Showing 189001 words to 192000 words out of 259198 words

Chapter 64 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13425

min 'ya ta" yai maganar idonsa fal ƙwalla, ko ba a gaya masa ba ya san a cikin maye Farhan take saboda surutan da take.

Ya koma ɗakinsa, wata irin ƙwallar baƙin ciki ta taru a idon sa, Umma ta biyo shi tana Malam meye abun yi akan Yarinyar nan, ni kam na gaji da wannan lamarin, ba yau ba gibe ta dinga janyo mana abun Magana".

Abba ya girgiza kai yace "kiyi haƙuri, muyi shiru da bakinmu mu dinga mata addu'a, takura ko tsauri ba za suyi aiki ba"

Cikin kuka Umma tace "kaga irin abunda nake ji ko? Da an haƙura anyi Auren nan da shikenan, koba Komai tana can Asirin mu a rufe, amma yanzu watan tonon Asirin mu ya tsaya, Malam kwana fa tai a waje, a ina ta kwana?"

Abba yace "kar ma ki kuskura ki tambaye ta a in da ta kwana, ba abunda hakan ze haifar banda ɓacin rai, muyi mata Addu'a Allah ne ya jarrabe mu, na san jarabta ce, yarinya ta me hankali ce da tarbiyya, Allah ya shirya ta"

"Shikenan, babu wani mataki da zaka ɗauka akan ta?"

Abba yace "to in ba addu'a ba, so kike in tsine mata? Ko kuma in koreta ta bar min gida? Addu'ar dai ita ce mafita"

Umma ta dinga kuka, Abba na mata nasiha, saboda hawayenta masifa ne a Rayuwar Farhan.

Se bayan la'asar Farhan ta gama dawowa hayyacinta, taje tai wanka ta jera sallolin da ake binta, ba tare da shakkar laifin da ta aikata ba, ita babbar damuwarta haɗa salloli da tai.

Shiru tai tana ƙoƙarin tuna abunda yafaru da ita, Gabanta ne yai mummunar faɗuwa da ta tuna, taje tana jiran Babba ya bata magani ne, aka ba ta ruwa ta sha, daga nan ta farka ta ganta a ɗakin Hotel.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyafaru da ni to? Meya sameni, me sukayi min? Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah yasa ba keta min mutunci su kai ba, naiwa Sadik Alƙawarin komai daren daɗewa ba wanda ze mallake ni se shi"
  'ji banza, yana can yai Aure, maimakon ki ta kanki, amma ke ta wani Sadik kike, bayan shi yana can yana shagalinsa' wata zuciyar ta tunatar da ita.

Wani irin gumi ne ya shiga keto mata, jikinta ya hau rawa, kenan bugar da ita sukai, su kai mata fyaɗe? Shikenan mutuncinta da kimarta, Mubarak ya yaudareta kenan, sun haɗa kai da 'yan ajinsu sun cutar da ita, shiru tai ta shiga tunanin yadda ake labarin taƙadirancin Mubarak.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un" shine abunda Farhan ta faɗa tare da dafe kanta, ta fashe da wani irin gigitaccen kuka, tabbas ta ta ta zo ƙarshe rayuwarta ta ɓaci.
"Wace irin masiface haka take bibiyata, da ga wannan se wannan, shikenan ba ni sa sa'a  rayuwa ta? Astagfirullah wa atubu ilaih"  ta shiga jujjuya kanta da ya riga yai mata Wani irin nauyi.






Da safe har Nana ta tafi Makaranta, Sadik baccin sa yake, tun da yai sallar Asuba ya koma gado ya naɗe ya cigaba da baccin sa.
Ba ta tashe shi ba, saboda yadda ya sha wahala jiya kan yai bacci, dan haka kawai ta tafi makaranta.
Ko da ta dawo gida, Sadik ba ya nan, nan ta tabbatar da lallai ya samu lafiya, tun da harya samu ƙafar yawo.

Nana na tsakar ɗakinta tana karatun exams, ta jiyo muryar Sadik a falo yana ƙwala mata kira "Friendy where are you?"

Daga ɗaki ta amsa masa "gani a nan, Lafiya Kuwa?"

Buɗe ƙofar ɗakin yai yace "Ashe kin dawo?"

"Na dawo tun ɗazu, naga ka ware harka fita"

SADIK yace "Yeah, come and see something"

Tace "something like what?"

