Showing 69001 words to 72000 words out of 259198 words

Chapter 24 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13394

zaci taji hirar tasu ba.

"Ƙwarai kuwa, ko dan kinga na ƙyaleki? Naji suna gaya miki wani yana bakin layi yana jiranki, Nana ita rayuwa ba'a mata gaggawa, duk saurayin kirki da yake sonki saboda Allah, gidanku ze zo ya nemi izini, ba wai ya dinga laɓewa a bakin hanya yana tsare ki ba.
Nana ke yarinya ce, kina kan ganiyarki ta RUƊIN ƘURUCIYA, Shiyasa abubuwa da dama kike ganin kamar ina takuramiki.
Ba takura miki nake ba, so nake rayuwarki ta inganta, ki guji ƙawaye barkatai, idan kika fiye ƙawaye da yawa zaki zama baki da sirri, sannan ba kamun kai, dan zaki suffantu da ɗabi'u daban daban daga gurin su, masu kyau da marasa kyau.
Dan haka duk abunda ya shige miki duhu, wanda kike buƙatar ƙarin haske ni zaki samu ki gayawa, duk wata shawara da ƙawa zata baki, in dai zaki iya ɓoyewa ba zaki faɗa ba to ba shawarar Allah da Annabi bace, dan haka ki kiyaye kinji abunda nace miki?"

Nana ta jinjina kai alamar eh.

Inna tace "Yawwa".










Koda Madam Joy ta raka Lilly gida, ta gaya musu kawai ciwonta ne ya tashi, sun bata taimakon da ya dace a Clinic ɗin Makaranta.

Maman Lilly ta karɓe ta cikin girmamawa tare da yi mata godiya.

Mamanta se jera mata sannu take, yayinda zuciyar Lillyn fal take da jin haushin Sir Nazir, babban abunda ya ƙara ƙular da ita be wuce yadda tana buɗe ido ta kalleshi, ya wani haɗe rai ya bar Clinic ɗin ba.
Ba ta san lokacin da tai ƙwafa a fili ba.
Mamanta ta kalleta tace "Lillyna meke faruwa ne? Nifa nayi mamakin yadda a kai ciwon nan naki ya tashi, ko dai an miki wani abun ne kinyi kuka?"

Cikin taɓara Lilly tace "please Mamma allow me to rest, am still feeling pain in my chest"

"Ohh God, ko a kira Doctor Kaseem ne?"

"No am ok, i just need rest"

"Ok rest my dear, amma zuwa magariba insha Allah zamuje Asibiti, bana son mahaifinki yaji ciwon nan ya tashi, ban kaiki Asibiti ba yaita sababi"

Lilly ba ta sake Magana ba se gyara kwanciyarta da tai.

(Cikakken sunan Lilly Fatima, itace 'yar Auta a gidan su, su huɗu ne a gidansu, babanta Babban General ne na Sojoji, yana matuƙar ji da ita, kasancewar sunan mahaifiyarsa ya samata, shine suke ce mata little daga baya kuma suka koma cewa Lilly, hakan yasa ba kowa yasan sunanta na gaskiya ba).

Da magariba ba yadda maman Lilly ba tai da ita ba akan suje Asibiti amma taƙi, se ƙyaleta tai.



Sadik kam Kamar yadda ya saba duk dare, hotonta yake ta zooming yana ƙare mata kallo, kamar a lokacin ya fara ganinta, yana jin wani abu yana cigaba da shigarsa a kanta.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kalli agogon wayarsa, ƙarfe ɗaya da rabi na dare, a hankali yai juyi tare da ƙanƙame wayar a jikinsa yana sauke numfashi.
"Allah ka amince min na mallaki Farhan"
Wani irin gumi ne yake tsatsafowa a goshinsa, a hankali ya ajiye wayar ya miƙe ya fito falon su.
Faruk ya tarar yana kallon wani Nigerian Film, kusancin jarumin da jarumar Film ɗin na nuna wani abu na shirin faruwa.
Tsakin da Sadik yai ne yasa Faruk ɗagowa ya kalli in da Sadik yake yace "kai kuma kai da waye?"
"Wannan shirmen da kake kallo mana Sadik ya bashi amsa yana buɗe fridge, ya ɗakko ruwa me sanyi.

