Showing 207001 words to 210000 words out of 259198 words
Chapter 70 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
dinga murna, dan dama Addu'a yake tayi kar ai mata aikin, ba ya son a yanka mata jiki.
Nurse ɗin ta kalli Nana tace "kinga in baki tsaya anyi ba, nan gaba da kansa ze sako ki gaba ya zo a ɗin ke ki, ki nutsu ayi"
Nana tace "taɓ waya gaya miki zan koma, ai bani ba Aure na gama dama ban isa Auren ba"
Tai dariya tace "Yarinya man kaza, ƙil nan da wata taran zaki dawo mana haihuwa ta biyu"
"Wallahi Allah ya kiyaye, ba dai ni ba"
Da ƙyar ta tsaya akai ɗinkin, ta gyara jikinta, akace ta bawa yaron Nono ama tace me za ta bashi, ba su kai girman yadda ake shayarwa ba, sedai in magani za'a bata su ƙara girma" haka Nana tai ta shirme suna mata dariya.
Kan ace su shigo tuni Oga Sadik ya zura kai ɗakin, ya ƙarasa gaban gadonta da Sauri ya rungumota yana "Sannu Besty na, sannu My Asma"
Tura baki tai taƙi kallonsa, "Sannu kin sha wahala na tausaya miki Sosai"
Tace "Ashe dai ba ka son in mutu, harda kuka" tai maganar tana masa dariya.
Yace "Kuka nake karki mutu, alhalin ki na wa miji rashin Kunya, wallahi ban san haka haihuwa take ba Nana"
"Hmm ai ba zan ƙara ba, daga wannan ɗan ba zan kuma haihuwa ba"
Murmushi yai ya miƙe, ya nufi in da aka kwantar da jaririn ya ɗakko shi yana cewa "Alhamdilillah, yanzu wannan namu ne Husna"
Nana tace "gashi nan da ƙaton kai kamar na babansa ba, ya ban wahala"
Sadik yace "wallahi bani da ƙaton kai, se kuma bakinsa irin na babarsa na tsiwa ba"
Nurse ta shigo tace "Ikon Allah, waye yace ka shigo ne?"
"Se ance in shigo ni da ɗa na da matata"
Tace "lallai kam"
Su Abba suka shigo tare da Mother, Sadik ya miƙe yana murmushi, ya danƙawa Abba jaririn, yana faɗin "Abba kalleshi, kamar mu ɗaya da shi ko?"
Abba yace "sosai makuwa"
Usman yace "Wai kai ba ka da kunya ne?"
Sadik yace "wace kunya, tunda Allah yayi ya zo duniya"
Nan da nan aka shiga buge bugen waya, Inna ta rasa in da zata sa kanta dan murna, a ranar tace a aika mota a ɗakkota.
Asibiti ya cika da jama'a, se zolayar su Sadik ake, wai yaran Iyaye.
Awan Nana shida a Asibiti bayan ta haihu aka sallame ta, sedai mursisi ta ƙi shayar da yaron, wai me ze sha.
Da labari ya samu Faruk ma, a ranar ya fara shirye-shiryen yadda ze dawo Nigeria, sun samu jariri a familyn, bayan shafe tsawon lokaci ba ai haihuwa ba, kasamcewar danginsu ba masu yawan haihuwa ba.
Mother ta riƙe jariri gam, Kamar ta haɗiye shi, saboda tana matuƙar ƙaunar yara.
Inna ta taho da kayayyakin ta da akewa mai jego, se da Inna ta zo ta sa Nana a gaba, sannan tai ƙoƙarin shayar da shi, shime da ya fara sha se ta sa kuka tace ita zafi.
Shi kuma Sadik da ya ɗan fita aka jima se ya dawo, ya shiga cikin 'yan barka ya karɓe ɗansa ya zauna yana kallonsa.
Inna tace "Yau naga abunda ya isheni, za'aga shiririta agun wannan sakarkarun iyayen".
Idan Sunusi baya nan, Haladu se yai ta bincike masa kaya, ko Allah ze sa ya gano wane irin Asiri yaiwa Farhan, Sunusi ya na ɗan taɓa harkar tsubbu, ya sa a ransa cewa duk yadda ze zeyi dan ya taimaki rayuwar Farhan da Sunusi ya tarwatsa.
