Showing 150001 words to 153000 words out of 259198 words

Chapter 51 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

kwanta"

Nana ta tashi jiki ba ƙwari ta shiga ɗakin, sedai ita gaba ɗaya ɗakin tsoro yake bata, ba ta tunanin zata iya kwana a ɗakin ita kaɗai.

Sadik yai shiru yana kallon Abba, yana tunanin wane irin zafi Abban ya ɗauka haka?

"Lafiya kake kallona?" Abba ya tambayi Sadik.

"Abba, dan Allah ka dena fushin nan da ni, ba na jin daɗi wallahi, baka taɓa yi min haka ba"

Abba yai murmushi yace "kai harka damu da fushi na Sadik? Ni da ko gaisheni ka dena saboda uwarka ta na ziga ka, Ni Sadik ku ka sa yi min alfarma in bi nawa iyayen sannan kuce kuna son cigaba da Ganin walwala ta, duk abunda kuke shiryawa da ita na sani ƙyale ku kawai nake.
Idan ka wulaƙanta Yarinyar nan ni ka wulaƙanta ka nunawa Duniya ban isa da kai ba, amma ka sani yadda wannan Auren igiyarsa take a hannunka yin wasa da shi, tamkar wasa da igiyar Auren mahaifiyar ka ne da ke hannuna, dan da iyaye na kuka sameni ba zan zaɓe ku a kansu ba!"

Gaban Sadik yai mummuna faɗuwa, be taɓa zaton haka daga Abbansa ba, Lallai Abba da gaske yake, amma ya san Abba faɗa yake ba ze taɓa iya sakin Mother ba, Komai ze biyo baya za suyi settling daga baya, Amma ba ze taɓa zama da Nana a matsayin matarsa ba dole kowa ya kama gabansa.

Nana ido biyu ta kwana, saboda tsananin tsoro da fargaba, gaba ɗaya ɗakin tsoro yake bata, ƙarshe ta fito falon kan kujera ta kwanta, shima bacci se ɓarawo ne ya ɗauke ta.

Da safe suka shirya suka bar Hotel ɗin, mutumin jiya ya kaisu gidansa, matarsa baturiya ce fara sol, se yaransu uku, biyu farare ɗaya baƙi.

A nan su kai breakfast, sam Nana ba ta gane turancin da suke, da ƙyar take picking wasu kalmomin, a nan suka karya, Abincin na su duk gashi nan ta kasa gane kansa, tea ta iya sha se chips, shima ba sabawa tai da cin irin sa ba.

Suna gama karyawa, Abba yace su tashi su tafi, a zaton Nana Hotel za su koma.

Ashe Makaranta za'a kaita, an gama mata Komai, hatta kayan da zata buƙata an tanadar mada su, aji da ɗaki kawai za'a bata, se 'yan kayan da Abba ya sa ta ɗakko a akwati.

Nan Nana ta tubure ta sa kuka, Mutanen da ko yarensu ba ta ji, ta ina zata iya rayuwa da su, Abba yai ta rarrashin ta yana nata Nasiha, aka bata Uniform da ɗan ƙaramin veil ta saka, saɓanin sauran ɗaliban ma da basa saka hijjabi gaba ɗaya jikinsu a buɗe yake, Nana ta gansu duk farare kamar zabiyai saboda fari.

Kuka sosai Nana ta dinga yi, aka wuce aka kaita aji, ajin akwai farare da baƙaƙe dan akwai wanda suka fi Nanan ma baƙi a ajin, dan tana da hasken fata.

Se da Abba ya tabbatar komai yayi normal, sannan ya tafi shi da Steve, wannan Black ɗin. Dama Sadik be bisu ba.


Farhan ta gama shirin Makaranta, ta fito yiwa Abba Sallama, yai mata addu'a ya bata kuɗin Makaranta, tana fitowa tsakar gida Umma ta kaalleta tace "Ina zaki haka?"

"Makaranta zani Umma"

"Ai wannan makarantar ma haƙura zaki da ita, tunda Aure zaki ai ba ta da wani Amfani ma a gareki"

Abba yana daga ɗaki yace "A'a, karatu akwai amfani, duk da Aure za tai, ai na gaya masa zata cigaba da Makaranta, ki ƙyaleta ta tafi"

Umma ji tai kamar ta gaya masa abunda ta kama Farhan da shi, Amma tai shiru ta fasa.

