Showing 171001 words to 174000 words out of 259198 words

Chapter 58 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

sannan yaji ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya, Kamar duk surutun da yai hankalinta ba ya kansa.

"Me kike tunani ne?"

"He's gone" ta faɗa a Sanyaye.

"Who?"

"Sadik, he replaced me with another girl"

Abbas yace "subhanallah, and how do you know that?"

"Gayamin a kai, na yadda da maganar ka, Sadik baze dawo ba, Dole se na Auri Sunusi, amma ka gayamin ta ya zan dena tunaninsa?" Tai maganar tana hawaye.

"You still love him?"

"Yes i do"

"Ki sawa zuciyarki ke Yanzu mallakin wani ce, ki nesanta kanki da duk wani abu da ze sa ki dinga tuna shi, Sannan kiyi haƙuri, ki miƙa lamarinki ga Allah"

Ta ɗan ja numfashi tace "shikenan, Nagode sosai doctor nagode"

"Karki kuma yi min godiya, Allah ya sanya Alkhairi"

Ba ta amsa ba ta cire wayar da ga kunnenta.

Haka kurum se ta tsinci kanta da saka lambar Sadik da ta haddace, a cikin wayar ta gwada kira amma wayar a kashe.

"Meyasa ba ki da zuciya ne Farhan?" Wata zuciyar ta tunasar da ita.

Ta ajiye wayar a gefe, ta kuma bin guri ta kwanta.





Yau unexpected, Steve ya kawowa su Nana ziyara, Nana tai murna sosai suka karɓe shi cikin girmamawa, Weekends ne dan haka Sadik ma ya na gida.

Nan yake sanar da Nana cewa, Ranar Litinin ze zo ya kaita sabuwar makarantar da zata cigaba da zuwa, Nana tai murna sosai dan dama zaman gidan duk ya isheta, ga wanda take zaune da shi ba shiga sabgarta yake ba.

Steve ya ɗakko wayarsa yace, bari in kira babanki yace in haɗaki da shi idan na zo"

Ta kalli Sadik da yake zaune yana kallo, ko uffan be ce musu ba.

Tace "kuma wallahi se na gayawa Abba duk abunda kakeyi, da yawon dare da kake da tara abokai da taɓa mata duk se na gaya masa".

Sadik a ransa yace 'wannan mahaukaciyar Yarinyar tsaf za ta kuma jamin wata damuwar fa' amma a fili kallo ɗaya yai mata ya maida idonsa kan tv ya cigaba da kallonsa.

Steve ya miƙawa Nana waya, se da wani murmushi ya kufce mata tace "Abba ina wuni"

"Lafiya ƙalau daughter na, ya kike ya gidan?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya su Yaya Faruk da Mother?"

"Suna lafiya, Faruk ya tafi karatu shime"

Nana tace "Allah sarki, Allah ya bads sa'a"

"Ameen ya Allah, Steve ya gaya miki ranar monday in Allah ya kaimu ze kaiki Makaranta da zaki cigaba da zuwa ko?"

"Eh ya gayamin Abba, ita ma boarding ce?"

"A'a ga mijinki Yaushe za'a kuma kaiki boarding, day ce, ko kin fi son boarding ɗin?"

"Eh Abba na fi son boarding"

Abba yace "Yana miki wani abun da ba kya so ko?"

"A'a ba ya min Komai"

"Ki gayamin gaskiya Nana, me yake miki na rashin kyautawa?"

"Allah Abba dagaske nake, ba abunda yake min na rashin kyautawa" Sadik ya ɗago yana kallonta, ya san koma mene akansa ake Magana.

Abba yace"in dai yai miki wani abu na rashin daidai, ko kika ga yana aikata wani abu na rashin kyautawa ki bugo ki gayamin"

Tace "to Abba"

"Yawwa, Allah yai miki Albarka, kina da buƙatar wani abu ne?"

"Eh Abba, ammm. Ina son siyan mayukan shafawa, wanda na zo da su daga school sun ƙare, kuma garin akwai sanyi sosai"

Abba yace "Ai Sadik zaki gayawa, na saka masa kuɗi a account ɗin sa, duk abunda kike buƙata ki gaya masa, in yaƙi yi kuma shima ki sanar da ni, bari in haɗaki da Hajiya, gani na zo garin"

Miƙewa tsaye Nana tayi, cike da murna.

"Salamu Alaikum"

"Inna ta ke ce?"

