Showing 177001 words to 180000 words out of 259198 words
Chapter 60 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ne Sadik ɗin nan, ya saba taɓa mata amma ban ta ɓa zaton ze yunƙurin yi min tsirara ba, Allah ka kiyayeni da Sharrin sa".
Da safe Nana har fargabar fitowa take, saboda ko haɗuwa da Sadik ba ta ƙaunar yi.
Amma ta tuna da kashedinsa, da sassafe ta tafi ɗakinsa ta shiga da sallama, dan gyara masa Sannan ta shirya ta tafi makaranta.
Sedai Ko tashi be ba daga baccin safe, haka ta shiga a gaggauce ta gyara masa toilet, ta tattare iya tsakar ɗakin, ta wuce ɗakinta dan ta shirya zuwa Makaranta.
A falo ta tarar da Sadik, ya fito jikinsa sanye da dogon wando da vest, ya kalleta ya yatsuna fuska, yayin da ita kuma se sunkuyar da kai take ko haɗa ido ba sa son yi.
"Kwomin coffee" ya faɗa cikin isa.
"Zan makara fa" ta faɗa a raunane.
"I don't care" ya faɗa yana ɗaukar remote.
Haka ta koma Kitchen cikin sauri, ta na kumbura baki ta dafa, ta zo ta aje masa tai waje ranta a ɓace.
Umman Farhan ta ɗaga labulen ɗakin Farhan tace "ki je babanki na kiranki a ɗakinsa"
Ta ɗan lumshe ido Sannan ta tashi, ta nufi ɗakin Abban.
Abba ya kalleta yace "Ya akai kika dena zuwa Makaranta ne?"
Tace "bakomai"
"A'a da komai, Gayamin meyasa?"
"Gani nai lokaci yana ƙaratowa, ba amfani cigaba da zuwana Makaranta"
Abba ya girgiza kai yace "A'a, Aure da zaki ba ya na nufin shikenan karatunki ba, karatunki na da matuƙar mahimmanci, dan mun riga munyi magana da mijin naki, ze barki ki cigaba dan haka se Allah ya kaimu satin bikin zaki dena zuwa, gobe in Allah ya kaimu ki shirya ki tafi makaranta"
Abba da ya san halin da zuwa Makaranta ke sawa ta shiga, da be ce ta koma ba, amma ba yadda ta iya, haka ta amsa masa cewar za ta koma ɗin.
Daga nan Abba yace "Yawwa Allah yai miki Albarka, aita haƙuri da rayuwa, shi Aure ɗan haƙuri ne, ba ni da shakka akan kibda tarbiyyar da muka baki, na san ke Yarinya ce ne ladabi, amma a ƙara ai ta haƙuri, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki yi biyayyar Aure, ki nemi aljannar ki, insha Allah ba zaki dana sanin wannan Auren ba, ina sa ran ze kula dake, kar ki kalli duk wani ƙyale ƙyale na rayuwa kwanciyar hankali a zaman Aure, ita ake nema"
"To Abba insha Allah"
"Yawwa ta shi kije, Allah yai miki Albarka"
Ta amsa da Ameen Abba.
Magungunan da Hajiya take bata ne, suka ƙara jefata cikin mawuyacin hali, da ma can ya lafiyar kura, balle yanzu da Hajiya ke aiko mata da kayan shirya amare.
Wani irin feelings ne ke sake takura mata, sedai tai ta juyi akan katifa kamar macijiya.
Ta kan tuno yadda akan Sadik ne ta san wani abu makamancin haka, a hankali take sauke ajiyar zuciya ta na lumshe ido.
A hankali ta fara tunani, ta taɓa jin yadda Taslim da Meena suke hirar, Mubarak Babba ya na ba su abunda yake sa mutum ya mata damuwarsa.
Take ta ji tana son sanin meyake ba su, idan da dama ita ma ya bata ko Allah ze sa ta manta da Sadik, taji sauƙin raɗaɗin da ke cikin zuciyarta.
Se kuma ta tuna ai Ance an kama Mubarak ɗin, dan haka ba ta san in da zata ganshi ba.
Dafe goshinta tayi, tana sake rintse idonta, saboda yadda kan nata ke wata irin sarawa kamar ana dukanta da guduma a kanta.
Nazir ne rungume da Lilly a Office ɗin sa, yana kwantar da kansa a jikinta yana lumshe ido.
