Showing 144001 words to 147000 words out of 259198 words

Chapter 49 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13308

maganar Abba ya faɗe ta.

Da sauri ya koma cikin gida, ya iske Mother a kitchen cikin ɓacin rai.

"Lafiya kuwa?" Mother tai Maganar tana ƙare masa kallo.

"Mother, wai Abba yace kar a kusakura a bari na fita, wai idan nace sena fita a harbeni, abun har ya kai haka?"

Mother tace "Ai babu uwar da ta tsuguna ta haifi baturen da ya sarrafa bindigar harbinka, duk wanda ya harbeka sena sa an ɓatarmin da shi, rabu da shi duk dan ya muzguna mana ne ni da kai, kuma ba gudu ba ja da baya sena kashe Auren nan murus, ƙyaleshi kar ka sake attempting zaka fita ma, ka nuna masa baka damu da hakan ba"

Sadik ya sauke ajiyar zuciya, cike da takaici ya juya ya bar Kitchen ɗin.

Abba da kansa ya kawowa Nana magani, ya bata ta sha, sannan ya fita.

Gaba ɗaya ya tattara Mother da Sadik yai watsi da su, ya dena shiga sabgar kowa a cikin su, ya cigaba da harkokin sa.

A masallaci ya sanar da ɗaurin Auren Sadik, kuma ya shirya ƙwarya ƙwaryar walima shi da abokansa, suka taya shi murnar Auren Sadik.

Yayin da a ɓangaren Mother abun kunya ne a ce anyi auren ɗanta a haka, Auren mara galihu.

Sunusi kuwa tunda ya bar Asibitin ya dinga mita yana masifa akan abunda Abbas yayi masa, tare da cin alwashin akan Farhan ze rama abunda a kai masa.

Tun da Sadik ya dawo, Khairat take son yi masa Magana, amma babu fuska dan ko falo baya fitowa a ɗaki yake wuni, ko BQ baya zuwa saboda yadda Faruk yake sa shi gaba yana masa Nasiha.
Ɓangaren Nana ma ko da wasa bata fitowa ko falo, saboda tasan aranagamarta da Mother abun baze mata kyau ba, kullum tana ɗaki Talatu ke kawo mata Abinci, kasancewar akwai banɗaki a ɗakin, a ciki take wanka ta wanke kayan da ta cire, ta shanya a ciki.

Talatu na ta son dukan cikin Nana, dan ta fuskanci abunda yake faruwa, amma Nana taƙi Magana.

Wata irin kewar gida take sosai da sosai, tana kewar Inna da makarantar ta da ƙawayenta.

Kullum se Abba ya zo ya dubata, sun gaisa da kansa yake tambayar ta idan tana buƙatar wani abu, se tace masa ba ta buƙatar komai.

Ƙarfe takwas na dare Dr. Ya zo gidan, ɓangaren Mother ya nufa kai tsaye, tana ganinsa tace "kai kaɗai, ina Jiddan?"

Yace "Ba ta jin daɗi ne, shiyasa na taho kawai"

Mother tace "too, ko ciki ne?"

Dr. Ya ɗan ɗage kafaɗa yace "i dont know"

"Kamar ya You don't know? Baku je Asibiti an dubata bane?"

"Bata son Zuwa Asibiti, wai tana tsoron Allura, she prepare to take drugs, ni ba zan takurata ba"

"But atleast, yakamata kuje Asibiti a tabattar da me ke damunta, zuwa yanzu ai ba abun mamaki bane ta samu ciki, ai kun huta dan nasan wataƙila wani abun ku kayi, shiyasa ba ta haihu ba"

Murmushi kawai Dr. Yai, bece Komai ba.

Mother ta sa aka kawo masa fruit, dan be fiye cin Abincin dare ba.

Yana cikin ci Mother ta kalleshi tace "hmmm ka san abinda Babanku kuwa yayi?"

Dr. Cikin ko in kula Yace "me yayi?"

"Sadik ya dawo ai shekaranjiya"

Yace "Wow, that's good se hankalinki ya kwanta ai"

"Hmmm, ka san wai Anyiwa Sadik Aure?"

"Aure Kamar yaya?"

"Hmm, ai ni nama rasa ta in da zan fara maka bayani, baƙin ciki ya hanani in kiraka in sanar da kai"

Dr. Yai murmushi yace "that's good"

"Kamar ya that's good?"

"Ahh abunda yake so ne ai ya samu?"

