad'a kansa gabad'ayan ta dan ita ba k'arfi gare ta ba.

Zafi yaji a jikinta alamun zazzab'i ya cize baki yana kallon idanun ta kafin ta sauke nata k'asa, muguwar soyayyar ta yake ji tana sake shiga ko ina na jikinsa, son kasancewa da ita har abada yana sake ninkuwa sau babu adadi a zuciyar sa. Baya son rabuwa da ita domin yana sonta kuma ita kad'ai ce sirrin sa tunda gashi itace ta suturta masa jikin sa lokacin da yake kwance babu lafiya, ko mahaifiyar sa tun yana yaro rabon da ta saka mishi suttura to me zai saka rabu da ita bayan wannan babban matsayin da ta samu wanda babu wacce ta same shi?.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login