Showing 129001 words to 132000 words out of 259198 words

Chapter 44 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

baƙin ciki.



Abban Farhan yana shirin fita aka shigo a kai sallama da shi, yace yana zuwa.

Yana fita yaga malamin su Sunusi ne, ya tsaya suka gaisa Sannan malamin Yace "to kamar yadda mukai magana da kai, naje garinsu Sunusi na samu mahaifinsa nai masa Magana, yayi murna ƙwarai yayi farinciki da jin hakan, yace a basu lamuni nan da wata guda zasu kawo kuɗin Auren"

Abba yace "Ahha Masha Allah, naji daɗi ƙwarai da gaske, nayi farinciki, ai nan da wata ɗayan kamar yaune a gurin Allah, Allah ya nuna mana ya sa zamu gani"

Ya amsa da "Ameen"

Abba ya nisa yace "Amma ina son idan anyi Auren nan, Farhan ta cigaba da karatun ta, saboda shine babban burinta a rayuwa, duk da shima Sunusin zan masa maganar"

"Eh ai karatu abune ne mahimmanci, mussaman tunda da abunta aka ganta, wannan ma abune me kyau, zan yiwa Sunusin Magana Insha Allah, fatanmu Allah ya tabbatar mana da Alkhairi".

Abba ya amsa da Ameen.

Kusan sati biyu, Sadik be sake shiga harkar Nana ba, duk yadda take takalarsa wasu lokutan ko in da take baya kallo, ga wayoyinsa da ya bata ta kai masa caji, ko sau ɗaya be yi mata maganar wayoyin ba, shi mantawa ma yake da waya, kawai dai gashi nan yana rayuwa, se ya dinga jin kansa kamar ba shi ba.

Farhan Kuwa sun koma zangon karatu na biyu, sedai jin makarantar take tamkar maƙabarta, gaba ɗaya ba ta da kuzari, ba abokin hira dama ita ba ƙawaye ne da ita ba, gashi ko a waya ta kasa samun Sadik fiye da wata guda, ga matsaloli sun taru sun mata yawa, hakan harya fara shafar karatunta, ya zamana ko excusing ɗin kanta tayi ta tafi Library karatu, ba ta iyawa, se tai ta kallon gurbin da Sadik yake zama yana tayata karatu.

Tana matuƙar kewarsa, se taji gaba ɗaya ta dena gane karatun, bata iya maida hankali yanzu sam.

Ga 'yan ajinsu lalacewa taci uban ta da, yanzu bayan karance karancen litattafan da suke, har memory suke bayarwa a turo musu abunda be dace ba, banda masu shaye shaye da sauran lalacewa, makarantar se ƙara lalacewa take.
Dama Sir Nazir ne me tsawatarwar, shima kuma Yanzu ya faɗa tarkon RUƊIN ƘURUCIYA, dan haka kowa yake cin karensa babu babbaka.

Bayan ta koma gida, ko Abinci ta kasa ci, duk ta rame tayi wani iri, tana kwance a ɗakin ta da Yamma, Taji Abba yana ƙwala mata kira.

Cikin hanzari ta fito tsakar gidan, ta durƙusa a gabansa.

"Yawwa, ɗazu malamin su Sunusi ya zo munyi Magana da shi, yace min in Allah ya yadda watan gobe za su kawo kuɗin Aure, dan tun kwanaki mu kai Magana zasu kawo kuɗin, amma yau ya tabattar min da watan gobe zasu kawo"

Gaban Farhan ya yanke ya faɗi, taji ta dena ganewa na wasu lokuta, ko motsi ta kasa yi a gurin.

Abba yace "ya naga duk kin canza, ko ba kya son Auren ne?"

Za tayi magana ta ɗago ta kalli Abba, se taga yai mata kwarjinin da ba zata iya buɗe baki tace masa ai ba ta son Sunusi ba.

Sedai cikin rauni da sanyin halinta tace "Abba karatuna fa?"

Abba yace "karki damu da wannan Farhan, nayi magana da malamin su akan ze barki ki cigaba da karatunki, nayi niyyar Aurar da ke ne saboda wani dalili, amma zaki cigaba da karatun ki insha Allah, tashi kije yadda kike mana biyayya Allah ya baki 'ya'ya masu biyayya kema, Allah ya albarkaci rayuwar ki ya tsare ki daga sharrin lalacewar ƙarshen zamani, Allah yai miki Albarka"

Farhan ta kasa amsawa, sedai ta miƙe akan ƙafafuwanta da take ji kamar an ɗaura musu duwatsu, ta koma ɗakinta.