"Kai Maganar Sadik wata maganar kirki ce? Me Sadik ya sani banda salon lalata shi da za'ai masa wani Aure? Me Sadik ya sani guda nawa yake? Ko degree be haɗa ba yaron da Just recently ya kammala secondary, shima dan an masa jumping, wai shi a kaiwa Aure, kuma a rasa wadda za'a aura masa se wannan 'yar ƙauyen jikar ta su"

Usman yai murmushi yace "Children of now adays are beyond your expectations, karki zafafa ki zo ya baki Kunya"

"Ai bazan ɗau wannan abun da a kaimin ba, dole in kashe Auren nan"

Usman a ransa Yace 'haifar Sadik ki kai, amma baki san waye ba, baze iya haƙurin da nai ba, ya fito gatse gatse ya gayamiki Aure yake so, amma kina cewa be san komai ba, be san komai ba ya akai yasan yana son Aure?"

Wani murmushi ya sake yi a fili yace "bari inje mu gaisa da Abban"

Mother ta ɗan taɓe baki tace "seka dawo"

Ya miƙe ya bar part ɗin Mother, yana mamakin yadda ta rintse idonta taƙi kallon gaskiya.

A falon sashin Abba ya tarar da shi yana kallon CNN.

Dr. Yace "barka da hutawa Abba, ai ban san ka dawo ba"

Abba yace "na shigo tun ɗazu ai, naga motarka na san kana gurin mahaifiyarka, kaima tana maka famfo akan yadda zaku haɗu ku juyan baya ko?"

"Haba dai Abba wane ni? Ba haka bane ba"

"Amma dai ta gaya maka abunda ke faruwa, ina ga tun a shakranjiya ta kiraka ta sanar da kai abun da ya faru?"

Usman ya gyara zama yace "No, ban san meke faruwa ba gaskiya se yanzu da na zo take gaya min"

Abba ya numfasa yace "Usman, ni kaina banji daɗin matakin da Hakimi ya ɗauka akan Sadik ba, Sadik yayi ƙanƙanta da Riƙe Aure baze iya ba, amma ba zan iya bijirewa umarnin mahaifina ba, saboda dani da ku duk mallakinsa ne, amma abun mamaki se ga mahaifiyarku tana nema ta ɗagan hankali ta sa in bijirewa umarnin su dan in faranta mata".

"A'a ba haka bane Abba, ka san tana kallon Sadik ɗin ne yaro har yanzu, kuma ya nuna mata baya son Auren, kasan yadda take son sa"

Yace "duk da haka dr. Ba yau mahaifiyarku ta fara nuna min iyakata ba akan dangina na ƙauye, tana nuna min abubuwa da dama amma ina kawar mata da kai ta kasa ganewa, yanzu kalli yarinyar nan matar Sadik ɗin, tare muka zo gidan nan da ita, tare zasu tafi London, amma Yarinyar nan ta wuni ta wayi gari ba a bata Abinci ba, ta kwana da zazzaɓi ba wanda yabi ta kanta seni, ai yau ku 'yar tsintuwa na kawo nace Hauwa ta riƙe min,be kamata tai min haka ba"

"Hakane Abba, amma kayi haƙuri dan Allah"

"Haƙuri ai sedai in ɗora akan na baya, sedai zan nuna mata ku da ita a ƙarƙashin ikona kuke, idan ita ban isa da ita ba, ku na isa da ku ai, dama dalilin da ya sa na kiraka shine, in ban takura maka ba, sonake ka tafi da Nana gidanka, zuwa lokacin da zasu tafi, dan tata visa haryanzu bata fito ba, amma in kana ganin ba matsala ban takura muku ba"

"Haba Abba, babu wata matsala ko takura, zan tafi da ita Insha Allah, ko cewa kai in riƙeta a gidana zan riƙe ta"

Abba yai murmushi yace "Allah sarki, haihuwa me rana, nasan da kai akaiwa Auren nan ko Faruk ba wanda ze ɗagan hankali, ta ɓangaren ka ba zan gane kai murna ko akasin haka ba, Faruku kuwa baze taɓa nunamin ɓacin ransa ba, se Sadik amma shima zanyi maganinsa, zuwa da safe in Allah ya kaimu se kazo ka ɗauketa koma in kawo ta da kaina"

"A'a Abba, a taso ta mu tafi yanzu kawai"

"Kana ganin ba matsala?"

"Abba babu wata matsala sam"

Abba yace "to shikenan, Allah yayi albarka ya a baka masu jin ƙan ka" ya amsa da Ameen Abba.

