Showing 84001 words to 87000 words out of 259198 words

Chapter 29 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13434

a hannunsa.

"Lilly' ya kira sunan ta.

Ta buɗe idanunta a kansa.

"Are You ok?"
Ta jinjina masa kai.

"Kina iya numfashi normal?"

Nan ma ta ɗaga masa kai.

Yace "sannu ko zaki tafi Class?"

Ta noƙe masa kafaɗa.

Ya tsuke fuska yace "meye hakane? Tashi ki tafi Class tunda ya lafa miki mana"

"Uhmm, Allah jiri nake ji, kaina ne yake juyawa"

"To bari in ajiyeki a ƙasan ki ɓata jikin ki"

Tashi tai daga jikinsa ta jingina da jikin table ɗin da kujeru suke.

Ya miƙe ya koma mazaunin sa ya ƙyaleta.

Jacket ɗinta dake ta ƙamshin turare ta cire ta ɗora akan table ɗin sa.

Ya ɗago ya kalleta "wai ke meye hakane, tashi ki barmin Office" ya faɗa a kausashe.

A raunane tace "Am sorry sir, i need air ne, da ƙyar nake numfashi and i mean it" tai maganar tana jan numfashi da kyar.

"Ok na gane, tashi ki lallaɓa maza ki tafi Class, su kai ki Clinic"

Yadda yake gumi da yadda yake har haɗo maganar da kyar ta tabattar da tarkonta yayi kamu, kuma ta gazgata abunda take karantawa a Novels.

Dama ba wani ciwonta da ze tashi, tayi hakanne dan ganin reaction ɗin sa, ta miƙe a hankali ta ɗau jacket ɗinta ta fice tana murmushi.

Har ta bar Office ɗin kallonta yake, se da ta fita sannan yai ajiyar zuciya, tabbas ya fara jin wani abu yana masa yawo a game da Yarinyar nan, kuma babu ko tantanma son ta yake.

But how comes will he falls in love with this little girl? Ya tambayi kan sa.

(Nace Mun gama Yaya Ammar, @ WATA kissar sai mata🙄 if you know you know, if you don't get it look for the book WATA KISSAR SAI MATA)



Seda Sadik ya tabattar da Farhan ta ɗan samu nutsuwa Sannan yace "zaki iya zuwa aji ko mu cigaba ds Zama a nan, kinfi son nan?"

"Zanje Class" ta bashi amsa.

"Ok"

Kawai ya ɗagota da kwanciyar da take, Sannan ya ɗan tsura mata ido.

A hankali yace "Sannu babyna, Allah ya baki mafita akan abunda yake damun ki"

Yai Maganar yana goge mata gumin dake goshinta da hannunsa.

Ta sakko daga kan gadon, ya rakata har Class ɗin su, Sannan ya koma aji, lokaci lokaci yana zagayowa yana dubata, tare da tunanin meke damunta haka a wannan ƙananan shekarun nata haka?.

Da aka tashi daga Makaranta ma, suna tafe a mota ta jingina da kujera ta lunshe idanunta tai shiru, taji hannun Sadik a nata.
Ba ta motsa tai shiru yana cigaba da wasa da yatsunta.
A haka har suka je in da suka sauketa, yau ko sallama ba suyi ba ta sauka ta nufi layinsu.

Da sallama a bakinta ta shiga gidan, sedai matar da tai karo da ita a tsakar gida ne, yasa Farhan yin murmushi tace "Adda kece kika zo?"

"Nice na zo yarinyar kirki, Ohh girman ɗan mutum ba wuya, kalli yadda Yarinyar nan ta ganɗame ta girma"

Farhan ta durƙusa har ƙasa ta gaisheta, matar tace "Farhan, gaskiya kin girma, yaushe rabonki damu?"

"Adda hanya ba kyau, kuma kusan duk lokacin da Umma za ta je ina Makaranta"

Adda tace "hakane kam, Allah ya taimaka"

Farhan tace "Ameen, ina su Amina baki zo da kowa ba?"

"Amina na can, na baro su a gida, an kawo mata kuɗin Aure wancan satin"

Jimm Farhan tayi, Aminan sa'arta ce, dan ita Farhan ɗin ma ta bata watanni kusan bakwai, amma har za'ai mata aure, dama su iyakacin karatun yaran su primary ne.

Umman Farhan na jinsu ba tace Komai ba, Farhan ta tashi, ta  shiga ɗaki ta canza kaya, ta ɗau bokiti ta shiga banɗaki dan yin wanka.