Farhan ta na tafe a hanya ta na kuka, kamar wata mara galihu, rana zafi inuwa ƙuna, zuciyarta a cunkushe haka taje makaranta.

Lilly na ganinta tace "Farhan lafiya kuwa kika dena zuwa makaranta?, Da fa yau zanje har gidan ku in ga ko lafiya?"

Farhan tai murmushin yaƙe tace "bani da lafiya ne"

"Eyya, shiyasa duk kin rame sosai wallahi, Allah ya sawwaƙe sannu"

Ta amsa da Ameen.

Kusan duk Malamin da ya shiga ajin in yaga Farhan se ya tambayi ya akai kwana biyu ba ta zuwa, Lilly tace ba ta da lafiya, sukaita mata sannu, dan kallo ɗaya za kai mata ka tabattar hakan.

Bayan an fita break ne, taji su Lilly suna hira, wai an kama Mubarak Babba, saboda ta'amalli da kayan maye, anje kame aka kama da shi.

Duk da hakan yayiwa Farhan daɗi, ko banza yanzu ba ta da fargaba, amma ita babban abunda ya dameta be wuce son sanin halin da Sadik ke ciki ba.

Ba ta gana yanke shawara ba, ta tashi ta nufi ajin su Sadik, tana jin kamar zata ganshi idan taje.

Sedai ta na zuwa ajin, ta tsaya ta window tana leƙawa, zubawa gurin zamansa ido, in da suke zama yaita damunta yana tsokanar ta, ko ya kwanta ya ɗora ƙafafunsa akan benci yana danna waya.

Wasu irin hawaye ne suka shiga zubowa daga idon ta, tana jin wata wutar ƙaunarsa na sake Ratsa ta.

"Zan wuce" taji an mata Magana.

Da sauri ta waiwayawa, taga Amin ne abokin Sadik.

Ya kalli Farhan yace "Lafiya? Kukan me kike haka?"

Tai saurin share hawayen ta tace "ba kuka nake ba"

"Ba kuka kike ba, wannan hawayen fa?"

Farhan tace "ba kuka nake bax

Yace "shikenan, amma tsayuwar me kike a nan?"

Cikin in da in da tace "da..daa..dama zuwa nayi" se kuma tai shiru.

"Ko akan Sadik kika zo?".

Ko Sannu ba ta haɗata da abikan Sadik, mussaman da ba jituwa suke ba, suna jin haushin ta, amma Da sauri ta ɗaga masa kai alamar eh.

Yace "kaddai kice kema ba ya nemanki?"

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Yace "Subhanallah, ni dai na san munyi waya, one month back, yace min yana ƙauye kuma in da yake ba service, tun daga nan ban sake jinsa a waya ba"

Farhan tace "Ni yafi wata ɗaya ma ban same shi a waya ba"

Amin yace "ki kwantar da hankalinki, insha Allah zan bincika miki, zanje har gidan su inji in da yake, zan zo in gayamiki insha Allah"

Farhan tai murmushi tace "to nagode"

Yace "bakomai jeki aji, ki dena kuka"

Jiki a sanyaye, ta bar ƙofar ajin nasu.


Amin na shiga class ɗin Nas ya fara murmushi yace "kai baba yane? Ko kai zaka maye gurbin Prince ne?"

Amin yace "kai bari Nas, Yarinyar nan tausayi take bani, ba ƙaramin so take wa Sadik ba, wai ashe more than a month, ba suyi ko waya ba shine ta zo tana leƙo ajin nan"

Nas yace "to shine me?, Dama wannan har wata Soyayya ce, ɓata lokaci ne kawai, soyayyar Makaranta ai shirme ce"

Amin yace "ba kowace Soyayya ce shirme ba, har kuka take wallahi, ta bani tausayi sosai"

"To kai meye naka a ciki, ya manta da ita, maybe yayi wata ne, mu da ya sanmu kafin ta, muma ai ba nemanmu yake ba, tun da mukaje gidan su akace baya nan"

"Ai ni ka san munyi waya, yace min yana ƙauye, gurin kakanninsa, amma insha Allah zanje gidansu in ji abunda ake ciki, ko dan Yarinyar nan"

Nas yace "ai se kayi"



Kamar an jefota haka Nazir ya ga Lilly a office ɗin sa, yace "lafiya?"