Abba da kansa yaje ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da Nana take, ta taso ta buɗe yace "maza ɗakko akwatinki"

Seda ta ɗan tsure, dan ba ta san dalilin hakan ba.

Ta ɗakko Akwatin ta, ta fito falo karon farko tun randa suka zo bata fito ba.

A falo taga Usman, ta gaishe shi ya amsa tare da cigaba da abunda yake.

Jin hayaniya a falo yasa Mother ta fito, ta tarar da Nana da Akwatinta, ga Dr.

Yace "Mother seda safe, dare ya fara yu"

Mother za tai magana amma Abba na tsaye a gun, ya kasa ya tsare ya raka su har bakin mota, se da suka tafi sannan ya dawo, da ya dawo ɗin ma be kula Mother ba, ya wuce sashinsa.

Nan Mother ta tsaya tana tunani, meyasa Dr. Ya tafi da Yarinyar nan.

Ɗakin Sadik ta nufa amma taga ya kashe fitila, dan haka tai tunanin ko bacci yake, Sadik kuwa idonsa biyu kallo yake a system ɗin sa, wanda ya haddasa masa damuwa, ya dafe kansa yana ƙoƙarin yin tunanin wani abu me mahimmanci a tare da shi amma ya kasa, gefe guda kuma ga wata irin fitina da take damunsa, a hankali ya fesar da iskar bakinsa ya kashingiɗa ya lumshe idonsa.

Tunda suka fara tafiya da Nana, ba wanda ya cewa wani komai daga dr. Har Nana, dama dr. Ba me magana bane dama Faruk ne.

Suna tafiya Mother ta kira dr. A waya, ba tunanin komai ya ɗaga ya sata a hansfree.

"Dan ubanka me kuke shiryawa kai da ubanka, ina zaka kai Yarinyar nan?"

"Gidana zata koma" ya bata amsa kai tsaye.

"Akan wani dalilin? Meyasa zata koma gidan naka?"

"Eh Abba ne yace ta koma can, shiyasa na zo na tafi da ita"

"Amma kuma shine baka gayamin ba? Za kai gaban kanka"

Usman yace "to Mother ai banga wani abu a ciki ba"

"Ai baka da hankali dama, kai da Faruk wasu lokutan baku san abunda yakamata ba dama, ka kyauta"

Usman kawai ya Ajiye wayar tare da girgiza kai.

Suka ƙarasa gidan dr., Ya buɗe bayan motar ya ɗakko Akwatin Nana yai cikin gida, ba ta da zaɓin da ya wuce tabi bayansa.

Cikin sauri tabi bayan nasa, sedai da yake cikin sauri yake tafiyar ya rigata shiga falon.

Tana zuwa ta tarar da shi a tsugune a gaban 3seater, Jidda na kwance da wasu irin fitinannun sleeping wears, yana magana ƙasa ƙasa "ko dai zamu tafi Asibiti, har yanzu jikin ki da zafi fa"

"A'a Baby na sha magani fa"

Kallo ɗaya Nana taiwa Jidda taji wata kunya ta kamata, yadda take zaune ƙanin tsirara ga dr. Yana kallonta (lolz🤭😂)

Yace "Munyi baƙuwa fa"

"Baƙuwa kuma?" Tai maganar tana ƙoƙarin tashi zaune, idonta ta sauke akan Nana, take Jidda tai murmushi tace "Ƙawata, yaushe suka zo?"

"Eh tun shekaranjiya tana gida, yau Abba yace inje in ɗakko ta"

"Kai amma naji daɗi, Nana ya kike ya Inna?"

Nana tace "lafiya ƙalau, tana sunkuyar da kai"

Usman yace "ga ɗakin dake kallon dining nan, ki shiga ki ajiye Akwatin naki, kije Kitchen ki ɗebi Abinci ki ci"

Nana ba tace komai ba ta ja Akwatinta, ta shiga ɗakin da akai mata umarni, tana jinjina fitsara irin ta Jidda.

Usman ya maida kallonsa kan Jidda yace "muje daga ciki, ki wanka da ruwan ɗumi seki kwanta zaki ji daɗin jikinki"

Ta kwanta a jikin dr. Tace "Nikam naji daɗin zuwan Nana, amma naji kunya baka taɓa kaini naje na gaida Inna ba, ga Hakimi yai rashin lafiya shima banje ba, gobe in Allah ya kaimu ka kaini gida mu gaisa da Innan"

"Ke in da ita aka zo zata bari a ɗakkota a taho da ita nan ne? Matar Sadik ce fa" yai maganar yana wata shu'umar dariya.

