Showing 102001 words to 105000 words out of 259198 words
Chapter 35 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ka barwa Hajiya Inna karagar"
Sosai Hakimi yai dariya, har seda wushiryarsa ta fito yace "waini ina Ango ne, da kuma shi wancan ɗaya abokin nawa?"
Abba yace "Usman baya gari, shi kuma Sadik basu daɗe da kammala jarrabawa ba, muna masa shirye shiryen tafiya karatu ne"
Tunda Abba ya fara wannan bayanin Inna ta ƙura masa ido, ya kai aya sannan tace "Ina ze tafi karatun?"
Abba yace "ƙasar waje ne, kamar yadda 'yan uwansa suma su kaje, Faruk ma ya kusa komawa Master's"
"Shi Wannan fitsararraen yaron zaka kai ƙasar waje karatun?"
Abba yace "Inna ai ba wata damuwa, karatu kawai zeje yayi"
Inna tace "gaskiya ne"
Faruk ya samu fura da kilishi ya dinga ci, Abba yace "kaga kaci a hankali, in ba haka ba ze ɓata maka ciki, kuma ba banɗaki a hanya sedai ka yanki jeki kaje kayi"
Faruk yace "Abba ai a can ba Fura me daɗin wannan" hira suke sosai, yayin da Inna ke ta maimaita batun tafiyar Sadik cikin turawa yayi karatu.
Suna nan zaune se ga Nana ta dawo daga Makaranta, kasancewar tsananin soyayya dake tsakanin Hakimi da Nana, tunda ya fara rashin lafiya, duk in da taje ta dawo gueinsa take fara zuwa ta ga jikinsa, ko cikin dare se ta ɗau fitila taje ta haska taga ko yana numfashi.
Ranar da jikinsa ya hana shi cin Abinci kuwa, ita ma ba zata ci ba.
Shiyasa tana shigowa ta nufi turakar sa, tana faɗin "Inna ya jikin Kakana?"
Inna tana daga ɗakin tace "ban sani ba, tunda ba zaki iya ƙarasowa ki gani ba"
"To ai Inna takalmi na nake cirewa, yau ba abunda na gane a makarantar nan, duk hankalina yana gida ji nake kamar in gudo gida in ganshi".
Ta ƙarasa maganar tana shigowa ɗakin, sedai tai turus ganin su Abba da Faruk.
Murmushi tai da ta ga Faruk, ya miƙa mata hannu da nufin su gaisa, wani irin kallo Inna tai mata, wanda ya sa Nana tsugunawa tana gaishe su.
Abba yace "Hajiya ta, ya makarantar?"
"Lafiya ƙalau, ya aiki?"
Abba yace "Alhamdilillah, ya me jiki?"
"Da sauƙi Alhamdilillah" ta miƙe ta nufi gurin Hakimi, ta ɗora hannunta a goshinsa tace "Sannu ya jikin naka?"
Hakimi yace "naji sauƙi tunda naga ɗana"
Nana tace "Inna kin bashi Abinci ne?"
"A'a babata ke nake jira ki zo ki dafa ki bashi, ke da ba'a iya miki daga ke har kakan naki"
Ba ƙaramin dariya Inna da Nana ke bashi ba.
Lokacin sallar Azahar yayi, Sukai alwala suka tafi salla, har da Hakimi.
Bayan sun idar Abba da Hakimi suka tsaya a ɗakinsa na waje, in da mutane ke cigaba da zuwa dubiya.
Faruk ya shigo gidan, ya tarar Nana tana cin Abinci, ya tsaya yana kallonta, ya shafi sumar kansa tare da yi mata murmushi yace "Shine kina kallona kika ƙi kulani ko?"
Murmushi tai tana ɓoye fuskarta a tsakanin cinyoyin ta.
Ya zauna a gabanta yace "Abincin ma baki iya yiwa mutane bismillah ba, bani cokalin muci tare"
Ɗagowa tai ta zaro ido, taci Abinci da namiji, taɓ ashe yau zata sha terere a gurin Inna, kan ta yunƙura ta tashi Inna ta fito daga banɗaki hannunta riƙe da buta.
07063065680
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Zazzare ido Nana tai, Inna ta zabga mata uwar harara, sannan tace "me nake gani haka?"
Faruk ya kalli Inna sannan yace "taƙi kulani, ta gaida babana amma ni tai min banza, kamar ba ta Sanni ba shine na zauna inji ba'asi, inji dalilin hakan"
Inna tace "eh Lallai kam, gara kaji ba'asi" tai maganar tare da ajiue butar hannunta ta shiga ɗaki.
