Showing 126001 words to 129000 words out of 259198 words
Chapter 43 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
min kuka haka kamar wani ɗan yaye, me ka rasa ci ko sha? Ka nutsu ka kwantar da hankalinka ka zauna, idan lokacin da suka ga ya dace zasu dawo da kai, ka gaishe su" Abba ya katse kiran.
Sadik ya ajiye wayar yana kuka yace "Abba Why"
Nana na tsaye a bakin ƙofar ɗakin, an aiketa ta kirashi taji duk wauar da yayi, jikinta yai matuƙar yin sanyi da jin yadda Sadik ke kuka, a saɓule ta koma tsakar gida ta zauna tai shiru.
Inna tace "yana ina?"
Nana tace "bacci yake"
"Wane irin bacci ba yanzu ya wuce ɗakin ba"
Nana tace "to Inna yayi bacci fa"
Inna ta ƙyaleta ta cigaba da aikin ta.
Se can daf da la'asar sannan Sadik ya fito, idanunsa sunyi jajir sun kumbura, kana kallo ka san kuka yayi.
Ya shiga banɗaki ya fito, ya kalli in da Nana ke kwance akan cinyar Inna, Innan na tsefe mata dogon gashin ta.
Sadik yace "ke a ina ake cajin waya a garin nan"?
Banza Nana tai masa ta cigaba da lumshe ido.
"Ba kya ji na ne?" Yai maganar yana kallonta.
Inna a ranta tace 'wannan ɗa ba dai tsarin ido ba'
"Ni karka sake cemin ke, kuma in dai garin nan ne se sati sati ake kunna inji a gurin masu caji"
Tsaki Sadik yai ya jiya ya nufi ɗakin da yake, Inna tace "ga alala can a ɗakina ka shiga ka ɗauka, na aika a taso ka tace min bacci kake"
"Ni bana cin wannan abar"
"Ka huta" Inna ta bashi amsa, sannan ta ɗora da "babu me sake takuraka kaci wani abu, in ka mutu da yunwa kai ka so"
Be kuma bi ta kan Inna ba ya shige ɗakin.
"Inna" Nana ta kira sunanta.
"Na'am"
"Inna dan girman Allah ku ƙyaleshi ya koma gida, wallahi har ya rame gashi baya cin abinci sosai, dan Allah ku bari ya koma gida"
"Sannu me ɗan uwa, ai seki maida shi dan ubanki"
"A'a ni ba ɗan uwana bane, amma Inna kuka fa ya ke yi ɗazu, wallahi ni tausayi yake bani, dan Allah ku barshi ya koma gidansu"
Inna tai mata shiru, ta cigaba dai mata tsifa.
Nana ba ta gaji ba ta kuma cewa "Inna nan fa Yayansa yace 'dan Allah ki ba dani su tafi dani kika hana, amma shi meyasa zaku riƙe shi?"
Wani uban duka da Inna taiwa Nana a ka seda ta tashi ta zauna tana kallon Inna.
"Sekije ki samu kakanki ki masa wannan tistiyen bani ba, mara kunya"
Nana tai shiru tana sosa kai, ita dai ba taga aibun maganar ta ba.
Ta faki idon Inna lokacin ta shiga banɗaki, ta ɗebo kilishi da Alkaki, cikin sanɗa ta shiga ɗakin da yake.
Ta tarar da shi a kwance yayi rigingine, yana kallon rufin ɗakin.
Ta jefa masa ledar kan katifarsa, ta juya ta bar gurin da sauri.
Kamar yadda Sir Nazir yai mata bayani, da daddare bayan taci Abinci tai shirin kwanciya, ta ɗakko jakar makarantar ta, ta ɗakko kwalbar nan tai bismillah ta shanye ɗan ruwan dake cikin kwalbar, da ta shanye ta buɗe tagar ɗakin ta ta baya, ta jefa kwalbar waje.
Ta dawo tais shiru tana jiran taji wani sauyi amma shiru.
Tana nan tana saurare Nazir ya kirata hankali a tashe, tana ɗagawa yace "Fatima yaya, ya fita kuwa?"
"Ni ba abunda naji" ta bashi amsa.
"Kuma kin shanye duka?"
"Eh na sha kamar yadda kace"
"To shikenan, ze fita insha Allah, Allah ya tashe mu Lafiya yasa kar a samu wata matsala"
Tace "Ameen"
Wasa wasa har bacci ya kwashe Lilly ba taji komai ba.