A nan banɗakin ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, tana jin daga ƙasa yadda mararta ke ƙullewa, ƙirjinta kuma na mata zafi, ta kalli kanta ta lumshe ido hawaye na zuba daga idonta ta hau tunani 'Anya Sadik ze yadda ya aureta idan yasan ta kamu da Cancer Mama, babban abunda yake ɗaure mata kai da ciwon shine se lokaci lokaci, ida  ga kusa period take jinsa, gashi ita ba abun ta tafi Asibiti ba'

Tana cikin tunanin ta jiyo Muryar Adda Hafsa tanawa Ummanta Magana da fullanci.

"Ke Mairo, yanzu haka zaku cigaba da barin yarinyar nan tana Girma a gaban ku da sunan boko? Kalli ƙirjinta fa kalli yadda 'ya ta cika haka"

Umma tace 'ni kaina abun yana damuna, babanta ne ke son tayi karatun, babban abunda ya ke bani tsoro shine watanni uku baya ta fara al'ada"

Dafe ƙirji Adda Hafsatu tai tace "Al'ada kuma Mairo, kinga tun wuri ku kawar da Yarinyar nan, bokon me yarinya ta zanƙale haka a gida"

"Ba laifina bane, na mahaifinta ne, shi kuma kin san ba'a tursasa shi, shine yake son tayi karatun nan, amma nima nafi ganewa tai Auren"

"To ina fatan dai akwai manemi?"

"Eh to, akwai wani a nan maƙwabtan mu, Almajiri ne, malaminsu yaiwa babanta Magana akan yana so a bawa Yaron, to yana da nustuwa dai, amma babanta yace karya fara zuwa se an kwana biyu, amma ya amince ya bashi ita"

"Wane irin se an kwana biyu, ke ni in be yuwuwa, se in ɗauketa be sani ba in tafi da ita can ƙauye, baffa ya aurar da ita a can, haka akeyi? Mu munyi bokon ne, amma duk gashi an aurar da mu mun zauna har mun haife su, me za'aci da wata boko yarinya kina zaune kuna haɗa kafaɗa da ita, kalli yadda ta zama uwar mata fa"

Farhan a hankali ta furta na shiga uku, ta toshe bakinta a banɗakin ta cigaba da kuka, bata taɓa bijirewa iyayenta ba ko akan mene, amma a wannan karon ba zata lamunci Aure Sunusi ba, ko ba zata auri Sadik ba, ba zata auri Sunusi ba gara ta haƙura da Auren.

Ta daɗe a banɗaki sannan ta fito, Adda Hafsatu na ta binta da kallo tana "kinga Yarinya ta zama uwar mata"




Da daddare har Lilly ta kwanta bacci, Nazir ya kirata, sabod haka nan zuciyarsa take azalzalarsa ya kirata yaji muryarta, dan zuwa yanzu ya tabattar da sonta yake.
Sun daɗe suna waya da shi, yana mata ya jiki, ta zage ta dinga zuba masa taɓara, seda ta gamsu tarkonta yayi kamu, saboda duk wasu alamu sun fara nuna sonta yake.

Zuwan Adda Hafsatu ta wani fannin Farhan taji daɗi, dan ta ɗan samu sakewa, ba kamar da ba, tana samun abokiyar hira, duk da ƙanwar mahaifiyarta ce amma, ta na janta a jiki saɓanin Ummanta.

Da yake a ɗakin Farhan take kwana, suna hira sosai.

"Adda, dan Allah meyasa Ummana ba ta sona ne, ba ta son kulani"

"Kee, ta dinga kula ki kina 'yar farin?, So kike ai mata gori? Ai badan baban ki baze yadda ba ni zan ɗauke ki, ai al'adara mu ba ruwanka da ɗan fari"

"Haba Adda, Al'ada ai ba Addini bace, kowa in ana hira yana hirar mahaifiyarsa, amma ban da ni, da na zo guri se ta tashi, ko Magana ba ta son yi min"

Ta ƙarasa maganar cikin damuwa.

"Ke ƙaniyarki, wato zuwa makarantar da kike shine har kike da bakin cewa Al'ada ba addini bace ko? To mu Al'ada ce me kyau a gurin mu,kuma muna girmama wannan al'adar a ƙa'ida ai nice Ummanki ba ita ba, da babanki ze yadda ai ɗauke ki zanyi mu tafi can mu zauna in miki Aure"

"Aure kuma Adda, karatun fa?"

"Shi karatun da kike faɗa Addini ne?"