Zuciyarta ta dinga zafi, hawayen ta suka ƙafe ta kasa kukan se ajiyar zuciya da take tayi.

"Sadik dan Allah ka dawo kar amin Auren nan, na kasa gayawa Abba bana son Auren, Kai nake so Sadik, duk wanda na Aura ba zan iya dena sonka ba"
Tai maganar tana jin yadda zuciyar ta ke ƙuna, ga kuka ya gagareta.

Wunin ranar Farhan ba tayi shi cikin kwanciyar hankali ba, haka da dare yayi shima bacci ya gagareta, dama kwana biyun nan dama baccin ma ba samuwa yake ta daɗin rai ba, balle ga wannan batun mafi dunguzuma mata zuciya, ko kusa ba ta ga yadda za ta iya zaman Aure da Sunusi ba, dan zuciyarta na tare da Sadik.

Washegari da safe haka taje makaranta, babu kuzari sam a jikinta, dan har a kai lesson aka gama ba ta fuskanci komai ba, sedai lokaci lokaci ta kanji hawaye na ƙoƙarin zubowa daga idanunta, amma se ta neme su ta rasa sedai zuciyarta ta cigaba da zafi.

Sam hankalin Farhan ba ya jikinta se da ta jiyo Muryar Yasmeen ta ambaci sunan Prince.

Take hankalin Farhan ya dawo jikinta, ta tattara hankalinta akan Su Yasmin dan jin me zasu ce akan masoyin nata.

Yasmeen tace "Ashe su Prince ana ƙauye, ni Wallahi ban taɓa tunanin gayen nan ze zauna a ƙauye ba"

Mamakine ya kama Farhan, ya a kai Yasmeen ta san Sadik yana ƙauye? Amma ba abun mamaki bani, wataƙila a bakin abokan Sadik na ajinsu taji" wata zuciyar ta bata amsa.

Yasmeen ta cigaba da cewa "gaskiya gidan su Sadik akwai zafafa Allah yai musu kyau masha Allah, kunga wani yayansa me kyau"

Lilly tace "wai ke me ya kaiki gidansu ne?"

Yasmeen tace "ina ruwanki da abunda ya kaini, ni da gidan sirikai na"

Se da Farhan ta ɗago ta kalli in da Yasmeen take, aikuwa Yasmeen ta galla mata harara.

Lilly tace "ba uwar da ta haɗaki da su Sadik wai gidan sirikanki"

"Ahaaf kika sani" Yasmeen ta faɗa tana murmushi.

Farahan taji jikinta har wani rawa yake, tana Addu'ar Allah yasa ba wani abun ne ya haɗa Yasmeen da Sadik ba.



Seda wayar Sadik tai sati uku ba ta tare da shi, gaba ɗaya ya rasa meke damunsa, ya rasa tunanin ma meya kamata ya yi.
Gaba ɗaya kamar deprssion ke nama ya kama shi.
Ji yai an ajiye masa abu a jikinsa, ya ɗaga kai ya kalli Nana, ba ta ce masa komai ba tai waje.

Ya ɗaga ya duba me ta ajiye masa, yaga wayoyinsa ne.

Kawai ya bi wayoyin nasa da ido, gaba ɗaya wayoyin ma sun fita daga kansa.

Ture wayoyin yai ya kwanta, yana ta ƙoƙarin yai tunani amma ya kasa.


Kusan kwanaki uku da kawo masa wayoyin, sannan ya kunna ƙaramar wayarsa.

Lambar Mother ya shiga dubawa, ya kira yaji ko wayar zata shiga, by luck yaji ta fara ringing, da Sauri ya tashi zaune yana gyara zama.

"Hello Autana"

Ajiyar zuciya yai Sannan yace "Mother kin manta da ni ko?"

"Haba Sadik kai kana tunanin akwai lokacin da ze zo in manta da kai? Kullum kana raina, wayarka ba t shiga nayi kuka harna gaji, babanku ya hanani ko zuwa in ganka ba yadda na iya"

"Shikenan Mother a nan zan cigaba da zama kenan?"

