Showing 39001 words to 42000 words out of 259198 words
Chapter 14 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
wata harka ta watsewa su ita suke so.
Haushi ne ya kuma kama Farhan, ta Tashi ta bar hall ɗin gaba ɗaya ta fito, zagayen ta ta shiga yi a makarantar, tana 'yan leƙe leƙen ta, makarantar shiru kamar ba kowa duk suna hall ɗin da ake gabatar da Debate ɗin.
Katsam idonta ya sauka akan corper George a cikin wani aji, abunda idanuwan ta su kai katarin gani ne ya kiɗimata, wanda har ya kusa awon gaba da nutsuwar ta na wani ɗan lokaci, a very deep Romance with his ss3 student, she don't even know the name of the lady, ta san dai shine class mastern finalist student ɗin.
Jikinta ne ya hau wata irin tsuma, kuma ta kasa motsi daga gurin, se idanunta da take ta faman jujjuyawa kamar taiwa Sarki ƙarya.
Ba tsammani George ya waigo ya ga Farhan tai musu ƙuri da ido, da sauri ya cika Nasreen, ɗalibar da suke watsewa taren, yana ƙoƙarin tattaro nutsuwarsa ya daidai ta.
Ganin da Farhan tayi sun ganta Ya bata ƙwarin gwiwar, fizgo kuzarin da ta rasa na wani ɗan lokaci, cikin sassarfa ta ja da baya cikin hanzari ta nufi hanyar da ta sauka daga kan benen.
Kana ganin ta kasan a firgice take, kamar wadda ke shirin zarewa, ba zato ba tsammani tai karo da Sir Nazir yana ƙoƙarin hawowa kan benan.
Cak ta tsaya tana cigaba da rarraba ido, kamar mara gaskiya.
Kallon tuhuma ya bi ta da shi, yana ƙare mata kallo yana son gano me ya razanata haka, fuskarta take bayyanar da alamun rashin gaskiya?
Hanya ta bashi, dan ya wuce sannan ita ma ta wuce, amma ya tsyaa kyam yana cigaba da kallon ta.
Ba tsammani taji muryarsa yace "me kike yi a nan?"
Girgiza masa kai tayi tare da faɗin "Nothing sir"
"Nothing as how? Ke da waye a saman gurin nan, bayan ba kowa duk ana hall ɗin da ake Debate?"
Rasa amsar da zata ba shi tai, ta cigaba da tsatstasare shi da ido.
"Ke da wannan shashashan yaron ne a saman ko?"
A razane ta kalli Sir Nazir, tana son tabattar da abunda yake faɗa.
Ganin Farham taƙi magana ta cigaba da bin sa da idanu ya sa ya ji zargin sa na neman zama gaskiya.
"You Are Much more than stupid Farhan, ki cigaba da biyewa RUƊIN ƘURUCIYA, Kina rusa Rayuwar ki, nan gaba se kin yi kuka da idonki, a lokacin da kuskuren da ki kai ba ze gyaru ba, ki cigaba da ba shi damar keɓewa da ke, sheɗan na buga muku ganga, nan gaba zaki gane shayi ruwa ne stupid girl"
Maimakon ya hau saman benen, se ya fasa ya juya ya sauka, zuciyarsa na ƙuna, ganin yadda rayuwar yara mata masu ƙananun shekaru, ke lalacewa saboda RUƊIN ƘURUCIYA.
Farhan kuwa kasa matsawa ta yi daga in da take, maganganun sir Nazir suka cigaba da sukar zuciyarta, yana zarginta da wani abu, wanda ba shi da tabbas a kai, dan duk wannan masifar da yake a yanzu, bashi da wata hujja da ze kafa, akan ta, amma ya sa mata ido yana binta da miyagun maganganu, tabbas duk da ƙanƙantar shekarunta, tasan idan har aka zarge ka da keɓewa da wani namiji, to kuna aikata wani abune da be kamata ba, take ta tuno abunda ta gani yanzu a saman benen, kenan da irin abun Nazir yake zarginta kenan?.
Hawayena ya shiga bin fuskarta, fan take ta ji ranta yai ƙololuwar ɓaci, haka ta sakko jikinta a sanyaye ta tafi hanyar gate ɗin fita ta zauna, ana kaɗa jiniya, tai gaba ba tare da ta jira kowa ba.
