Showing 204001 words to 207000 words out of 259198 words

Chapter 69 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

ne, sannan aje ai siyayyar da ya dace na haihuwa"

"Abba ni ta yaya zan fara wannan tambayar, ni na rasa kunya zanji ko me zanyi," tai maganar tana dafe kanta.

Murmushi kawai Abba yai ya cigaba da abunda yake.

Daga bisani yace "kinga yanzu kince wataƙila ta kusa haihuwa, ki tambayesu kiji, kuma ta dawo ɗakinsa su dinga kwana tare, dan na sh ganinsa yana sanɗa daga ɗakinta, ki ɗauke kanki akan su, da da hali gida zan ba su su koma su zauna, amma ban san yadda cigaba da karatunsu ze yuwu ba, kuma ba abun ince su koma BQ ba, ban san yadda haihuwar zata zo mata ba, kinga daga shi har ita ba me wani hankalin kirki.

Ajiyar zuciya kawai Mother Tai, amma bakinta ya gaza furta komai.

A waya ta kira Sadik tace ya sameta a ɗakinta, be daɗe ba se gashi yaje, sedai shi kansa Kunyar Mother yake ji.

Tun da ya shigo take binsa da kallo tana ƙare masa kallo Daga sama har ƙasa, ya nemi guri ya zauna.

"Sannu ko" Mother ta faɗa tana kallonsa, yai shiru tare da sunkuyar da kai.

"Ka bani mamaki Sadik, ina ta ɓaɓatu akan an maka auren wuri, Auren dole se gashi ka kunyata ni, so as you are you can impregnent a lady?"

Tsuke Fuskar sa yai a ransa yana faɗin 'wannnan wace irin magana ce Mother'

"Wai ni garin yaya ma a kai haka ta faru Sadik? Gaba ɗaya ka shammaceni"

"Mother dan Allah, ni Wallahi gaba ɗaya kin sani a kwana in ba so kike in gaya miki komai ba, dan Allah ni dai kiyi haƙuri ki manta da zancen nan"

"A'a nina isa in tambayeka yadda abu ya faru, Allah ya kyauta amma ka kunyatani, haryanzu ƙanƙantar ka nake gani Sadik"

Sadik ya sunkuyar da kai ya ƙi Magana.

"Hmm, cikin nata wata nawa ne?"

"Tara" ya bata amsa.

"Kuma shine da kuka dawo baku faɗa ba, balle a sa ran kaita Asibiti"

Yace "munje ɗazu da ba kya nan, an mata scanning da booking na komai da komai na masu ciki, sunce da ta fara naƙuda aje Asibiti"

"Ikon Allah, ashe har Asibiti kuka je, hmm aishi kenan, se batun siyayyar haihuwa, ko baka san anayi ba, cikin kawai ka iya"

Sadik yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un"

"Ni kake jawa wannan innalillahi dan ubanka"

Cikin shagwaɓa yace "Mother ni wallahi na rasa me ma zance, dan Allah ki dena wannan maganar, munyi siyayyar mu tun a can"

"Ina abunda kuka siyo ɗin?"

Sadik yace "Suna ɗakinta"

Mother ta sa shi a gaba zuwa ɗakin Nana, Nana duk tai wuri wuri da ido.

Sadik ya kalli Nana yace "Ina Akwatunan nan, da mu ka sai kayan babies?"

Nana ta nuna masa in da Akwatunan suke, Sadik ya ɗakko ya ajiyewa Mother a gabanta, ta bubbuɗe sun sai komai, hatta net ɗin jariri sun siya, abun shanya da kayan robobi ne kawai babu.

Mother tace "kai waya nuna muku duk wannan kayan ake siya?"

Nana ta kalli Sadik, dan ko da sukaje siyayyar ku san shi ya sai komai.

Yace "a waya nai browsing"

Mother ta sasu a gaba tana ƙare musu kallo, ta rasa murnar samun jika za tai a'a ko kuwa, idan ta kalli Fuskar Nana gaba ɗaya tausayi take bata, tana tausaya mata idan labor ya zo, kuma se Yanzu ta lura Ashe tun da suka dawo a hankali take tafiya, bata abubuwa da kuzari sam hankalin Mother be kai kansu ba.

Mother tace "to seka tattara mata kayanta, ku koma ɗakinka saboda ko da wani abu ze taso cikin dare, kar a barta ita kaɗai, sannan ka bani result ɗin teses ɗin da a kai mata, zan haɗa Akwati a shirya mata kayan haihuwa, dan zata iya haihuwa a Kowane lokaci.

Sadik yaji daɗin yadda Mother ta nuna kulawarta akan Nana.

