Showing 162001 words to 165000 words out of 259198 words

Chapter 55 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

kurum inje ta koma son sa, ni nayi nayi ta soni Yarinyar nan taƙi, kwata kwata aiki baya tasiri a kanta sam, yi nake amma Kamar bana yi"

Haladu yace "to ai kaine baka mata yadda suke mata, shiyasa taƙi sonka, ka dena mata hargowa da nuna isa, kalli Ranar da suka fito da ɗan gidan Hajiyar nan, kamar ze shige cikin ta, babba da shi amma yayi ƙasa da muryar sa, se Magana yake mata cikin nutsuwa, kai kuma komai naka cikin hargowa kake yi mata, kalli yadda ka tara mu a ƙofar Gidan nan dan Allah, ka gayamata miyagun maganganu a gaban mu, ta yaya zata soka?"

"To nima ɗin ce maka a nai bana mata, wallahi ina lallaɓa Yarinyar nan shegen taurin kai ne da ita da kuma kwaɗayi, su suke ɗawainiya da ita kawai"

Haladu yace "to Allah ya kyauta, kamata yai dai ka gano in da matsalar take ka gayara, ni zanje aiken da malam da yai min"

Sunusi yace "seka dawo"

Farhan ba ta sake sanin in da kanta yake ba, se bayan sallar magariba, ba ƙaramin jin daɗin baccin nan tai ba, dan rabonta da bacci haka har ta manta.

Adda Maryam ta haɗa mata ruwa tai wanka, amma Abinci ya gagara ciwuwa, da ƙyar ta sha tea, tace ta ƙoshi.





Abba ya ƙi gayawa Mother matakin da ze ɗauka akan Sadik, tunda yace se Sadik ya dawo gida be kuma ce mata komai ba.

Ta sameshi a ɗaki yana danna waya, ta zauna kusa da shi ta kalleshi tace "Abba nifa haryanzu baka gayamin wani mataki zaka ɗauka akan Auta ba"

"Ai na gama magana, me kike so ince miki kuma? Gida ze dawo ya haƙura da karatun kawai, da ya lalace gara ya dawo ya zauna, in ya ga dama yayi karatun a nan"

Mother tace "dan Allah kar kayi haka, ka dai ja masa kunne, kuma nima na kirashi, nai masa faɗa dan Allah ka ƙyaleshi"

Abba ya girgiza kai yace "is too late"

"Is not late, kaga yaro ne shirirtar Ƙuruciya ce ke damunsa, amma baze ƙara ba"

"Ya a kai kika san ba ze ƙara ba?"

Mother ta gyara zama tace "Munyi waya da shi ai, yace baze sake ba"

Abba ya sake girgiza kai yace "na gama yanke hukunci kuma ba zan canza ba"

"Dan Allah kar kayi haka,kas...

"Kinga, ya isa haka na gama magana"

Abba ya fututtuke yaƙi saurarar Mother, haka ta tashi jiki ba ƙwari ta bar ɗakin ta koma sashinta.

Dr. ta kira a waya, ta sanar masa abunda Sadik yai, da hukuncin da Abba ya yanke.

Usman yace "Wallahi Mother Sadik is  so much spoiled, mu meyasa ba muyi haka ba da mukai karatun a waje, se shi?"

A fusace Mother tace "ba kiranka nai kai min faɗa ba, na ga mahaifinka yana shawara da kai, shiyasa na kiraka ka taushe shi kaima, dan ni yaƙi saurarata sam"

Usman yace "to Allah yasa ni ɗin ya saurare ni, dan abunda kika kasa yi ba lallai mu mu iya ba".

"Ai kwanan nan duk ya canza wallahi, ka dai tuntuɓe shin, ko Allah ze sa ya yadda"

Usman yace "shikenan, zan shigo gidan zuwa gobe insha Allah"

Mother tace "Allah ya kaimu, ka gaida Jiddan"

Ya amsa da "za taji insha Allah".



Lokacin Auren Farhan na ta ƙaratowa, ba tare da samun wata fahimtar juna tsakanin ta da Sunusi ba, kullum cikin faɗa suke da tashin hankali, Gashi ta kasa fidda ran Sadik ze dawo rayuwarta, wasu lokutan ta kan tuna da Doctor Abbas, dan ba zata taɓa manta Alkhairinsa ba, dan set ɗin tukwane non stick ya sai mata, da gas cooker, da kuɗi har dubu hamsin, haka Hajiya ta kai gidansu Farhan tace inji Abbas.