Tun ranar da Nazir yai mata wannan zargin, gaba ɗaya se ta tsargu take ganin kamar kowama haka yake kallonta, dan haka kasancewar da ma sun kammala jarrabawa, ba ta sake zuwa makarantar ba har aka yi hutu.
Hakan ya damu Sadik sosai, ganin ba ta zuwa har a kai hutu, ranar da za'ai hutu ya zo da system ɗin sa, aka tura masa fina finai, wanda ze dinga kallo kan a koma school.
Satin da a kai hutu, a satin za'a fara bikin Ussy, ana ta shirye shirye, mussaman Sadik ya bugo nasa invitationsa ɗin, da ze rabawa abokan sa.
Gefe ga son ganin Farhan da yake yi, gashi yasan gidan su Farhan Akwai tsaro sosai, dan mahaifinta malami ne, idan ya je gidan su Farham be san me zece ba.
Shiryawa yai, ya tafi gidan su Khairat, a falo ya tarar da ita tana cin Abinci.
Sadik yace "Ina Mama?"
"Ba ta nan, lafiya na ganka kamar an jefo ka? Ka wani sha Manyan kaya kamar wani ango, ni na taɓa ganin ka a manyan kaya kuwa?"
Sadik yace "Khairat gidan su Farhan na ke so ki rakani dan Allah"
Yamutsa fuska Khairat ta yi tace "wace hakan?"
"So nake na bata invitation, tace idan ban kai mata gida ba baza'a barta taje ba, ni kuma i dont know how to explain myself idan naje, shiyasa nace bari in zo muje tare"
Khairat tace "to ai ita Farhan ɗin nake son jin wacece?"
" 'yar ajinmu ce" ya bata amsa.
"Gaskiya ban yadda ba, kana yawan kirana da Sunan ta, ko 'yar ajin ku ce akwai wani abu a tsakanin ku"
"Eh budurwa ta ce"
Yatsuna fuska Khairat tayi tace "kuma shine ni zan raka ka?"
"Kinga idan ba zaki ba ba se kin rainamin hankali ba" ya faɗa a kausashe.
"Naji zani" ta faɗa cike da ɓata rai.
Ta tashi taje ta canza kaya, ta fito ta tarar da shi in da ta barshi.
Yau Sadik da kan sa yake driving, suna tafe yana tsarawa Khairat abunda za su faɗa.
A bakin layin su Farhan yai parking, gabansa se faɗuwa yake, ya hango mahaifin Farhan zaune a kan dadduma, yana tilawar Alƙur'ani.
Khairat kuwa ganin gidan da Sadik ke dosa ya sa ta ɓata fuska, tun daga farkon unguwar kasan ta talakawa ce, ko ina kwata, se wari kwatocin ke yi, ga wasu gungu gungun awaki da tumaki da ke kaiwa suna komowa a tsakanin layukan.
Ga kaji da ke ta sake haƙe kwatar da aka kwashe aka zubar a gefen hanya, gaba ɗaya haushin Sadik Yakamata, gasky Prince ya faɗo ya rasa in da ze samo budurwa se a wannan unguwar talakawan, sedai ba ta da ikon Magana, yanzu ze hayayyaƙo mata, haka tai shiru ta cigaba da bin sa.
Suna zuwa in da Mahaifin Farhan yake, Sadik ya samu guri ya ɗan risuna.
Mahaifin Farhan ya rufe Alƙur'anin gabansa ya kalli Sadik da Khairat, yace "Sannun ku da zuwa"
Sadik ya ƙara nustuwa yace "Abba ina wuni"
Baban Farhan yace "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya gida?"
Sadik ya ƙara nutsuwa yace "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, dama ni ɗan makarantar su Farhan ne, wannan ƙanwata ce ajinsu ɗaya da Farhan a Makaranta, Yayan mu ne ze Aure, shine muka kawo mata katin gayyata ko za'a barta taje"
Sadik yai maganar tare da ɗakko katuna a aljihunsa ya miƙawa Baban Farhan.
Ya sa hannu ya karɓa ya duba, ya kalli Sadik ya jinjina kai, dan sunan mahaifinsa d sananne ne, ya ƙara tabattar da Allah ne kawai ya yi Farhan za tai wannan Makaranta, ban da haka ina ita ina karatu da 'ya'yan Alhaji Abdullahi.