"Please ka ƙyaleni, in tafi bana son wani ya zo ya ganni a Office ɗin nan, zargi ya fara shiga"
Muryarsa ƙasa ƙasa yace "wane irin zargi kuma, ba wanda ze ganmu ai duk ana Class, bari in saka key please karki tafi"
Tace "gaskiya am not in mood, ka ƙyaleni"
Yai ajiyar zuciya yace "to, naji amma yaushe zaki zo gidan, nai missing girkinki"
Lilly tace "Daddy fa ya na gari, ba yadda za ai in zo, ni ka ƙyaleni in huta mana haba"
Murmushi yai yace "duk wannan hutun da ki kai, yaushe rabonmu da juna? Ke ko missing ɗi na ba kya yi?"
"Hmmm, ai ni kwana biyun nan hutu na ne"
"Ko dai kin samu wani ne? Shine kike ƙoƙarin juyan baya?"
Dariya tai tace "kai ka sani a layi, kuma ba wanda nake mu'amala da shi se kai, Karma ka sake kawo wannan tunanin a ranka, and lokacin sake ɗaukar allura ta yayi, shiyasa ka ga naƙi sakin jiki, ba na son a samu matsala"
"No karki damu, babu wata matsala da za a samu Insha Allah, allurar za ta iya ɗaukar dogon zango a jiknki, but allow me to enjoy please"
Haka suka saka key a Office ɗin, suka sheƙe ayarsu, tsakanin Malami da ɗalibarsa (waiyazubillah, Allah ya shirya mana zuriya).
Khairat ta tattare kayanta ta bar gidan Mother, tana cikin damuwa sosai, saboda tun daga lokacin da Faruk ya ƙi amincewa da soyayyar ta, ta ji zaman Gidan ya isheta, ta tattara ta koma na su gidan, ta na cigaba da jin yadda ta ke matuƙar jin kewarsa.
Kwana biyu Nana ta ɗan nutsu, ta rage yiwa Sadik tsiwa da rashin kunya, dan da gaske ta yadda ze mata tsirara, ita kuwa da yai mata tsirara ga ra ta bi shi a sannu.
Sadik kuwa ya samu dama, ya ke juyata yadda yake so, saboda ya gano lagonta, dan har gugar kaya yake sata, yai ta sata aiki kamar baiwa.
Yau da daddare Sadik ya samu Nana a falo, tana duba litattafanta.
"Jeki shirya zamu fita" ya faɗa a taƙsice.
"Ina zamu?"
"Ban sani ba" ya bata amsa.
Seda ta ɗan tura baki, sannan ta miƙe.
"Idan kika sako wannan uban hijjabin, sukace kin ɓoye bom ba abunda yai min zafi kamaki za suyi su kaiki prison"
"Kai wannan masifa da me tai kama?"
Tai maganar tana jan ƙaramin tsaki.
Doguwar rigar abaya ta saka, da mayafinta sannan ta fito.
Seda ta ɗan jira Sannan Sadik ya fito, haka ta biyo bayansa tana mamakin in da za su a daren nan.
Taxi suka hau, suka tafi ba tare da ta san in da za su ba.
Wani katafaren mall suka je, Tun da Nana ta zo London ba ta taɓa yawo aka garin ba, nan ta saki baki ta na kallon ƙayatuwar garin.
Cikin mall ɗin suka shiga, Nan Nana ta zama cikakkiyar 'yar ƙauye saboda kallo.
Ya kalleta yace "ki shiga ki ɗau abunda kike buƙata"
"To ina zan je?"
"Bakiga in da mutane suke bi ba?"
"Dan Allah ka zo muje, ni wallahi ba zan iya zuwa nikaɗai ba".
"Tun da cinye ki za suyi ko?"
"A'a dan Allah ba danni ba" tai maganar tana langaɓe kai.
Guntun tsaki ya ja, yai gaba ta bi bayansa.
Nan ta dinga ɗibar abunda ta ke so, abunda Sadik ya siya babu yawa, yace ta zo su tafi.
Ta kalleshi tace "to kayan fa?"
Be kulata ba ya kuma yin gaba, tana binsa kamar jela.
Farfajiyar mall ɗin suka koma, ya sa aka kawo musu coffee, be ce ta sha ba, be ce kar ta sha ba, shi dai ya ɗau na sa yana sha.
Wayarsa ya ɗakko ya daddana, ya saka a kunnensa.
Nana ta ɗau coffee ɗin ta tana sha, tana lumshe ido da alama yanayin yana mata daɗi.
"Hello Mother"
Se da cikin Nana ya kaɗa jin ya kira sunan Mother.