"A'a ya ma za'a ce a nan zaka cigaba da zama, ai anyi wa Faruk waya ance ana neman babanku a nan gidan"

Sadik ya ɗan taɓe baki yace "ni ban ma sani ba, Allah yasa idan ya zo ya tafi dani, Mother na gaji am tired wallahi"

"Na sani Autana, amma dan Allah kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, kar kaje kayi wani abun da zasu hanaka tafiya, Abbanka yana nan yana nema maka admission a London, insha Allah da ya samu zaka tafi, naji ance an saki Waec ma, amma ban tabattar ba"

"Amma ai Swiden Abba yace min ze kaini"

"Ai Sweden ɗin ne, su se nan da kusan wata huɗu za su fara bada admission, su kuwa nan very soon, abunda ya sa nafi bada ƙarfin ka tafi London ɗin dan kayi ka baro ƙauyen nan"

Sadik yace "shieknan, ina bro ko nemana ba ya yi, tunda suka tafi suka barni a nan, dama dr. Wannan da ina nan da ba na nan duk ɗaya a gurinsa"

Mother tace "Wallahi Faruk yana Maganar ka, da zuwa ya so yi ma, amma yana tsoron abunda mahaifinku ze ce dan kwanan duk ya canza kamar ba shi ba"

"Shikenan Mother"

Jiki a sanyaye Mother tace "kayi haƙuri kaji Autana, ka kusa baro garin nan Insha Allah, Abban ma a satin nan ze dawo insha Allah"

"To Mother Allah ya sa"

"Ameen ya Allah"

Su kai sallama.

Messages sun kai goma a wayar, amma ya kasa buɗe ko ɗaya, ya Ajiye wayar ya murgina ya juya, ya lumshe idonsa.

Yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani irin bugu da sauri da sauri, ya rasa dalilin jin fargabar nan da yake yi.

Da sauri Kamar an mintsine shi, ya tashi zaune, ya kuma ɗakko wayarsa ya shiga dubawa.

Messages ɗin Farhan ne a wayarsa , se yanzu ya tuna da Farhan, a gigice ya shiga duba messages ɗin.

"Am missing You so much, please ina kana lafiya ko message kai min"

"Akwai matsala Please pick my call, or check my messages"

Wayar Farhan ya shiga kira, amma a kashe, take wani irin gumi ya ding tsatsafowa a goshinsa, yayi mamakin yadda ya kwashi tsawon lokaci ba tare da ƙoƙarin sanin halin da Farhan ke ciki ba.

Take Ya shiga tunanin meke damunsa haka? Har yake ƙoƙarin mantawa da abunda ruhinsa ke bege ba dare ba rana.



Ya kira wayarta, ya kira ya kira amma ba ta shiga sam.

Gaba ɗaya hankalinsa ya ƙi kwanciya, har kusan kwana biyu yana faman neman layinta amma ya ƙi shiga.

Hankalin Sadik fa yaƙi kwanciya, kasancewar rashin samun Farhan a waya, abun duniya ya dame shi, ya cigaba da mamakin yadda a kai, tsawon lokacin nan be damu da sanin halin da take ciki ba.


A rana ta uku ne, yaji wayar ta shiga, sedai taƙi ɗagawa sam.


Sadik ya kirata ya kai sau ashirin, Sannan ta ɗaga sedai tana ɗagawa kukanta ya fara ji.

"Farhan" ya kira sunanta a hankali.

Bata amsa ba ta cigaba da kuka.

"Ban san da wace kalmar zan fara miki Magana ba, Farhan ban san meya sameni ba"

"Sadik har ka manta dani ko, Sadik kuɗin Aurena za'a kawo next month, Ina cikin matsala"

"What the fucking shit are you talking about, ban gane kuɗin Aure ba"

"Zan maka ƙarya ne? Wallahi Abba ze karɓi kuɗin Aurena, Sadik na shiga uku zuciyata kamar ta tsaga ƙirjina ta fito, wallahi bana son shi kai nake so"

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Sadik ya sauke, yace "ba wanda ze aurar da ke ga wani, ke tawa ce, wallahi ko an Aura miki wani, sena biki har Gidan na ɗauke ki, kuma wallahi duk wanda yai gangancin Aurenki sena illata shi, sena masa tabo me muni, koma in sa a ɓatarmin da shi, ke tawa ce Farhan" ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji.


Kasa cewa komai Farhan tai se sheshsheƙar kuka da take, a hankali ta furta "Ina sonka Sadik, dan Allah kar barni, kar ka juyamin baya, ka riƙe alƙawari dan Allah, ina sonka sosai Sadik".