Tana zaune a gurin cin Abinci ita da Alhajinta, da yake kashe mata kuɗi, yana ɗan duba wayarsa yace "Farhan, kalli wasu young couples, kina cewa wai ke baki isa Aure ba, kin ƙi yadda muyi Aure, ko ki bani haɗin kai mu huta, kalli wannan young couples ɗin, sun haihu"
Ta sa hannu ta karɓi wayar tana kallon screen ɗin wayar, a Instagram ne, hoton Nana da Sadik sun haɗa kai suna murmushi, gefe an saka hoton jaririn.
Take Jikin Farhan ya kama rawa, yawun da take ƙoƙarin haɗiya ya kasa wucewa, take ta saki wayar ta fara tari!.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Tari ne ya sarƙe Farhan, ya shiga jera mata sannu, sedai a sannun nasa ko ɗaya ba ta amsa ba, ta miƙe ta ɗau jakarta tai hanyar fita, ko gabanta ba ta gani sosai tafiya kawai take.
Bayanta ya biyo yana kiran sunanta, amma ba ta saurare shi ba, ta tari abun hawa ta shige, suna tafe tana kuka, kuka me tsuma zuciya, me Napep ɗin yana ta cewa Baiwar Allah kiyi haƙuri, ki sassauta kukan nan dan Allah.
Ko saurarensa ba tai ba ta cigaba da rera kukanta.
Suna zuwa gida ƙofar gidansu, ta cillawa me Napep ɗin dubu ɗaya ta shige gida, a ɗakinta ta tsaya ta rufe ƙofa ta sa sakata, ta zube a gurin ta dinga kuka, kamar zuciyarta zata tsaga ƙirjinta ta fito.
Allah ya temake ta gidan ba kowa balle a rarrashe ta, ta rasa wace irin Soyayya da shaƙuwsce haka tsakanin ta da Sadik, ta kasa mantawa da shi, ta kasa rufe babinsa daga rayuwar ta, yayi Aurensa har an haifa masa ɗa, ita kuwa tana nan tana gararamba a titi, ba Auren ba karatu sema lalacewa.
Ta sake fashewa da kuka, ga Wani irin kishinsa da ya dinga taso mata, ya haɗa jikinsa da wata, bayan ta riga ta yadda da shi, shine namiji na farko da ta amince ta haɗa jikinta na sa.
Ji tai wani irin abu yana taso mata daga zuciyarta, ga wani irin ciwon kai da ya addabe ta, ta watso kayan drower ɗinta, ta ɗau wata kwalba, ta shanye abunda ke ciki tas, ta jefar da kwalbar ta kife kan katifarta tana cigaba da zubda hawaye.
"Sadik ka Cutar dani, cutarwa mafi muni, ka rusa rayuwata da ban sanka ba da ba lallai wannan abubuwan su faru da ni ba, nayi dana sanin saninka, ba zan maka Allah ya isa ba, ba zan iya ba, Allah ya dawwamar da kai a cikin farinciki ni kuma ya bani mafita" ta ƙarasa maganar cike da rauni.
Tana jin yadda zuciyar ta keta tafasa, ga wayarta se ringing take, amma ta kasa ko da motsa yatsanta ne, saboda maganin da ta sha ya fara aiki a jikinta, wani irin bacci ya fara fizgarta.
Da yawa mutane ba su san Sadik yai Aure ba, se labarin haihuwa suka ji, ga yaron Kamar Sadik yai kaki ya ajiye, kamarsa ɗaya da Sadik sosai da sosai.
Kwanansu uku da haihuwa, Faruk ya iso Nigeria, cike da ɗokin ganin ɗan Sadik, Sadik kamar su cinye juna shi da Faruk, gidan aka rasa wanda yafi wani ƙaunar jaririn nan, hatta Khairat rawar kai take akan jairin nan.
Se jaririn nan yaita kuka, Nana tai mursisi kamar bata san yanayi ba.