"Dole ka tambaye ni lafiya mana, haba Nazir ya kake so in yi ne? Ka ƙi zuwa gurin mahaifina so kake yai fushi da ni ne?"

"Lilly ba haka bane, wallahi tsoro nake ji"

"Au tsoro kake ji ko?"

"Wallahi abunda ya hanani zuwa kenan, ban san ya ze krɓe ni ba"

"Nazir in kaga dama, yau da daddare kaje, dan na ce masa yau zaka zo, idan kuma ba haka ba shikenan shi ze zo ya sameka"

A gigice yace "ai ba za'ai haka ba ma, zan zo insha Allah yau ɗin nan ba se gobe ba"

Tai ajiyar zuciya tace "da ka temaki kan ka" ta jiya ta fice.

Dafe kansa yai yace "wannan wane irin bala'i ne? Wace irin masifa na jefa kaina a ciki haka?"

Farhan har ba ta son a tashi daga Makaranta ta koma gida, saboda ba ta san abunda zata tarar a gidan ba, gaba ɗaya ta kuma susucewa ta zama wata iri kamar mara jini a jika.


A daren Nazir ya shirya ya tafi gidansu Lilly, cike da Zullumi da tsoron abunda ze tarar, dan tun a gate aka tare shi, aka kira baban Lilly, yace a kai masa shi guest room ɗin sa.

Yana nan a zaune yana tsuma, yana rarraba ido, Daddyn Farhan ya shigo ɗakin, seda kayan cikin sir Nazir  suka juya.
Ganin baban Farhan, babban mutum me cike da siffar ƙarfi da kwarjini, dan da hannu ɗaya ze iya sama da sir Nazir.

Ya nemi guri ya zauna ya kalli Nazir, sir Nazir cikin rawar jiki yace "barka da yamma ranka ya daɗe"

"Kai ne corper ɗin da kake son Lilly?"

"Eh nine"

"Meye sana'arka, sannan kuma ɗan waye kai?"

"Sunana Nazir, ni ɗan Jigawa ne, na kammala degree na ne nai service a Kano, yanzu ina aiki da wata private school ne, kafiiin samu aiki"

"Kaine kake hure mata kunne kenan, kar tai karatu tace aure take so ko?"

"A'a ranka y...

"Shut up! Ƙarya tani za kai kenan? Kana hure mata kunne, yarinyar guda nawa take, me ta sani a Auren da zata ce ba ta son karatu se Aure? Ba dan na ganka a kamile da siffar mutunci ba, da sena sojoji sun ragaragaza min kai, an casa min kai aje a watsar da banza, kai kalli rigar jikinka ma kawai, har kana da ƙwarin gwiwar da zaka tunkari 'ya ta kace ka na so? Ba ma wannan ba da ma ta kai munzalin auren ne, na nema maka abunyi in aura maka ita, amma 'yar mitsitsiyar yarinya kamar wannan har ta samu ƙwarin gwiwar cewa Aure take so, ai daga jin wannan batu ka san zigata ake"

Ya kalli wani Soja yace "kiramin Lillyn dan ubanta"

Cikin ƙanƙanin lokaci, se ga Lilly, dan ba ta ma son Nazir ɗin ya zo ba.

"Daddy gani"

"Ke yanzu dama wannan ne ke hure miki kunne, kike cewa ba zaki karatu ba aure kike so? To ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, ba ke ba wannan mutumin, ke da Aure sekin kammala degree, dama na kirashi ne dan in ga ko mutumin banza ne, in sa a koya masa hankali, amma se na ganshi a kamile dan haka bake ba shi kaima ba kai ba 'ya ta, idan ba haka ba i will show you what am capable of doing, tashi ka ban guri mutumin banza kawai"

Jiki a sanyaye sir Nazir ya miƙe ya nufi hanyar fita, yaji zafin abunda baban Lillyn yai masa, kuma se yaji ba daɗi hana shi Lillyn da babanta yayi.

"Ke kuma wuce ki koma ciki, sakarya kin bi ƙyal ƙyal banza kin bi kyau, kalli sosasshen yadin jikinsa, har kina gayamin Aure kike so, get inside before I slap you, hopeless kid"

Da gudu Lilly ta shige tana kuka, bata taɓa zaton Daddyn ta ze disappointing ɗinta ba, ta ɗauka dagaske ze mata Aure kamar yadda ta buƙata, amma yaci zarafin Nazir haka.