Farhan tace "Adda ai Addini ne yai mana umarni da mu nemi ilimi, ko daga nan zuwa birnin sin ne"

"Amma ai ba boko aka ce ba ko?"

Farhan tai murmushi tace "Adda, shi ilimi ai ilimi ne, tunda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ilimi kawai yace, to kowane ilimi ne in dai be saɓa da addinin mu ba"

"Ke ya isheni haka, ki min shiru, Aure dai shine gaba da komai"

Farhan tace "shikenan" 

yana daga daɗin da Farhan ke ji shine, a wayar Addan takewa Sadik messages, se ya saka mata kati su raba dare suna hira ta saƙon message, Adda Hafsatu na can na bacci, wani lokacin har makarantar dare take tafiya da wayar, suyi waya a can ita ba ta damu ba sam.

Se dai kan tafiyar Adda Hafsatu, ba yadda ba tai da Abban Farhan akan a ƙyale bokon nan tunda ta na da manemi Ai mata aure ba, amma ya nuna nata mahimmancin karatun 'ya mace.

************************************

Kwanci tashi asarar rai, lokacin zana jarabawar Karshe da Sadik zeyi da 'yan SS3 ta ƙarato, wato lokacin barinsa makarantar ya ƙarato sosai.

A lokacin Farhan tana Jss3, ta ƙara girma abunta, ta cika Sosai.

Sedai Farhan duk ta rasa nutsuwarta, da ta tuna Sadik ze bar makarantar ya barta se tai ta kuka, sauƙinta ma shida manyan 'yan iskan dake damunta ze gama makarantar su Babba da kuma Salma.

Duk da sun cigaba da kawo mata farmaki ta ɓangarori daban-daban, ba tare da Sadik ya sani ba.

Idan ta tashi kuka ya dinga rarrashi kenan, tare da Alƙawarin ze Aureta, Wannan shine babban dalilin da ze sa ya kammala secondary a shekarar.

Batun irin kusanci da shaƙuwar da ke tsakanin Sadik da Farhan kuwa ba'a magana, Sunyi shaƙuwa me ƙarfin gaske, ji take idan ya bar makarantar ta rasa wani abu me matuƙar mahimmanci a kusa da ita.

Yau bayan sallar isha'i, Farhan ta dawo daga makarantar dare, ƙaninta Imam ya sanar da ita cewar Abban su yana kiranta.

Ta maida hijjabinta ta fito, ta nufi ɗakin Abban, ta shiga da Sallama a bakinta.

Abba ya amsa mata, taga Umma a zaune a gefensa, ta durƙusa ƙasa tace "Abba gani"

Abba yai gyaran murya yace "Farhan, waye yake kawoki a mota daga Makaranta?"

Cikinta ne yai wata irin ƙara, gumi ya shiga tsatsafowa daga goshin ta, ya a kai Abba ya san haka, bayan a can baya ake ajiye ta?.

"Magana nake miki, ki bani amsa waye yake kawoki a Mota, ɗazu Sunusi ya gayawa malam bara'u, shikuma ya zo ya sameni"

Farhan ta sunkuyar da kai ba tace komai ba.

Umma tace "kaga abunda nake gaya maka ko malam, ana miki magana ba kya ji ne?"

Farhan ta ɗanyi jimm, ta karanto duk Addu'oin da zata iya sannan tace "Abba bani kaɗai ake kawowa ba, 'yar ajinmu ce ake zuwa ɗauka, idan ta tashi duk na hanya se a ɗakko mu tare, kowa a sauke shi se a ƙarsa da ita gida"

"Kuɗin motar da nake baki ne baya isarki?" Abba ya jefo mata tambayar.

"A'a Abba suna isata"

"To meyasa sedai ki biyo motar yaran masu kuɗi?"

"Babu komai Abba"

"Farhan lalacewar zamani nake jiye miki, yaran masu kuɗin nan wasu ba Kirki ne da su ba, wataƙila a banza wataran za'a goranta miki, wanda babu daɗi, dan Allah Farhan ki kula da kanki ki tsare mutuncinki"

"To Abba insha Allah"

Abba yace "se magana ta biyu, da tuntuni yakamata in miki amma ban miki ba, malam Uba ya zomin da batun Yana son in bawa Almajiransa Sunusi ke, to na yaba da hankalin Yaron da nutsuwarsa, ba shi da wata damuwa, kuma an gayamin garinsu da suwaye iyayen sa, duk ba su da wata matsala dan haka gobe in Allah ya kaimu ze fara zuwa wajenki, ku fuskanci juna, dan Mahaifiyar ki ta nuna da wur take son ai miki Aure, tunda kinga mu dangin mu duk ba karatun muke ba, kuma baffan Ummanki har waya yayo yana mitar ance kin girma amma ba'a fara zancen Aurenki ba se karatun boko"

Gaba ɗaya Farhan ta dena gane komai, se tsananin bugubda zuciyarta keyi, ta rasa meke mata daɗi sam.