"Sadik, kai kuwa meyasamu wayarka? Duk na bi na ɗaga hankalina, har na fara shirye-shiryen sawa a duba min kai, fiye da wata guda wayarka ba ta shiga"
Sadik ya ɗan gyara zama yace "Abba ne da ya zo, yai seizing ɗin wayata, ban san dalili ba, se da na sai wata na canza sim, so ban samu liscesne ɗin amfani da layin bane, se jiya shiyasa kika jini shiru"
"Kai, amma hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, wallahi na shiga damuwa sosai, amma ni sam be nuna min cewar ya zo in da kake ba, cemin yai gurin 'yarsa zeje"
"A'a ya zo"
"Shikenan, ina fatan ba wata matsala dai?"
"Ba wata matsala, am just missing You mum"
Mother tace "Allah sarki Autana, ya makarantar?"
"Makaranta Lafiya ƙalau, komai normal"
"To Masha Allah, Allah ya bada sa'a, ka kula da kanka sosai da sosai, ina kuma jadadda maka ba kai ba yarinyar nan, karka kuskura kaje in da take, ina nan ina wani shiri yadda zan raba Auren nan kan ku dawo, ba tare da mahaifinka ya ji haushin mu ba"
Kallon Nana Sadik yai, ya ga She's busy siffin her Coffee, tana yi ta na kalle kalle.
Ranar da Steve ya zo gidansu, ya haɗa shi da Abba a waya, Abba ya ja kunnensa sosai sannan yai masa Nasiha yace "Yanzu Sadik, idan ni ko mahaifiyarka ya mutu, ya zakaji?"
Sadik yace "haba Abba, dan Allah ka dena irin wannan maganar"
Abba yace "ina son ka bani amsa ne"
Sadik yace "zan shiga damuwa, ban san yadda zan misalta halin da zan shiga ba"
Abba yace "idan kuma ka rasa mu duka fa?"
"Abba, dan Allah ka dena wannan maganar, kar ka sa zuciyata ta karye"
"To ina son ka misalta kanka a matsayin Nana, haka fa ta tashi ba uwa ba uba, ba ta san daɗinsu ba sam, ta dai tashi tsakanin kakaninta, ka sanya kanka a matsayin da Nana take na maraici, duk gatan da za'a maka ba kamar gatan iyaye ba ne, ni ba zan takura maka se ka sota ba, amma dan Allah ina roƙonka, kar ka cutar da ita, ka yi haƙuri da ita ka dubi maraicinta, akwai falala me girma a cikin riƙon maraya, ba ita tai maka laifi ba, kar ka huce a kanta, kayi haƙuri, ina lallaɓaka a yanzu, amma idan kaje ka aikata son zuciyar ka, to duk hukuncin da Ubangiji yai maka sedai in kalleka"
Wannan maganganu na Abba ne ya sa jikinsa Sadik yin sanyi sosai, ya zamana da ya kalli Nana, se yaji tausayinta haka ta tashi ba ta san mamanta ba, ba ta san babanta ba ta rasa wannan Soyayyar ta su har abada, wannan dalilin ne ya sa ya ɗan sassauto da ga wannan ƙiyayyar da yake mata.
"Kai wai ba ka jina ne?" Se yanzu Sadik ya tuna waya yake da Mother, yace "Ina jinki, dan Allah ki turomin lambar bro, da yake amfani da ita yanzu"
Mother tace "shikenan, zan turo maka"
A hankali ya sauke wayar daga kunnnsa yana kallon Nana, da take ta lunshe ido alamar bacci take ji.
Ya miƙe tsaye ya kalleta yace "mu tafi"
Ya samo taxi suka ɗauki siyayyar da sukai, suka tafi gida, sedai kan suje tun ta ɓingire ta na bacci a Mota.
Kallonta yake, yana tunanin yadda ze tashe ta ba tare da ta masa ihu ba, dan ya san kaɗan da aikinta.
Ya fita daga Motar, ya sassauke kayan, ya buɗe gida sannan ya dawo ya ɗauketa, zuwa cikin gida.
A kan gadonta ya ajiyeta, Sannan ya shigo da kayan da suka siyo.
Duk wannan budurin da Sadik yake ba ta san yanayi ba, saboda baccin nata yai nisa sosai.
Bisa ga umarnin Abba, Farhan ta komaa Makaranta, ta cigaba da zuwa, sedai ba ta gane Komai, kuma ba ta son mutane gaba ɗaya.