Nana kam ta kasa dena kuka, har a kai lesson ɗin ranar ba ta fahimci komai ba, ɗakin da aka kaita ita da wata yarinya ne, su biyu ne a ɗakin, komai akwai a cikin ɗakin nan na buƙata, Nana ba ta komai se dai tai wanka tai salla, idan tana salla se Yarinyar tai ta kallonta.
Idan yarinyar taiwa Nana Magana, sedai tabi Yarinyar da ido, dan ba ta fahimtar abunda Yarinyar ke cewa, gashi tana son tayiwa Nanan Magana, amma Nana ba ta kulata, wani abun tana jin abunda yarinyar ke faɗa kaɗan kaɗan amma ba zata iya mayarwa ba, se in ta gaji ta ƙarewa Yarinyar zagi da hausa 😂.

Washegari Abba ya koma Nigeria, Sadik ma ya tafi tasa makarantar, sedai a hostel yake shi, Sadik be sha wata wahala ba, dan ya saba zuwa ƙasashen waje, kuma ya iya turanci sosai, nan da nan ya fara mantawa da halin damuwa da yake ciki da haushin Auren da a kai masa, sedai in sunyi waya da Mother ne yake tuna yana da Aure, dan kullum sun kai waya cikin kashedi take masa akan Nana.


Farhan taji sauƙi, sedai jiki kam babu ƙwari, se idanuwa a cikin fuskarta, duk tayi fayau, saboda kuka da damuwa, bacci dama sedai in ɓarawo ya ɗauketa, Amma kullum cikin tunani take.

Farhan na kwance a ɗaki, tana matsar ƙwalla, tana tunanin anya zancen Abbas ba gaskiya bane da yace ta manta da Sadik ba, ya barta.

Abba ta jiyo a tsakar gida yana gayawa Umma, wai sun haɗu a gidan su Huzaifa an karɓi kuɗin Aurenta daga gurin iyayen Sunusi Naira dubu Ashirin da biyar, sunce sun saka watanni biyar!



Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.







Wani makirin kallo Sunusi ya bi Farhan da shi, amma tai kamar ba ta ganshi ba, ta miƙe ta fara tafiyarta.

"Ke, saboda tsabar baki da mutunci, ba ki da ta ido wato har yanzu baki fasa bin maza a mota ba ko? Kuma dan wulaƙanci in ganki amma ki nuna ko a jikinki, kamar baki ganni ba?"

"Idan har zan bi maza ban ji kunyar Ubangiji ba, kai waye da dan na ganka zanji tsoro? So kai in zura da gudu ko kuma in yi yaya?"

A fusace Sunusi yace "wallahi tirr da halinki, kuma sena gayawa mahaifinki yawon fasiƙanci kike, ko da yake na sha gaya masa amma banga wani mataki da yake ɗauka akan ki ba, idan tsoron ki suke ji ba zasu iya tsawatar miki ba, ni dai dai nake da ke, kwaɗayayyiya kawai"

Kalmar fasiƙa da ya gaya mata ta doki ranta fiye da kima, take taji jikinta har wani rawa yake ta kalli Sunusi tace "Allah ya karɓa min hakkina na sharri da kai min" nan da nan se hawaye.

Abbas ya fito daga mota, ya nufo in da suke da sauri yana faɗin "lafiya kuwa, meke faruwa ne?"

Sunusi na ganinsa ya gane shi yce "to munafukin Allah, dama ba tun yau naga alamun watsewa ku ke ba, shine da iskanci ka ɗakko ta a mota, tana matsayin matar Aure"

Se yanzu Abbas ya gane shi, ya kalli in da Farhan ke tsaye tana kuka yace "Farhan waye kuma wannan?"

"Shine zaɓin iyayena, wai shi suke da burin su aura min, yana nuna musu shi na Allah ne amma kullum yana jifana da miyagun furuci, na barka da Allah"
Ta juya da sauri ta nufi ta nufi hanyar gidansu.

Ƙarewa Sunusi kallo Abbas yayi, tun da ga sama har zuwa ƙasa, ya kalli kayan jikin Sunusi kamar ɗan gudun hijira, be ga in da Sunusi ya dace da Farhan ba.