"Ai seka tsaya ka gani kan ka yanke hukunci, tunda ba wani abun a kai ba"

Ɗan taɓe baki Sadik yai yace "Ni wannan ɗin ma shirme ne, mutum na zaman zamansa ya kallowa kansa damuwa"

Dariya Faruk yai yace "Allah nawan?"

Sadik ya zauna akan kujera one seater ya ɗora ƙafarsa, a kan ƙaramin teburin dake falon ya kalli Faruk yace "bro, am telling you the truth, wallahi bana iya jure kallon wannan fina finan, a simple Romance can put me in trouble, you understand what I mean"

Faruk yai murmushi yace "So, seka dena kallon Film gaba ɗaya ka koma cartoon"

"Ba zaka gane bane" Sadik ya faɗa yana shan ruwan da ya zuba a kofi.

"Ya zakace ba zan gane ba, i went through same situation as you, kawai Lokaci ne da jiki ke girma, da alamu na zama cikakken mutum shine kawai, amma nan da wani lokaci zaka koma normal"

Ɗan guntun tsaki Sadik yai yace "ni bana tunanin wannan yanayi ne da zan iya fita daga gareshi lokaci guda, duk kallace kallacen fina finai da nayi a baya, bana jin komai se haɗuwata da Wata yarinya a makarantar mu, i really fall for her, gaba ɗaya na kasa gane kaina, nayi ƙoƙarin nusar da Mother ni Aure nake so, amma se ta shareni koma taimin faɗa"

"Hmm ai dole tai maka faɗa, Sadik dudu guda nawa kake ne? Shekarun ka nawa a duniya da har zaka fara zancen Aure? Ni ban yi wannan zancen ba se kai, kasan Aƙidar Gidan nan ko? Boko first before anything"

"Aƙidar banza, ai ba dokar Allah bace, ni wallahi idan aka cigaba da tafiya a haka, ba zan iya wani karatu ba" yai maganar yana tsuke fuska.

Faruk ya tashi daga in da yake zaune, ya dawo kusa da Sadik ya zauna ya dafa kafaɗarsa yace "Sadik, ita yarinyar da kace sanadinta ne ka shiga wannan halin, ba wani abu bane face RUƊIN ƘURUCIYA, wanda yake faruwa a lokacin tashen balaga, wani abune na ɗan lokaci, kuma abun da kake ji kowa ma yaji, amma dannewa ake, kar ka sake wannan feelings ɗin yasa ka rusa Rayuwar ka, kayi ƙanƙanta dafara ɗaukar stress na marital life, just forget about her, focus on your life, da zarar ka samu abunda kake so zaka dena jin wannan son, dan haka ka kula"

Shiru Sadik yai yana sauraron Faruk, a hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya ajiye kofin hannunsa, ya miƙe tafi bedroom ɗinsa ba tare da ya kuma cewa komai ba.

Safa da marwa ya shigayi, yana son tabattar da dagaske son da yakewa Farhan RUƊIN ƘURUCIYA ne? Ya rasa dalilin da yasa kowa yake ce masa ai Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai.
Sedai abunda yake ji akan Farhan ya wuce a kirashi RUƊIN ƘURUCIYA kawai, shikaɗai yasan meyake ji a kanta.

Da wannan tunanin ya kwanta, har bacci ya ɗauke shi.


Kwana biyu Lilly ba ta Zuwa school, se ana uku taje, lokacin ta warware sosai, aikuwa tana zuwa su Haseena suka dinga ihu suna rungumeta.

Ture su Lilly tai tace "dalla can marasa mutunci, ba wadda taje dubani a cikin ku"

Yasmin tace "Wallahi yau muke cewa zamuje dubaki, jiya mutumin ki yazo yana tambayar ko kin zo?"

Lilly tace "waye mutumina?"

"Sir Nazir mana" Haseena ta bata amsa.

"Uwar mutumina, ai gayen nan Allah ya sakamin kneel down fa ya sani, na dinga kuka ina roƙonsa amma yaƙi saurarata, seda ya ga dama yace in tafi aji, kawai na faɗi a hanya"

"Dama ya za'ai ya saurareki, ai shi wannan ciwon naki gaba ta kaishi, ya samu abunda yake so"

Da mamaki ta kallesu tace "kamar yaya?"