Inna tace "ji wani shirme, to da wace in ba ni ba"

"Wayyo Allah, Yaushe rabon da inji muryarki Innata? Dan Allah ba ki kewata ba?"

"Kice haryanzu dai Nutsuwar da sauƙi ba ta ratsa ki ba"

Nana ta ɗan tura baki tace "haba Inna, in ban kewarku ba kewar wa zanyi, ina Kakana? Ya jikinsa?"

"Jiki da sauƙi sosai Alhamdilillah, sunje gangare ɗaurin Aure, ai yanzun nan baban naki ya zo, yace takanas ya zo dan ya haɗamu a waya"

"Allah sarki, wallahi Inna ina kewar gida sosai"

Inna tace "kin dena koke koken kenan? Ina mijin naki?"

Nana ta kalli inda Sadik yake, ta harare shi tace "Allah ya kiyaye ni ba mijina bane"

Inna tace "Meki ka ce?"

"Ni Inna dan Allah a dena wani ce masa mijina, haba dan Allah wannan ɗan yaron ai abun kunya ne ace mijina ne, nan gaba idan na ƙara tsawo fa sena kamo shi a tsawo, Ni babba zan aura me hankali, kawai ku dinga min Addu'a Allah ya bani miji nagari, se ki ga ma na kawo miki bature a matsayin sirikinki"

Inna tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ke baki da hankali ko, dan ubanki Aure abun wasa ne? Wato nan ɗin ma zuwa ku kai kuka cigaba da raba abun faɗa ko Nana, duk nasihar da nai miki ba ki ji ba kenan?"

"Ni wallahi Inna ba na son shi, Auren dole fa akai min, wannan yaron ban da hantara da masifa meya iya, a gabanki fa har dukana ya dinga yi, ni dai kawai ki min fatan Allah ya bani miji nagari"

Inna tace "na shige su, a nan ɗin ma dukanki yake?"

"A'a ni be dakeni ba, amma dai wallahi ba na son shi, shima kuma ba ya sona, dan Allah ba se ya sakeni ba, in Auri wanda nake so".

Inna tace "Allah ya sa uban Yaron nan ya fita salla, da a gabansa zaki dinga wannan sakin bakin, dan ubanki a ba kya son nasa kike satar jiki, ki ɗau Abinci ki kai masa a ɓoye ko? Lokacin da yake garin nan"

Nana tai mamakin yadda akai Inna ta gane, amma ta maze tace "To ai wannan tausayinsa nake ji"

"To yanzu ma ki cigaba da jin tausayin nasa, Nana Aure ba abun wasa ba ne fa, karki kuma cewa ba kya son sa, ko kina son sa ko ba kya son sa mijinki ne, dole ki masa biyayya kiyi haƙuri, zama yau da gobe zaki ji kina son nasa, karki kuskura yaji ko ki bari mahaifinsa yaji kins cewa ba kya son sa"

Nana tace "Na nawa kuma? To yana zaune ya na jin wayar da nake"

"Inna tace Eh na ƙara tabattar da Baki da hankali Nana, doguwar banza da ta wofi se tsawo ba hankali, Nana miji yafi gaban wasa, Allah ƙara nunamin kinyi wannan furicin se naci ubanki, mara hankali kawai"

Nana dai tai shiru tana tura baki, Sadik kuwa yana jin duk abunda Nana take faɗa, babu babban abunda ya fi tsaye masa irin kalmar yaro da ta dinga ce masa, kawai yai ƙwafa ya ƙyaleta.

Ta gama wayarta, ta bawa Steve wayar tana tai masa godiya.

Ya tashi ze tafi, Abba ya kuma kiran Steve, ya nemi ya haɗashi da Sadik, aikuwa ya bawa Sadik wayar, sedai Sadik be zauna a falon ba ya fita.

Ya kai mintuna goma Se gashi ya dawo jikinsa a sanyaye, Ya raka Steve ya tafi, be kuma tankawa Nana ba ya cigaba da sabgogin sa.

Kamar yadda Steve ya gaya mata, Ranar Litinin ya kaita sabuwar makarantar da zata cigaba da zuwa, Farhan tai murna sosai ko ba Komai yanzu ta dena zaman gadi, ta huta da zaman kaɗaici.
Wannan makarantar ta lura akwai yaran Musulmai sosai a ciki, dan akwai masu saka hijjabi bayan ita.

Tun da ta fara zuwa Makaranta ba ta haɗuwa da Sadik se dare, idan ta fita tun safe se la'asar take dawowa gida, School bus ce ke zuwa ta ɗauketa ta dawo da ita.