Duk wuya duk rintsi Farhan, ke tawace kuma Wallahi duk wanda yai gangancin taɓa abunda yake nawa se na masa illa, ko waye shi.

Yana cikin maganar be sake sanin in da kansa yake ba, seda Asuba tayi, ya buɗe ido cikin hanzari.

Sedai yai yai ya tuna abunda ya faru, amma abu ya gagara, tabbas yasan bacci ko makamancin haka ya ɗauke shi, yana tsaka da wani abu me mahimmanci, Amma ya kasa tuna ko menene, ga abun yana ji a ramsa amma ya kasa tuna komai!




Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.



Ɓangaren Farhan suna tsaka da waya, tana masa magana, kawai taji yayi shiru, ta kira sunansa amma taji kamar ya amsa cikin magagin bacci, zuwa can taji yayi shiru.

Abun ya bata mamaki ba ta taɓa sanin Sadik da magagin bacci ba, ko ƙarfe nawa za su kai na dare suna waya ba ya jin Komai, wataran ita ce me cewa ma ita bacci take ji.

Take taji jikinta yai sanyi ƙalau, ba ta da wani kuzari, se yanzu ta samu damar yin hawaye, amma da zuciyarta ta bushe.

"Ohh Allah meke shirin faruwa ne haka?" Tai maganar tana sheshsheƙar kuka.

Bacci kuwa dama wannan gagararta yai, ta kasa shi gaba ɗaya, se tarin saƙe saƙe da tunani.

Da garin Allah ya waye, gaba ɗaya Sadik ya manta sunyi wata waya da Farhan, dan shi ya manta da ita ma gaba ɗaya.

Ƙarfe kusan goma na safiya, ya fito daga ɗakin sa, a gefen ɗakin Inna ya hangi Nana tana watsawa tattabaru Gero, tana sanye cikin hijjabi, tunda ya zo Gidan nan, kullum cikin hijjabi yake ganinta, se Ranar da ya mareta ya ganta da ɗaurin ƙirji, amma duk zafin duniya Nana tana sanye da Hijjabi, ba ta taɓa rabuwa da shi, abun har mamaki yake ba shi.

A hankali ya furta "Stupid girl" dan in za'a lissafo abunda ya tsana, to da Nana a ciki, duk da tarin Alkhairan da tai masa a zamansa a gidan, amma ba ya duba wannan se tsagwaron rashin mutuncinta da tsiwa da yake gani.

Zancen zucin da yake ne, ya sa ƙureta da ido, ba tare da yasan yayi hakan ba, seda yaji saukar ruwa a fuskarsa sannan ya farga ya kalli Inda Inna take shirin yin alwalar sallar walha, ita ta watso masa ruwan.

A hankali ya janye idanunsa daga kan Nanan, tare da goge ruwan da Innan ta watsa masa.

A ransa yace 'yanzu fa wannan tsohuwar se ta zata wata tsiyar nake kallo a jikin wannan komaɗaɗɗiyar yarinyar, aba kamar taliya, dan ita ba wahala ta yiwa abu fassara, ko abunda kake nufi kenan ko ba shi kake nufi ba"

Wayarsa dake cikin aljihunsa ce ta fara ringing, ya zura hannu ya ɗakko wayar, tare da nufar soro dan amsa Wayar.

Muryar Amin yaji yace "Mazaaa, Allah ya temaki yarima namu"

Murmushi Sadik yai yace "gayu dama kuna nan? Ba waya ba saƙo?"

"Kai zamu tambaya ai, you just disappeared, mun zaci karatun ka tafi, har gidanku muka je amma akace baka nan wai kayi tafiya, ko a waya ba a samunka gaba ɗaya ko ta social media ba a ganinka"

Sadik yace "ya ma za'ayi in tafi karatu baku sani ba, kuma ma ai Jarrabawar ta mu ba ta fito ba"

"Ahh ta fito almost two weeks ago fa"

"Haba dai, bani da labari ne sam, ya school ɗin?"

"School Lafiya ƙalau, wai dan Allah ina ka tafi ne haka?"

"Wallahi ina wani useless village ne"

"Village as how? Babban yaro me kake a ƙauye kuma for whole this long?"