Yau an fita break, Lilly ta shigo da ledar takeaway a hannunta, Farhan ta kalli Lilly tace "dan Allah Fatima, ina Mubarak Babba?"
Da mamaki Lilly tace "meyasa kike nemansa? Ina bakwa shiri da shi?"
"Eh na tambaya ne kawai, naji kamar rannan kince an kama shi ko?"
Lilly tace "eh hakane, ai dama shi wannan kusan kullum cikin kama shi ake, Amma karki mamakin yanzu haka ya fito, saboda babansa ya tsaya masa"
Farhan ta jinjina kai tace "shikenan Nagode"
"Ko dai ya cigaba da bibiyar ki ne?"
Farhan tace "A'a na tambaya ne kawai"
Amma a ƙasan zuciyar ta, so ta ke ta haɗu da Babba dan ta samu abun rage damuwa, hatsarin da ke cikin hakan be dameta ba, ita mafita kawai take nema.
Nana taji daɗin siyayyar da sukai, sedai Assignment ne da ita na Maths, na ta rasa yadda za tai solving ɗin sa, ga shi yanzu tsoron Sadik take ji.
Ba ta da zaɓi illa zuwa ta sameshi, yana aikin na sa na video game tace "Amm.. dan Allah Assignment zaka koya min"
Ya ɗan ɗago ya kalleta ya cigaba da game ɗin sa.
"Dan Allah ka koyamin in ka iya"
"Ban hanaki ki zo kaina ki tsaya ba, kina min magana a haka ba, me nace ki dinga kirana da shi"
"Yi hakuri, na manta ne"
Ya miƙa mata hannu, alamar ta bashi littafin.
Ba musu ta miƙa masa, ya ɗan kalli Assignment ɗin sannan ya kalleta yace "ke wannan ne se an koya miki? Meye abun wahalar a nan?"
"To ba nayi na kasa ba" tai maganar tana cuna baki.
Tsaki yai ya karɓi biron hannunta, ba tare da yace mata komai na, ko yayi using calculator b, ya fara solving.
Abun ya bata mamaki sosai, ba ta taɓa ganin Sadik na karatu ba, sedai video game ko litattafan turanci, se kuma yawonsa.
Amma cikin nutsuwa yake solving ɗin, a mintuna ƙalilan ya kammala ya miƙo mata, ya karɓa ta kalla tace "to ai ban san yadda kai ba, idan kuma aka tambaye ni ya akai nayi fa?"
"Se kice, yi miki a kai ke ba ki iya ba"
"Hmm Allah sa ma daida kai min, kar in kai inci zero, kawai ka karɓi biro ka min rubutu a cikin littafi"
Kallonta yake da mamakin tsiwa irin ta Nana, sedai yaji gabansa ya faɗi, gani yake kamar abu makamancin wannan ya taɓa faruwa da shi a gaske, kamar wannan abun ya taɓa faruwa.
Take kansa ya fara juyawa, ya fara kokawa da memory ɗin sa, akan ya tuna meyafaru, wani abu me mahimmanci yana cin sa a zuciya, amma ya kasa tuna ko meye.
Jifa yai da remote ɗin hannunsa yana dafe kansa, a gigice Nana ta kalleshi tace "Subhanallah, meke faruwa ne meya same ka?"
Cigaba da rintse ido yai Sosai, yana jujjuya kansa akan ya tuna wannan abun, amma se yaji kamar kansa ze rave biyu.
Ta jefar da littafin hannunta, ta yo kan Sadik da sauri tace "baka da lafiya ne?"
Ya girgiza mata kai alamar a'a, da sauri taje fridge ta ɗakko ruwa ta kawo masa tace "karɓi ka sha ruwa"
Ba musu ya karɓa, ya ɗaga kai ya sha sosai, Sannan ya ajiye.
A sanyaye tace "ko Steve za ka kira, a kaika Asibiti?"
Ua girgiza mata kai, ya nemi guri ya kwanta yana ajiyar zuciya.
Nana ta zauna tai tagumi tana kallon sa.
Ya kai awa guda a wannan yanayin sannan ya watstsake, ya tashi ya fita.
Yau saura sati biyu, Auren Farhan ta sake susucewa, gaba ɗaya ta koma wata wujiga wujiga, kamar korarriya, banda azabar ƙiyayyar Sunusi da kuma son Sadik ba abunda yake ɗawainiya da ita.
Yau bisa ga jagorancin makauniyar zuciyar Farhan, me cike da neman mafita ta tafi ajinsu Sadik, gurin Tasleem.