Sadik kam ba ta ganinsa se dare, yau kamar an sata ta shiga ɗakinsa, ya hargitsa komai hatta wardrobe ɗin sa, yai kaca kaca da ita Sadik ba ya son ƙazanta amma be iya gyara ba.

Tana mita haka ta zage, ta gyara masa ɗakinsa tsaf, saboda Nana ta gaji tsafta a gurin Hajiya Inna.

Ba ƙaramin daɗi Sadik yaji ba, da ya dawo ya tarar ta gyara masa ɗakinsa, sedai ko nuna mata ya gani beba balle yai mata godiya.

A Kitchen ya tarar da Nanan, tana wanke fruits, ya kalleta yace "wai uban wa yace miki ana shiga Kitchen da hijjabi, ke kenan kullum cikin hijjabi?"

"Ina ruwanka da hijjabina ne, kayi rayuwar ka mana"

Se da Sadik ya ji haushin kansa na tanka mata ma da yayi.







Farhan maganinta da take sha na bacci ya ƙare, ta koma 'yar gidan jiya babu bacci, ta dinga jin kanta Kamar ze rabe biyu ga wani irin nauyi da yai mata.
A haka ta daure take zuwa Makaranta, saboda zamanta a gidan ba abunda yake ƙara mata se matsananciyar damuwa.

Ta ɗauki takaddar maganin da me Chemist ya bata ranar, ta tafi da shi wani Chemis ɗin,  dan ta siya amma me Chemist ɗin yace ba ze siyar ba se da katin Asibiti.

Gaba ɗaya makarantar su ta ɗauka, Sadik ya yaudareta yayi Aure, wasu suna tausaya mata wasu na mata dariya suna cewa dama ai kyan ƙwarya ta bi ƙwarya, Ita ba sa'ar Aurensa bace ta na 'yar talakawa.

Ba a tashi tayar da zancen ma se an ganta, se a hau hirar Sadik, hakan ba ƙaramin sake jefa Farhan cikin mummunar damuwa yayi ba, ta ƙara tsangwamar kanta, daga baya makarantar ma ta ajiye ta dena zuwa gaba ɗaya.

Ba ta cin Abincin kirki, ba walwala kamar me takaba haka take rayuwa, Umma ta bar hakan a mazaunin alhinin Aure ne da za tai yake damunta.

Ta cigaba da bincika yadda za tai ta samu maganin nan amma abu ya gagara, ba ta samu maganin ba.

Ɗan kuɗin gyaran jikin nan, dana walima da ango ke bawa Amarya ba wanda Sunusi ya bawa Farahan, hasali ma duk majalissar da ya zauna se yace ai temakawa ze ya aureta, dan binnmaza take, ƙarshe ya shirya ya tafi ƙauyansu dan cigaba da shirye-shiryen biki.





"Gaskiya na gaji da wannan abun da kake Min, kullum ba zaka dawo ba se cikin dare, in ta faman jin tsoro yanzu idan wani abu ya sameni fa? Ba kowa a gida se ni kaɗai?"
Shigowar Sadik kenan take ta wannan mitar.

Ko kulata be ba, ya nemi Guri ya zauna, ya ɗakko wayarsa yana waya.

Da mace yake wayar, dan a hankali yake Magana, cikin harshen turanci, haryanzu bakomai Nana ke iya fuskanta a Turancin ba, amma dai ta gane da mace yake waya.

Wato ya maida ita kamar wata Mahaukaciya, ta na ta banbami amma yai mata banza Yana waya.

Bata san lokacin da ta ja wani uban tsaki ba tace "Aikin banza" Ta wuce ta nufi hanyar ɗakinta.

Bayanta yabi da kallo tare da yin ƙwafa.

Ita kaɗai a ɗaki, amma ta cigaba da yin mita, ta shiga tai wanka ta fito, ta saka kayan baccin ta, vest da wani guntun wando, sedai babu man da zata shafa ya ƙare tas.

Tsaki tai ta jefar da doguwar robar cream ɗin, ta saka hijjabi ta nufi ɗakin Sadik.

Yauma sanye yake cikin Rigar wanka, ze shiga banɗaki, se gata ba sallama bakomai.

Ya ɗago ya kalleta, cikin tsiwa tace "Nifa man shafawata ya ƙare, Abba yace duk abunda nake buƙata in gaya maka, amma kaƙi saurarata, ina buƙatar abubuwa da yawa, amma kullum ba zaka dawo ba se dare balle in gayamaka"

Kallo ɗaya yai mata ya shiga banɗaki, ya barta a tsaye a ɗakin.