Cikin bacci taji wani irin azababben ciwo, tun daga kanta har yatsun ƙafarta, ga wani irin ciwo da mararta keyi kamar ana fizgo wani abu.
A razane ta buɗe idonta, taja jikinta ta kunna fitilar ɗakin, gadon da take kai yayi kaca kaca da jini, wanda hakan ya tsorata matuƙa ta fasa ihu da ƙarfi!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
Zabura Nana tai ta miƙe daga kan kwanon gabanta, ta kalli Sadik a fusace tace "meye haka zaka shigo mana ɗaki ba sallama" tai maganar tana waiwayen in da zata ga hijjabi ta sa ta suturta jikin ta.
Kan ta kai ga miƙa hannu ta ɗakko hijjabin, ya kai hannu ya danƙota, zazzare ido ta shiga yi ƙirjinta na dukan uku uku.
"Ka sakarmin hannu meye haka? Idan Inna ta zo ta ganka fa, kalen ka jamin masifa?" Tai maganar ƙirjinta na bugawa da sauri, saboda rashin sabo kasamcewar sun samu kusanci Sosai a tsakanin su.
Ba tare da yace mata uffan ba ya bata wasu irin lafiyayyun maruka guda biyu a kowane kunci.
Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki, Zani na neman kwancewa saboda Azabar zafi, da wayonta dai wani be taɓa marinta ba.
Wani irin kuka ne ya ƙwace mata, tana wata irin sheshsheƙa tana neman ta shiɗe.
"Kin ɗauka ƙarya nake da nake miki warning akan ki kiyayeni? Ni zaki kalla ki dinga zagi sa'anki ne ni? Ko dan kinga ina zaune a gidan ku shine zaki dinga gayamin abunda kika ga dama?"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, me zan gani haka? Kai Sadik wane irin abu ne haka? Wannan wace irin fitsara ce a cikin ɗakina?"
Hankaɗe Nana yayi, ta zauna a ƙasa daɓas, tare da dafe kuncinta da ke mata wani irin Azabar zafi, zanin nata ma ya gagare ta riƙewa, yana neman ya kwance gaba ɗaya.
Inna ta kalli Sadik tace "me kai mata haka?"
"Na sha gayamata ta kiyayeni, amma taƙi gani take ƙarya nake, shiyasa na dake ta"
"Kuma shine dukan saboda tsabar rashin ta ido ka biyo ta har ɗakina daga ita se zani ka daketa saboda kain' dai fitsararrene ba ka da kunya, daga ita se zani fa, da zanin ya faɗi fa, ka ganga tsirara?"
Sadik ya waigo ya kalli Inna yace "to meye a ciki? Wannan har mace ce? Aba kamar an daki gwangwanin madara, wannan ai bata wuce 'yar yaye ba, ƙwaila ce kuma ni ba abunda ya dameni kenan ba, zuwa nai dan in koya mata hankali"
Baki Inna ta buɗe kamar wata shashasha ta bi Sadik da kallo, wato har ya san wata ƙwaila da wadda ba ƙwaila ba.
"Allah ya sakamin, azzalumi mara imani, wallahi ban yafe maka ba, Allah yasa ai maka abunda ze baƙanta maka rai kamar yadda kai min"
Ko a jikinsa, yana jin ta ya bar ɗakin,ko waigowa be ba, saboda atleast ya rage haushin da ke cunkushe a ransa.
Nana kam sosai ta cigaba kuka, har fuskarta ta jawur saboda ta maru, ga shedar yatsunsa kwance akan kyakyawar fuskarta.
Inna ta kalleta tace "ince ko dai be miki komai ba?"
Cikin kuka tace "Inna fa marina yai har sau biyu"
Inna tace "to ina ruwana da marinki yayi? Ban sha gayamiki ki kiyayi yaron nan ba? Sam ba shi da ta ido, da ya miki tsirara ai da ya gama cutarki"
"Inna wallahi na tsane shi, dan Manzon Allah a maida shi gidansu kan ya kashe ni, ba wanda ya taɓa marina seshi wallahi Allah ya isa"
"Ba zaki dena wannan surutan da kike ba, in kuma jin bakinki, ke ganinki ma da yai daga ke se ɗaurin ƙirji be dame ki ba"
"Wallahi marin da yai min yafi zafi, ni Wallahi na zata ma zanin ya faɗi"
Duk da yadda Inna take a ƙule, seda taji tausayin Nana, Saboda yadda fuskarta ta koma jawur kamar ɗanyen Nama.