"Zo ki gani mana"

Ta ɗan lanƙwasa wuya tace "karatun exams fa nake"

Yace "dan Allah ta so ki gani"

Ta miƙe ta biyo bayan Sadik, ƙofar gida ya jata ya nuna mata sabon babur dal.

Ta kalleshi tace "Friend wannan kuma na waye?"

Yace "Namu ne? Har lasisin tuƙi na yi"

Tace "wai siya kayi?"

"Eh mana, be kyau bane?"

Ta naɗe hannayenta a ƙirjinta tace "yayi kyau sosai, amma ba ka ganin muna yiwa Abba ɓarnar kuɗi da yawa"

"Ke wai fina son Abban nan ki kai ne? Allowance ɗina ne, na ƙwallo da shi na siyo mana"

Tace "Au har biyanka suke?"

Yai murmushi yace "au ke da duk wannan facakar da muke da kuɗi kin zata duk kuɗin Abba ne? Ina samun kuɗi da ball ɗin nan, ba dan karatu ba ma da babban club ne za su siyeni, business zan fara fa"

"A siyeka kuma, se kace Zamanin bayi?"

"Ke fa Matsala ta da ke kenan, wauta ke ba ki taɓa jin ance an sai ɗan ball ba?"

Nana tace "yo ina gida, a ƙuryar turakar Inna ta ina zan sani.
yanzu masha Allah, Congratulations to us, ubangiji Allah ya tsare mana, saura kuma ka dinga tafiya kana barina"

"Ɗakko ɗan kwalinki, ki zo muje ɗani"

Nana ta ɗan ɓata fuska tace "karatun exams fa?"

"Ke dalla, shikenan rayuwa bawa ba ze huta ba, ki dinga hutawa kan ki da bokon nan, maza jeki shirya mu ware kawai, yau ba zama munyi ƙafa"

Nana tai murmushi ta koma gida, ta ɗakko mayafi, tai rolling akan abayarta, ta hau sabon babur ɗin Sadik suka shiga zaga gari.

Sun sha yawo sosai, sun zaga gari Sosai, sannan Sadik ya maida Nana gida ya sake fita gararambarsa.

Se taran dare ya dawo, ya wuce ɗakin Nana, ze sa ta girki, dan yawon da yai, yunwa yake ji sosai.

Yana shiga ya tarar tana banɗaki tana wanka, ya kalli yadda ta ɗame gadonta, ɗakin se ƙamshi yake, aikuwa dan ya tsokane ta yaje ya haye gadon, ya kwanta.

Ya kai mintuna goma a kwance akan gadon, yana game a wayarsa, Nana ta buɗe toilet daga ita se towel ta fito.

Se da ta razana ganin Sadik a kwance a kan gadonta tace "meya haka dan Allah zaka shigo min ɗaki ba sallama?"

Ya ɗan kalleta yace "yunwa nake ji wallahi, sonake ki ɗan dafamin wani abun"

Ta riƙe ƙugu tace "taɓ, ni baiwarka ce? Ina shirin kwanciyar zan maka girki, ai yaseen ba zan ba" tana cikin yi masa tsiwa, ta ga ashe har da takalmi ya hau mata kan gado.

A fusace ta nufo kan gadon tace "dan Allah meye haka, na gyara gadon ka hau min kan gado da takalmi, wannan ai wulaƙanci ne, dan Allah ka saukar min daga kan gado"

Shareta yai ya ci-gaba da game ɗin sa, a fusace taje ta sa hannu ta cire takalaman da ke ƙafar Sadik, ta ajiye su a ƙasa tana cigaba da masifa.

Ganin ba shi da niyyar kulata ne, ya sa ta ɗau kayan baccinta, ta shiga banɗaki ta saka, ta fito ta shafe jikinta da mai, ta shafa turaruka, ta ɗako turare ta ɗau lallausan duvet daga wardrobe, ta feffesa masa turare, ta zo kan gadon ta ɗau fululluka ma, ta shafa musu turare.
Sadik yana kallonta ta wutsiyar idonsa, a ransa yace 'wannan Yarinyar akwai ɓarna'

Sedai ƙamshin da ya gauraye ɗakin, ya saukar masa da kasala, se wani lumshe ido yake yana shaƙar ƙamshin turarukan da suka gauraye ɗakin.

Kan sa ta zo ta tsaya, hannunta rungume da bargonta, ta kalli Sadik tace "Ni ka tashi, zan kwanta"

"Ai ban hanaki ba" yai maganar ba tare da ya kalleta ba.