Guri ta nema ta zauna, tace "Ai duk abu ba zaka kwana a banɗakin ba, dole zaka fito ina nan ina jiran ka"

Se huci take, dan gaba ɗaya haushin Sadik take ji.

Jin ƙarar buɗe ƙofar banɗakin ne ya sata ɗaga idonta ta kalli ƙofar.

Sadik ne ya fito daga shi se towel a ƙugunsa, ya yafa wani a kafaɗarsa, jikinsa jiƙe da ruwa.

A razane tace "Subhanallah" ba ƙaramin shiga kiɗima tayi ba, ba ta taɓa ganin namiji tsirara ba se yau, dan Sadik ba shi da maraba da tsirara, to ina ma zata ga namijin balle ta ganshi haka.

Tashi tai cikin azama za ta fice ta bar masa ɗakin, amma ya riƙeta ya ajiye towel ɗin dake kafaɗarsa, ya rage saura na ƙugunsa.

Nan da ta shiga razana, jikinta ya hau rawa, ta haɗiye wani irin yawu da ƙyar.

Sadik yai wani shakiyyin murmushi, ya ƙara mata manyan idanunsa, yace "uwar marasa kunya, kin ɗauka na canza da ga yadda kika sanni, dan kinga ina kawar miki da kai shine kike zaƙewa haka? A gabana kinyi waya kin gama ƙaren rashin mutunci kina cemin yaro, ke ba kya so na, yau kuma ina waya kin yi tsaki kince min Aikin banza, kina kishi na kenan?"

Kasa Magana tai se zare ido, baki ya mutu.

"Ke kina Tunanin Ni Sadik zan so ki ne? Ai nima ba son naki nake ba, Sadakar kifa aka bani kalleki fa wata ƙwaila da ke, ba gaba ba baya, kedai gaki nan ba wani alamar girma a tare da ke, balle a sa ran zaki zama cikakkiyar mace nan kusa, da har zan sa ran in kalleki ki burgeni, ke nan kawai a matsayin 'yar aikina kike, zaman da kike kenan, kuma yau sena cire wannan hijjabin in ga abunda kika taka kike min wannan fitsarar kike kirana da yaro!!!.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah karka ciren hijjabi na, dan girman Allah"

Kan ta rufe baki, Sadik yai sama da hijjabin nata, hakan ya sa ta ƙwala ihu da ƙarfi.....

(Malam Sadik ya haka ne?🙄)


Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
AYI HAƘURI BA EDITING....





Gaba ɗaya Nana ta razane, ta sa hannu ya kare ƙirjinta, se zare ido da take, ko Inna ba ta yadda ta ganta ba hijjabi, Se Sadik da ya taɓa ganin ta sau ɗaya ba hijjabi, shima kuma be kalleta Sosai ba.

Sadik kam yayi mamakin ganin Nana, saboda Yadda take zunduma hijjabai ba za kai zaton ma ta na da wani fasali ba.

Yayi mamakin yadda jikinta ya bayyanar da alamun girma haka, sedai ba hankali a tare da ita sam.

Ya sa hannu ya riƙe vest ɗin, ita ma ze cire mata.

Cikin magiya tace "dan girman Allah kayi haƙuri, ba zan sake ba kar kai min tsirara, ni marainiya ce dan Allah kark min haka"

"Ai ba kya tsoro, ni da nake Yaro,gara ai mu kece raini tsakanin ni da ke"

Tana jin yadda fatarsa me ɗauke da ruwan wanka, ke ƙara mannuwa a jikin ta ta fatar.

Kawai ta fashe masa da kuka, saboda tun da take ba ta taɓa shiga fargaba kamar yau ba, wai ita ce a hannun namiji yana mata wannan tijara, wanda ko hannun wani namiji ba ta taɓa riƙewa ba.

Sadik ya kama vest ɗin ta, da gaske ze cireta, ta sa hannu ɗaya ta riƙe rigar, ɗaya kuma ta rufe ƙirjinta ta na kuka.

Janyota yai zuwa gaban gado, tana turjewa ta na masa magiya, ga hawaye ya kalli Fuskar ta, yadda tai shaɓe shaɓe da hawaye, yace "kneeldown"

"To ka cika min rigar se inyi"

Ya cikata, aikuwa tai kneeldown, har da ɗaga hannu ta rufe ido.