Yasmin tace "ai ni zan labarta miki, da aka kai ki Clinic ɗin nan, kin kasa numfashi bakinsa yasa a naki yana hura miki iska"

"What, dalla bana son ƙarya"

Haseena tace "to ubanwaye ze miki ƙaryar, Wallahi dagaske ne, ya sa aka cire miki hijjabi daga ke se Long sleep, yaita hura miki iska, a wayance kuma dai kamar dai ba iya hura iskar yake ba" ta ƙarasa maganar suna kwashewa da dariya, banda Lilly da ta haɗe rai kamar zata fashe.

"Allah ya isa na" ta faɗa tana jan tsaki.

Suka sata  a gaba suka ding tsokanar ta suna dariya.


Sunan zaune malamin da suke da shi ya shigo, yai lesson ɗinsa ya gama ya fita, yana fita sega ɗan aiken Sir Nazir yana kiran Fatima Hakeem.

Tsaki tayi, dan a lokacin saura mintuna bakwai a fita break, su Haseena kuwa dariya suka cigaba da yi mata, wanda hakan ba ƙaramin ƙular da ita yai ba.

Haka ta tashi ta tafi Office ɗinsa, sedai ko da taje kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa.
Wani haushi ne ya sake mamayeta, ta tsaya a tsaye ƙiƙam taƙi Magana, shima ya cigaba da sabgar gabansa.

Jin ƙafafuwan ta na rawa ta gaji da tsaiwar ne yasa tace "Sir gani"

"Gaki, baki iya gaisuwa ba kenan ko?"

Kamar tayi masa tsaki, amma ta dake ta gaishe shi, be amsa yace "me nace miki ranar a Office ɗin nan?"

"Ai bani da lafiya"

"Will you shut up? Maza kije aji ki ɗakko littafinki kizo, in kin ga dama karki dawo"

Juyawa tai ta fita a matuƙar hasale, harda ƙwallar baƙin ciki.

Tana zuwa Class ta tarar da su suna karatun littafin watsewa da suka saba.

Tace "ke Yasmin shine kuka cigaba bana nan?"

"Ba dole mu cigaba ba, yaushe zamu tsaya jiranki?"

Suka cigaba da karatunsu, ta ɗauki littafinta tai waje, dan bata son dalilin da zesa Nazir ya kuma yi mata wulaƙanci.

Babban abunda ya bata haushi, be wuce yadda takasa faɗar abunda yai mata harta shiga halin rashin lafiya ba, da ko ba komai babanta yasa azo ai masa warning koma yasa a haɗa masa jikinsa.

Haka ta cigaba da Tunani, harta je Office ɗin.

Kujerar da ke facing ɗinsa ya nuna mata, ta nemi guri ta zauna.

Ya ɗakko wani littafi ya miƙa mata yace "maza ki duba daga in da kika tsaya da kwafar note ki fara kwafa yanzu Yanzu.

Kamar ta fasa kuka haka ta karɓa, tana jin haushin ajinsu ana can ana karatun Novel ɗin nan ba ita, ya kashe mata break ɗin ta.

Note ɗin da ake binta ba kaɗan bane, dan haka tasan ƙaryarta ta kammala shi a yau ɗin nan.

A hankali ta fara kwafa, sedai tun ba'aje ko ina ba ta gaji, ta fara tunanin me zatayi wanda zesa ya ƙyaleta ta tafi.

Ɗagowa tai ta kalleshi, shirt ce baƙa me gajeren hannu a jikinsa, damatsensa sun cika hannun rigar, sumar kansa zuwa sajensa se shining suke, ta kalli faffaɗan ƙirjinsa ta fara kamanta shi da jaruman da ake siffantawa a cikin book.

A ƙalla yana da kaso sittin cikin ɗari na yadda ake fasalta ƙirar jaruman littafi, ba shi da ƙaton baki ga gashi yaiwa haɓarsa ado. ƙirjinsa zuwa dantsensa ta cigaba da bi da kallo, she just imagine how will she feels if he hugs her?

Ta tuna yadda aka bata labarin yadda ya ɗauke ta da ta suma, da yadda ya bata artificial respiration, nan da nan ƙwaƙwalwarta ta shiga bata wasu lissafe lissafe da hasaso abunda suke karantawa a littafi game da malamin nata.

"Note ɗin zaki kwafa ko kallona zaki cigaba da yi?"