A fili yai murmushi yace "Masha Allah, ai komai da sanarwa yana da daɗi, Allah ya sanya Alkhairi, shiga ki kai mata katin"
Khairat ta karɓa, ta nufi gidan da mahaifin Farhan ya nuna mata, tana sake tsantsame jikinta, dan ita ƙyamar gurin take.
Baban Farhan yana da kirki sosai, ya din ga jan Sadik da hira, tun Sadik na jin nauyin sa, harya saki jiki suka cigaba da hira sosai.
Yadda Sadik ya zo cikin shiga ta mutunci da girmamawa, ba ƙaramin burge mahaifin Farhan yai ba.
Khairat kuwa sallama ta yi tana ƙarewa gidan kallo.
Gidan tsaf da shi, ko tsinke ba bu a tsakar gidan, se ƙamshin turaren wuta da ke tashi.
(Dama ita tsafta ai ba se me kuɗi ba)
Sallama Khairat ta yi, ta tsaya a tsakar gida, Umman Farhan ce ta amsa mata, sannan ta bata izinin shiga.
Ta shiga ta gaida maman Farhan, ta amsa mata cikin kulawa.
Khairat tace "dama gurin Farhan na zo, na kawo mata katin bikin yayan mu"
Umman Farhan tace "Allah sarki, Allah ya sanya Alkhairi.
Ta nunawa Khairat ɗakin da Farhan ke ciki.
Ta shiga ta tarar da Farhan, sanye da dogon hijjabi ta na karatun Alqur'ani.
Khairat ta samu guri ta zauna, Farhan ta dakata ta kalli Khairat, dan ba ta santa ba "Sannu da zuwa"
Khairat tace "Yawwa, Farhan ko?"
"Eh, sedai ban ganeki ba"
"Ƙanwar Sadik ce"
Kunya ce ta kama Farhan, tai murmushi tace "Allah sarki, sannu bari in kawo miki ruwa"
Khairat tace "No, ba se kin kawo ba, dama katin gayyata ne na bikin Yayan sa, yace mu zo mu kawo miki yana waje, idan da hali yana san ya ganki"
Shiru Farhan ta ɗanyi tace "ai ban san yadda zan fitan ba ne, ina jin tsoro Abba na yana nan"
Khairat ta ɗan ƙare mata kallo a ranta tace 'taɓ, rayuwar yaran talakawa ba tai ba sam, wace irin jaraba ce wannan dan baban ka yana nana ace ba zaka fita ba?'
A fili tace "ai ba daɗewa za ki ba, kice kawai zaki rakani ne, se muje ku gaisa kawai"
Har ga Allah, Farham na son ganin Sadik, cikin sanyin jiki ta miƙe ta tafi ɗakin Umman ta, ta nemi iznin raka Khairat, ga mamakin ta se Umma ta amince, har da bawa Khairat ɗin kyautar turare, zaton ta ƙawar Farhan ce.
Khairat kuwa a ranta mamakin irin wannan rayuwa take, saboda tsabar abu Yarinyar ko wayon yadda zata fita ba ta da shi, fita rakiyar ma seta tambaya, lallai 'ya'yan talakawa na rayuwar takura da rashin 'yanci.
Cike da faragaba ta bi Khairat suka fita, cikin sa'a da suka fito baban Farhan ba ya ƙofar Gidan.
Ta hangi Sadik zaune akan barandar da ke gefen gidan su, ya sha shadda dark blue, harda hula kai kace wani babban mutum ne, ba ta san lokacin da ta saki wani ƙasaitaccen murmushi ba, shima ɗagowa yayi ya kalleta yai mata murmushin, tare da sauke ajiyar zuciya a jejjere.
Suna zuwa in da Sadik ke zaune ta sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta.
Sadik yace "Madam kawai se nemanki nai na rasa a makaranta, ki ka dena zuwa why? Ki ka bari ina ta cigiyar ki"
Kasa Magana tayi, saboda fargabar kar wani ya ganta ko babanta ya dawo, ga Khairat a tsaye a gurin.
Ganin yadda ta kasa sakewa, ya sa Sadik yace "zo muje daga bayan layin ku naga You are not comfortable here"
Duk da Farhan na cikin fargaba, amma ba zata iya yiwa Sadik musu ba, ta bisu suka nufi in da sukai parking.
