Showing 210001 words to 213000 words out of 259198 words

Chapter 71 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

a nan, na miki alƙawarin za'a kula miki da ita, ko ki zauna a nan se ki kula da ita"

"Shi kuma baban naku waze kulamin da shi?"

Abba yace "ga hadimansa nan da suke hidima da shi, shi kansa Sadik rigima ze sa akan a raba shi da yaron nan, kina ganin fitsarar da yake akan yaron, ba ya kara ko jin kunya sam, in yaso idan tai Arba'in se kuje ƙauye ko sati ɗaya tayi, kuma Hakimi ya ga ɗan jikansa".

Inna tace "ni ba zan zauna a garin nan har kwana Arba'in ba, tana yin sati uku zan tafi"

Da ƙyar Abba ya lallaɓa Inna ta Amince da shi.





"Baban Lilly kana ganin matakin da kale shirin ɗauka akan Yarinyar nan shine daidai? Kayi haƙuri a sasanta ai musu Aure da yaron nan kawai kowa ya huta"

Ya ɗan ɓata fuska yace "hmmm, Amina kenan, haryanzu maza sunan mu kike ji ba ki san suwaye mu ba, kina tunanin za tai daraja ko wani mutunci a idon yaron nan ne? Bayan abunda duk za'aiwa ɗokin ta gama ba shi, har da ciki ana zubarwa kashi kashi, wahala kawai za ta sha, matakin da na yanke akanta shine daidai"

"To shikuma malamin na su ya za kai da shi?"

"Se yai prison wallahi, Allah ma ya rufa masa Asiri, da wallahi duka na so in sa kurata suyi masa, dukan da se sun karya kowace gaɓa ta jikinsa, sannan aje a watsar da shi, zan saki kuɗi se an ɗaure min shi, ɗaurin wulaƙanci aita jan shari'ar se an manta da shi a prison".

"Amma yakamata shima ai masa adalci, yanzu ka gama cewa haryanzu ban san maza ba, duk da yawon da kai a duniya banjin haryanzu ka san menene kaidin mace, Lilly itace musababbin faɗawar yaron nan halaka, dan da bakinta tace da ba ruwansa, yanzu ka sassauta masa, Sannan ka sa a ranka kaima laifukan da ka aikata ne a baya suke bibiyar ka, ko ka manta irin gwagwarmayar da akai a baya?".

Yai ajiyar zuciya Tare da girgiza kai yace "Allah ya yafe mana kawai, amna jibi insha Allah zan wuce da ita can"

"Banji daɗin rabani da Lilly da za kai ba, amma ina fatan hakan ya zama silar shiriyarta".

Baban Lilly ya yanke shawarar kai Lilly gidan wani babban amininsa da ke aiki a Benue shima babban soja ne, ze kaita can ta cigaba da makaranta a can, ƙarƙashin kulawa da tsaro me ƙarfin gaske. Abokin baban Lilly ya santa farin sani, kuma shi ya bawa Baban Lilly shawarar ya kai masa ita can, ta ƙarasa makarantar a can, in ya so ko a cikin sojojin da ke Barrack ɗin ne a samu a aura mata wani, wanda be san Meta aikata ba.



Da safe Abbas yaje har gida yai sallama da Abba, suka gaisa yai masa bayanin mai da Farhan Makaranta da yayi, Abba ya nuna farincikinsa amma yace "ka dena zura jiki gurin ɗawainiya da Yarinyar nan, kasan haryanzu tana ƙasa tana dabo ne, ba ta amsa cewar za ta Aureka ba, kuma kaga haryanzu ba ta dena yawace yawacen da take ba, ka dena ɓarmar kuɗinka akanta"

Abbas yace "bakomai Abba, ko ban Auri Farhan ba, idan Allah yasa ta dena shaye shaye, ta cigaba da karatunta, anci riba sosai, a cigaba da yi mata Addu'a , Allah ya sa ta tsaya tai karatun"

Abba yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, Allah yai maka albarka"

Abba yana shiga gida ya tarar Farhan, ta shirya cikin dogon hijjabi, yai mata nasiha da Addu'oi Sannan ta fita.

Har makarantar Abbas ya kaita, ya danƙata a hannun shugabar makarantar, wadda kusan 'yar uwace gareshi, dan haka tun kan ya kai Farhan yai mata bayanin Komai.

Ta karɓi Farhan hannu bibbiyu, a kai mata interview ta jinjina kaifin ƙwaƙwalwa irin na Farhan tace za ta kaita ss2 kawai.

Abbas ya ja mata kunne akan in an tashi ta jira ze zo ya ɗauketa ta amsa masa da to, sedai tun bayan kaita aji an mata jumping ɗin Class ɗaya, ta tuna romon bakan da Sadik ya dinga yi mata, yai jumping ɗin Class ɗaya shima, saboda ya gama Makaranta ya Aureta, aikuwa maimakon ta maida hankali akan karatu, se kuka haka taita kuka har aka tashi.




Sadik yaji daɗi da ya zamana Nana ba zata tafi ƙauye tai Arba'in ba, ko ba komai jaririnsa ba ze yi nisa da shi ba, dan da sedai ya bisu ayi Arba'in ɗin tare da shi, ko Mother ba ya yiwa kara akan Sahal, wanda yake kira da Junior papa, ko yace masa J papa, kowa so yake ya ɗauke shi, tun yana koke koke har ya saba da jagwalgwalon hannun mutane.

Sadik suka haɗu da Abba a masallaci gurin sallar isha'i, akan hanyar su ta dawowa Abba yake cewa Sadik "yaushe zaka koma Makaranta ne? Na san kun kusa cigaba da lectures"

Sadik yace "Abba ni dai a nemo min transfer, in cigaba da karatuna a Nigeria"

"Saboda me?"

Sadik yace "Abba ka ga baze yuwu in tafi da su Nana ba, a ina zamu dinga barin Sahal in zamu tafi school? Kuma ba na son ya tashi a tsakanin masu raino ne"

Abba yace "hakane, shikenan zan duba in ga me yakamata ayi, amma dai gara ka koma ɗin" haka suka cigaba da hira har zuwa gida.

Suka haɗu da Faruk, Faruk ya dinga yiwa Sadik mitar yayi ɗa ya dena kwanan quarters wai shi me mata, Sadik yai ta murmushi yace "yes call me abu Sahal, wo ni Daddy da ya fara magana zaka ji yana cewa Daddy ina yes my boy"

Faruk yace "eh kuma kai ma a gabansa za'a dinga kiranka boy ba, ana ce mak Autax

Sadik yace "naji bakomai" haka suka cigaba da zolayar juna.

Sadik ya wuce ɗakinsa, yai wanka ya canza kaya, yana son ya fita ya ci Abinci ya je ya ga Nana, ya janyo wata drower, se ga System ɗin sa da yake amfani da ita a Nijeriya, dama be tafi da ita ba a nan ya barta.

Ya sa hannu ya ɗakkota, sedai yana ɗakkota kansa ya sara, gabansa ya faɗi take bugun zuciyarsa ya ƙaru.
Maida system ɗin yai ya ajiye, ya tashi yana layi, ya nufi sashin da Nana take, yai sa'a ba kowa tana zaune tan kallo a ɗakinta.

Zuwa yai ya zube akan cinyarta yana kokawa da numfashi.

A rikice tace "Subhanallah besty menene?"

Ya kamo hannunta ya ɗora akan ƙirjinsa saitin zuciyarsa.

Tai ajiyar zuciya tace "Anya kuwa kana Azkar, bana saka a gaba muyi tare ka dena ko?"

Shiru yai bece komai ba, a hankali ta fara karanto masa duk Addu'ar da ta zo bakinta, sun kai mintun ashirin a haka, ta tsinkaye shi yana ajiyar zuciya alamar yayi bacci.

Inna ce ta shigo ta samesu, Inna tace "Au har ya fara lallaɓowa yana zagayowa, har kin mata wahalar naƙudar kenan, kin shirya yin wata?"

Nana tai mata alamar tai shiru bacci yake, nan ta kwashe komai ta gayawa Inna, yadda yake shiga wannan yanayin tun suna London.

Inna tace "iyayensa ne 'yan boko, yanzu da kace wani abu se su ce su ba haka ba, ba se a zuba musu ido ba"

Nana ta marairaice tace "Inna, kar abi ta tasu, dan Allah ai waya ƙauye, ko in kin koma a dinga yi masa saukar Alqur'ani, da ya fara idan nai masa Addu'a se yai bacci"

Inna tace "to Allah ya kyauta, ba shi kaɗai ba ma, dukkanin ku yakamata ai muku dan neman tsari da kariya daga miyagu, kana da ido bana ganin gari ba".