Sunusi yace "ƙaremin kallo da kyau, nine zan Aureta mata ta ce"

Baƙin ciki ya hana Abbas magana, se shiga cikin gidan Hajiya da yai a fusace.

Hajiya tana zaune tana kallon Sunna TV, taga Abbas ya faɗo ba ko sallama.

"Kai ya haka kai da wa kake wannan hucin?"

Be iya magana ba se cigaba da gwagwagwama numfashi da yake, se da ya sakko dan kan sa sannan yace "wai dama dagaske kike Aure za'aiwa Farhan?"

"Dan ƙaniyarka na saba yi maka ƙarya ne? Meyafaru to?"

"Na zaci wani mutumin kirki za a aura, ashe wani sakaran yaro ne da nake gani a layin nan, kwanaki yaje Asibiti duba ta, yau a wajen makarantar su na ganota, muka taho tare Shine ya tare ta yana mata masifa"

Hajiya ta zare glashin fuskarta tace "Ya salam, gaskiya nima nayi mitar haɗa Aurenta da wannan yaron, Yarinyar ba ajinsa bace sam, duk da shi mutum ba abun ƙyama bane, kuma arziki na Allah ne, amma kyakykyawar yarinya me nutsuwa kamarta, wallahi da gidan hutu ta dace"

Tsaki Abbas yai yace "Ni wallahi ji nake kamar in kai iyayenta ƙara human rights"

Buɗe baki Hajiya tai tace "kai ka kiyayeni, akan me zaka kai su ƙara su da 'yar su, su suka san me suka gani suke yanke mata wannan hukuncin"

"Yarinyar nan ba ta son mutumin nan, sun san negative impact ɗin abunda suke shirin yi ka iya haifarwa? Yarinyar da ta farfaɗo da kyar kamar zata mutu saboda damuwa, ni da ita ta gayamin ba ta son sa, akwai wanda take so fa, tayi ƙanƙanta da irin wannan stress ɗin, what If she commit suicide? Ko ta faɗa wani hali da ba'a so?"

Hajiya tace "to rufeni da duka Abbas, tunda nice zan mata Auren, ko dai kishi ka ke ne, wannan zaƙalƙalewa haka?"

Abbas ya sassauta muryarsa yace "Hajiya, am a doctor, ina hangewa iyayenta abunda ze iya faruwa akan Yarinyar nan, mutane masu irin ɗabi'arta na zurfin ciki damuwa na iya kashe su lokaci ɗaya, ko kuma su sami taɓin hankali, da alama ba ta da wani wanda zata raɓa taji daɗi, sedai ba abunda take yawan nanata wa kamar Sadik, that means he means a lot to her, se su bincika waye Sadik? Kuma su ƙyaleta da Auren nan tunda ba ta so, tana nunawa iyayen duk hukuncin da su kai akanta dai-dai ne, su kuma zasu kashe ta indirectly, nace zan Magana da babanta amma taƙi yadda, wace irin rayuwa ce haka za'a kashe ƙaramar yarinya, waya san baiwar da Allah ya ajiye a tare da ita?"

"To, ni dai bani da ta cewa, tun da ba 'ya ta bace, abunda yafi kawai mu tayata da Addu'a, tunda 'yar su ce bamu da iko da ita"

Abbas yace "Allah dai kawai ya kyauta, Allah ya basu 'ya ta gari, amma za suyi dalilin shigarta wani yanayi a banza"

Ƙarshe Hajiya se bin Abbas tai da ido, saboda yadda ya zage yana ta surfa bala'i akan Farhan.

Farhan kuwa da Sauri ta wuce gida, tai sa'a ba kowa a tsakar gida, tana zuwa tai cilli da jakarta, ta faɗa kan katifa ta rintse idanunta, tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa, da tsananin ƙiyayyar Sunusi, so take ko bacci ta samu tayi, amma abu ya gagare ta gaba ɗaya, 'yan kwanakin nan sam ba ta bacci, se dai tai ta juyi  in ta gaji ta tashi tayi Alwala tai salla, tai ta gayawa Allah damuwarta.







"Yanzu dan Allah kaima Yaya Faruk tafiya za kai?" Khairat da ke zaune a kusa da Faruk yana shan tea tai maganar a shagwaɓe.

"Eh mana, me zan zauna in muku?"

Khairat tace "wallahi i will Miss you, the house will be so boring, ba kai ba Auta"

Dariya Faruk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login