Inna na tafiya Nana ta miƙe tsaye, Faruk yace "ina zaki kuma?"
"Wanka zanyi in tafi makarantar Islamiyya"
Yace "To shikenan, ki ɗauke sauran Abincin kije ki rufe" Nana ta ɗauka ta tafi ta ajiye sauran Abincin.
Faruk ya shiga ɗakin Inna da sallama, ta amsa masa ya samu guri ya zauna.
Yace "Inna dan Allah ki bar mana Nana, mu tafi da ita a canza mata Makaranta"
Inna tace "Tofa wani sabon fi'ili, Nan ɗin ce maka aka yi bata karatu?"
"A'a ba haka nake nufi ba, gidanmu ba 'ya mace ƙarama haka kamar ita, nifa wallahi ina son 'yar uwa mace, inji tana Yaya, ince na'am Sisto what do you want"
Inna ta bishi da kallo tace "kai kam akwai ka da iyayi na gaske, ba naga wannan Yarinyar a gidanku ba ai itama ƙanwarku ce"
Faruk yace 'Khairat ai ba ta zama a gidan mu, sannan dai ni Nana nake son ki bamu, in ga ina koya mata Assignment, in dinga kaita outing, in sai mata abubuwan da take so, i want pampered her"
"Kai ka san me kake faɗa ni ban san me kake cewa ba"
Yace "haba Inna, Ki bar mana ita dan Allah"
Inna tace "wai ni ko san Nanan nan kake ne a Aura maka mu huta? Wannan magiya haka"
Zare ido yai yace "Aure kuma? yanzu se aiwa wannan yarinyar Aure? Ai this is child abuse, ni ba Aurenta nake son yi ba, kawai so nake in ganta a gidanmu, ace ƙanwarmu ce"
"To bazan bayar ba" Inna tai maganar tana hararsa
"Inna dan Allah ki bamu ita"
"Kai nace Ba zan bayar ba, babanka ma yayi nacin ya gaji, zan iya bada komai da na mallaka dan a barmin Nana, idan ina ganin ta Kamar mahaifinta nake gani, kuma idan na baku ita shikenan ba wanda zan kalla a gabana, ku ba zuwa in da muke kuke ba, wannan ɗin guda ɗaya ai kwa barmin" Inna tai Maganar ƙwalla na taruwa a idon ta.
Faruk yace "eyya, am sorry i understand you, na gane Inna, bakomai kiyi haƙuri, Allah ya jiƙan 'ya'yanki da kika rasa, ita kuma Allah ya rayata da Imani, dan Allah kar ki kuka, sannan in dai mune insha Allah kan in koma Master's zan dinga zuwa inyi kwanaki tare da ku" yai maganar cike da damuwa.
"Inna tace bakomai kar ka damu, mahaifiyarku ba zata bari ku zo ƙauye ba, amma duk da hakan da ka faɗa naji daɗi sosai, Allah yai maka Albarka" tai maganar tana jin ƙaunar Faruk, yaron ba dai jin ƙai ba da tausayi, baya son yaga wani a damuwa.
Suka cigaba da hira shi da Inna, yana bata labarin yanayin rayuwar turai.
Nana tai shirin tafiya Makaranta ta zo ɗakin Inna tace "Inna zan tafi makaranta"
Inna tace "to a dawo lafiya, ban da biye biyen ƙawaye, banda tsayawa da namiji a waje, a tafi ana sa hannu a hijjabi, banda kalle kalle ko ciye ciye a hanya, kar wani yace miki je kij, banda bin lumguna abi hanya sosai.
Nana se signa ta kewa Inna akan ta ɗan tsahirta da zubo wannan jawaban, saboda ga Faruk a gurin, amma ba abunda yai mata zafi se zuba take, tana sake jaddada mata.
Shi Faruk ma abun dariya ya bashi, wai wannan 'yar Nanan akewa wanna jan kunnen, Yarinyar guda nawa take, ana ta wani ta sa hannu a hijjabi, ɗan abunda ke ƙirjin nata be taka kara karya ba, yanzu yake fitowa.
Faruk ya miƙe yace "muje in rakaki Makarantar"
Nana tace "A'a Inna ta hanani jerawa da maza"
Faruk yace "Ikon Allah, Inna duk kin takura mana ƙanwa, ni gashi ban gama ganinta bama, ai shikenan sekin dawo Allah ya tsare ayi karatu da kyau, zan bawa Inna saƙo ta ajiye miki"
Nana tace "to ku gaida gida"
Yace "Ba zaki ce in gaida Sadik ba?" Yai Maganar cike da zolaya.