Haka kuwa akayi, Sadik cikin ɗoki da murna ya kwashe kayan Nana zuwa ɗakinsa da ke cikin falon.






Abbas yai ƙuri da ido yana kallon Farhan da ke cikin motarsa, tana ta dannan wayarta.
"Waya ta fini mahimmanci ko Farhan"
Ta ajiye wayar tace "Ni na isa ince haka, Tuba nake ranka ya daɗe"

Yai murmushi tare da shafar ƙasumbarsa yace "Farhan, ashe an rufe Makarantar ku?"

Tace "Eh, na gani a news, dama ai ta cancanci a rufeta, da za'a bi shawarata ma ƙoneta yakamata ayi"

"Meyasa?"

"Saboda makarantar nan tayi silar rusa rayuwar matasan yara da yawa irina, koma me ya faru da ni makarantar nan ce sila, malamin da abun ya faru akansa, yayi iya yin sa ya rabani da Sadik, yana akrar dani RUƊIN ƘURUCIYA ne yasa muke soyayya amma na ƙi yadda, laifinsa ɗaya ya dinga aibata mu da miyagun maganganu ni da Sadik, se shi kuma Allah ya sa ya faɗa tarkon RUƊIN ƘURUCIYA"

Abbas yace "Yasalam, abu be daɗi ba, Allah ya tsare ya kiyaye, yanzu in Allah ya kaimu ranar Monday, zan zo in ɗauke ki muje makarantar da zan sa ki, ina son su kai ki ss2 ne, da kin fara se azo ai maganar Aurenmu ko beuty na?"

Haɗe rai tai ta tura baki, yace "laifin me kuma nayi?"

Tace "ni gaskiya na gama boko a rayuwata, ba zan sake ba"

"Yanzu wannan dalilin ze sa ki zaɓi dena makaranta, ki hana al'umma amfanuwa da baiwar da Allah yai miki?"

"Ni gaskiya ba zani ba" tai maganar a hankali tare da jingina da seat ɗin Motar.

"Dan Allah ayi haƙuri a temakawa marayan Allah a koma makaranta, ko dan saboda feature kids ɗin da zamu haifa"

Shiru tai masa taƙi magana, ya kira sunanta amma tai shiru, kamo hannunta yai cikin nasa yana murzawa a hankali, yana cigaba da kiran sunanta.

"Sadik dan Allah ka bar.... Se kuma tai shiru.

"Sadik kuma? Believe me haryanzu kina son Sadik, ina kishin ki fa ki dena kiran sunansa a gabana"

"Dan Allah kayi haƙuri, wallahi bana son Sadik yanzu, haka kurum se jikina ya dinga bani yana daf dani, ko kuna kamar muna tare, amma na san sharrin ƙwayoyin da nake sha ne, amma ba zan kuna ba insha Allah kar kai fushi kaji Doctor, ba ka fushi fa"

Tai maganar tana leƙa fuskar sa.

"Ina fushi mana, in dai za'a taɓaki Dole in yi fushi, kuma ni na mayi fushin am jealous"

Ta marairaice murya tace "Ohh God am sorry please, na dena ba zan kuma ba ka dena fushi kaji Doctor"

"To shikenan na dena, dan Allah ki kwana a gida yau kinji"

"Insha Allah a gida zan kwana, na maka alƙawarin yau ba in da zani"

"Shikenan, good night za muyi waya kan in shiga gida"

Dariya Farhan tai tace "Mijin tace, in ba tsoro ba mutum ya bari se ya shiga gida muyi wayar mana"

Dariya yai yana sosa kai, Farhan ta fice daga motar.


Yai reverse ya koma ƙofar gidan Hajiyarsa yai parking ɗin motarsa, ya sakko ya shiga gidan.

Ya tarar da Hajiya na kallon Sunna TV, yai sallama ta ɗago ta amsa masa, ya nemi guri ya zauna yace "Barka da Yamma Hajiya"

"Yawwa barka, daga ina kake haka?"

Ya ɗan sosa kai yace "daga Asibiti"

"Ni na kasa gane wannan sintirin da kake min a gida, tun da ka dawo kusan kullum kana layin nan, ka gayamin gaskiya me kake zuwa yi ne?"

"Hajiya bakomai fa, ba abunda nake zuwa yi"

"To ya akai se yanzu ka shigo, bayan tun ɗazu naji ƙarar motarka ka wuce"

Ƙuuu cikinsa yai ƙara, yai wuri wuri da ido.

Hajiya tace "daa gurin Farhan kake ko?"

Yai Shiru ya sunkuyar da kai.