Suna zuwa Khairat ta buɗe gaban mota ta shige, ta bar Sadik da Farhan.
Ganin Khairat ta basu guri, yasa Farhan yin ajiyar zuciya tace "ina wuni?"
"Se Yanzu zaki gaishe ni, kin ƙi ko kallona se wani ƙasa kike da ido kina kallo na, ki ɗago ki kalleni sosai"
Murmushi tai, ta rufe fuskarta tace "kayan nan sun maka kyau"
Sadik yace "dagaske?"
Ta jinjina kai alamar eh.
Yai murmushi yace "Alhamdilillah, Tunda sun burgeki, na haɗu da Abba a waje, munyi hira da shi sosai, Your father is very kind, Allah yasa idan aka zo nema min Auren ki ya bani, kar yace nayi yaro da yawa"
Shiru tai ta sake sunkuyar da kanta tana murmushi.
Shima murmushin yai yace "Anyway, meyasa ki ka dena zuwa school?"
Gaban ta ne ya faɗi, da tuna abunda sir Nazir yake zarginta da shi, a zahiri ta basar tace "Nothing naga ba'a komai ne a school ɗin"
"Shine, kika dena zuwa duk tunanin ki ya dameni, ga shi ba ki da waya balle in dinga kiran ki a waya"
Tai shiru ba tace komai ba.
Sadik yace "yanzu dai zaki zo bikin yayan nawa?"
Farhan tace "Ai ka kawo katin gayyata, za'a barni insha Allah"
Murmushi Sadik yai, wani farinciki ya kama shi, yace "Alhamdilillah, naji daɗi sosai"
Farhan tace "meyasa kake murna dan zan zo?"
Ya so ya gaya mata dalilin sa, amma se ya fasa dan yasan tsaf zata fasa zuwa, ya gyara tsayuwar sa yace "My dan Allah ya zan dinga samunki a waya ne? Kin ga hutu za'ai ina son in dinga jin muryar ki, ko in dinga zuwa gida in ganki?"
Zare ido Farhan tai, ta girgiza masa kai tace "A'a, Abba ze tambayi dalilin zuwanka"
"To meye a ciki? Se mu faɗa masa gaskiya"
"A'a dan Allah kar ka dinga zuwa"
Sadik yace "to naji, yanzu ki bani lambar da zan dinga kiran ki in same ki a waya"
Farhan ta ɗan yi shiru, dan tabbas ita ma tana son hanyar da zata dinga waya da shi, dan ko ba komai a yanzu bayan karatun ta ba wanda yake ɗebe mata kewa sama da Sadik.
A hankali tace "ka bani lamabar wayar ta ka, idan na samu waya ni se in kira ka"
Yace "ki min ko flashing ne, ni kuma zan kiraki insha Allah"
Ya ɗakko jotter ya rubuta mata ya bata.
Tace "Bari in koma gida, kar a fara nema na"
"Ok to shikenan, amma tsaya muyi hotuna, wand zan din ga kalla ina jin daɗi"
Ba tace komai ba se murmushin nan nata me ɗaukar hankali.
Ya ciro wayarsa yai mata hotuna, sannan ya kalle ta yace "se Allah ya kaimu Lokacin bikin, i love You, take a good care of yourself"
Juya tai tana murmushi ta na jin yadda kalaman nasa ke sake tasiri a zuciyar ta.
Shi kuma ya koma motar su.
Yana shiga Khairat tai tsaki.
Ya kalleta yace "ke kuma lafiya?"
Khairat ta yamutsa fuska tace "kai kam me ka gani a wannan bagidajiyar 'yar talakawa?"
A hargitse Sadik ya kalleta yace "wallahi ki ka kuma zaginta sena miki rashin mutunci, a haka nake sonta"
"Allah ya baka haƙuri, amma gaskiya ta fiye kidahumanci, ace dabarar da zatai ta fito ma se da na gaya mata, ta fiye tsoro gashi kamar ba wayayyiya ba, ga ta yarinya sosai"
Sadik be ce mata uffana ba ya fara jan motar, jin yai mata banza ya sa ta ja bakinta ta tsuke, dan ta san idan ta matsa kuma, faɗa za suyi.