Abba yace "naji kinyi shiru"

Cikin rauni Farhan tace "Abba karatu na fa?"

"Ai ba yanzu za'ai Auren ba, a samu dai ku fuskanci juna, kinga Farhan gara ki auri talaka dai dai ke, ba zan so aurar da ke in da za'a wulaƙanta ki ba dan bamu da Komai, amma kinga wannan shima ba shi da koma, kin ga se kuyi arzikin tare"

Farhan tai shiru ta kasa ko ƙwaƙwaƙwaran motsi.

Abba yace "ko akwai abunda zaki ce?"

Farhan ta girgiza kai alamar a'a.

Yace "yawwa, tashi kije Allah yai mil albarka"

Ai ko amsawa ba ta iya yi ba, ta tashi jiki a matuƙar sanyaye, ta nufi ɗakinta, ta na zuwa ta zube akan katifarta, ta fashe da kuka.

Wata irin masifaffayar soyayyar Sadik ce ke bijiro mata, ga shi ba ta son yin duk wani abu da ze sa ta saɓawa iyayen ta, amma ya za'ai ta auri wanda ba ta so kwata kwata, bayan ga wanda zuciyarta ke so? Dole tajewa Sadik da wannan maganar dan samo bakin zaren.

Tunda ta shiga ɗakin nan ba ta sake fitowa ba har gari ya waye.


A Library taje ta samu Sadik, ya duƙufa yana karatu, ta sa hannu ta rufe littafin.

Da sauri ya ɗago ya kalleta, se kuma yai murmushi yace "kefa kin fiye neman Magana, da na tashi a zuciye na make ki fa?"

Tai murmushi tace "sannu da hutawa"

"Hmm ina fa hutu, lokacin exams na ta ƙaratowa, gaba ɗaya kamar kaina ya fashe"

"To ka dinga hutawa mana, ba naji ance expo ce za'a baku ba"

Sadik ya harareta yace "me kika maida mijin nakinne? Daƙiƙi ko me? Dan abun kunya duk tsawon shekarun nan Abba na kashe kuɗin makaranta a ƙarshe ace se an bani expo wuce nan"

Tai mit tace "kaga gifted, ni ban taɓa tunanin gifted suna karatu ba ai"

"Waye yace miki ni gifted ne, ba wani gifted, yanzu dai meye labari?"

Tai ajiyar zuciya ta kalli Sadik tace "labari babu daɗi"

"Subhanallahi how comes? Meke faruwa kuma?"

"An gayawa Abba kana kawoni a mota, jiya yai min Magana"

Sadik yace "garin yaya, wanene ya gaya masa?"

"Ba ma ita ce babbar matsalar ba, kwanakin baya ƙanwar Umma ta zo gidanmu, tana ta mita akan lallai wai se an min Aure, Abba yace se na gama makaranta, tunda ta koma suke kiran Abba a waya, akan lallai a fitarmin da miji, wai tunda 'yarta sa'ata ce ita ma Aure za'ai mata"

Sadik yai mata ƙuri da ido yace "ina jinki"

"Sadik Abba yamin miji"

Dammm! Yaji ƙirjinsa ya buga yace "ina jinki"

Cikin matuƙar rauni ta cigaba da cewa "Sadik i don't know what to do, you are leaving me soon, zaka tafi karatu, zaka barni idan ka tafi mahaifina ze iya yanke Kowane irin hukunci, dan Yanzu haka ya ba da ni, harya ba shi damar ya fara zuwa gurina, da na kammala secondary School yace ze aura masa ni". Ta ƙarasa maganar ƙwalla ta taru a idonta.

Kasancewar suka ɗai ne a cikin Library, ya sa ya kamo hannunta cikin nasa, duk da wani irin azababben kishi da yaji yana taso masa, ga matuƙar tashin zuciya da ya shiga, amma ya dake cikin tattausar murya yace "Allah ne yake da nan da shekaru ukun, ke mallakina ce, duk wanna fafutukar da nake saboda mu kasance tare ne, kuma Insha Allah zamu kasance tare, dagaske nake sonki Farhan ba kamar yadda ake cewa RUƊIN ƘURUCIYA bane"

"I know, but bana son bijirewa iyaye na"

"Ba zamu bijire musu ba, zasu fahimce mu Insha Allah"

Haka Sadik ya cigaba da lallaɓata yana kwantar mata da hankali, amma ƙasan zuciyarsa wata irin fargaba ce da tashin hankali mara misaltuwa.