Tasleem tayi mamaki da Farhan tace wai gurinta ta zo.
Farhan tace "dan Allah temaka min nake son kiyi"
Tasleem tace "wane irin taimako kenan?"
Farhan tace "da daɗewa naji kuna cewa, akwai maganin rage damuwa da sa bacci, shine nake son dan Allah zan siya ba na iya bacci sam"
Tasleem tai murmushi tace "duk tunanin Sadik ɗin ne?"
Farhan tai shiru ba tace komai ba, Tasleem tace "welcome to the jungle Yarinya, Allah ya baki kyau da ƙira, ki mori ƙuruciyar ki, amma kika tsaya biyewa Soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, a wannan surara ta ki, ba iya kayan caji Yakamata ki tsaya ba, Yakamata ace kina ehhhh" Tasleem tai maganar tana shafa bayan Farhan...........
ME KUKE TUNANIN ZE FARU? FARHAN BA IYA DAMUWA KE DAMUNTA BA, HAR DA MATSANANCIN FEELINGS, ZATA SHIGA GANG ƊIN SU TASLEEM, LET'S DISCUSSED THIS BEFORE ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLA)
(Amin afuwa, typing ba yawa, saboda yanayi na Salla, in Allah ya kaimu gobe ranar Arfa, zanje hutu se Allah ya kaimu bayan salla insha Allah zamu ɗora, dan Allah kar ku manta da ni a cikin Addu'oin ku a ranar Arfa.)
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Kasa ɗaga ƙafarta tai da ga in da take tsaye, tai shiru ta shiga tunani "yanzu idan ki ka fita ina zaki a Wannan dare? Wa kike da shi da zaki gurinsa? Idan ki kai haka kin wa kanki adalci kenan? Mutuncinki da kimar ki za su zube a idon duniya, kuma ki bawa iyayenki kunya, ace kin gudu ranar ɗaurin Auren ki.
To amma ai auren dole za'aimin, yanzu shikenan nai bankwana da farinciki? Shikenan haka rayuwata za ta ƙare, in rayu da mutumin da babu alamar Soyayyar sa a raina? Ta ya zan iya Rayuwar Aure da Soyayyar wani a raina? Abba meyasa kuka kasa fahimtar kawaici nai muku? Bana son wanda zaku Auramin?" A hankali wasu siraran hawaye suka fara zirarowa daga Idonta.
A hankali ta ja ƙafarta ta koma cikin ɗakinta, ta ɗakko maganin da Babba ya ba ta, ta ɓallo ɗaya ta ɗau ruwa ta shanye, a tunanin ta ko tai bacci ta samu sassauci.
Ta nemi guri ta kwanta ta ƙurawa guri ɗaya ido, tana tunani daban daban a zuciyar ta.
Befi mintuna goma da shan maganin nan ba, ta ji kanta yana mata wani irin abu, Kamar duniyar na jujjuyawa, ta rintse idonta ta buɗe amma ta ga komai yana juya mata, gani tamkar ginin ɗakin da take ciki ze ruso kanta.
Hannu ta sa ta danne kanta, ta rintse ido, wani irin gumi ya shiga kwaranyo mata, ta rasa gane a wace duniyar take, a zahiri abunda take gani ne, ko kuma ita kaɗai take ganin abunda take gani.
Haka ta wanzu a wannan hali, ba tare da sanin in da kanta yake ba.
Sadik yayi bajinta sosai a wasan ƙwallon da akai a makarantar su, duk da kasancewar sa baƙar fata, amma yana da magoya baya sosai da sosai, club ɗin sa ne suka ci 4 abokan karawar su kuma suka ci 2, Sadik ne ya saka ƙwallaye uku a raga.
Bayan an tashi daga wasan, aka dinga hotuna da Sadik, Nana tana gefe tana kallonsa tana murmushi.
Tana nan zaune tana kallon yadda ake ɗaga shi sama ana hotuna da shi, sedai abun takaicin bayan ya je ya canza kaya, sun shiga cikin makarantar, nan 'yan matan turawan nan ma suka dinga rungumarsa, suna ɗaukar hotuna har da masu masa kiss a goshinsa.
Hakan ba ƙaramin ɓatawa Nana rai yai ba, dan haka Sadik ya nemata ya rasa a gurin ko sama ko ƙasa.
Hankalinsa ya tashi sosai ya shiga nemanta a gurin, sedai be ganta ba sam, ga guri