Kwanci tashi asarar rai, Nana ta kwan Arba'in cif da haihuwa, Sadik kam kwana Arba'in ɗin nan kuwa a takure yayi ta, dan Inna ta kasa ta tsare, ko ɗan shishshsigi ta ga yana yiwa Nana, se ta fara yi masa kwakwazo a cikin mutane, ta kunyata shi.

Anyi shirin tafiyar su Nana ƙauye, se murna take zata yawon Arba'in, dan a ƙalla za tai sati biyu a ƙauye ta ɗan sake ta huta sosai.

Sega Mother da yin rakiya har bakin mota, kamar tace su tafi su a bar mata Sahal, Inna kallon Mother kawai take tana girgiza kai, hadda Sadik za'aje kai su Nana ƙauye, ji yake kamar yace a bar masa ɗan sa a gida.

Se da su ka kai su Nana har can, Hakimi kamar ya maida Sahal cikinsa dan murna, yai ta masa Addu'a da shi da iyayensa. Hakimiya kalli Abba yace "yanzu ka gane dalilin da yasa mu kaiwa ɗanka Aure? Ba muyi dan muna ƙin sa ba, amma ka sani da ba'ai masa Airen nan ba idan lokacin zuwan ɗan nan duniya yai, ko kuna so ko ba kwa so ta halak ko ta haram, se ya zo duniya, zaman Sadik a gidan kawai na ga abubuwa da dama da ku da kuka daɗe da shi ba ku lura ba, ina fatan Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwarsu baki ɗaya" Abba ya amsa da Ameen.

Sadik kuwa yana can yana sallama da Nana yana mita "ina Alla Alla ki Arba'in ɗin nan, mu koma ruwa, kuma kinyi Arba'in an wani ce se kin zo nan kin yi sati biyu haka akeyi?"

Nana tace "kai da wa zaku koma ruwan? Ai ni kuwa da ɗin hakan naji yaseen"

Harararta yai yace "zaki bayani idan nace a nan zan zauna, Allah sarki J papa na ze missing ɗina na san"

Nan tace "To ka tafi da shi mana na huta nima"

"Dan dai babu abun ba shi ne, da da shi zan tafi, ko ki tara masa bokiti bokiti in yai kuka a dinga ba shi"

Nana tace "eh tun da ga Nonon saniya ko?"

Dariya ya dinga yi yace "ba ruwana bani na faɗa ba, ke kika faɗa da bakinki"

Tace "Ali shike nan, dan Allah ka kular min da kanka kaji Besty, ka dinga Azkar yadda yakamata, Tun kan mu taho Inna ta sa ana mana saukar Alqur'ani, Allah ya ye maka damuwar ka, kuma ina ta maka Addu'a"

Yai murmushi yace "Allah yai miki Albarka, insha Allah zan kula Sosai, let me kiss you am missing you"

Murmushi Nana tai, jin takun Inna da maganarta ne ya sa shi cika Nana, ya fita daga ɗakin da sauri, yana jin yadda yake kewar ta Sosai.

Su kai musu sallama suka juya, wanda ba su samu damar zuwa can yi musu barka ba, suka dinga zuwa suna ganin Jaririn Nana, fari sol da shi gashi da cikar suma gwanin sha'awa.


Kwanan su Nana uku da tafiya, Ama Sadik ji yake kamar sun shekara, duk yai kewarsu mussaman ɗan jaririnsa, Mother kanta kullum se tai zancen Sahal.
Faruk ma tuni yai shirinsa ya koma in da yake karatu.

Sadik na kwance akan gadonsa, yana kallon musabaƙar Alqur'ani, shi duk irin wannan ba su dame shi ba, a dalilin Nana yake jin wani wa'azi da sauran su.

Ɗauke wuta a kai, Solar ta kama ya miƙa hannu ya kashe socket ɗin TV, ji yai kamar an yaye masa wani bargo daga kansa.

Kamar an tsikare shi, ya miƙe ya kuma zuwa gaban drower nan, ya ɗakko system ɗin nan ya goge ta, ya jona ta a caji, yana son ya gwada ya ga ko haryanzu tana yi, ya tashi dan ya ɗakko memoryn hotunan sunan Sahal, dan tunda a kai masa copying ɗin sa a jikin memoryn be dub ba, yana cikin dubawa se ga sim cards ɗin sa nan da ya ɗakko a ƙauye.