Nana tace "wallahi bana gaida shi" tai maganar tana fita daga ɗakin.
Taje waje taiwa Abba da Hakimi sallama ta tafi makaranta.
Se bayan la'asar sannan sukai harmar tafiya, dan Alhamdilillah jin Hakimi da sauƙi.
Inna tace "ya dai kamata kaiwa kanka faɗa Abdullahi, ka nunawa iyalinka mahimmancin iyayenka, kakansu ko a daji yake yakama yaci darajar ya haifeka suzo su duba shi, amma ba su da uzuri ace su kasa zuwa suga jikinsa, dama ziyara ma su zo in da muke wannan mun yafe, tunda ba sa son Zuwa, amma halin rashin lafiya ai abune da Yakamata ace sun san yakamata"
Faruk yai saurin cewa "Ayi haƙuri Inna zamu dinga zuwa Insha Allah"
"Da kai nake Magana?" Inna tai maganar tana kllonsa.
Faruk yace "Allah ya bada haƙuri" yai gaba abunsa yana murmushi.
Seda Inna ta gama mitar ta sannan Abba yace "dan Allah kiyi haƙuri, insha Allah za'a gyara, kuma duk zamu sake dawowa mu duba shi haba ɗaya".
Inna tace "ya dai kamata kasan abunda ya dace"
Yai ta bata haƙuri, daga nan suka kama hanyar komawa gida.
ko da Nana ta dawo daga Islamiyya ta tarar sun tafi.
Nana tace "Inna har sun tafi?"
Inna tace "eh sun tafi, ga sababbun litattafai can, Yayanki ya bayar a ajiye miki, hadda jakar Makaranta sabuwa fil me kyau"
Nana tai murmushi tace "aikuwa nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"
Inna tace "Ai nan ya zauna ya na min magiya akan lallai se na bar musu ke sun tafi da ke, ni kuwa ba zan iya ba, dan ban yadda da tarbiyyar wannan gidan ba, gidan nan nasu se a hankali"
Nana tace "taɓɗijan, ni ma ba zan zauna a wannan gidan ba, ba zan bisu gidan su ba, wannan masifaffayar babar ta su, me wa mutane kallon banza, ga wannan wawan masifaffafe wanda be san darajar mutane ba"
Inna tace "ke dan ubanki ba ki san kara ba? Ko dan yadda ɗan ta ke nuna miki so ai kyayi kara, yanzu idan yaji kina cewa uwarsu me yiwa mutane kallon bamza zeji daɗi? kuma ban hanaki faɗar mummunar magana akan wanda yake gaba da ke ba?"
Nana ta ɗan tura baki tace "yi haƙuri na dena, gaskiya dai Faruk ya na da kirki ba kamar wannan me hura hancin ba kamar wani kasa"
Inna tace "i taku dai ke da shi ɗin"
"Ai wallahi Faruk duk yafi kirki" Nama ta faɗa tana murmushi.
Inna tace "wai ni meye tsakanin ki da Faruku ɗin nan? Ko dai son sa kike? Ayi 'yar gida mu huta?"
Nana ta zaro ido tace "taɓ Wannan ne ze Aure ni, kina ganin sa ɗan birni me kyau, me ze da 'yar ƙauye, ƙauyen ma na ƙayau?"
Inna tace "in dai kina son sa ai shikenan, ba wata damuwa"
Nana tace "Inna ya ake jin son ne to?"
Inna tai murmushi tace "a bar wannan maganar, tashi kije ki karɓo zumar ki a gidan kuka, Hakimi ya bayar da kuɗi a kawo miki"
Cikin murna Nana ta tashi tana Allah ka yiwa Kakana Albarka".
Inna ta bita da kallo tana murmushi.
Se bayan magariba sannan su Abba suka koma gida, suka tsaya a masallaci su kai sallar isha'i, Abba yace suje restaurant su ci Abinci, se kusan ƙarfe goma na dare sannan suka dawo gida.
Faruk ya wuce BQ, Abba kuma ya shiga cikin gidan, kai tsaye ya wuce part ɗin sa ya rufe ƙofarsa.
Romeo Sadik kuwa baban Soyayya, yaƙi kula Farhan se wanata yake, har kiran wayarsa tai, amma ya ƙi ɗagawa, amma ya sa hotunan ta a gaba yana kallo, yana murmushi.