Da Sadik ya koma gida ɗakinsa na cikin falo ya tafi, sedai ji yake kamar yai kuka, yana son Farhan matuƙar so, idan aka aura masa ita ze iya riƙeta amma kowa ya kasa fahimtar su.

Jiki a Sanyaye yai wanka ya fito falon, a falon yai karo da Mother, ya ɗan ƙura mata, ta dube shi tace "Lafiya kake min wannan kallon haka?"

Yace "ƙamshin Abba naji"

"Iyayi, Abban naka har wani ƙamshi ne da shi na musamman?"

"Eh mana ya dawo ne?"

Tai murmushi tace "ya dawo, amma yana hutawa ne"

Yai murna yace "I know I guess it right, bari inje idan ya tashi na ganshi anjima"

Mother tace "Abinci fa?"

"Mother zan dawo ba yanzu ba" ya juya ya fita yana ta lissafin abun yi.




Lilly Kuwa da ta koma gida ta tarar mamanta wai ta tafi Sokoto anyi haihuwa, dama babanta ba mazauni bane, daga ita se masu aiki kenan a gidan.
Dama ba yau aka saba tafiya a barta a gidan ba, daga ita se masu aiki, Mum ɗinta ta maida zuwa Sakwatto bakomai ba, nan da nan taje ta dawo, wataran idan ta tafi se tai kwanaki ba ta dawo ba.

Hakan ya ƙara bata damar sakewa sosai a gidan.

Sir Nazir mutum ne me matuƙar aji da kwarjini, ba student ba har a staffs mata akwai masu son shi, amma tsabar kwarjininsa yasa ba su samu fuska a gurinsa ba, amma gashi a karon banza yarinya ƙarama ta samo kansa tana juya shi yadda take so, da tenakon ƙawayenta da kuma kallace kallacen fina finai da uwa uba karance karancen dake ƙara ruɗa tunanin yaran da ke tashen ƙuruciya.



Sadik kuwa gidan su Khairat ya tafi, yana tunanin ko ze samu mafita Khairat ta bashi shawara, dan wasu lokutan duk shirirtar ta ta kan bada shawarar da ke ɓullewa.


"Kace min magana za muyi kuma kayi shiru"

Sadik yace "Khairat na rasa ta ina zan fara ne, abun ya cushemin da yawa"

"To daure dai ka gayamin" cewar Khairat dake kallonsa.

"Khairat, kin gane Farhan ai?"

Khairat tace "ji wata tambaya, ganewa kai"

"Khairat, ina matuƙar son yarinyar nan, a dalilinta na takura in gama makaranta a SS2, yanzu zancen da nake miki babanta ya bawa wani ita, nan da 3years za'a aurar da ita, ni Kuma lokacin ina level 3 kenan, bana son in rasata, na so yiwa Mother bayani, amma taƙi saurarata, na rasa yadda zanyi"

Khairat tace "bro, lokacin mace fa da na namiji na ɗaya bane, idan kace se an jira ja gama karatu zaka aureta kasan shekarun da saura, kuma haryanzu yarintar ka ake gani"

"Naji na gane, ai dama ba cewa nai yanzu ba, sonake a neman aurenta, ni ta jira zuwa kan ta gama secondary ina level 3 se muyi auren, na rasa wanda zan tunkara, Faruk ma ya ƙi fuskanta ta na rasa abunyi gaba ɗaya"

Khairat tace "Nima kaina ya kulle wallahi, amma kayi magana ds Abba mana kaji me zece"

"Khairat, Mother ma ba ta saurareni ba balle shi"

"Kuma kaga ra'ayin su ɗaya da ko Daddy, da se ince ko shi za'a gayawa yaiwa Abba Magana, amma nasan ba zasu amince ba, cewa za suyi kayi yarinta da yawa"


Sadik ya dafe kai yai shiru, kawai ya miƙe ya fice daga falon jikinsa ba ƙwari




Misalin ƙarfe takwas na dare, Alhaji Abdullahi yana falon dake shashensa shi da kafatanin iyalan sa, ciki hards dr. Da matarsa Jidda suna cin abincin dare.


Sedai Sadik se jujjuya spoon yake, ya kasa cin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login