Suna tafe lokaci lokaci, seya shafi sumar kansa yai murmushi, yana jin so da ƙaunar Farhan ɗin na ratsa shi.
Kai tsaye gidansu suka wuce, suna zuwa yai parking a waje ya kalli Khairat yace "sauka, ni zani wani guri ne yanzu, maybe za'a kawomin wandon jeans, ki karɓa ki bawa Mother ta ajiyemin"
Khairat ta ɗan taɓe baki tace "to" ta buɗe motar ta fice, shi kuma ya ja motar yai gaba.
Khairat kuma ta shiga cikin gidan, sosai gida ya fara ɗaukar harami, saboda shirin shiga hada hadar biki.
A falo Khairat tai karo da Nana, tana ta hira ita da talatu me aiki, ta kalli Nana tai tsaki.
Nana ta kalli Khairat tace "Sannu tsaka"
Ba ta kuma kula Nana ba, ta shiga Kitchen ta ɗakko madara a roba, ta dawo falo ta na sha.
Dawowarta babu daɗewa, Sadik ya kirata a waya.
Ta ɗaga tace "Yaya ina jin ka"
"Kije gate ki karɓo min saƙon nan ki ajiyemin"
Khairat tace "to"
Ta ajiye robar hannunta ta fita, ba daɗewa ta dawo hannunta ɗauke da wata leda me kyan gaske.
Ta zauna ta buɗe ledar ta fito da wani haɗaɗɗen wandon jeans, kai da gani kasan wandon me tsada ne sosai, sedai abun takaici duk an yayyaga wandon ta cinya zuwa gwiwa, kamar kare ya tattauna.
Nana ta kalli wandon a ranta tace 'wannan wane irin wando ne?'
Faruk da ke fitowa daga ɓangaren Mother yace "Khairiyya, wannan wandon fa?"
Khairat tace "Wandon Prince ne, yace in karɓa in bawa Mother ta ajiye masa, kuma ban ganta ba"
Faruk yace "wannan wandon na ganshi Online ana advertising ɗin sa, yafi dubu goma a kuɗin Nigeria"
Khairat tace "Ai Sadik akwai rigima in yaso abu, amma wandon yayi kyau sosai"
Faruk yace "hakane, ina ga dai Mother ba ta nan, amma ki ajiye masa shi a wani gurin"
"Ko kuma in baka ka ajiye masa?"
Faruk yace "No, ajiye masa, Mother yace ko bawa, akan wandon nan se ya ɗagamin hankali"
Khairat tace "ok bari in Ajiye masa kawai"
Nana kam jinjina lamarin ta cigaba da yi a zuciyar ta, yanzu wannan wandon me kama da tsumma ne wai yafi dubu goma, gaskiya mutan Gidan nan ba su san darajar kuɗi ba, wannan ai almubazzaranci ne"
Faruk kuwa tuni ya bar falon, Wayar Khairat ce ta fara ringing, dan haka ta miƙe ta fita waje dan ta amsa wayar.
Tana fita zuciyar Nana ta dinga raya mata abubuwa daban daban, dama a ƙule take da Sadik da Khairat ɗin gaba ɗaya, dan haka ta miƙe ta waiga falon taga babu wanda yake kallonta.
A hankali ta ɗau ledar da wandon yake, ta ciro wandon ta zura a hijjabin ta, ta zaga kan baranda ta samu wani ruwan mopping da aka gama mopping da shi yai baƙiƙirin saboda datti, ta zura wandon a ciki.
Seda ya naɗi ruwan dattin nan Sosai Sannan ta matse shi, ta yar a gurin ta ƙara gaba.
A ranta tace "gobe ma ka sake zagina da kai da wannan shashashar Khairat ɗin, zaku gane kuren ku"
Ita kam Khairat ko da ta koma, ta cigaba da sha'anin ta, ta manta da batun wandon Prince.
WANDA SUKA RIGA SUKAI PAYMENT, IDAN FREE PAGES SUKA ƘARE SU KAWAI ZAN TURAWA TA WHAT'S APP, WANDA BE PAYMENT BA ZE IYA SA A MANHAJAR AREWABOOKS, DAN YAFI SAUƘI.
DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
RUƊIN ƘURUCIYA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Writer of
WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)
_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_
⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️
SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN