Showing 114001 words to 117000 words out of 259198 words

Chapter 39 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13378

a hankali ya ƙarewa Nana kallo da take tsaye a kansa da kofin ruwa.

A fusace yace "ke wace irin dabba ce zaki watsamin ruwa haka?"

"Cewa a kai in tashe ka, kuma ahir ɗin ka da sake zagina"

Juyawa yai akan katifar ze cigaba da bacci, yaji muryar Inna a kansa "zaka fito ne ko se an sa an fito da kai mara Kunya"

Tashi yai yana kumbura baki ya fita tsakar gida yana tunanin wannan wane irin abu ne haka?"

A tsakar gida ya ga An shimfiɗawa Hakimi dadduma, yana kashingiɗe, gefensa ga wasu dogarai guda biyu riƙe da bulalai, Sadik ya nemi guri ya zauna yana tura baki.

Hakimi ya kalleshi yace 'ina kwana?"

Shiru Sadik yai yaƙi amsawa.

"Ya kai shiru baka amsa ba, can a gidan naku ma haka kake wannan rashin ɗa'ar baka gaida iyayen ka da safe ko?"

Sadik ya sunkuyar da kai yaƙi Magana.

Hakimi yace "a bashi Abincin safe"

Nana ta kawo wani kwano ta ajiye.

Hakimi yace "bismillah, maza ɗau Abinci ka ci"

Sadik ya buɗe kwanon nan, tuwon masara ne a ciki da miyar kuɓewa ɗanya.

Sadik ya gyatsine fuska yace "ni bana ci"

Hakimi ya kalli ɗaya daga dogaran yace "A sashi yaci Abinci"

Ai ganin da Sadik yai dogarin ya ɗaga bulala, ze zumbuɗa masa yasa Sadik a gigice yace "zanci dan Allah, a bani cokali"

"Bame baka cokali, sa hannunka kaci da shi"

Haka Sadik Ya janyo kwanon ya runtse ido ya kai loma ɗaya bakinsa, da kyar ya haɗiye saboda warin daddawar da ya addabe shi, sega ƙwalla a idon Sadik ya kai loma ta biyu amma ya kasa haɗiyewa se kakarin amai da yake.

Hakimi yace "idan yai amai, ku zane shi sannan a ƙaro masa wani tuwon, zakaci ƙaniyarka, seka kwan uku kana cin gabza, saboda rashin ta ido har ayi Abinci a baku kace kai ba zaka ci ba ko, za'a ladabtar da kai ai"

Haka A saka Sadik a gaba, seda ya cike gurbin Abincin da be ci na na jiya, seda ya cinye tuwon nan tas.

Sannan aka kai masa ruwa banɗaki yai wanka, sedai shi kansa banɗakin tsoro ya bawa Sadik, ga wani soson wanka irin na mutan da ɗin nan me zafi a jiki, ga ruwan wanka a bucket ko abun zuba ruwa babu, masan dake banɗakin ma tsoro ta bashi, kar yaje yana cikin wankan ya faɗa ciki.

sabulun kawai ya goga ya watsa ruwa ya fito da sauri, dan tsoro idan ya kalli rufin azarar nan se yaga kamar zega maciji a ciki.

Da ya fito, Aka kawo masa wasu irin kaya over size, wanda ko Abbansa aka bawa kayan nan sun masa yawa, akace ya saka kayan.

Sadik ya dinga kuka, hawaye shaɓe shaɓe yana tunanin wannan wane irin abune se kace zamanin bayi.

Akai masa rawani kamar dagacin ƙauye, aka fita da shi zaman fada.

Shigar da a kai masa tasa Nana ta dinga tuntsura dariya, duk gayun Sadik yau an maida shi ɗan ƙauye typical.


Farhan duk ta damu kanta sosai akan rashin jin Sadik kwana biyu, ta kalli group ɗin su Lilly da suke kiran kansu da Sweet fifteen, suna ta shirmen su a ajin, sedai Lilly tayi shiru da alama tana tunanin wani abun ne.

Haseena tace "ke Lilly, wai kwana biyu meke damunki ne, kullum cikin zancen zuci?"

Lilly tai ajiyar zuciya tace "bakomai Normal"

Yasmin tace "Ni sirrin Wannan glowing ɗin da kike zaki bani, kinga yadda kika ƙara ja kuwa, ga kumatunki sun sake girma"

Banza tai musu suka cigaba da surutan su, Haseena tace "Yasmin zoki rakani Clinic in karɓi pad, a kowane lokaci zan iya ganin abun nan, kuna ban zo da pad ba"

Yasmin tace "i thought you are pregnant ai"

"Ke pragnent ɗin uban wa, ke kika min cikin dalla tashi muje ki rakani"

Gaban Lilly ne ya faɗi jin hirar da sukeyi, cikin hanzari ta tashi ta tafi Office ɗin Sir Nazir.

Sedai baya Office ɗin, ta nemi guri ta zauna tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa da sauri da sauri.

Ta daɗe tana jiransa se ga shi ya dawo, hannunsa riƙe da litattafai da maka.

Yana ganinta ya fara murmushi yace "Baby yaya?"

Ta kalleshi tace "Akwai matsala fa"

Yace "subhanallah, matsalar me kuma Fateena?"

"Am sick wallahi, bani da lafiya fa"

Yace "eyyya sorry, ai baki gayamin bane, muje in rakaki clinic a duba min ke"

Tace "Bafa yadda kake tunani bane"

Yace "to yaya ne?"

"Sir, wata biyu kenan ban period ba fa, kuma fa hakan na nufin ciki ne dani"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Lilly ya a kai kika san ciki ne da ke?"

"Ina karantawa a Novels, kuma ka kanka ka mana lesson, ni gaba ɗaya hankalina ya tashi, ina jin tsoro idan babana ya sani ze iya harbeni wallahi"

Cikin dirircewa yace "kinga, kwantar da hankalinki ki nutsu, haryanzu bamu tabattar da abinda kike zargi ba"

Cikin kuka tace "meya rage wanda zamu tabattar ka sani a bala'i, duk wasu signs na ciki su nake ji a jikina, and kana cewa bamu tabattar ba"

Nazir cikin tashin hankali yace "kinga calm down, yanzu bari in baki robar ruwa, kiyi fitsari a ciki, zanje in siyo pt strip dan mu tabattar se mu san abunyi.

Ba tace masa komai ba ta cigaba da kuka.

"Dan Allah Lilly ki nustu kar asirinmu ya tonu ki dena wannan kukan, bari inje yanzu zan dawo"

Ya fita daga Office ɗin cikin sauri.

Abba kuwa gani yai be kyautawa Mother ba da ya fita a sabgarta ba, tabbas an mata ba daidai ba amma yadda ya haƙura yai biyayya ita ma dole tayi.

Sashinta ya nufa, bata falo ya wuce bedroom ɗin ta, aikuwa ya tarar da ita akan gado a zaune, tayi shiru ta zubawa guri ɗaya ido.

Sallamar da yai ne ta dawo da ita hankalin ta daga dogon tunanin da take.

A ciki ta amsa masa sallamar ta ɗauke kanta.

Ƙarasowa yai ya zauna a kusa da ita, ya ɗan ƙura mata ido, yaga yadda idanunta su kai ja, da alama ba ta samu isashen bacci ba.

"Barka da safiya" ya faɗa yana kallonta.

Tura baki tayi ƙwalla na taruwa a Idonta.

"Hauwa'u, nasan abunda a kai miki ba'a kyauta miki ba, amma tunda naiwa iyayena biyayya ya zama dole kema ki haƙura, nasan ba za su taɓa yi masa abunda zasu cutar da shi ba, dan haka kiyi haƙuri ki dena wannan damuwar, dan ban shirya yin musu ko jayayya da iyayena ba saboda ke"

Ta ɗago ta kalle shi tace "Amma...

Ya katseta ta hanyar ɗaga mata hannu tare da cewa "bana son sake jin wata magana akan wannan lamarin, na riga na rufe wannan babin, ki kai min breakfast ɗina part ɗina zan karya in fita"

Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, ya juya ya fita daga ɗakin.

Wasu hawayen baƙin ciki suka shiga zubo mata, da ta san a can za'a baro mata Sadik, da duk yadda za tai seta hana shi zuwa garin, da wani aka bari a cikin yaran ba Sadik ba, da ba zata damu haka ba, amma Sadik tun tasowarsa be taɓa nesa da ita da kwanaki ba, har gara dr. Da Faruk suna zuwa cikin Family, har ƙasashen waje sunje karatu, amma Sadik baya zuwa ko ina ya zauna se in da Mother take, rana ɗaya ta ƙarfin tsiya an ɗauke mata shi.


Lilly na nan zaune Office ɗin Nazir, se gashi ya dawo, kamar wanda zaki ya rarako, kallo ɗaya za kai masa ka san yana cikin matsanancin tashin hankali da zunzurutun damuwa.

Ya shigo Office ɗin, ya rufe ƙofa ya kalleta yace "kinyi fitsarin?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya karɓi robar, ya saka tsinken gwajin sedai yana zaro tsinken ba tare da jan lokaci ba ya nuna ɓaro ɓaro, Akwai ciki.

Wani irin gumi ya shiga tsatsafowa daga goshinsa, ya ɗaga kai ya kalli in da take zaune ta ƙuro masa ido.

Tace "Yana ga ka canza meyafaru? Me ka gani ne?"

"You Are pregnant!" Ya bata amsa.



Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
07063065680.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.








Saurin toshe bakinta tayi, dan bata son abunda ihun nata ka iya haifarwa a tsohon daren nan ba.

Bedsheet ɗin da take kai, duk ya ɓaci da jini, ga wani irin gigitaccen ciwo da marar ta keyi, se uban gumi take kamar me naƙuda.

A hankali ta ja jikinta zuwa banɗaki, dan gyara jikinta, sedai abu ya gagara  ƙarshe ma ta zube akan gwiwowinta, jini na cigaba da zuba daga jikinta.

Ita kanta ta firgita da jinin da ta zubar daga jikinta, yunƙurawar da tai zata miƙe, cikin ya faɗi gaba ɗaya.

Ta dinga sauke numfashi, idonta har wani lumshewa yake saboda Azabar wahala.

Ta daɗe a durƙushe a banɗakin, kan taji ya ɗan lafa mata, ta miƙe a durƙushe, ta gyara jikinta, ta cire bedsheet ɗin da ta ɓata, da kayan jikinta ta naɗe su ta ajiye su guri ɗaya, sannan ta koma ta kwanta.

Sedai tun ba'aje ko ina ba ta kuma ɓaci da jini, saboda yadda take cigaba da zubda jinin ba ƙaƙƙautsws, haka ta dinga sintiri tsakanin ɗakin da banɗakin tana gyara jikinta, ga ciwon mara da ke cigaba da nuƙirƙusarta.

Da ƙyar ta samu jinin ya tsagaita, sedai yana tsagaitawar kuma ta fara jin wani irin sanyi, ga jiri da ya fara kwasarta, da wani irin matsanancin ciwon kai, haka ta kwanta ta duƙunƙu ne, jikinta na cigaba da rawa.



Sadik ba ƙaramin jin daɗin Alkaki da kilishin da Nana ta jefo masa yai ba, da gari banza ne se yai mata rashin mutunci saboda ta jefe shi da abu, amma da yake nema yake ba ƙorafi ba wani abu haka ya ɗauka ya ci.




Mother ce zaune a gaban Abba, tana kuka wiwi kamar ƙaramar yarinya.

"Dan girman Allah ka koma ka ɗakkomin ɗana, kana jin yadda yake min kuka a waya, wallahi yana cikin matsananciyar damuwa, dan Allah ka dawomin da ɗa na"

"Wai dan Allah ya kike so nayi ne? Inyi fito na fito da Iyaye na, yau Sadik ko mutuwa yai a hannunsu na san ba zasu kashe shi da gangan ba, ko tunda kike haihuwa an taɓa ɗaukar ɗa ɗaya yaje garin ya zauna, meyasa kike hakane, kamar fa kina nuna sena nunawa iyayena basu isa bane ba fa"

"Ni ba haka nake nufi ba, amma dan Allah ka basu haƙuri koma me yayi su barshi ya dawo gida, dan Allah ba danni ba"

Abba ya kalli Mother yace "yanzu da yaron nan mutuwa yai fa? Ko kuma aka sace shi ya za kiyi?"

"Wannan daban na san Allah ne ya karɓe shi, amma yana raye ina raye a nesanta ni da shi, ba zanji daɗi ba, dan Allah a dawomin da shi"

Abba gyara kwanciyarsa yai, ya juya mata baya, dan ya gaji tun yana lallaɓata za ta sa su fara faɗa.

Lilly da safe miƙewa ta gagareta se da ƙyar, da ta tashi se jiri ya dinga kwasarta, duk yadda taso ta fita falo ta kasa, se kwanciya tayi.

Ganin har wajen sha ɗaya ba ta fito ba, yasa mamanta biyo ta taga ko lafiya, ta na zuwa ta tarar da ita a cikin bargo ta rufe kanta.

A hankali ta kai hannu ta yaye bargon tace "Lilly, lafiya kuwa? Meya sameki haka?"

"Mummy bani da lafiya" Lilly ta faɗa cikin karkarwa.

"Yasalam, amma baki gayamin ba, meyasameki haka?"

Seda gabn Lilly ya faɗi jin tambayar da Mum tai mata, amma ta basar tace "zazzaɓi nake da gudawa"

"Amma baki zo kin gayamin ba, taso maza muje ki karya mu tafi Asibiti"

Ta kamata da nufin ta miƙe, sedai tana miƙewa tai baya saboda jiri.

Hankali a tashe Mummy ta riƙota tana salati, ta duba jikin Lilly taga jini tace "jinin meye wannan kuma a jikin ki?"

"Mummy period nake, yana min rushing Sosai, tun jiya haka yake zuwa"

Gaba ɗaya Mummy ta rikice, ta kama Lilly Zuwa banɗaki, ta taimaka mata ta gyara mata jikinta, ta sa kaya ta ɗauketa zuwa Asibiti.

Idon Lilly harya nuna alamun ƙarancin jini, a yadda Lilly tai musu bayani, tace zazzaɓi tayi na kusan sati biyu se gudawar kwana uku, dan haka ba wanda ya kawo waccan ta'asar da tayi.

Nan likita ya hauta da faɗa "ke dan shirme kina zaune ba lafiya kina nema ki kashe kanki, meyasa zaki zauna tsawon lokaci da larura ki ƙi faɗa"

Mummy tace "nima abun ya bani mamaki, ya za'ai ace tsawon wannan lokacin, baki da lafiya ki kasa faɗamin, salon babanki ya dawo yace ina sane na barki ba lafiya"

Lilly dai tai shiru, tana jin yadda kanta ke cigaba da juyawa.

Nan da nan aka bata gado aka kwantar da ita, aka ɗebi jinita dan yin gwaje gwaje.

Nan aka gano yadda jininta yai ƙasa, dan har tana buƙatar a ƙara mata jini, saboda yadda jininta yai ƙasa.

Gashi duk gwaje gwajen da a kai mata sun nuna lafiyarta ƙalau, se 'yar malaria kaɗan a cikin jininta.

Mummy ta fita waje dan kiran Mahaifin Lilly ta sanar masa halin da ake ciki.

Likitan da ya duba Lilly ya shigo, ya kalli yadda ruwan da aka samata yake shiga jikinta a hankali.

Ya ƙarasa gaban gadonta ya kalleta yace "Fatima, duk teses ɗin da akai miki sun nuna ba wani abu da yake damunki, malaria da ke jininki ma ba ta kai ace tayi tasirin da zaki rasa jini haka ba, ki gayamin tsakani da Allah, meke damunki?"

Shiru tai tana binsa da kallo taƙi magana.

"Magana fa nake miki"

"Ni ba abunda yake damuna, kawai zazzaɓi nai da gudawa" tai maganar cike da ƙosawa.

"Amma jinin da kika zubar yayi yawa, se fa an ƙara miki jini"

"Nima ban san meya sameni ba" ta faɗa idonta na cikowa da hawaye.

Yace "ok shikenan, Allah ya baki lafiya"

Ta amsa da Ameen.

Bayan fitar doctor, ta lumshe idanunta, ta tuna Nazir na can na hutawarsa, ita kuwa gata tana faman wahala tsakanin rayuwa da mutuwa.

Me aikin su Lilly kuwa, ta shiga ɗakin Lillyn dan gyara mata, ta tarar da duƙunƙunen nan bedsheet da kayan Lillyn kaca kaca da jini, abun ban tsoro.

Tai shiru tana tunani, ta san Lilly ta fara period, amma wannan Jinin yayi yawa ace na al'ada ne ya ɓata guri haka.

Haka ta je ta zuba kayan a washing machine ta Wanke, tana cigaba da mamakin wannan jini haka.

Nazir Kuwa tun daren jiya ya kuma kiran Lilly yaji bata ɗauka hankalinsa ya tashi, ya rasa in da ze sa kansa, bacci ma ya gagare shi yi, se kaiwa da komowa yana tunani, ya kira harya gaji amma wayar bata shiga.

Da safe kasa zuwa makaranta yayi, dan yana cike da zullumin ko wani abune ya faru da ita, kar Asirin sa ya tonu.




Allah ya temaki Sadik an ɗan rage wannan takurar da ake masa, mussaman akan cin Abinci, sedai fa babu hanyar fita, dan duk wani yunƙuri da ze ido na kansa ana kallonsa.

Se dai ya auri zaman ɗaki, kullum yana ɗaki a zaune, idan ya fito to salla za'a je.