Ji yai kamar yai dariya, amma ya dake yace buɗe idon ki ki sauke hannunki".

Ta buɗe ido, ta sauke hannayentA, ta kuma rufe ƙijinta.

"Wai uban me kike ɓoyewa, sauke hannayenki" yai maganar cikin tsawa.

Haka ta sauke hannun, tana cigaba da kuka.

Ya kalleta yace "ke mara kunya ko? Ni kike wa tsiwa ki na gayawa Magana ko?"

Ta girgiza kai.

Yace "to bari in tuɓeki, in ga abunda kika taka da zaki kalli kamarni kice min yaro"

"Nace dan Allah kayi haƙuri fa"

"Naji zan haƙura amma bisa wasu sharuɗɗai"

Tace "to"

"Na farko, daga yau karki ƙara zuwa kaina kina magana ba girmamawa, ba ma kya faɗar suna na, sedai kawai ki fara Magana da ni kai tsaye, to da ga yau am your boss, na gaya miki ke 'yar aikina ce, Boss Sadik zaki dinga kirana.
Abu na gaba, zaki dinga gyaran ɗaki da wanken toilet kullum sau biyu a rana.
Kuma zan downloading different receipe, da za'a iya sarrafawa a nan ƙasar, zaki dinga mana girki dan na gaji da yawon siyan Abinci, kuma ki kai jagwalgwalo se na miki abunda ba ki zata ba.
Always talk to me with respect and manners, am not your mate, idan ba haka ba se na tuɓeki na turaki ƙofar gida ki kwana a haka"

Cikin kuka tace "to zan dinga yi, amma dan Allah ka ƙyaleni in saka hijjabi na"

"Ba zaki saka ɗin ba, abu na gaba kince ai ba kya sona ko?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Yace "good, dama nima ba son ki nake ba, dan ban yi kalar Auren 'yar ƙauye ba, Naji kina gaywa kakarki zaki samo mata siriki Bature Allah ya temaka, Amma ki faɗa da bakinki"

Ta ɗan tura baki tace "Ni ko ma dai saki nawa ne, amma kawai ka sakeni"

"Shikenan, zan sake ki, amma nan da lokacin da zamu kammala karatu, yanzu dai ki kiyaye dokokin da na shimfiɗa miki, idan kuwa ba haka ba sena aikata abinda nai niyya"

Da sauri ta jinjina kai tace "to"

"Tashi ki ban guri"

Da sauri ta tashi ta na cigaba da rufe jikinta, ta fice da sauri Daga ɗakin.

Bayanta Sadik ya bi da kallo, yai murmushi da be san ya kufce masa ba ya tafi kan mudubi dan shafa maia.

Nana kuwa haki ta dinga yi da taje ɗaki, tace "yau na ga masifa, da ma tun ba yau ba na fuskanci ɗan iska ne Sadik ɗin nan, ya saba taɓa mata amma ban ta ɓa zaton ze yunƙurin yi min tsirara ba, Allah ka kiyayeni da Sharrin sa".

Da safe Nana har fargabar fitowa take, saboda ko haɗuwa da Sadik ba ta ƙaunar yi.

Amma ta tuna da kashedinsa, da sassafe ta tafi ɗakinsa ta shiga da sallama, dan gyara masa Sannan ta shirya ta tafi makaranta.

Sedai Ko tashi be ba daga baccin safe, haka ta shiga a gaggauce ta gyara masa toilet, ta tattare iya tsakar ɗakin, ta wuce ɗakinta dan ta shirya zuwa Makaranta.

A falo ta tarar da Sadik, ya fito jikinsa sanye da dogon wando da vest, ya kalleta ya yatsuna fuska, yayin da ita kuma se sunkuyar da kai take ko haɗa ido ba sa son yi.

"Kwomin coffee" ya faɗa cikin isa.

"Zan makara fa" ta faɗa a raunane.

"I don't care" ya faɗa yana ɗaukar remote.

Haka ta koma Kitchen cikin sauri, ta na kumbura baki ta dafa, ta zo ta aje masa tai waje ranta a ɓace.






Umman Farhan ta ɗaga labulen ɗakin Farhan tace "ki je babanki na kiranki a ɗakinsa"

Ta ɗan lumshe ido Sannan ta tashi, ta nufi ɗakin Abban.

Abba ya kalleta yace "Ya akai kika dena zuwa Makaranta ne?"

Tace "bakomai"

"A'a da komai, Gayamin meyasa?"

"Gani nai lokaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login