"Abbas, tun kan ka tafi na gane son Yarinyar nan kake, ni kaina na maka sha'awar Aurenta a da, amma yanzu ba ka ga yadda ta koma ba?"

Ya ɗan marairaice yace "Hajiya, a ganina Farhan za'a iya taimaka mata ta gyara Rayuwar ta, saboda na san bakin zaren matsalar ta, kuma Insha Allah ina tunanin zan iya taimaka mata, idan aka ƙyaleta Rayuwar ta zata cigaba da lalacewa, dan Allah ki bari in Aureta"

Hajiya ta numfasa tace "tun kan ka fara tausayinta nake jin tausayin ta, se dai ni ba irin iyayen nan ce masu kafiya ba, dan ban san yadda Allah ze da tawa zuriyar ba, ba ka da matsala daga gareni, amma ka san dangin mahaifinka ba za su amince ba, dan dole se sunyi bincike akanta kan su yadda su nema maka Aurenta"

Abbas ya sharce gumi, dan ya san dangin mahaifinsu ba ƙanan masifaffu bane ga su da kafiyar tsiya, ko da mahaifinsu ba ya raye, a tsaye suke a kansu, ya san ba zasu amince ba, dan za'a kai ruwa rana sosai, mussaman da matar da yake Aure, daga ɓangaren su aka haɗa su.

Hajiya tace "kaje kai ta Addu'a, Allah ya zaɓa abunda yafi Alkhairi"

Ya amsa da Ameen Sannan yai shiru ya cigaba tunani.






Haladu ne ya shigo ya tarar da Sunusi yana ta zazzage wata 'yar ƙaramar jaka, Haladu yace "ya dai me kake nema ne?"

Sunusi yace "wani aiki zazzafan aiki zanyi ne"

"Allah mutumina, wane irin aiki kenan kuma wa za kaiwa aikin? Nasan an shaƙa maka kuɗi"

Sunusi yace "ba wani zanwa ba se Yarinyar nan Farhan da wannan shegen me motar"

Haladu yace "wannan karon me kuma tai maka?"

Sunusi yace "ni zata kalla tana gayawa baƙaƙen maganganu, kuma naga wannan ɗan Gidan matar can ya dage, dan haka dole inyi wani abu a kai"

"Haba Sunusi, wallahi yakamata ka bar Yarinyar nan ta huta haka, wallahi ka cutar da ita da yawa, ka rabata da masoyinta duk ta zama wata iri"

"Kaga ba ruwanka, yadda suka min wulaƙanci suka hanani ita Ranar ɗaurin Aure, se baƙincikinta ya kashe su, babu me Aurenta, dani suke zancen"

"Amma Sunusi yakamata....." "Kaga Haladu ka samun ido kawai, ka ƙyaleni"

Haladu yace "shikenan, daɗinta dai shi Allah ba Azzalumin sarki bane"
Sunusi yai masa Shiru, ya tattara jakarsa ya fice.

Haladu yai shiru yana nazari, gaba ɗaya tausayin Farhan yake, Sunusi ya cutar da ita sosai da sosai.








Khairat ta shigo falo ta tarar da Mother zaune, da uban kaya a gabanta, Khairat tace "Mother me zaki da kayan jego?"

"Hmm jika zan ɗauka"

"Jika kamar yaya?"

"Matar Sadik ce ta kusa haihuwa"

Zaro ido Khairat tai tace "wai wannan Yarinyar?"

"Ita fa tsohon ciki ne da ita"

Khairat tace "turƙashi, ke kina nan kina fafutukar raba Aure ashe kallonki kawai suke?"

"Kema dai kya faɗa, ni duk kaina ya kwance" haka suka gaba da jajanta lamarin.

Mother tayo siyayya abunda ya rage ba su siya ba, tana yi tana sake cika da Mamaki, wai Sadik za'aiwa haihuwa.



Duk da halin da Nana ke ciki na wannan tsohon ciki, Sadik yaji daɗin dawowar ta ɗakinsa, ɓangaren Nana kuwa ba ta so wannan haɗen ba, dan Sadik akwai takura, seda ta samu yai bacci, ita kuma ta kasa baccin gaba ɗaya ta tashi ta koma falo.
Cikin dare Mother ta fito ɗaukar ruwa, ta tarar da Nana a zaune a babban falo se juyi take akan kujera.
"Ke lafiya kuwa?" Mother tai maganar tana ƙarasowa cikin falon.

Nana ta miƙe zaune a hankali tace "bakomai"

"To me kike a zaune a falo haka?"

"Na kasa bacci ne"

"Ko kina jin wani ciwo ne?"

Nana ta girgiza kai alamar a'a.

"Ina Sadik ɗin?"

"Yayi bacci"

Mother ta wuce ɗakin na su, ta tarar da Sadik ya baje yana ta bacci.

Ɗala masa duka tai ya tashi a gigice yana mutsutsuke ido tace "ka bar 'yar mutane na fama, kai kana nan kana bacci, se ka tashi kaje kaji me take buƙata"
Sadik yai miƙa ya sakko daga kan gadon, ya fito falo, ya tarar da Nana a zaune akan kujera, Kamar za tai kuka.

"Friend lafiya kike kuwa?"

"Lafiya ƙalau" ta bashi amsa.
Mother kuwa wucewa tai part ɗinta ta barsu.

Sadik yace "ko Asibiti zamu tafi?" Tace "A'a"

"To menene?" Ya faɗa cikin kulawa.

"Na kasa bacci, duk na gaji, ko ina na jikina ciwo yake cikin nan ya min nauyi, na rasa ta yadda zan kwanta inji daɗi, gashi abincin da na ci ya tsaya a ƙirjina yaƙi wucewa kuma na kasa amayar da shi" tai maganar hawaye na zubo mata.

Sadik yace "shikenan na gane, zo muje ɗaki nai miki tausa ko zaki iya baccin"

Tai saurin girgiza kai tace 'kaje ka kwanta ka barni a nan"

"A'a ba za'ai haka ba" ya zauna yana mammatsa mata ƙafafunta, se hamma yake yi kamar ze ci babu.

Nana tace "zo ka kwanta, naga kana jin bacci" ba musu yai kwanciyarsa a kan cinyarta yana baccin sa.

Ita kuwa Nana, naƙuda ta fara ba ta sani ba, dan a hankali yake tsira mata, se taji mararta ta ɗaure amma ta daure.

Se gefin Asuba ciwon ya lafa mata, bacci ya kwashe ta, Abba ya ci karo da su Nana a falo, Sadik ya kwanta a cinyar ta yana baccinsa, ita kuma ta jingina da kujera tana baccinta.

Abba ya koma ya kira Mother, yace "kizo ki tashi ɗanki"

Mother da ta fito ta gansu tace "yanzu da haka za'a raini ɗan idan an haife shi, kai Sadik, Sadik" a firgice suka farka gaba ɗaya, Kunya ta lulluɓe Nana, Abba ya fice kamar be ga Komai ba.

Gaba ɗaya wunin ranar Nana haka tayi shi babu daɗi sam, daurewa kawai take, amma tana jin ciwo kaɗan kaɗan, Mother kuwa ita yanzu Nana ce take bata tausayi, saboda abunda take tunkara, wato naƙuda ga nauyin ciki duk se haƙuri.

Seda Nana ta jera kwana tana ciwo a tsaye, Mother tace Nana ta koma ɓangarenta ta dinga kwana, Nana tai matuƙar mamaki dan rabonta da shiga sashin Mother, tun bikin dr. Da ta shiga aka korota.

Tace su kwana tare da Khairat a ɗakinta da ke cikin sashen Mother, Nana tace ita a ƙasa zata kwanta ba ta jin daɗin kwanciyar Kan gado.

Khairat ko kallon kirki ba taiwa Nana ba, dan haushin Nanan take ji.

Cikin dare Khairat ta dinga jin nishi, ta farka ta kunna wayarta, taga Nana ta haɗa gumi se salati take tana kiran sunan Inna.

Da sauri Khairat ta kira Mother, ta sanar mata da halin da Nana ke ciki, aikuwa Mother ta taso cikin magagin bacci.

A daren suka sa Nana a mota zuwa Asibiti, sedai aka duba akace haihuwa ce Amma da saura.

Sadik yana can yana bacci be san budurin da ake ba, se da Safe ya samu labari, ya shirya ya tafi Asibitin.

Sadik duk a zatonsa haihuwar ba wahala, yaje ya tarar da Nana a zaune, fuskarta duk tai wani iri, gumi kawai take.

Yace "wai haryanzu baki haihun ba?" Ji tai kamar ta kife Sadik da mari, dan a yanzu hausinsa take ji, dan duk shi ya sata a wannan bala'in.

Yace bari yaje gida ya ɗakko ruwan tofin da suka zo da shi daga ƙauye.

Harya koma gida ya dawo Nana na cikin jazabar labor, kuma ance haihuwa da saura, Mother ce a gurinta se sannu take mata.

Ko da Sadik ya kawo tofin nan Nana ta sha, tamkar an tunkuɗo ciwon, ta gigice gaba ɗaya, aka shiga da ita labor room, Sadik ya zata ana shiga da ita za'ace ta haihu, amma abu shiru.