Riga Nana ta zura, ta fice daga ɗakin zuwa turakar Hakimi.
Tana zuwa ta tarar da Sadik a turakar Hakimi a zaune, da alama Magana suke.
Yana daga abunda Hakimi ba ya son gani, ganin damuwa a fuskar marainiyar jikar sa, saboda yana matuƙar tausayinta.
"Ya akayi ne? Kukan me kike na zaki Makaranta bane?" Ya jero mata tambayoyin.
Jikin Hakimi taje ta zube tana kuka. Sadik kuwa ya basar kamar ma be santa ba.
Hakimi yace "Ke da kakar taki ne?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.
'to meya faru?"
"Dan Allah Alhaji ka maida Yaron nan gidansu"
Wani shu'umin kallo Sadik yai mata, tare da maimaita kalmar yaro a hankali.
Hakimi yace "wane yaron tukuna?"
Ba Kunya ta nuna Sadik tace "gashi nan, wallahi na tsane shi, ko ganinsa ba na son yi"
Take Hakimi ya haɗe rai yace "ɗan uwanki ne fa, meyasa kuke furtawa juna miyagun maganganu haka ne?"
Cikin kuka Nana ta ɗago, ta nunawa Hakimi Fuskarta tace "kalli Fuskata, dukana fa yayi, da ni 'yar uwarsa ce ai baze dakeni haka ba kome nai masa"
Hakimi yace "Ke me ki kai masa ya dake kin?"
"Ko laifi nai masa seya dakeni haka?" Nana tai maganar wasu hawayen na zubowa daga idonta.
Hakimi ya maida idonsa kan Sadik yace "me tai maka kai mata wannan dukan haka? Kalli shedar yatsunka a fuskar ta?"
Kallo ɗaya Sadik yai mata, ya ɗauke kai yaƙi sake kallonta, kuma yaƙi Magana kamar gunki.
"Magana fa nake maka"
Sadik yai shiru ya sunkuyar da kai.
Hakimi yai murmushi yace "Yanzu nan, ka zo ka sani a gaba, kana min magiyar in bari ka koma gida, amma na fuskanci haryanzu ba kai laushi ba da sauranka, tashi ka bani guri"
Seda Sadik yai jimm kamar ba ze tashi ba, se kuma ya tashi yana kumbura baki ya bar ɗakin.
Nana kuwa ta cigaba da kuka Hakimi na rarrashin ta, Inna ce da ta shigo ta koretaz tace maza taje ta saka Uniform ta tafi Makaranta a haka, gobe ta kiyayi shiga sabgar Sadik.
Bayan fitar Nana Inna ta kalli Hakimi tace "Allah ya baka Nasara, nifa lamarin Yaron nan ya fara bani tsoro"
Hakimi ya numfasa yace "ba ke kaɗai ba, ni kaina haka, amma hakan ya samo asali ne daga rashin kyakyawar tarbiyya da be samu ba a gidan su"
"Tabbas ni zan faɗi wannan ma, kasan zuwa nai na tarar ya ritsata a ɗaki daga ita se ɗaurin ƙirji ya mareta, nai masa magana nace masa duk hukuncin da ze mata kamata yai ya bari se tana cikin sutura, a haka zata iyayin tsirara, Yaron nan ba kunya ba tsoron Allah yace min wai ai wannan ba mace nace ƙwaila ce, Yaron nan fa idan ba ai dagaske ba se abunda Allah yai, wai harya san ƙwaila ya san mace, ko da yake ba abun mamaki bane, tunda a kunne na naji yana gayawa uwarsa wai Aure yake so"
Hakimi yai murmushi yace "Manya gatan wasa, to be isa Auren bane?"
Inna tace "ya isa mana, da a zamanin mu ne ai tuni an masa mata, kuma jiya da Asubar fari ya shiga ya hau wanka, kaga kuwa ya tabatta ya isa Aure"
"Amma shine mahaifinsa yake son turashi ƙasar waje karatu? Shi duk baya ganin abubuwan mu da muka gani?"