A ɗan kunyace ta dawo hankalinta, amma ta kwaɓe fuska cikin shagwaɓa tace "Am starve'

Ya ɗago ya kalleta yace "oya die here"

Kwaɓe fuska ta kumayi tace "Allah sir am hungry, let me go and eat food"

Drower gabansa ya janyo, ya ɗakko donut da drink, ya ajiye mata yace "oya kina ci kina rubutu"

Ta janyo donut ɗinta ta fara ci, sedai ƙwaƙwalwarta na mata saƙa a Mugun zare game da malamin nata.

A nasa ɓangaren shima yana basarwa ne, amma haka kurum yanzu da yaga yarinyar ƙirjinsa ke tsananta bugawa.

Seda aka koma class, Sannan ya bata damar tafiya, ta ɗau littafinta ta juya ta fara wata irin tafiya, wadda seda ya bita da ido harta fita.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya cigaba da aikin da yake.

Ko da ta koma aji har wani malamin ya shiga, dan haka kawai ta nemi Guri ta zauna, tana cigaba da tunanin Sir Nazir ɗin.

Sadik har yaje ya biya kuɗin ɗan maidaidacin hall ɗin da za'ai partyn, duk wani abu da za'a buƙata ya tanada, hatta rigar da Farhan zata saka ya siya. Sedai Farhan na ta fargabar yadda za'ai wannan lamari iyayenta basu sani ba, tana fargabar Idan Asirinta ya tonu da wani idon zata kalle su?.
      Har ƙanan invitation card ya bugo, ya bawa mutane ƙalilan, dan ba gayya yayi ba yadda za'ai komai a tsari ayi a gama.
Ya bawa Farhan invitations yace koda wanda zata gayyata, amma tace baby duk wanda ya gayyata shikenan.

Yau juma'a ta kama ranar da za'a gudanar da murnar zagayowar haihuwar Farhan, sedai gabanta nata faɗuwa ƙirjinta na ta bugawa, tabbas ba dan Sadii bane bijirewa wannan partyn za tai, dan haka nan taji ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri da zarar ta tuna.

In da suka saba ajiye Farhan su kai parking, ya kalleta yace "Anjima su Taslim da Khairat zasu zo su ɗakkomin ke, kin riƙe abunda nace ki faɗa a gida ko?" Farhan ta jinjina masa kai jiki a sanyaye.

Yace "good, see you later"

A hankali tasa hannu ta buɗe motar ta fita, ta nufi layinsu tana ta saƙawa tana warwarewa.

Bayan an sakko daga masallaci, Abban Farhan ya dawo gida, taje ta same shi a ɗakinsa suka gaisa Sannan tace "Abba dama..dama maman malamin mu aka kwantar a Asibiti, anjima za'aje dubata shine nake son ka barni"

Abba yace "Farhan bana san yawan fitar nan da kike fa, kiyi masa Addu'a kawai ya isa"

"Ammm...Abba ai ba ni kaɗai zanje ba, a motar gidansu 'yar ajinmu za'aje su zasu zo mu tafi, su dawo dani gida"

"Nifa bana son yawan shishshsigewa 'yan ajin nan naku, kin san dai ba ƙarfinku ɗaya da iyayensu ba, shikenan Allah ya bashi lafiya, ki kula da kanki Allah ya tsare"

"To Abba nagode" ta tashi ta fito daga ɗakin nasa, sedai jikinta a matuƙar sanyaye saboda ƙaryar da tai Masa.

Shi ya sanar da Ummanta anjima za suje dubiya, ta gaya masa.

Ƙarfe uku da 'yan mintuna sega Taslim da Khairat ƙanwar Sadik, sun sha dogayen hijjabai, Taslim nata ƙarewa gidan kallo.

Farhan tai sallama da Umma cikin dogon hijjabi, tabi su Taslim suka fita daga gidan.


Kai tsaye in da za'ai partyn suka nufa, maimakon su shiga hall ɗin partyn, wani ɗaki suka nufa da ita a cikin gurin, Taslim ce take ƙoƙarin shiryata, ta ba ta wata doguwar gown dark blue tace ta shiga toilet ta saka.

Farhan ta dinga juya rigar nan kan ta saka, dan da gani rigar me tsada ce, rigar ta rufe mata ko ina na jikinta, sedai ta kamata tsam a jikinta.