Seda Safe sannan Sadik ya san su Faruk sun dawo da suka haɗu da Asuba, Sadik yace "Ai na zaci a can zaku kwana da naga dare yayi baku dawo ba"
Faruk yace "A'a ba'a can muka kwana ba, jikin nasa ma da sauƙi sedai duk ya rame sosai"
Sadik yace "Aka bibiya ma ba wata cutar kirki bace, ake ta wannan kwaroroton ba shi da lafiya"
Faruk yace "Wai Sadik Yaushe za kai hankali ne? Nan Abba yai zazzaɓi da mura, har kuka kayi saboda damuwa, yadda fa kake son babanka shima haka yake son nasa, hawan jini ne fa yake damunsa"
Sadik yace "haba dai hawan jini kuma? wallahi na zaci be fi zazzaɓi ba"
"To hawan jini ne, duk ya rame ƙafafunsa sun kumbura"
Sadik yace "Subhanallah, Allah ya bashi lafiya, dole hankalin Abba ya tashi, dan naga hawan jinin nan shike kwashe mana tsofaffin nan, Allah dai ya bashi lafiya, shima ya tsufa ya haƙura da wannan Sarautar amma kamar da sarautar aka haife shi yaƙi haƙura"
"Idan ya sauka daga sarautar kai zaka je ka riƙe masa?"
Sadik yace "Allah ya kiyaye inje in zauna a wannan garin da ko ruwan roba babu, ba wata tsayayyiar wutar lantarki, gari duk se uban shanu da gonaki, ga ƙudaje ha warin kashin shanu, wai ma sarautar dole ce haba, ba abunda ya nema ya rasa da Abba ba ya ba shi, amma yaita wahala da ɗawainiyar mutane, wannan yace kaza wancan ma yazo da tasa matsalar, banda 'yan jarida da ke zuwar masa ba yau ba gobe, faɗan filayen magada duk fa haka Abba yake bada labarin wahalar da yake sha akan sarautar, sekace Dole ya haƙura mana"
Faruk yace "dan ubanka kai meya hana ka ajiye sarautar da akai maka ta yariman Hausawa, har wani taƙama kake wai kai Prince, daga zuwa rakiya ba'a bawa dr. Ba se kai a kaiwa Sarauta, banga uwar da kake tsinanawa a sarautar da a kai maka ba ɗin"
Sadik ya wani gyaɗa kafaɗa yana murmushi yace "ya ranka, You are talking to Prince, kayi magana da girmamawa mana"
Tsaki Faruk yai tsaki yace "dalla ware, ni zan kwanta saboda a gajiye nake in ka rigani tashi ka shiga cikin gidan, ka miƙamin gaisuwa gurin Mother kan in shiga"
Sadik yace "ok"
Faruk yace "Aff na manta ban gaya maka ba, Inna na gaishe ka, da kuma Nana"
Tsaki Sadik yai yace "Nifa bana son Maganar da ba shikenan ba, wannan tsohuwar yadda ta tsaneni ne za ta ce a gaishe ni, ai ko zan mutu ba zata faɗa ba, wannan Yarinyar kuwa me ɗan kai kamar an roƙo mata ita ma ba zata faɗa ba, ni harka ban haushi da kai zacen Yarinyar nan, dan na manta da ita ma a duniya"
Faruk yai dariya ya wuce ɗakinsa, dama dan ya tsokani Sadik ya faɗa.
Sha ɗaya na Safe Sannan Abba ya buɗe part ɗin sa ya fito cikin shirin fita, Mother ta tareshi tace "Yallaɓi jiya da kuka dawo kan in fito na tarar ka rufe ƙofa, ya me jiki?"
"Ke kina da damuwa da me jiki ne? Ai mara lafiya na ne, dan haka ni ya shafa ba ke ba"
"Dan Allah Abba ka bar wannan maganar, kuskure ne na yadda nayi shi, amma dan Allah kayi haƙuri"
"Wane haƙuri kuma ban da wanda nake yi Hauwa'u, ai ba tun yanzu kike nunamin wariya akan dangina ba, kallonki kawai nake, dan haka kowa ya riƙe nasa, rashin lafiyar mahaifina ni ta shafa bake ba, dan haka ki ƙyale ni"
Cike da ƙwarewa da iya kissa ta fara kuka tana faɗin "haba Love, dan Allah kayi haƙuri Hakimi ai babana ne nima, bekamata ka dinga nuna ai basu shafeni ba, lokacin da mu kai waya ba su gayamin abunda ke damunsa ba, shiyasa ban zaci babban ciwone haka ba dan Allah kayi haƙuri"
Abba zeyi Magana ya ɗaga kai su kai ido huɗu da Sadik, dan haka ya fasa ya janyo ta jikinsa, ya fara share mata hawaye yace "is ok ya wuce"
Sadik da ke tsaye yai murmushi, kawai ya nufi Kitchen.