Inna tace "wayasan masa? Yasa Aƙidar boko da yahudawa a zuciyar sa, gashi Allah ya haɗashi da matar da ita ma ba ta san abunda ya dace ba"
"Lallai kam, shikenan zanyi abunda ya dace a kai, na san abunyi, ai da zuwa yai ya sani a gaba yana so in bari ya koma gidansu, da har zan amince wannan yarinyar ta zo tana kuka, tunda abun masa hakane nasan maganinsa"
Inna tace "meye maganin nasa?"
"Ki zuba ido zaki gani".
Abu kamar wasa Lilly suka koma yadda suke ita da Sir Nazir, sedai haryanzu sheɗan na cigaba da hura musu wuta, tun da suka aikata son zuciya sheɗan ke ta sake ruru musu wutar fitina a tsakanin su.
Gashi Nazir ya tuba, yace baze sake aikata makamancin abunda yai ba dama be taɓa ba se a kanta, kuma baya sha'awar sake aikata abunda yai ɗin.
Sedai a duk lokacin da suke tare, se yai ta maza yake iya daure kansa, dan wasu lokutan idan a wayane ma ya dinga sakin layi kenan.
Yanzu ma ta gama zana jarabawar da zata zana, kasancewar makarantar ba kowa ya basu damar sakewa sosai da juna.
"Fatima" ya kira sunan ta.
"Na'am" ta amsa tana kallonsa.
"Babanki ze bani Aurenki kuwa?"
"Wallahi sir ban sani ba, amma meyasa ka tambaya?"
"Bana son mu sake aikata ɓarna ne, wallahi ina sonki da gaske, idan zaki iya Auren talaka kamata"
"Nima ina sonka sosai sir, sedai ban sani ba ko Daddy ze yadda ba, kuma ai kaga baze yuwu yai min Aure yanzu ba, a Jss3 fa nake"
Ya lumshe idonsa yana fesar da iska daga bakinsa yace "in my opinion, ina ga zan bar aikin nan in koma Jigawa kawai, ai dama na gama service ɗin naji daɗin zaman garin nan ne"
Ɗan zare ido tai tace "meyasa zaka koma?"
"Saboda in dena ganinki ko na samu nutsuwa, a baya ni babu wata mace da nake shiga wani yanayi saboda ita, amma idan har zan ganki da ƙyar nake samun saita kaina"
"To seka tafi ka barni?" Tai maganar a shagwaɓe.
"To ya zanyi Lilly, haka shine samun nutsuwa ta"
"But i love You, Please kar ka koma dan Allah" tai maganar kamar za tai masa kuka.
A hankali ya janyo ta jikinsa, ya ɗora hannunta a saitin ƙirjinsa, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri sauri, yace "kinji fa halin da nake shiga a duk lokacin da muke tare ko na ganki, ƙaddara ta kawoki cikin rayuwata, idan ban same ki ba, i better go back to my village"
Gyara kwanciyarta tai a jikin Nazir tace "no ba za ai haka ba, zan san abunyi nima gaba ɗaya karatun nan ya fita daga raina, dama ba wani ja nake ba, gara aimin Auren in huta"
"Karatun yana da kyau, amma idan munyi Aure zan bari ki cigaba, but Please help me"
Ta ɗago tana wasa da sajensa tace "don't worry Baby" a nan ma dai Allah ne ya rufa Asiri basu watse ba ni dai nai gaba.
Faruk na kwance a falo daga shi se boxers, yana kallon TV, yana missing ɗin Sadik sosai, se yaita kallon ɗakin Sadik ɗin yaga kamar ze ga Sadik ɗin ya fito daga ɗakin.
Knocking ɗin ƙofar yaji yana ayi, ya miƙe ya nufi ƙofar dan ya buɗe, yana mamakin waye da tsakar ranar nan haka.
Yana buɗewa ya ga Khairat a tsaye da tray a hannunta, seda gabanta ya faɗi ganin Faruk, jikinta ya ɗau rawa kamar mazari, ta shiga bin sa da ido, yadda gashi ya kwanta a jikinsa.
Yatsunsa biyu ya haɗa ya murza suka bada sauti, a saitin fuskarta Yace "ya dai? Ya akayi ne?"
Da ƙyar ta haɗiye yawu jikinta na rawa ta miƙa masa trayn da ke hannunta.
"Meye wannan?"