Jidda tace "kace 'yar gida za'ai idan ya kammala Makaranta, to Allah ya nuna mana kuma sunyi matching Sosai"

"Ai an riga anyi ma"

"Akayi me?" Tai tambayar cikin mamaki.

"Akai Auren, jiya ma Abba yai walima da abokansa"

"Dan Allah Baby be serious, wane irin Aure kuma ana zaune ƙalau"

Usman yace "na saba yi miki ƙarya ne? Am serious Hakimi ya masa Aure, tare ma zasu tafi London, maganinsa kenan dama ba shi mara kunya ba, a gaban uban kowa ma faɗa yake Aure yake so, yanzu kuma an masa wai baya so"

Kawai Jidda ta kwashe da dariya, Usman ma ya tayata.

Nana fitowa tai dan ta nemi ruwan da zata sha, dan tana jin ƙishirwa.

Ta tarar da su a manne da juna suna dariya, Nana a ranta tace "Wannan wace irin watsewa ce?"

Tace "zan sha ruwa"

Dr. Ne ya ɗago ya kalleta yace ta shiga Kitchen ta duba fridge.

Jidda kuwa na kallon Nana se dariya ta kuma kamata, tace "but seriously dr., She's still young an katse mata hanzari, bana tunanin zata iya ɗaukar ɗawainiyar Aure, yarinya ce Sosai daga ita har Sadik ɗin sunyi ƙanƙanta sosai"

"Su sukace miki sunyi ƙanƙanta?"

Jidda ta toshe baki tana cigaba da dariya, Usman ya miƙe ya ɗagata suka nufi ɗaki suna cigaba da dariya.

Nana kam daskarewa tai a gurin, wannan wace irin taɓara ce da watsewa haka? Kamar ba Musulmai ba.

Dama haka Usman ɗin nan yake tana kallonsa wani shiru shiru da shi, wannan ai ba yi bane.

Jiki a sanyaye cike da kunya, Nana ta koma in da aka bata ta zauna, tana mamakin abunda su Jidda su kai.

Kwana biyu 'yan ajinsu Farhan ba sa ganinta, Lilly ce kawai ta damu da tambayar wai Ina Farhan ta shiga kwana biyu ba ta zuwa.

Rashin samun amsar ta ne yasa ta tafi Ofishin Sir Nazir, cike da ɗokin sanar da shi mahaifinta ya amince ya fito.

Ta tarar da shi da su Taslim a Office ɗin nasa yana koya musu karatu, kasancewar yanzu sune zasui jarrabawar ƙarshe.

Yana ganin Lilly, ya sallame su yace sa cigaba an jima, bayan sun fita ta maida idonta kansa tace "me suke a gurinka?"

'karatu muke, baki gani ba gimbiyata?"

Ta ɗan tura baki, sannan tace "Albishirinka"

"Goro fari tas"

Lilly tace "Daddy yace ka zo ya ganka"

Cikin Sir Nazir ne ya bada wata irin ƙara ƙuuuu, wani gumi ya shiga tsatsafowa daga goshin sa.

Tace "ya naga kayi wani iri? Meyafaru"

"Hakanan naji ina fargaba Lilly"

"Fargaba kamar yaya?"

Yace "fuskantar babban mutum kamar mahaifinki ba abune me sauƙi ga talaka kamata ba"

"Kaga kar ka damu, ni dai karka watsan ƙasa a ido na samu ya amince, kar yace ƙarya nake masa ma"

Nazir ya jinjina kai yace "shikenan, zuwa yaushe kike ganin yakamata in je?"

"Ko a Weekends ɗin nan ne, next week ze koma aiki fa"

"Shikenan Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Allah yasa ya Amince ya bani ke"

"Ameen ze ma baka"

Nan suka zauna suka cigaba da hira ita da shi, sedai bayan fitarta yai shiru wani tunani ya ziyarce shi, yanzu Allah ne kaɗai ya san bayan shi bata mu'amala da wani ko tana yi? Anya ya dace ya zaɓi yarinyar nan a matsayin matar Aure, kuma uwar 'ya'yansa? Idan kuma da Auren nasa ta cigaba da bibiyar wasu mazan fa? Dan ku san ita ta fara nuna masa alamomin buƙatar ta a gare shi.
Nan fa ya shiga tunane tunane daban daban, yana ƙoƙarin tsayar da mafita guda ɗaya, amma ya rasa meyakamata ya zaɓa a matsayin mafitar, daga ƙarshe dai ya tsaya akan zashi yaga mahaifin nata, ya gani in abunda ze yuwu ne, yace musu in ta gama Sakandire ze Aureta, kafin lokacin ya bar Kano ba tare da sanin kowa ba, dan ya fara kokwanto akan Auren Lilly.


