Showing 231001 words to 234000 words out of 259198 words
Chapter 78 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
labarin abunda Sadik ya ɗakko, kuma kakansa ya bashi goyon baya, har gida ya zo, ya samu Sadik ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, yai masa tatas ya zage shi.
"Guda nawa kake dudu, shekarunka nawa saboda hauka da rashin hankali, kace wai zaka ƙara Aure, dan ubanka dukiyar da kake taƙama da ita, ai ubanmu ne ya tara sanannan muka samu, kuma kasuwanci yi maka ake, ba kai kake yi ba, ba ka san wahalar komai ba, makaranta ma kaƙi komawa, sedai ka ci ka tara mata, kai ga wanda ya kawo jarabar bin mata duniya, to Wallahi ka shiga hankalinka idan ka sake ɗaga wannan maganar se nai maganinka Wallahi"
Sadik ya fusata ainun, su ba su san ɓarnar da ya tafka a bayan ƙasa ba, su ƙyleshi tun da yana da halin riƙewa yayi, amma anyi caa a kansa, iya haihuwar da Nana tai, ya isa su ɗau darasi amma an kasa fahimtar sa, shi ba dan Nana ta gaza ze Auri Farhan ba, sedai Auren Farhan shine mafita ɗaya da ze cetota kuma ya wanke lafimsa na baya, ya nawa Farhan son da baya tunanin ko Aure tai ze iya rabuwa da ita, a irin son da yake mata, kowane hali take ze iya haƙuri ya aureta, amma kowa yaƙi fahimtar sa, yaji haushin maganganun da dr. Yai masa, amma be ce uffan ba ya bar masa falon shi da Mother, kuma be ji alamar ze janye abunda yai ƙuuduri ba.
Da azahar rana tsaka Sadik yaje gidansu Farhan, se ya haɗu da Huzaifa ze shiga gidan ya tsaya suka gaisa da Huzaifa sannan yace masa 'dan Allah cikin gidan nan zaka shiga?"
Huzaifa yace "eh ciki zan shiga"
Yace "dan Allah in ka shiga ka cewa Farhan tana da baƙo a waje"
Huzaifa yace "to zan gaya mata insha Allah"
Shigarsa babu daɗewa se ga Farhan ta fito, tana waige waige dan ta ga wake nemanta da tsakar ranar nan?.
Tana ganin Sadik ta haɗe fuska tace "lafiya?"
"Ba Lafiya ba, meyasa kike guduna kike wulaƙanta ni haka? Kulluma na zo seki ƙi fitowa"
Cikin ko in kula tace "idan na zo me zan maka? Sadik na gaya maka kar ka sake zuwa ƙofar gidan mu, na gaya maka, idan kuma ka cigaba da zuwa ka dinga ganin wulaƙanci da rashin mutunci da ga gurina kenan"
"Yanzu kina ganin wulaƙanta nin shine mafita?"
"Shine babbar mafita a gurina, a gurinka kuma dena zuwanka shine mafita, kowa yayi rayuwarsa".
"Kamar Sadik naji kina cewa?" Cewar Abba da yake ƙoƙarin fitowa daga cikin gida.
Gaba ɗaya suka sha jinin jikinsu, Sadik ya rusuna yana gaida Abba, Abba ya ƙare masa kallo tabbas ba ze ta ɓa mantawa da Sadik ba, ya sha ganinsa dan baze manta zuwan da yai kawowa Farhan kati ba.
"Kai ne Sadik ɗin dama?"
Sadik yace "Eh nine Abba"
Abba yace "kaine dam silar duk wannan wahalar da ɓacin rai da na shiga akan Farhan? Kai ne ka dinga hure mata kunne da soyayya, ka tafi ka barta ta shiga mummunar rayuwa irin wannan, ni na ɗauka wani babban mutum ne ma ashe kaine, kaje ba zance maka komai ba, amma idan abunda kai dai dai ne, zaka gani a ƙwaryar shanka, ka tafi ka barmin ƙofar gida kar in sake ganinka, na samu wani ze Aureta ba ze yuwu ka zo ka cigaba da hure mata kunne bax
Sadik kamar ze yi kuka yace "Abba dan Allah".
Abba ya ɗaga masa hannun yace "ka ɓace min daga ƙofar gida kar in sake ganinka". Abba ya ƙarasa maganar yana nuna masa hanya.
Gaba ɗaya se jikin Farhan yai sanyi, Abba ya kalleta yace "ke kuma wuce gida, idan na kuma ganin ya zo kin fita sena ɓata miki rai, mara zuciya kawai" Farhan jiki ba ƙwari ta koma cikin gida.
Sadik kuwa kifa kansa yai a saman motarsa, ya rasa abunda yake masa daɗi, a hankali ya buɗe ƙofar motar, yana ƙoƙarin shiga, a dai dai lokacin kuma Sunusi ya kawo kai, ƙiƙifta ido Sunusi ya shiga yi dan tabbatar da dagaske Sadik yake gani ko gizo ne, sedai kan ya gama murje idon, Sadik ya bawa motar wuta ya bule Sunusi da ƙura.
Kusan a guje Sunusi ya ƙarasa makarantar su, yana son tabattar da in abunda ya ganewa idonsa gaske ne.
Mahaifin Lilly yaje har can in da ya kai ajiyar ta, saboda rashin lafiyar da akace masa tana yi, an kaita Asibiti amma ba wani cigaba.
Ya tsorata sosai da ganin yadda ta rame, tai duhu tana ganinsa se kuka, tana "dan Allah Daddy ka yafemin ka maida ni gida, na tuba ba zan sake ba Daddy" abunka da ɗa da mahaifi, se tausayinta ya kama Major, dan haka yace da ita ze taho Kano.
Ita kanta Mummy ta tsorata da ganin yadda Lilly ta koma, fara ce jawur Lilly amma ta koma duk tai wani iri.
Ƙanwar mahaifin Lilly Anty Sa'a, tana gidan Major ya dawo da Lilly, tayi mamakin ganin yadda Lilly ta koma, nan ta tambayi ba'asin abunda ya sa aka kai Lillyn can kudancin Nigeria gidan abokin Major aka barta.
Mummy ba ta ɓoyewa Anty Sa'a komai ba, ta gayamata abubuwan da suka faru.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku kaico na".
Mummy tace "Anty Sa'a, lafiya kike wannan salatin haka?"
Anty Sa'a ba ta amsa ba ta kalli Lilly tace "Lilly, waye ya kawo muku irin wannan litattafan kuka karanta?"
Lilly bata ɓoye mata ba, ta gayamata yadda ƙawarsu Yasmeen ke tura a wayar yayarta ta turo musu su karanta, ko ta kawo musu su karanta a aji.
Anty Sa'a ta kalli Mummy tace. "Yanzu kuna me kuka bar yarinya ƙarama kamar Lilly da wayar hannu ba tare da kuna bibiyarta ba"
Mummy tace "wallahi saboda Assigment, kusan kullum cikin ɗaukar tawa wayar take, wai tana Assigment shiyasa ya siya ya bata dan ta bar min tawa".
Anty sa'a tace 'ban taɓa dana sani a rayuwata ba kamar na yau, ina da sa hannu a lalacewar Lilly, kuma ba ita kaɗai ba yaran mutane da yawa, nayi nadama a lokacin da bani da halin gyarawa, mugun abun da na aikata ya riga ya cika duniya".
Mummy tace "to ai ni ban fuskanci abunda kike nufi ba".
Anty Sa'a ta share hawaye tace "irin litattafan da su Lilly ke karantawa, irinsa nake rubutawa, na fara wannan salon rubutu ne saboda ina burin in suna a harkar rubutuna, na fara irin wannan rubuce rubucen, ba irin nasihar da ba aimin ba, amma na ƙi na kasa denawa, katsam Allah yaiwa ɗaya daga cikin wadda muke irin wannan rubutun rasuwa, kuma rubutun be dena yawo a duniya mutane na la'antar rubutun ba, a gaɓar da jikina yai sanyi na dena, se gashi ashe 'yar ɗan uwana ta lalace ta sanadiyyar irin wannan rubutu, kaico na ba zan taɓa yafewa kaina ba wannan abu da na aikata, dan Allah ku yafemin, nayi ƙoƙarin sauke duk irin rubutun a kafafen da na san na ɗora, amma wasu site ɗin ba ni da bani na ɗora ba bani da ikon saukewa, dan Allah ku yafemin".
Mummy tai shiru ta rasa abunda yake mata daɗi, ta rasa abunda za tace, sam ba taji a zuciyarta zata iya yafewa Anty Sa'a ba, duk da kasancewar ta ƙanwar mijinta.
Sadik kam ya koma salihin ƙarfi da yaji, ya zamana rana zafi inuwa ƙuna, Amma duk da hakan sam baya jin ze iya janye ƙudurinsa na Auren Farhan, kuma mahaifinta ma ze cigaba da bibiyarsa yana sa ran ze haƙura ya ba shi ita. Da wannan ƙwarin gwiwar ya kuma tunkarar Abbansa yana masa magiya "Abba dan girman Allah ka fahimceni, kar ka duba ƙanƙantar shekaruna, tun da ka ga na dage akan lallai ina son yin Auren nan, Akwai dalilin hakan"
Abba yace "to meye dalilin naka?"
Sadik yace "Abba, a bar batun tona dalilin ni dai dan Allah ka amince min, Wallahi ba zan wulaƙanta Nana ba, ina sonta, Amma Farhan na fara so a rayuwata, ban san yadda a kai al'amura suka juye min ba"
"Yanzu kai Sadik ban da haɗama ya za kai da mata har biyu, kai kanka haryanzu da saura ba ka gama hankali ba, ya za kai da mace har biyu saboda rashin hankali"
"Au Sadik haryanzu ba ka janye maganar Auren nan ba ko? Duk faɗa da cin mutuncin da nai maka a kai, kaje kai abunda ka ga ya dace da kai, tun da kai dai ba ɗan Arziki bane, ban isa ince bana son abu ka bar shi ba, Allah sarki Faruk Wallahi da shi ne da tuni ya bar maganar nan, amma banda kai, nayi dana sanin sangarta ka da nai, to the extent da baka jin maganata".
Sadik kamar ze fashe da kuka yace "haba Mother, Dan Allah.....
"Rufemin baki, Aure ko kaje kayi amma ba da yawu na ba, kuma ka nemi wata uwar bani ba, wadda ta isa da kai"
Dummmmm haka Sadik ya ji kansa yayi, cikin jiri ya fara tafiya a hankali, ya bar sashin yana lumshe idonsa, da ya fara ganin duhu.
Nana na zaune a falo, tana yiwa Sahal wasa, tana babana ya fi na kowa, se ɓaɓɓaka dariya yake, yana kallonta tare da miƙa hannu ze kamo fuskarta.
Ba ta ji Sallamar Sadik ba, se ganinsa tai ya shigo yana dafa bango, ɗan binsa da kallo tai dan ta gano ma'anar hakan da yake yi, a hankali ya fara kiran sunanta yana miƙo mata hannunsa.
Tai sauri ta tashi ta ƙarasa in da yake tace "ya dai meke faruwa?"
"Jiri nake ji, kuma duhu nake gani a idona"
Nana tace "Yasalam, ta ya haka?" Ta riƙo hannunsa za tai masa jagora zuwa kujera, kawai ta ga ya faɗi ƙasa!
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680
A gigice Nana ta durƙusa akan Sadik, tana jijjiga shi, se dai ko motsi ba ya yi, kuma idanunsa sun rufe, gaba ɗaya jikinsa yai sanyi.
A guje Nana ta ruga cikin gida, ta nufi shashin Abba, se dai da ta je ɗin kasa magana tayi, se nuna masa hanyar waje take, ganin ta kasa magana ya sa da Abban da Mother suka biyo bayanta dan ganin meke faruwa, suna zuwa suka tarar da Sadik a ƙasa cikin fita hayyaci.
Nan suka shiga rafka salati, Abba yace wa Nana ta bashi ruwa me sanyi a fridge, ta je ta ɗakko ta kawo, aka shashshafa masa a fuska, amma be ko motsa ba.
Abba yace wa Nana, maza je ki cewa Sabo ya fito da mota mu tafi da shi Asibiti.
Haka Nana ta kuma kwasa tai waje, taje ta gayawa Sabo saƙon Abba, bayan fito da motar, Sabo da kansa ya ƙarasa BQ suka ɗakko Sadik shi da Abba, suka kai shi mota, ita kanta Mother hankainta a tashe yake.
Abba ya kalli Nana yace "Nana, koma maza gurin Sahal, ki zauna duk abunda ake ciki ma kira ki a waya"
Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska tace "Abba dan Allah ku bari in biku"
Abba yace "A'a maza koma cikin gida". Daga haka ya shiga motar ya rungume Sadik a jikinsa, Mother ta zauna a ɗaya gefen suka nufi Asibiti.
Kai tsaye Asibitin da suke da file suka tafi, A emergency aka karɓi Sadik, aka shiga da shi likitoci suka rufu a kansa, dan ƙoƙarin ceto rayuwar sa.
Kusan awa guda su Mother na waje, sedai likitocin da Nurses su zo su wuce su, ba wanda yace musu komai, Mother ta kira dr. A waya ta sanar masa halin da ake ciki, ba daɗewa se gashi da Jidda sun zo Asibitin.
Se bayan kusan awa ɗaya da mintuna sha biyar sannan babban likitan ya fito yana cire safar hannunsa ya cewa Abba suje Office ɗinsa.
Bayan sunje suka sake gaisawa, doctor ya kalli Abba yace "Yallaɓai, ya akai aka bar abokina ya shiga wannan yanayin haka a wannan ƙananan shekarun nasa?" Da yake likitan da Familyn Abba sun daɗe tare suna zuwa Asibiti sosai, dan haka ya san Sadik sosai mutuminsa ne.
Abba yace "meya same shi ne haka?"
Likitan ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "well, jininsa ya hau ranka ya daɗe, hawa ba na wasa ba kam, da shekarunsa sun ja sosai fiye da haka, yadda jinin nan nasa ya hau, kuma ya faɗi da ya kamu da paralyse" Abba ya zaro ido yana kallon doctor.
Doctor ya cigaba da cewa "na sa an ɗebi jininsa an kai lap, dan yin wasu gwaje-gwaje, yanzu kuma zan rubuta hoton ƙwaƙwalwa da na zuciya idan ruwan da aka saka masa ya ƙare, se kuje ayo a waje, dan nan bama yi"
Abba ya jinjina kai yace "Ikon Allah, to Allah ya bashi lafiya".
Doctor yace "Ameen, se ai ta kula ana kwantar masa da hankali, amma a shekarunsa ace jininsa yana irin wannan hawan gaskiya akwai matsala"
Haka Abba ya fito jiki a sanyaye, yaiwa su Mother bayani, Usman ya hau faɗa "yanzu akan an ce baze Auren ba shine yake nema ya kashe kansa? Aikuwa sedai ya mutu dan ubansa a wannan karon ba ze samu yadda yake so ba".
Jidda tace "haba dr., Dan Allah ka tausayawa halin da yake ciki ka bar wannan Maganar dan Allah, a bari ya samu lafiya".
Mother na shirin yin Magana, wayarta ta fara ringing kan ta cirota ta katse, missed calls ɗin Nana kusan guda Ashirin, Mother ba ta sani ba, ta bi lambar Nanan, tana ɗagawa kukanta ta fara jiyowa, Nana tace "Mother ya jikin nasa? Ya tashi kuwa?"
Mother tace "ki kwantar da hankalinki, yaji sauƙi an masa allura ne yana bacci".
Tace "to Mother in biyoku?"
Tace "A'a, ki zamanki likita yace a barshi yai baccinsa karki damu, tare zamu dawo gida insha Allah".
Nana tace "to, dan Allah a masa sannu, amma ba abunda ya same shi ko?x
Mother tace "eh, malaria ce, kuma an ba shi magani".
"To Allah ya ba shi Lafiya".
Mother ta amsa mata da Ameen.
Zuwa jimawa se ga Mummyn Khairat ma, tare da Khairat sun zo duba Sadik, nan suka dinga jajanta lamarin wai Sadik da hawan jini.
Har akaje gurin hoton ƙwaƙwalwar da zuciya Sadik be san anyi ba, saboda ƙarfin Allurar da a kai masa.
Abu Kamar wasa Sadik se bayan sallar isha'i sannan ya farka da ga nannauyan baccin da ya wuce da shi bayan suman da yai, likita ya zo kansa ya dudduba hoton ƙwaƙwalwa da akai masa, da na zuciya duk lafiya ƙalau ba matsala.
Likita yace "Alhamdilillah, zuciyarsa lafiya ƙalau haka ƙwaƙwalwarsa, amm he is at risk of stroke, saboda jininsa yadda ya hau, yanzu dai muna ta ƙoƙarin jinin ya sauka zuwa normal, gashi can ya farka a samu a bashi Abinci, yai salla zamu kuma yi masa Allurar bacci, amma kar a matsanta masa se yai Magana, sannan kar a ɗaga murya a ɗakin nasa, komai ai masa a hankali".