Ta fito daga banɗakin tana kakkare jikinta, Taslim tasa comb ta taje mata gashin ta, ta kawo ribboms ta ɗaure mata shi, su kai mata simple make up, aka samata wata hula nan da nan Farhan ta sake haskawa, kamar ba ita ba tai kyau matuƙa, sedai ita duk a tsorace take.

Seda suka gama shiryata tsaf sannan suka nufi main hall ɗin da za'ai birthday.

Abun mamaki suna zuwa duk an gama hallara, an ƙawata gurin matuƙa, idonta ya sauka akan Mubarak Babba da yake binta da wani irin mayen kallo, take wani Mugun haushin sa da tsanarsa ya sake baibaye ta.

Haɗa ido sukai da Sadik yana waya, ya kashe mata ido ɗaya, ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Duk kunya ta isheta, saboda kayan dake jikinta.

Kan a fara Komai Sadik yasa duk wanda ze shigo seya ajiye wayarsa a waje, dan yace be yadda ayi video ko ɗaukar hoto ba, se Camera ɗinsa da ya kawo.

Nan aka shiga shagalin ciye ciye da shaye shaye, amma banda Farhan da ta takure kamar ace ket ta zura da gudu dan fargaba da Zullumi.

Nas shine yake MC a gurin, ya ɗau mic yace  "Kafin mu cigaba da abunda ya taramu, wato taya abokiyar karatu, kuma wife to be ɗin abokin mu shagalin birthday ɗin ta, akwai wani game da za muyi Yanzu a gurin nan, Prince Sadik zan ajiye wasu papers, zaka fito kai da ita zaka zaɓi paper ɗaya, duk abunda ka ɗauka will be the birthday gift for your Beb"

Sadik yace "I already bought the birthday gifts for her"

"Wannan ai kai da ita ne, wannan kuma game ne kawai"

Sadik yace shikenan ya taso shi da Farhan, Zuwa tsakiyar hall ɗin.

Aka zube takaddu da aka ninke a kan tebur akace Sadik ya zaɓa.

Yasa hannu ya ɗakko takadda ɗaya, Nas ya karɓi takaddar ya buɗe, take yai shouting "wow, this is an amazing Love game, Prince takaddar da ka ɗakko tace :you will kiss her for good 3minutes as her special lovely, birthday gift"

Ƙuuuu cikin Farhan ya kaɗa, ta fara gumi ta zubawa Sadik ido taga reaction ɗin sa.

Girgiza kai Sadik yai zeyi Magana, amma suka ƙi bashi dama, suka kaure da shewa da ihu.

Nas yace "zamu gani, as a young man abokin namu ya cika namiji ze iya kokuwa ragone haryanzu yaro ne? Ita ma beb ɗin zamuga can she sacrifice to make him happy, zata yadda dan ganin ba ta bashi kunya ba? Ko kuma zata sa yaji kunya a gaban abikansa, Yau dai zamu tabattar namijine ko kuma maza ya rako? Ya kai mutum ko kuwa haryanzu be wuce goyon Mother ba yaro ne"

Ire iren wannan maganganun na Nas, suka shiga tunzura Sadik, dan sosai yake jin haushin kalmar yaro da suke kiransa da shi wasu lokutan.
Dan haka kai tsaye ya fara takawa a hankali yana tunkarar in da Farhan take.
Nan da nan suka ɗau tafi da shewa a gurin.
Yayin da ita kuma ta shiga zazzare ido, tana jan numfashi da ƙyar!

Kome ze faru? Akwai cakwakiya da tarin darussa me yawan gaske, gefe ga Lilly da Sir Nazir, ga Nana da kakarta RUƊIN ƘURUCIYA karku bari a baku labari yanzu aka fara.

Da fari book1 naso in baku free kamar yadda mukai a AƘIDATA se ku sai 2, amma an maida ni gantalallliya, ina posting ba kwa Comment kuma kuna karantawa, dan haka zan cigaba da sawa a Arewabooks, me son cigaba ya siya a can, me buƙatar ƙarin bayani yai min magana ta lambata.

Iya wanda sukai payment tunda fari su zan cigaba da turawa ta what's app, nagode ina Alfahari da ku masoya a duk inda kuke.

Taku har kullum Ayshercool.

Domin gyara Sharhi ko shawara
07063065680.


Share please 🙏
[6/4, 9:58 PM] Jakadiyar Arewa: SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.                   



                              31

A hankali ya ƙaraso in da Farhan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login