Da safe ma a gurin karyawa, Nana duk a ɗarare take, se soyayyarsu kawai suke a gaban Nana hankalinsu a kwance, dan dr. Ne ma ya ke bawa Jidda Abinci a baki, har aka gama karyawar, yayin da Nana take ta sunkuyar da kai da ganin rashin dacewar abunda suke.
Seda dr. Ze fita Jidda ta tafi rakashi, sanna Nana ta samu damar cin Abincin nata Sosai, tana jin mace kamar Jidda goɗai goɗai take narkewa tana zubawa dr. Shagwaɓa abun ko tsari babu a gurin Nana.

Bayan ya fita Jidda ta wuce ta shiga wanka, Nana ta tattara kwanukan da aka karya, ta shiga Kitchen ta wanke su tsaf, ta gyara Kitchen ɗin ta share ko ina, ita ma taje tai wanka ta canza kaya, ta ɗora hijjabi akan kayan, sannan ta fito falon, da niyyar ta zo ta kalli cartoon, amma ta tarar da Jidda tana kallon wani shiri.

Murmushi Jidda tai tace "Amaryarmu"

Sunkuyar da kai Nana tai, tare da ɗan tura baki ta nemi guri ta zauna.

"To ki cire hijjabin mana, ba kya jin zafi ne?"

Nana tace "bana jin zafi, ni ko a gida da shi nake yawo"

Jidda ta jinjina kai sannan tace "Amaryar Sadik, dr. Yace min next week zaku tafi ai"

Nana tace "hmmm, ai kafin nan ma ya sakeni, na koma ƙauyenmu shi kuma ya tafi"

"Wane irin saki kuma ana zaune ƙalau?"

Cike da Yarinta Nana tace "Ba fa sona yake ba, kuma nima bana son shi"

Jidda tace "Subhanallah, haba Nana me Sadik ɗin yai da ba kya so?"

"Wannan ɗan yaron, kawai se ince mijina ne, nan gaba  fa sena kamo shi a tsawo, dan nima doguwa ce, gashi masifaffafe ga takurar tsiya, ni bana son shi"

Wata irin dariya ce ta zowa Jidda, Lallai Nana Yarinya ce sosai da sosai.

Tace "Haba Nana, saki ai ba abun so bane, babu macen da za ta so tai Aure a saketa, Sadik yana da sauƙin kai sosai da sosai zaku zauna lafiya"

"Lallai Anty baki san halin Yaron nan ba, a ƙauye daga ni se zani har ɗakin kakata ya biyo ni ya kwasheni da maruka, se a nan in da ba Kowane ze ƙyaleni?" Nana tai Maganar jiki a sanyaye.

Jidda tace "Nana, karki kuma cewa Sadik yaro, koma menene yanzu mijinki ne, akwai dalilin da ya sa aka haɗa Aurenku, kiyi haƙuri kinji ki dena masa tsiwa kina da kirki kema zaku zauna lafiya"

Nana tai shiru tana share hawaye, ita ba ta taɓa ganin wani abun kirki da Sadik ya taɓa aikatawa ba.

Jidda ta so ta ɗan yiwa Nana lectures akan Aure da yadda zata tafiyar da Sadik, amma ita kanta kunya take ji, ba ta san da wane yaren za tai mata amfani ba yadda zata gane, dan akwai zunzurutun yarinta akan Nanan, dan ma kuma Nana a hakan 'yar gayu ce ba ta fiye nuna ƙauyanci ba.

Ɗan zaman da su kai da Jidda, Jidda ta lura Nana akwai tsafta sosai da sosai, nan Jidda ta bata turaruka da kayan kwalliya, duk da iya kwalliyar Nana kwalli ne se man leɓe hoda ma bata dameta ba, saboda ba baƙace sosai ba tana da haske.

Zaman Nana a gidan dr. Ya sa ta ma manta da wani batun Aure da a kai mata, sedai kewar gida da ke matuƙar damunta, gefe guda kuma taɓarar Jidda da mijinta, wasu lokutan in dai dr. Na nan ko falo ba ta fitowa, saboda idonta baya hanasu abunda Allah ya nufe su da yi, duk shakkar dr. Da take ji, se da taga mutuncinsa ya ragu a idonta saboda watsewar da suke a gabanta, gashi a lokuta kaɗan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login