Idan Farhan ta ga kayan da ake siya da sunan Aurenta, se taji ina ma gidan Sadik za'a kaita da kayan nan ba gidan Sunusi ba.

Tayi duk yadda za tai ta cire Sadik daga ranta, amma abu ya gagara, gashi kamar wadda akaiwa Asirin farinjini, duk da ƙanƙantar shekarunta, kusan kullum idan ta fita se tai saurayi, suyi ta binta, abunda yake ƙara caza mata kai kenan, shikuma Sunusi da ya ganta da wani se ya hau bala'i yana surfa mata jaraba.

Gashi ya ɓata mata suna a unguwa, tun lokacin da ya tara mata Mutane a ƙofar Gidan su Abbas.

Abubuwa suka sake damalmalewa Farhan, ta rasa in da zata saka ranta taji sanyi.




Lilly kuwa abu kamar wasa, suka koma ruwa ita da Nazir, dan tamkar matar da ya sa sadaki ya auro haka ya maida ita, duk lokacin da ya buƙace ta, za taje ba musu ba komai.

Mussaman yake mata allurar family planing, saboda gudun sake samun matsala, makarantar kanta wasu lokutan ba ta zuwa, se tai tafiyar ta gidan sa, fafur taƙi yadda direba ya cigaba da kaita yana ɗakkota, a cewar ta ai yanzu tai girman da ta wuce wannan level ɗin.


Abba yai banza da batun Sadik, be kuma yin Maganar ba, har Mother tai zaton ya haƙura da batun ne, ta cigaba da sabgogin ta.

Rana tsaka yace mata zeje London. Ta tashi hankalinta "dan Allah idan akan maganar yaron nan zakaje kayi haƙuri, na gaya naka baze sake ba"

Abba yace "Ai ba Sadik kawai na ajiye a London ba, ina da 'yar da zanje in ga halin da take ciki, dan haka ni yanzu babu ruwana da lamarin ɗanki, 'ya ta zanje in gano"

Maganar Abba taiwa Mother ciwo nesa ba kusa ba, ta so ta mayar masa, amma ta ƙyaleshi, dan yanzu se su kuma haurawa da shi, dan haka ta ƙyaleshi.


Nana farinciki take yau kamar me, tana murna yau za'ai musu hutun session, watanninta huɗu kenan tunda aka kawota ba ta sake ganin wani yazo mata daga Nigeria ba, kuma ba ta fita daga makarantar ba.

Ta sa ran ganin Abba, Amma ga mamakinta se taga Steve, duk da ba haka ta so ba, amma hakan be hanata nuna farinciki da ganin sa ba.

Shine ya ɗauke ta, ya tafi da ita gidansa in da suka taɓa zuwa farkon zuwan su garin.

Matarsa da yaransa na da kirki matuƙa, suka karɓeta cikin mutunci.

Tana son ta tambayi ina Abba, amma se taga zasuga kamar abunda suke mata suna ta tarairayarta, kamar ba tai appreciating ba, dan haka tai shiru.

Se yamma liƙis, ba tsammani taji muryar Abba, kamar an mata kyakyawan Albishir haka ta tashi cikin murna da fara'a.

Abba yaga Nana tai fresh da ita kamar ba ita ba, yai murna ƙwarai da gaske da ganin Nana.

Yaci Abinci yai salla, ta dinga ba shi labarin Makaranta da kuma ƙawayen da tayi a makaranta.

Wannan karon a gidan Steve Abba ya kwana shima, da safe taga an fito da Akwatin ta, da kuma Akwatin kayanta na farko da ta zo da su, duk an saka a Mota.

Tai ta murna tana tunanin Nigeria za su dawo, sedai ta ga sunyi doguwar tafiya, sannan suka shiga wata unguwa, me ƙarancin gidaje, kusan gidajen da suke unguwar iya wani ɗan rukuni ne kawai.

Wani matsakaicin gida akai parking, taga su Abba sun buɗe motar sun fita, Abba ya leƙa yace "Nana fito"

Ba musu ta fito, taga Steve ya sauke Akwati nan ta daga Motar.
Kai tsaye Abba ya nufi Gidan, yasa hannu ya buɗe ƙofar Gidan, suka bi bayan Abba.

A falo Nana tai tozali da Sadik, ba ƙarya yayi kyau fatarsa tai fresh, sumarsa se ƙyalli take ya ƙara wani kyau na musamman.

Seda gabanta ya faɗi, dan rabon da ta ganshi tun Ranar da suka bar gidan Steve aka kaita Makaranta.

Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa, suka nemi guri suka zauna, Steve ya fita waje ya basu guri.

Abba ya nemi guri ya zauna, sannan yai wa Nana umarnin ta zauna, ba musu ta nemi guri ta zauna tana rarraba ido, tare da satar kallon Sadik da yake ta haɗe rai.

Abba ya kalli Sadik yace "Wannan shine hukuncin da na yanke a kanka, wallahi da niyyata hatta makarantar, se ka barta ka koma Nigeria, amma 'yan uwanka su kai ta bani haƙuri, da ne nake maka kallon yaro ƙarami, amma tunda abunda ka zaɓawa kan ka kenan, ga matarka na kawo maka, idan ka ga dama ka kwaɗata ka cinye, sedai ba zan cigaba da maimaita maka ba, duk abunda ka ga dama kai mata, daidai nake da kai, dan ba zan sa ido ka lalace a banza ba, ka ɓatamin suna".

Ya maida idonsa kan Nana yace "Nana, Steve ya karɓo miki takardar transfer, in aka koma Makaranta ze kaiki sabuwar makarantar da zaki koma, daga nan gidan zuwa makarantar ba nisa, day ce Makarantar, Steve ze dinga zuwa yana duba ku, duk lokacin da yai miki wani abu, na rashin jin daɗi, ki karɓi wayar Steve ki kirani ki gayamin.
ki kwantar da hankalinki, ki masa biyayya tunda Allah ya ƙaddara mijinki ne, kai kuma in kaga dama, kai mata riƙon da ka ga dama, zaka ga yadda zan da kai, miƙomin wayarka"

Sadik ya ciro wayar ya miƙawa Abba, Abba ya zare layukan wayar, da wayar ya sa a aljihunsa, ya miƙe ya nufi hanyar fita.

Nana tabi Abba da kallo, kamar ta tashi ta bi Abban da gudu, dan ta san kashinta ya bushe tun da aka ce ta zauna  ita da shi a gida ɗaya, ba ta san laifin da yayi Abba yake masa faɗa haka ba, amma da alama laifin da yayi babba ne.
Ba ta ƙara tsurewa ba, se da taga irin ɗan banzan kallon da yake binta da shi, nan da nan ta sake jin jikinta yai sanyi.

Daga Nana har Sadik aka rasa wanda ze raka Abba, saboda kowa da abunda yake saƙawa a zuciyar sa.

Suna jiyo ƙarar motar Steve, Sun tafi.

Nana ta ɗaga kai ta kalli Sadik, suna haɗa ido ya ja wani uban tsaki ya tashi ya fice ya bar gidan gaba ɗaya.

Nana ta zauna tsuruu ita kaɗai a zaune, ba tai zaton za'a mata transfer ba, se yanzu take jin ta shaƙu da su Linda Sosai.



Farhan dai gata nan gata nan, wasu lokutan kamar mara hankali, gaba ɗaya gudun mutane take yanzu sosai da sosai, kullum se dai ta ƙule a ɗaki, tai kuka tai tunani rashin son maganarta ya ƙaru fiye da da, babban abunda yake damunta shine rashin bacci da matsanancin feelings da take fama da shi, wanda Duk silar Sadik ne ta shiga wannan halin da take ciki.

Ta dawo daga makarantar dare, ta biya ta gurin me chemist ɗin nan da ya zo ya dubata.

Suka gaisa Sannan tace masa "dan Allah maganin bacci nake so ka bani, da rage damuwa"

Ya kalleta yace "wane irin maganin bacci kuma da rage damuwa?"

Tace "wallahi nafi wata uku bana bacci duka dare, se ciwon kai bana iya bacci"

"To ai kinga jininki ne yake hawa yana sauka, haƙuri zaki ki cire duk wata damuwa da take ranki"

Farhan tace "dan Allah ka temaka min, ko baccin ne in samu in dinga yi, kaga allurar da kai min kwanaki naji daɗin ta, ka temaka min kar kaina ya tarwatse"

Ya ɗanyi shiru Sannan yace "shikenan ba damuwa, bari in baki amma kaɗan kije ki gwada, duk in da kika sha na kwana uku zuwa huɗu, se ki dena sha"

Farhan tace "to, nawa ne?"

Yace "karki damu, ki bar kuɗin kawai, kije ki jarraba Allah yasa a dace"

Ta karɓa tai masa godiya ta tafi gida.


Nana gajiya tai da zama, dan babu alamar Sadik ze dawo Gidan nan, ta tashi ta shiga lelleƙa ɗakunan, haka kurum gidan yake mata kama da wani gida, a wani film na horo da ta taɓa kalla a gidan Dr. A tsorace ta samu banɗaki tai alwala tai salla ta dawo falon ta zauna, se zazzare ido take kamar korarriya.

Wata irin yunwa se sakatar ta take, ta rasa in da zata sa kanta, wasa wasa har duhun magariba ya fara yi, babu Sadik babu alamarsa, hankalin Nana ya tashi, tsoro take ji sosai ta koma wajen ƙofa ta zauna, tana ɗaɗɗaga kai tana kallon gidan.

Ba zato ba tsammani taji an buɗe ƙofa, a gigice ta tashi zata zura da gud, amma taga Sadik ne, kallo ɗaya yai mata ya tsaki ya wuce ya nufi wani ɗaki, yasa mukulli ya buɗe ɗakin ya shiga.

Miƙewa Nana tayi ta koma kan kujera ta zauna, tana jiran Sadik ya nuna mata in da zata ajiye Akwatunan ta.

Sedai ko motsinsa ba ta kuma ji ba, tashi tai ta nufi in da ya shiga, ta tura ƙofar da sallama.

Yana zaune a gefen gado, hannunsa ɗauke da sabuwar waya yana dudduba ta, ya ɗaga kai ya kalleta yace "uban me kika biyo ni ki min?"

Ta cuna baki tace "ni yunwa nake ji, kuma baka nunan in da zan ajiye kayana ba"

"Meya hana ki tambayi wanda ya kawo ki abun da zaki ci?" Mamaki ya kama Nana, meyasa Sadik sam ba shi da ta ido ba shi kunya?

"In da zaki kwana kuma, in kin ga dama ki kwana a waje, matsalar ki ce, ki ɓace min daga gani na kan in zo in saɓa miki" mamaki ya hana Nana motsawa daga in da take, Sadik ya taso ya turata waje, ya rufe ƙofar ɗakinsa.

Jiki a sanyaye, ta koma kan kujera ta kwanta, zuciyarta na wani irin tafasa, nan da nan ta fara kuka, dama ba ai mata wannan transfer ɗin ba, an barta a boarding ɗin ta, dan babu alamar imani a tare da Sadik sam.

Garin akwai sanyi sosai, ta buɗe kayanta ta ɗakko bargo ta lulluɓa, ta dinga kuka a cikin bargon, ta san kashinta ya bushe a wannan zama da za suyi.


Da Abba ya koma gida ba yadda Mother ba tai ba, akan se taji matakin da Abba ya ɗauka akan Sadik, amma fafur yaƙi gaya mata, ta kira wayar Sadik amma wayar ba ta shiga.

"Dan Allah ka gayamin matakin da ka ɗauka akan Yaron nan"

Abba yace "Ai na gaya miki ni ba gurinsa naje ba, gurin 'yata naje"

"Amma na kira layinsa baya shiga fa"

Abba yace "wannan kuma ban san dalili ba"

Cikin damuwa Mother tace "Yanzu kaje har ƙasar ka dawo, ba ka je ka ganshi ba?"

Abba yace "to menene a ciki, tunda ya nuna ban isa da shi ba"

Kan Mother ta kuma magana, yai tafiyarsa ya barta a gurin.

In da a kai sa'a, in da su Nana suke akwai wani ɗan ƙaramin masallaci, kasancewar akwai musulmi a unguwar.

Kan Sadik ya tashi Nana ta tashi, dan sanyi ya dameta sosai da sosai, tai alwala ta tada salla, Sadik ya wuce ta ya fice ya tafi masallaci.

Bacci ne ya kuma kwashe Nana, motsin Sadik ne ya tashe ta, ta buɗe ido taga ya shirya ya ɗau jaka, alamar fita zeyi.
Nana ta kwaɓe fuska tace "wai yanzu ma fita za kai? Ni wallahi tsoro nake ji"

Wani Mugun kallo yai mata, yace "uwar tsoro kike ji ba tsoro ba"

"Dan Allah to ka bani abunda zan ci, kar yunwa tai min illa"

Ko saurarar Nana be ba, ya fice yace "zaki gane baki da wayo, izayar da kakanninki su kai min akan ki zan rama".

Haka Nana ta kuma wuni da yunwa, banda kuka ba abun da ta ke yi, se wajen ƙarfe tara na dare sannan Sadik ya koma gida, ya tarar da ita ta ci kuka, idanunta sunyi wuri wuri, ya wuce ɗaki abunsa, wajen mintuna goma da wucewar sa Nana ta tashi ta bi shi ɗakin.

Yana zaune yana cin Abinci, wanda Nana sam ba ta san me yake ci ɗin ba, kawai se ganinta yai a gabansa, ta sa hannu ta fara cin Abunda yake cin.

Ba shiri ta furzar da abunda ta sa a bakin nata saboda azabar yaji, kawai ta kuma fashewa da kuka.

Sadik ya bita da ido, yace "ubanwa yace ki zo min ɗaki?"

"Yunwa nake ji wallahi, gaba ɗaya cikina ciwo yake"

"To ni na ajiye ki da zan nemo abun baki?"

"Dan Allah ka temaka min, kar in mutu"

Kawai Sadik ya tuna yadda ta dinga sintirin ba shi Abinci a ɓoye, idan aka bashi abunda ba ya so a ƙauye.

Tashi yai ya barta a ɗakin, mintuna kaɗan se ga shi ya dawo, ya ajiye mata madara da fruit a gabanta.

Ta kalleshi tace "nifa Abinci nake son naci, yunwa nake ji, ta yaya wannan zam ci in ƙoshi?"

Tana faɗar haka ya durƙusa ya ɗau plate ɗin ya koma gefe, ya fara yankawa ya na ci.

Haushi ya kama Nana, hankalinsa kwance yake cin abunsa, wato ta mutu da yunwa.

Tashi tai ta ɗauke plate ɗin daga gaban Sadik, tai waje tana kuka, dan ba yadda za'ai ta ƙoshi yadda ta kwana biyu ba ta ci ba.


Farhan taji daɗin maganin nan da ta karɓa a chemist, tayi bacci Sosai da sosai, wanda rabon da Farhan tayi shi tun suna tare da Sadik, taji ta samu sassaucin baƙin cikin da take ciki.

Kamar yadda me Chemist ya gaya mata, kwana uku ta ajiye ta dena sha, amma fa damuwa ta kuma dawowa, mussaman yanzu da saura wata ɗaya ya rage Aurenta da Sunusi!!!



Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.








Haka Farhan ta cigaba da gudanar da rayuwarta, kamar mara cikakkiyar lafiya.

Babu wanda ta gayawa batun za tai Aure a cikin 'yan makarantar su, dama ba harkar mutane take shiga ba, dan ba ta da wasu ƙawaye, rayuwarta kawai take yi.

Tana zaune a ajinsu, tai zurfi a cikin tunani, taji an dafa ta, a hankali ta waiga taga waye ya dafata.
Tai tozali da Lilly, Lilly ta zauna a kusa da ita tace "Farhan, wai dan Allah meyake damunki haka?"

Fahan tace "me kika gani?"

"Kin ga yadda ki kai wata irin rama kuwa? Kullum cikin tunani kike, ga malamai suna ta complain akan kin dena karatu yanzu haba Farhan"

Shiru Farhan tai ta sunkuyar da kai ƙasa.

"Farhan" Lilly ta kira sunanta.

Ta ɗago ta kalli Lilly.

"Ko dai dan Sadik ba ya makarantar nan ne yasa duk kika zama wani iri?"

Jurewa Farhan take ƙoƙarin yi, ta girgizawa Lilly kai, amma cikin rashin sa'a ƙwalla ta taru a idon Farhan, dan tun bayan Doctor Abbas babu wanda ya kuma taɓo mata abun da yake damunta.

"Yasalam, yi haƙuri idan na faɗi wani abu da be miki daɗi ba, amma ki yi haƙuri, naji ance babu wanda ya san ze yi tafiyar nan, ciki kuwa har da ke, sam be kyauta ba, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login