"Amm..dama nayi juice ne na cucumber na san kana so shine na kawo maka"
Yace "Wow, aikuwa kin kyauta, shiga ki ajiye"
Ta shiga cikin falon ta ajiye, tana cigaba da kallonsa, ba ta taɓa sanin kyan Faruk ya kai haka ba, gashi da ƙira me kyau, ga wani six packs a cikinsa.
Bedroom ya shiga ya sako jallabiya fara ya dawo falon ya zauna.
Se taji dama be saka ba ta cigaba da kallonsa a haka.
Yace "yau me kuka dafa ne a gidan?"
"Ai ba a gama girkin ba" ta bashi amsa.
"Ai ba cewa nai ko an gama ko ba a gama ba, cewa nai me kuka dafa, ko ince me kuke dafawa?"
"Ina ga shinkafa da miyar zogale"
Yace "what? Shinkafa da miyar zogale kuma?"
Tai saurin dawowa hayyacinta tace "shinkafa da miya ne"
"It seems something is wrong with you, tashi ki tafi"
Ɗan noƙe kafaɗa tayi, alamar ba zata tafi ba.
Yace "ai shikenan seki ta zama"
Ya maida idonsa ga tv, yana cigaba da shan juice ɗin.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ɗauka tare da yin sallama.
"Wa'alaikum salam Malam Faruku"
Cikin sauri Faruk ya gyara zama yace "ranka ya daɗe barka da warhaka"
"Yawwa barka, kuna lafiya?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah"
"Ka manta da mu, tunda kuka tafi ba ka sake zuwa ba"
"Ranka ya daɗe ai kai kace karmu sake zuwa, kuma wayarku ba ta shiga, saboda ba network"
"Ƙwarai kuwa anyi haka"
Faruk yace "Ya Sadik ɗin yake?"
Hakimi yai murmushi yace "yana lafiya ƙalau, muma sa'a akai wayar ta shiga, tun jiya ake neman layin mahaifinka yaƙi, kaima da kyar naka yayi, amma duk matsalar network ɗin nan ne, muna muna ƙoƙarin ganin yadda za'a shawo kan matsalar"
Faruk yace "Allah sarki, Allah ya temaka ranka ya daɗe"
"Ameen ya Allah, nace baban naka yana gari ne?"
"A'a ranka ya daɗe, kwanansa biyar da tafiya kuma ina ga se ƙarshen watan nan ze dawo"
"To shikenan, idan kunyi waya ka gaya masa, lallai lallai idan ya shigo gari ya zo ya sameni a nan"
"Insha Allah zan gaya masa ranka ya daɗe" Faruk ya so tambayar Hakimi a bashi Sadik su gaisa, amma se yaji nauyin hakan, tunda shi Hakimin be bashi ba, kawai ya ƙyale sukai sallama, ya bawa Hakimi saƙon gaisuwa ga Nana da su Inna.
Harya gama wayar Khairat kallonsa take.
Faruk kam haka nan ya tsargu da kallon da take masa yace "can You excuse me please?"
Seda ta ɗan tura baki sannan ta tashi, ta koma cikin gidan, a falo ta samu Mother tana Shan kankana, Mother ta dubeta tace "ya na ganki kina tafiya a hankali menene?"
"Bakomai Mother, yanzu Faruk su kai waya da kakansu"
Da sauri Mother ta ajiye kankanra da ta ɗauka take shirin kaiwa bakinta tace "meya ce masa?"
"Na dai ji yace wai yana neman Abba ne, idan Abba ya zo ace yana nemansa"
"Ko dai wani abun ne ya samu Sadik ɗin?"
Khairat tace "Anya kuwa? Ni dai banji yace wani abu ya sameshi ba, dan da wani abun ya sameshi baze ce se lokacin da Abba ya dawo Sannan zeje ba"
Mother ta girgiza kai tace "Allah sarki yarona"
"To Mother tunda Abban baya gari, ki shirya mana kije garin da kanki, ki ɗakko shi"
Mother ta girgiza kai tace "da ze yuwu ai da tuni nayi, zan fuskanci fishi da tashin hankali a gurin babansa idan naje, amma zan zuba musu ido in ga iya gudun ruwansu, fiye da watanni biyu an riƙemin ɗa an hanani ganinsa"
Ta ƙarasa maganar tana jin ƙwallar