Abba ya san illar dake tattare da bayyanar da saɓanin ma'aurata har 'ya'yan su su sani, saboda hakan na haifar da matsala da rarrabuwar kawunan Iyali.
Ma'aurata na iya faɗa su dawo su sasanta kansu, amma muddin 'ya'ya ko iyaye suka sani, ba sa mantawa kuma hakan ya na iya kawowa wannan Iyali matsala.
Dan haka Abba ya wayance, ya bar Komai ya ƙyale Mother Saboda Sadik da ya shigo, dan baze so ya ga mahaifiyarsa na kuka ba.
Se da Sadik ya shige sannan yace "bana son dinga yi miki faɗa, ko makamancin haka a gaban 'ya'yan ki, saboda ba na son martabata ta zube a idanun su, ba na son farincikin da na kafa a gidana in sa ƙafa in rushe shi, shiyasa nake kawar miki da kai, amma naga kin ɗau abun wani fanni daban, Yakamata ko yaya nima ki dinga kamanta yi min kara akan ahalina, ko ba komai nima zan ji daɗi"
Share hawayenta tai ta riƙe hannunsa tace "insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, kuma zanje in duba sji insha Allah, amma dan Allah ka dena fushin nan dani ba zan iya jurewa ba"
Abba yai murmushi, ya ɗan ja hancinta yace "ya wuce"
Tai murmushi tace "to muje part ɗina in rarrasheka"
Abba yace "Ai yanzu ma na rarrasu"
A ɗan shagwaɓe tace "ni ban yadda ba, dan Allah muje, kaci Abinci ka canza wannan wankan da kayi"
"Ke dai ba zaki Girma ba ko? Gashi kin ajiye sirika, wadda a kowane lokaci za'a iya cewa ta haihu amma kin ƙi girma"
"Yaushe zan bari in Girma ka hango min wata, ai gara in ƙi girman"
Murmushi sukai tare, suka nufi part ɗin ta.
Rashin zuwan Sadik ba ƙaramin damun Farhan yai ba, ya sata a matuƙar damuwa, kullum direbansa zeje ya maida ita gida, amma yaƙi zuwa, kuma yaƙi ɗaga wayarta ko responding ɗin messages ɗin ta.
Shima a ɓangaren sa hakan da yai yana damunsa, amma a ganinsa hakan shine matakin da ya dace ya ɗauka, dan ya zama gargaɗi kar ta kuma aikata laifin da tai masa.
Mother ta fara noticing kusan kullum direba dai dai lokacin tashin Sadik daga Makaranta seya fita, ita dai ta san ba aikensa take ba, kuma Sadik ya kammala Makaranta, amma ta rasa ina yake zuwa.
Yanzu ma kusan awa guda tana jiransa ta aike shi, amma ba ya nan ta rasa in da ya tafi haka, dan haka tace idan ya dawo ace ta na son ganinsa.
Haka kuwa akayi, bayan ya dawo daga cika umarnin megida Sadik, ya nufi amsa kiran da matar gidan ke masa.
Ya ɗan jira a falo kafin ta fito, cikin takunta na isa ta ƙaraso falon ta zauna, ta kalle shi tace "Yawwa, dama na aika a kiramin kai ne dan inji in da kake tafiya, kusan kullum seka fita, ni ba aiken ka nake ba, kuma dai ga Sadik ya kammala Makaranta, ina kake zuwa haka? Yanzu tun ɗazu fa ina zaune ina zaman jiranka zan aike ka amma baka nan, ina kaje?"
Ɗan Jimm Direban yayi, yana ɗan nazari yana jin kamar ya gayawa Hajiya Hauwa abunda ɗanta ke aikatawa, amma wata zuciyar tace masa 'kul ɗinka, wannan matar da bata son laifin 'ya'yanta kana gaya mata zata iya cewa ƙarya kake, za kaiwa ɗanta sharri, koma shi yaron ya ƙaryata ka, dama dai mahaifinsa ne'
"Ina magana kai shiru ka ƙyaleni" muryar