"Kai bari kawai, daga zuwa garin nan dubiya Granny ya hanani tafiya, gaba ɗaya a takure nake, na rasa abunda yake min daɗi, sam bana jin daɗin garin nan, ji nake kamar ma bani da lafiya, kamar me jinya haka nake jina"

"Amma kai kana me ka bari aka barka a ƙauye kamar ba Prince ba, sekace wani ɗan yaye kaine ma ka yadda"

"Haba Amin, ka san da hankalina ba zan bari in zaunaa ƙauye ba, anfi ƙarfina ne kawai ba yadda zanyi, amma very soon insha Allah zan dawo, na kusa tafiya karatu"

"Wow, ai gara ka dawo ɗin, haba a ɗanyi chilling before you leave the country, kai kaga wasu zafafan babies da aka kawo makarantar nan, kai Makaranta fa ana ta yi ba kai"

Sadik yace "ai koma ina nan bani ɗin za'ai, tunda barin ƙasar zanyi"

"Duk da haka school ɗin babu daɗi ba ka nan wallahi"

"Please my regards to all, insha Allah kan in tafi zan shigo school ɗin"

"To shikenan, ba ka tambayi ya beb ɗin ta ka ba?"

Sadik be tsaya sauraron me Amin ɗin ke faɗa ba, ya katse kiran wayar. Tare da sakin ajiyar zuciya a jejjere.

Farhan dai gaba ɗaya ta rasa nustuwar ta, a makaranta ma kiran Sadik ta dinga yi a waya, amma idan ya duba se ya manta lambar waye, kawai se yai ignoring ɗin kiran, ya cigaba da sabgogin gabansa.

A gida Sadik ya saba masu aiki ne ke gyara musu ɗaki, wasu lokutan dan sangarta ko Abinci suka ci a gurin suke barin kwano, sedai a zo a kwashe, a gyara gurin amma yanzu shi yake fitar da kwanon da yaci Abinci da gyaran ɗaki.

Gashi wataran yana tsaka da hutawa, za'a taso shi a haɗashi da dogarai suyi sharar burgarr dawaki, tun yana toshe hanci kamar ze amai saboda warin kashin dawaki har ya saba.

Yanzu ma Har ya koma ɗakin da yake, ya kalli ɗakin kusan kwana uku be share ɗakin ba, duk da ɗakin ba wani datti yai ba amma se yaji duk ƙyamar ɗakin yake.

Ya ɗakko kwanukan da yaci tun Abincin safe, da na rana ya fito da su, Nana na zaune tana wanke Wanke, yazo ya zube mata, dan kusan ta ma gama wanke wanken sannan ya kawo.

Sheƙeƙe ta kalleshi tace "wannan wane irin wulaƙanci ne haka? Dan me ba zaka fito da kwanukan tun da Girma da Arziki ba, se sun gama bushewa, kuma kana kallon na gama Wanke wanken sannan zaka kawo min"

Maimakon ya bata amsa yace "in kin gama, ki sharen ɗakina"

"Kut uban kuturu ma yayi kaɗan wallahi, kai ka isa? Ni zaka kalli idona kace in share maka ɗaki saboda tsaurin ido to wall... Bata ƙarasa ba taga Sadik yai ball da robar wanke wanken gaban ta, kwanukan sun watse.

Saroro tai tana binsa da kallo tare da mamakin jarabar Sadik.

Da yatsansa ya nuna ta yace "idan kika kuskura kika min rashin kunya, yadda nai da kwanukan nan haka zan miki"

Aikuwa ta miƙe zata fara zazzaga masa bala'i itama, taji gyaran muryar Hakimi, hakan ya tilasata mata haɗiye maganganun da suke cinta, take so tai amansu.

Hakimi yace"In kin gama wanke wanken, ki share masa ɗakin ai yayanki ne gaba yake da ke, kuma ya isa dake"

Seda Nana ta buɗe baki dan mamaki, ita ce ma zata sharewa wannan fitinannan ɗaki, shiru tai ta fara tattara kayan wanke wanken, tana jin yadda ranta ke mata ƙuna, tare da ƙudurce ramuwar gayya.

Se da ta gama wanke wanken, Sannan ta tafi yin sharar, ta tarar da shi ya barbaje ƙafafuwansa a tsakar ɗakin, ya Ajiye pillow a ƙasa ya kashingiɗa.

Ba ta ko kula shi ba, ta hau shararta facar facar, facar tana watsa masa datti a jiki.

"Ke Mahaukaciya! Ba kya gani nee?"

Ba ta ko saurare shi ba, ta cigaba da abunda take, tana watsa masa shara a jiki Sam Sadik baya son ƙura, dan haka ba shiri ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login