Abba ma da kansa ya zo Asibitin, amma Nana babu labari, nan Sadik jikinsa ya fara sanyi, dan be zaci abun ya ka haka ba.

Gashi an hana kowa shiga gurin Nana, suna nan tsaye Nurses suka kira likitar da take duta akan tazo ta duba Nana, dan sun kasa gane kan labor ɗin na ta, kamar ba ya progressing, Sadik ya faki idon Mother ya shige ciki shima.

Yaje ya tarar da Nana ta fita hayyacinta, ga fanka amma kamar an jiƙata da ruwa, ga wata a gefe tana danna cikin Nana, wata na ƙoƙarin yadda za'ai kan ɗan ya fito, ga Nurse ɗin riƙe da forcep zata bata tear.

Ai gigice ya ƙarasa ya ture Nurse ɗin, idanunsa su kai ja yace "wace irin mara imani ce ke? Ya zaki sa mata wannan ƙarafan a jiki" ya ɗago Nana da zuwa yanzu ta fara galabaita, idanunta sunyi ƙanana saboda Azabar ciwo.

"Nana, buɗe idonki kina ganina?" Yai maganar yana girgiza ta.

"Sadik mutuwa zanyi, ba zan iya haihuwa ba, na gaji ba zan iya ba, ka yafemin"

"No, ba zaki mutu ba Nana, zaki haihu lafiya Insha Allah"

Likitar ta fita tana faɗa akan dan me Sadik ze shiga ɗakin haihuwa ze han su aikinsu, shi kuwa ya rirriƙeta se hawaye, saboda ya tausaya mata, be taɓa tunanin Azabar labor ta kai haka ba.

Usman ne yace "Doctor dan Allah kiyi haƙuri, mijinta ne bakiga duk yara ne ba, ba hankali kiyi haƙuri"

Ta zaro ido tace "mijinta? Amma gashi na ganku manyan mutane wayayyu, akaiwa yara Auren wuri haka mussaman ita"

Mother tace "doctor, yanzu ba lokaci ne na tattauna wannan magana ba, ya ake ciki?"

"Eh to, ta samu prolonged labor, aiki za'ayi a cire babyn, kuje a biya kuɗin nan da ƙarfe goma insha Allah surgical team ɗin za su iso, ayi mata aiki"

Da ƙyar aka ɓanɓaro Sadik aka fito da shi daga ɗakin, sedai yana fitowa yaji ance aiki za'ai ya kuma gigicewa, ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro.


Usman yace "wai kai wannan wane irin shirme kake, kai da zaka bata ƙwarin gwiwa"

Abba yace "de na yi masa faɗa, ka kwantar da hankalinka auta na, insha Allah Lafiya ƙalau za'ai mata aikin a fito da ita"

Se da Sadik ya bawa Mother haushi, yadda yake kuka Kamar wani yaro, rabon da ta ga yai kuka har ta manta, amma shine yake kuka haka, Hakan ya tabattar mata da cewa yana son Nana kenan.

Jidda kanta da ba ita ke naƙudar ba, ta shiga tashin hankali nesa ba kusa ba.

Ana ta shirin shigar da Nana tiyata, tana ta ambaton Allah, dan sam ta dena jin nishin ma gaba ɗaya, ƙarfinta ya gama ƙarewa, cikin ikon Allah tai wani yunƙuri sega sankacecen jariri ƙato ya fito gaba ɗaya tare da mabiyiya.

Nurse ɗin tace "Alhamdilillah ala kulli halin, sannu kinji"

Nana ta lumshe ido kawai, saboda wani sanyi da ya dinga ratsata, ta ƙudurce a ranta ita da haihuwa har abada, Auren ma ta haƙura dan wannan Azabar da ta sha yau, ba ta san ya zata kamanta ta ba, tun da ta ɗau cikin nan take wahala har zuwa haihuwa, Nurse ɗin ta yanke cibiya, ta ɗagowa Nana jaririn tace "kalli me kika haifa?"

Nana tace "ke dan Allah ƙyaleni, haba wannan wahala haka, Allah ka jiƙan Mamana, Allah duk wata uwa ka sata a Aljanna, wanda ba su haifa ba Allah ka basu, ka shirya al'ummar Musulmi"
Ta ƙarasa Addu'ar tana hawayen wahala.

Sosai ta bawa Nurse ɗin dariya, aka gama gyara jaririn aka zo ɗinki, Nana tace Allah kar ta baza'a kuma gana mata wata Azabar ba.

Sadik kuwa tuni aka sanar musu ta haihu, Sadik ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login