Ji yai kansa yana sarawa, cikin hanzari ya buɗe wayarsa ya zare layukan cikin wayar, ya saka wannan layukan, ya buɗe system ɗin ya kunnata, kamar me jiran wani abu ya faru haka zuciyarsa tai ta azalzalarsa.

Hoton Farhan ne ya Bayyana a jikin screen ɗin wayar, wanda tun Asali dama hotonta ne a jiki, turus yai yana bin hoton da kallo, wayarsa kuwa wani irin vibrating ta dinga yi, tamkar zatai tsalle sama, saboda Azabar saƙonni da suke shigowa.

Jikinsa ne ya ɗau rawa, ya zubawa screen ɗin ido yana kokawa da zuciyarsa zuwa ƙwaƙwalwarsa akan ya tuna sunanta.

A hankali ya janyo wayarsa dake ta vibrating, ya shiga duba tulin saƙonnin da ke ciki.

"Dan Allah Sadik kai responding in kaga message ɗina, zuciyata tana kewarka, za'a Auramin Sunusi idan ba ka dawo rayuwata ba"

Wani irin jifa yai da wayar, ya ambaci "Farhaaaaaaaaaannn!" Ji yai kamar ya farka daga wani irin nannauyan bacci da ya jima yana yi.

Tashi yai a zabure jikinsa na wata irin tsuma, yai waje ba tare da yasan ina za shi ba!
Kamar wanda ya ga wani abun tsoro, haka Sadik ya fito falo ya nufi hanyar fita, be san ma ina Yakamata yaje ba, kawai tafiya yake, hakan yai daidai da shigowar Usman, ya tunkari Sadik yan faɗin "kai lafiya kake kuwa? Meye haka kake yi ne?"

Idanun Sadik sunyi jawur, be saurari dr. Ba ya fara ƙoƙarin fita, riƙo shi Abbas yai yana faɗin ina zaka haka? Meke damunka?"

"Dan Allah ka cika ni, zuciyata zata tarwatse, ka cikani" Sadik yai maganar a hasale.

Dr. Ya kuma riƙe Sadik yace "meye hakane Sadik" gaba ɗaya ya lura Sadik baya hayyacinsa.

Da ƙarfin tsaya Usman ya janyo Sadik zuwa cikin falo, se fizge fizge yake akan Usman ya ƙyaleshi ya fita.

"Buɗe idonka ka kalleni, meke damunka?" Dr. Yai maganar yana kallon Sadik.

Sadik yace "bakomai, nima na kasa gane meke faruwa dani, Kamar mafarki nake yi, amma shikenan"

Ya juya ya nufi ɗakinsa, ya zube a ƙasa, ya zubawa hoton Farhan ido, yai yai ya tuna dalilin ya sa ya manta da Farhan a duniyarsa.

Ya zubawa hoton ido cikin rauni yace "how comes? How? Farhan ya akai haka ta faru da ni, meya sameni ne? Ko na haukace ne, ya salama anya kuwa nine? Meke damuna ne haka? Ya Allah"
Yai maganar yana dafe kansa, wani irin zafi kansa ya ɗauka jikinsa ya dinga wata irin tsuma.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. 






Kamar wanda ya ga wani abun tsoro, haka Sadik ya fito falo ya nufi hanyar fita, be san ma ina Yakamata yaje ba, kawai tafiya yake, hakan yai daidai da shigowar Usman, ya tunkari Sadik yan faɗin "kai lafiya kake kuwa? Meye haka kake yi ne?"

Idanun Sadik sunyi jawur, be saurari dr. Ba ya fara ƙoƙarin fita, riƙo shi Usman yai yana faɗin ina zaka haka? Meke damunka?"

"Dan Allah ka cika ni, zuciyata zata tarwatse, ka cikani" Sadik yai maganar a hasale.

Dr. Ya kuma riƙe Sadik yace "meye hakane Sadik" gaba ɗaya ya lura Sadik baya hayyacinsa.

Da ƙarfin tsiya Usman ya janyo Sadik zuwa cikin falo, se fizge fizge yake akan Usman ya ƙyaleshi ya fita.

"Buɗe idonka ka kalleni, meke damunka?" Dr. Yai maganar yana kallon Sadik.