"To ka saukar min daga kan gado, kasan dai na zan kwanta tare da kai akan gado ba"

"Ashe kuwa zaki kwana a ƙasa, dan ba zan tashi ba"

Haushi ne ya kama Nana, ta san Sadik da taurin kai, ta ɗakko pillow, za ta kwanta a ƙasa ta tsaya tace "kaiii, ni da ɗakina kuma gadona in kwana a ƙasa, rannan da nake jin tsoro naje ɗakinka ai a ƙasa na kwana, yau kuma se ka kwana a gadona ni kuma ina ƙasa, to wallahi ba ze yuwu ba" ta ƙarasa maganar tana hayewa kan gadon.

Fulo ta sa a tsakanin su, ta nemi guri ta kwanta.

Take Sadik ya ji shi a wata duniya ta daban, kasancewar Nana a kusa da shi, tana wannan ƙamshi me daɗi.

Lumshe ido tai tana Addu'oin ta na kwanciya bacci.

Ɗiff taga Sadik ya kashe lantarkin ɗakin.

Tace "A'a ya naga haka, ya zaka kashe fitila, ga ka ɗare ɗare akan gado, wannan ai ba ɗabi'ar arziki bace"
Ji yai kamar ya kwashe da dariya, yace "ni ba na iya bacci fitila a kunne.

"Gaskiya idan muka kwana gado ɗaya baka kyauta min ba wallahi, gaskiya ka shiga hakkina"

Shareta yai, yana cigaba da tattaɓa wayarsa.

Har bacci na ƙoƙarin kwashe Nana, ta ji Sadik a jikinta, muryarsa ƙasa ƙasa yace "Husna, haka zaki barni in kwana, yunwa nake ji wallahi"

"Ni na aike ka yawo? Wai ma wa ya gaya maka sunana na gaskiya? Ba wanda ya san sunan nan se wanda suka raɗamin"

Kamar ze mata kuka ya zagayeta da hannayensa yana sa hancimsa a wuyanta yace "So kike Ulcer ta kamani ko? Husna" ya kuma faɗa a hankali.

"A gaskiya bana son irin wannan abun da kake min, ni wallahi jikina wani iri nake ji in ka taɓa ni, gaskiya ka dena, kaga ni cikani in koma falo, naji zan bar maka ɗakin"

Cikata yai yace "Sorry, na ƙyaleki ba se kin fita falo ba, yanzu zan tafi, have a nice dreams"

Murguɗa baki tai kamar yana kallonta a ranta tace "Mutum shi dai in be naniƙi mace ba ba yajin daɗi, shiyasa rayuwa cikin turawa be ba, mutum yai ta kwafar banzayen ɗabi'u'

Ta koma can ƙarshen gado, ta takure, a haka har bacci ya kuma kwasheta.

Sadik kam ya rasa meye ma abun yi, yayi dana sanin zuwa ɗakin Nana, ya rintse idanunsa, yana ajiyar zuciya.

So yake ya tashi ya bar ɗakin, amma ya kasa motsawa, yana nan a kwance, dare ya cigaba da tsalawa ba tare da ya samo mafita ba.

Nana akwai make-make in ta na bacci, yo ta saba da kwana ita kaɗai, ta buga masa hannu a ƙirji, in aka jima ta maka masa ƙafa, ƙarshe gaba ɗaya ta dawo kansa tana baccinta.

A gigice Nana ta farka daga baccin da take, jin wani baƙon al'amari da ba ta taɓa zata ba.
Sedai Sadik ba wani tausayi ko makamancin haka, yai abunda zuciyar sa ke raya masa, se dai bayan ya nutsu ya dinga jin kamar ya aikata ba daidai ba, tamkar ya aikata wani gagarumin laifi, duk da yasan Nana matarsa ce, amma ya kasa gane dalilin da yasa yake jin hakan
Se dai ya bar abun a Nana tai ƙanƙanta da abunda yai mata, shi kansa be san yadda akai al'amuran suka kasance ba, jinsa yake kamar ba shi ba, kamar wani sabon mutum daban haka yake jin kansa.

Nana kam baki ya mutu ƙus, se kuka da take ko Magana ta kasa, se Allah ya isa da take masa a zuciyar ta.

A hankali ya janyo Nana jikinsa yace "Am sorry Husna Please..... Ai be ƙarasa ba, ta ƙwace daga jikinsa tana kuka, sedai ta kasa Magana sam.

Ya lumshe ido, yana son rarrabe wane irin yanayi yake ciki a halin yanzu.

Ya ɗau dogon lokaci a haka, Sannan ya miƙe ya shiga toilet ɗin dake ɗakin Nana.

Ya ɗan jima Sannan ya fito daga toilet ɗin, ya samu guri ya zauna a gefen gado, ya zubawa Nana ido, dan be san meya kamata yai mata ba.

Wayarsa ya ɗakko, yana ɗan daddanawa, daga ba ya koma banɗakin, sannan ya dawo a hankali yace "ki tashi ki shiga toilet ki gyara jikinki"

Banza tai masa ta sake shigewa cikin bargo.

Cikin tsawa yace "ba kiji me mace bane?" Ai a razane ta diro daga kan gadon, ta Sanya doguwar Rigar baccin ta, ta nufi banɗaki tana kuka me sauti.

Yace "kuma ba wankan soso da sabulu za ki ba"

"To wann zan yi?" Ta faɗa tana share hawaye.

"Ba'a koya miki wankan tsarki a Islamiyya ba, shi za kiyi"

Wani kukan kura ne ya ƙara ƙwacewa Nana, Sadik ya gama raina mata hankali.

Ƙasan zuciyarsa kuwa, wani irin tausayin Nana ne ya mamaye shi, amma ya san halinta, yana lallaɓata zata lanƙwashe tai ta Iskanci.

Bayan tai wankan ta fito, ta ga Sadik ya kuma kwanciya akan gadon nata, har da lulluɓa da bargo.

Ta canza kayan baccin ta, ta ɗau pillow ta koma ƙasa ta kwanta, tana ta sheshsheƙar kuka.

Sadik yana jinta, yai mata shiru. Se da yaji alamun tai bacci, sannan ya sakko daga kan gadon, kansa yana wata irin sarawa, ya ƙaraso in da Nana ke kwance, ya kwanta a kusa da ita, ya lulluɓe su da bargo, ya rungumeta tsam a jikinsa, yana faɗin "Am sorry Friend, na miki laifi but am so sorry" yai maganar yana sake ƙanƙameta, yana jin yadda jikinta yai zafi, se ajiyar zuciya take a bacci.



Ras!Ras!!Ras!!! Gaban Farhan yai wata irin mummunar faɗuwa, ƙirjinta ya buga da ƙarfi a jere, wanda se da numfashinta yai barazanar ɗaukewa.



Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.








Miƙewa tsaye Farhan tai, taje gaban Window ta tsaya, ba tare da ta san dalilin hakan da tai ba.

Har gari ya waye idon Farhan biyu, ba ta rintsa ba, zuciyarta se suya take, mussaman idan ta tuna abunda su Mubarak Babba su kai mata.

Da safe Umma na can na fafutukar shirya yara su tafi makaranta, Farhan ta ɗakko wayar Umma, ta ɗakko lambar Mubarak Babba, da ya bata Ranar da ya kawota gida.

Bugu biyu ya ɗauka yace "hello waye?"

"Farhan ce" ta bashi amsa.

Yace "Ohh beb ya kike?"

Farhan tace "ina zamu haɗu? Ina son ka bani abun nan"

Mamakine ya kama Mubarak, yadda be ji ta tambaye shi, abunda ya faru da ita ba.

Yace "mu haɗu a Hotel ɗin nan"

Farhan tace "ka jirani ƙarfe huɗu na yamma"

Ta kashe wayar, taje ta ajiyewa Umma, tana ƙoƙarin Fitowa daga ɗakin, su kai karo da Umma, ta kalli Farhan tace "me kike min a ɗaki?"

Farhan ba tace mata uffan ba, ta raɓata ta fice daga ɗakin.

Tana jin yadda Umma ta rakata da zagi, da ƙanan maganganu amma tai shiru ba tace komai ba.




Da Asubar fari Sadik ya tashi yai alwalwa, ya dawo ya tashi Nana dan tai salla.
Daga haka ya fice ya bar mata ɗakin, Nana tana alwala tana kuka, har ta zo tai salla ta idar, koke koken ta take yi.

Har wajen ƙarfe tara na safe, se da Nana taji yunwa za ta mata illa, sannan ta lallaɓa ta fito falo.

Sadik na kwance akan doguwar kujera, hannunsa riƙe da remote, Kallo ɗaya tai masa, ta ɗauke kanta daga kallonsa ta wuce Kitchen.

Binta yai da kallo, yana gano zunzurutun fushi a fuskar ta, ga tausayin ta da ya ke ratsa zuciyarsa.

Kitchen ta shiga ta haɗo tea, ta soya ƙwai ta ɗakko bredi ta fito, har zata wuce ɗakinta Sadik yace "ke, ni kenan da yunwa zan zauna?"

Ranta a haɗe ta koma Kitchen, ta haɗo masa kayan Abinci, ta kawo ta ajiye masa, zata koma ɗakinta yace "nemi guri ki zauna"

Ba dan ta so ba, ta samu guri ta zauna tana hura hanci, saboda yadda take jin haushin Sadik.

Sadik ya ci Abincin sa ya ƙoshi, ya ƙare mata kallo yace "wai ke uban me akai miki, se wani huran hanci kike?"

Ai kuwa dama ƙiris take jira, ta fashe da kuka tace "bayan ka lalata min rayuwata, kuma kake tambayata me kai min, a kafi kowa sanin abunda kai min.
Duk yadda Inna ke ƙoƙari a kaina kar in lalace, ta ke tai min nasiha akan in kiyayi maza, shine ka lalata min rayuwata, yanzu da wani idon zan kalli Inna? Sun turoni inyi karatu, ka lalata ni, me zance musu?" Ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka.

A ransa yace 'anya wannan 'yar ta na da kai kuwa?'

A fili yace 'ni kike tambaya me zaki gayawa Inna? Ki gaya mata Sadik ya ɓata miki rayuwa, ga amsa a bayyane"

"Au haka ma zakace, ka cuceni kuma kana gayan baƙar magana? Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, shikenan mutuncina ya zube"

Sadik yace "ai seki bi shi ki kwaso shi, sokuwa kawai"

Baƙin cikin duniya ya ishi Nana, Sadik ya mata wannan abu kuma ya koma yana raina mata hankali, kamar be yi komai ba.





Kamar yadda Farhan su kai da Mubarak, ba tare da neman izinin kowa ba, ta shirya ta fita daga gida, se dai babu wayar da zata kira shi tace masa gata ta zo.

Tana nan tsaye ta hango shi yana fitowa daga reception, yana ganinta ya hau murmushi irin na 'yan Duniya yace "My baby, ashe kin ƙaraso?"

Farhan ta kalleshi cikin tsana, dan ko fuskarsa ba ta son gani.

Yace "muje daga ciki ko?"

Ba musu ta bi bayansa, wani ɗaki ya kai ta a cikin Hotel ɗin, ta tsaya tana ƙare wa ɗakin kallo.

Yace "zauna mana, bari in kawo miki abun taɓawa ko"

Farhan ta kalleshi tace "ba shi na zo yi ba, Mubarak me ku kai min ranar da na zo Hotel ɗin nan?"

Yace"Normal ne, ki basar kawai beb"

Cikin ɓacin rai tace "Kar ka kuma cemin wata beb, Mubarak me ku kai min? Ka gayamin?" Ta faɗa cikin kuka.

Yai ajiyar zuciya yace "Am sorry, kawai ki ɗau haƙuri, ba shi da amfani sanin abunda ya faru"

"Kamar yaya me kake nufi?" tai maganar hawaye wani na bin wani.

Mubarak yace "Farhan, ai bana alƙawari in saɓa, tun da na ƙyalla ido na ga Sadik ya mutu akan sonki, nai alƙawarin se na miki illa na ɗanɗana masa baƙin ciki me raɗaɗin gaske"

Kamar Mahaukaciya Farhan tace "Meye nawa a ciki? Ni laifin me nai maka? Ina ruwana da abunda ya haɗa ku?"

Mubarak yace "ok har kin manta lokacin da kika mareni kenan, kin ɗauka kin ci bulus?, na samu abunda nake so, kuma ba ni kaɗai ba ne nai, ko ba Komai na barwa Sadik ajiya me muni.
Mu huɗu mu kai amfani da ke, kuma ki sani ko kin kai gaba ba abunda aka isa ai min, saboda ke ba 'yar uban kowa bace, face 'yar talakawa mara amfani, ba ki da kuɗin da zaki ja da ni, ai Tasleem ta ga ma min komai"

Farhan ta haɗiyi wata irin muguwar ƙwallar baƙin ciki ta kalli Mubarak tace "ni 'yar talakawa ce, amma ba mara amfani ba, tabbas ka zalunce ni saboda abunda ya haɗo ku da Sadik daban, ni kuma alaƙata da shi daban.
Kayi naka ɓangaren, saura nawa zakaga abunda zan iya yi"

Ta juya ta fice daga ɗakin cikin sassarfa, wani duhu da ƙunci ya mamaye zuciyarta.

Mutum huɗu su kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login