Mother ta amsa da "to".
Usman ne ya kai Sadik ya kama ruwa, ya zo yai salla ba wanda yace wa Uffan, aka kawo masa Abinci ba wani ci yai ba, ya ɗauke kai, ya gyara kwanciyar sa ya lumshe idanunsa.
Se jera masa sannu suke, amma babu wanda ya amsa.
Usman yace Su Mother su tafi gida, shi ze zauna a gurin Sadik, musamman saboda Nana da ta na can cikin damuwa.
Jin an ambaci Nana Sadik ya buɗe ido yace "Nana tana ina?"
Mother tace "tana gida, ita da Sahal"
"Ace mata tayi haƙuri dan Allah, Mother ku bata haƙuri dan Allah".
Sadik kamar yana cikin magagi ne, be san meyake faɗa ba, surutai kawai yake yi.
Mother da Abba su kai sallama da dr., Suka tafi gida, dama Jidda tuni ta koma gida tai musu girki ta aiko musu da shi.
A falo Mother suka tarar da Nana, tai shiru kana ganinta ka san a cikin tashin hankali take, tana ganin su Abba ta miƙe tana faɗin "Abba, ina yake? Ina baban Sahal ɗin?"
Abba yace "kwantar da hankalinki, se Allah ya kaimu da safe, Sannan za'a sallame shi".
Nana tace "to waze kwana da shi a can?"
Mother tace "Usman yana can, tare da shi zasu kwana"
"Mother da ma ni aka bari na kwana da shi"
Abba yace "ba damuwa, ki kwantar da hankalinki, ya warke ai, ai gobe in Allah y kaimu za ki je ki duba shi"
Da kyar suka kwantar wa da Nana da hankali, sedai se aikin kuka take tana Allah ya ba shi Lafiya.
Ba Mummyn Lillyn ba, shi kansa Major ya ji baƙi ciki da takaicin abunda 'yar uwassa ta aikata, dan da fari cewa yai ya barta da Allah, dan ba ya jin ze iya yafe mata abunda ta aikata, taje ta yi abu ya dawo kan 'yar sa.
Mummy ce tace "kaga Major kayi haƙuri ka yafe mata dan Allah, ka san kaima Akwai naka laifukan da ka aikata, mu bar hakan a mazaunin ƙaddara kawai, Allah ya ƙara shirya mana zuri'a".
Major yace "wannan abu da me yai kama? Ina amfanin irin wannan rubutu da tai, Yanzu idan ta mutu yaran mutne suka cigaba da karantawa suna lalacewa fa? Allah kaɗai ya san adadin yaran da suka gurɓace a sanadin abunda ta rubuta, Wallahi ji nake kamar in mata Allah ya isa"
"A'a Major, kayi haƙuri tun da har tai nadama, Aikin gama ya gama, se fatan Allah ya kiyaye gaba"
Haka Mummy tai ta bashi baki, tana kwantar masa da hankali.
Bayan fitar Major, Lilly ta shigo ɗakin Mummy, gaba ɗaya tai wani iri ta zama saliha sosai da sosai.
Mummy ta kalleta tace "ya dai?"
Jiki a sanyaye tace "Mummy alfarma na zo nema a gurinki".
"Wace irin Alfarma kenan?"
"Mummy, dan Allah karki bari Daddy ya auran wannan sojan bana son sa, ya min girma sosai, dan Allah kuyi haƙuri ku yafemin ba zan sake ba, kuma bana son a maida ni garin nan, dan Allah kumin rai".
Mummy tace "A'a, ba dai ba kya jin magana ba, ba ruwans duk hukuncin da ya yanke a kanki daidia ne, tun da ubanki ne".
"Mummy dan Allah, ku min rai Wallahi bana son sa".
Mummy tace "ba kya son sa to wa kike so?"
"Mummy, dan Allah ki saka Daddy ya sa a saki sir Nazir, idan aka sake shi se muyi Aure, tun da shine.... Se kuma tai shiru.
Mummy tace "ƙarasa mana, sarauniyar marasa kunya, ashe ma haryanzu ba ki nadama ba
Lilly ta girgiza Kai cikin hawaye tace "Mummy nayi nadama, ina neman afuwarku, amma haryanzu ba zan dena zargin kaina, da ni nai silar komai ba, Sir