Sadik yace "bakomai, nima na kasa gane meke faruwa dani, Kamar mafarki nake yi, amma shikenan"

Ya juya ya nufi ɗakinsa, yana zuwa zube a ƙasa, ya zubawa hoton Farhan ido, yai yai ya tuna dalilin ya sa ya manta da Farhan a duniyarsa amma ya kasa.

Ya zubawa hoton ido cikin rauni yace "how comes? How? Farhan ya akai haka ta faru da ni, meya sameni ne? Ko na haukace ne, ya salam anya kuwa nine? Meke damuna ne haka? Ya Allah"
Yai maganar yana dafe kansa, wani irin zafi kansa ya ɗauka jikinsa ya dinga wata irin tsuma.

Ya koma gefe ya kwanta, ya zubawa laptop ɗin ido, har ta ɗauke gaba ɗaya Sadik ya kasa gane a wace duniyar yake, so yake ya tabattar da gaske Farhan ɗinsa yake gani, ko dai wata duniyar ce take masa gizo.

Ko da akai sallar isha'i a ƙila wa ƙala, yai salla yana tunanin ko dai haukacewa yai, ya kwanta a ƙasa kan tiles yai shiru a haka har bacci ya kwashe shi.

Cikin baccin ba abunda ya dinga mafarki se Farhan tana kuka, da ya tunkari in da take ze rarrasheta se ta fara jifansa da duwatsu.

Haka ya farka firgigit daga baccin da yake, ana ta sallar Asuba ya tashi jiki ba ƙwari, ya shiga yai Alwala yai sallar raka'atanul fajir, sannan yai sallar Asuba wanda duk sanadin Nana yake yin su, ita ta koya masa.

Ya fara karanto azakar, ya idar ya karanta fourty Rabbana da sauran Addu'oin da ya saba yi, wanda duk Nana ce ta koya masa su.

Yai shiru ya tuna rayuwar da yai a ƙauye, da yadda suka dinga communicating, da irin rayuwar da su kai da Farhan, tsananin Soyayya da shaƙuwa da yadda ya cire Sim cards ɗinsa ya bar su a ƙauye, zuwa yadda ya manta da ita da rayuwar da su kai a London da Nana zuwa yanzu, komai ya dawo masa tsaf a kansa.
Zumbur ya miƙe yana faɗin, "Allah yasa ba haukacewa nai ba, meya sameni haka ne?"

Ya koma kan System ɗin da sauri, ya sake buɗe ta hoton Farhan ya sake bayyana a kai.

Ya zuba mata ido yace "Farhan, meyasa kika barni tsawon wannan lokaci kika bar cikin duniyata, na rayu tsawon wannan lokaci ba kya tare da ni, ba ki neme ni baki nemi in da nake ba"

Yana wannan surutan, haka ya shiga cikin gallery ɗin sa, ya duba in da ya tara hotunan ta kala kala, har da na gurin brithday ɗin ta.

Ya sa hannu bibbiyu ya dafe kansa, ya rasa abunda yake masa daɗi ga wata irin sabuwar soyaya da ke cin zuciyarsa game sa Farhan.

Ƙarfe bakwai na safe dai-dai, Sadik ya je ɗakin Mother ya ɗau key, yaje ya ɗau mota ze fita, megadi zeyi Magana amma wata gigitacciyar tsawa da Sadik  yai masa take jiki na rawa ya buɗe masa gate ɗin, ya fafari motar kamar ze tashi sama yai waje.

Tiryan tiryan ya kama hanyar zuwa gidansu Farhan, gari shiru babu kowa se jefi jefi mutane ke gilmawa, yai parking in da yake tsayawa da motar su sha Soyaya, ya ƙare wa gurin kallo, ya fito jiki a sanyaye yana waige waige ya.

Ƙofar gidan su Farhan yaje, ya samu wani dakali ya zauna ya zubawa gidan ido, ji yake tamkar ya tashi ya shiga cikin gidan, saboda wata irin azaba da azalzala da zuciyarsa take masa.

Seda yai kusan awa guda a zaune a gurin, se ga Amir ya fito da shirin sa na zuwa makaranta.

Sadik cikin azama ya tashi yace "Amir, Yaya tana nan kuwa?"

Yaron tsayawa yai yana kallonsa jin ya ambaci sunansa.

Sadik ya sake maimaita masa tambayar, Amir yace "bata nan"

"Ina ta tafi?"

Amir yace "nima ban sani ba"

Sadik ya kalli Amir yace "dan Allah ka gayamin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login