Yau da daddare yana kwance yana kallon ƙaramar wayarsa, wadda gidan cajin yai ja alamar kowane lokaci zata iya ɗaukewa.

Yau kusan kwanki huɗu beji muryar Farhan ko Mother ba, dan ma ƙaramar wayarsa akwai riƙe caji sosai.

Gaba ɗaya ba bu lambar wanda take shiga.

Ya duba agogo kusan ƙarfe goma da rabi na dare, amma zuciyarsa ta dinga azalzalarsa ya kira Farhan, ya Danna lambarta ya fara kira, yai ƙuri ya zubawa screen ɗin wayar ido.

Be san wayar ta shiga ba, se jin muryarta yai yai can ƙasa ƙasa ta daki dodon kunnuwansa "Assalam Alaikum"

Se da yai nannauyar ajiyar zuciya sannan ya ce "wa'alaikum salam" daga nan kuma yai shiru.

Cikin sassanyar muryarta tace "kana lafiya?"

"Kin manta dani ko?"

"Ya za'ai in manta da kai, kasan wayarka ba ta shiga"

"Hakane, ya Makaranta"

"Lafiya ƙalau ya gidan, ya kowa da kowa"

"Ƙyaleni da wannan gidan, meyasa baki bacci ba?"

"Karatu nayi, kuma na zauna tunaninka"

"Allah sarki matar Sadik, wallahi nima duk kewarki ta isheni, ina son in ganki"

Murya a Sanyaye Farhan tace "nima ina son in ganka am missing you so much"

"Kinga wayata ma ta kusa ɗaukewa saboda rashin caji, ban zaci wayarki zata shiga ba, but Alhamdilillah tunda na samu wayar ta shigo, ina fatan dai ba wata matsala ko?"

Se da Farhan ta ɗanyi jimm, dan ta so tai masa maganar Sunusi, amma ta basar tace "ba wata matsala se guda ɗaya"

"Matsalar menene?"

"Ina so in ganka"

Sadik yai murmushi yace "Nafi ki son mu haɗu, se in dinga jin kamar kafin in dawo wani ze ƙwacemin ke"

"Ba wanda ze ƙwaceni, sedai ina fatan ka dawo da wuri, saboda idan kana nan zan fi samun ƙwarin gwiwa, rashin ka a kusa nima yana sani karaya"

Haka kurum Sadik yaji wasu hawaye masu ɗumi, suna zirarowa gefen idonsa.

"Farhan, ina sonki sosai, ni na san son da mukewa juna ba RUƊIN ƘURUCIYA bane, Allah ya cika mana burinmu"

"Nima ina wannan fatan, bana son wata Magana ta kuma tasowa tsakani na da Sunusi, shiyasa na damu ka dawo"

"Insha Allah ba wani abu da ze faru, ke tawace, wayata zata ɗauke Farhan se kuma in Allah yayi na samu caji, kimin Addu'a Allah yasa in dawo gida nan kusa"

"Insha Allah zaka dawo nan kusa, I love You"

Sadik yai murmushi yace "sake faɗa inji, in kika fadi kalmar nan ji nake kin tafiyar da mafi yawan damuwata, ina ma kina kusa dani kika faɗa, in kalli ɗan bakin nan son raina"

Murmushi Farhan tai tace "good night"

"Good night ko, am missing Your body warm and sweet fumes, just want kiss you again"

Duk da matsananciyar kunyar da Sadik ya bata, amma hakan be hana ta jin wata kasala, da kuma jin yadda take missing ɗin sa ba.

Farhan tace "Seda safe, kaga mun fara exams, gobe in Allah ya kaimu da wuri zan tafi makaranta"

Sadik yace "Na sani, bari in zo mu kwanta tare"

Seda Farhan ta buɗe baki jin abunda Sadik ya faɗa, bata san meke damun Sadik yau ba.

"Ya ki kai shiru?"

"To me zance?" Ta faɗa cikin shagwaɓa.

"Ba kya son in tayaki kwanan? Aikuwa tare zamu kwana yau, hug your pillow, you will feel me with you"

Murmushi kawai Farhan take, tana jin sabon salon soyaya a gurin Sadik, duk da yadda yake magana a hankali zaka san a cikin damuwa yake dan a muryarsa kawai taji yadda take ɗauke da damuwa.

"Ba kice komai ba"

"Naji, ka kwanta kai bacci"

'kona kwanta ba na iyawa seda kyar, kinga in da nake kwana kuwa? Haryanzu ban saba ba"

"Zaka saba ne, lumshe idonka in maka addu'a kayi baccin"

Be kai ga lumshe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login