Sadik ya shigo ya tarar da Mummyn Khairat taiwa jaririn wanka, se rarrashin sa take amma se tsala kuka yake.
Sadik yace "Mummy ba yunwa yake ji ba kuwa?"
Mummy tace "to ai uwar ta sa ce se a hankali, ina ga Madara yakamata a nemowa yaron nan a dinga haɗa masa da ita"
Sadik yace "kawo shi" ya karɓe ɗansa ya saɓa shi a kafaɗa, yana shafa bayansa ya nufi ɗakin sa Nana take.
Ta harɗe ƙafa tana shan shayi da farfesun kaza.
Sadik yace "Friend meyasa kike haka ne? Yaro se kuka yake amma ke kina nan kina cin Abincin ki, shi kuma ko oho?"
"To ni ya zan masa, shikenan ni ba zanci Abinci ba?"
"A'a waye yace karki ci Abinci? Amma shima seki ba shi nasa"
"Dan ba ka san zafin da nake ji ba ko? To ka ba shi naka ya sha, shikenan da na motsa ko a cikin mutane ne sai ya ta kuka"
Sadik yace "to yanzu ai ba a cikin mutane bane, dan Allah ki karɓe shi ki bashi"
Ta ƙara tura baki tana tauna bredinta.
"So kike ya mutu da yunwa?"
Ta zazzare ido tace "ya mutu kuma?"
"Eh mana, kalli yadda yake kuka fa, anya kina son sa?"
Nana tace "wallahi ina son shi sosai, zafi nake ji sosai in zan Shayar da shi, tun daga ciki har raino duk ba sauƙi friend"
Sadik ya gyara zamansa yace "ai duk aikin lada babu sauƙi, a cikin sa yanzu dai daure ki karɓe shi,"
Ta sa hannu ta karɓe shi, ta fara ƙoƙarin Shayar da shi, sedai yadda take rintse idonta, zaka gane tabbas da gaske take zafi take ji.
Sadik ya zuba mata ido cike da tausaywa, gaba ɗaya lamarin babu me sauƙi, yace "Sannu" tace "yawwa"
Yana tsaka da sha, Nana ta tsige shi ta miƙawa Sadik shi tace "karɓe shi na gaji wallahi"
"Haba Nana, be ƙoshi ba fa"
"Kar ka kuma cemin Nana" tai maganar tana zumɓura baki.
"To naji, amma kinga fa kuka yake, Allah Sarki babyna, yi haƙuri ita ma maman naka ba'a daɗe da yayeta ba, shiyasa take baka wahala"
Inna ce ta shigo tana ƙwalawa Nana kira "ke ki taso ga ruwa can an kai banɗaki"
Nana ta ɗora hannu a ka tace "Na shiga uku, daga wannan se wancan, wallahi wankan nan da zafi dan Allah ku min rai"
Inna tace "yau naga shashasha, in ba'ai wankan ba so kike ki lalaltaccen jego? Kaikuma kasa ta a gaba, da ɗa hannu yana faman kuka, ka bata shi mana"
Sadik yace "Ai yanzu ta bani shi, bari in kaiwa Mother shi ta goya shi ko ze bacci"
Inna tace "A'a wataƙila yunwa yake ji, ki karɓe shi"
Sadik yace "A'a Inna, ƙyaleshi Kawai, amma dan Allah wankan a bari ruwan ya huce, naji tana cewa yai mata zafi da yawa"
Inna tace "jimin ɗa da feleƙe, ni tafi ka bani guri, ke kuma zaki ta so ko sena zo na janyo ki?"
Haka Nana ta taso, tana ta zubar da hawaye, ta wuce akai wankan nan.
Sosai Mother ke shiri akan taron Suna da za'ai abun har mamaki yake bawa Inna, ba Inna ba hatta Nana abun mamaki yake bata.
Katin gayyata na Online da na bugawa, anyi Nana ba ta san adadin su ba.
Daga haihuwar zuwa yanzu kuwa, 'yan barka kawai sun tarawa Nana sha tara ta arziki, dan ma wani abun Mother ake bawa, kowa yai sallama da abunda ze kawo.
Kayan fitar Suna kuwa, lefe da ba'aiwa Nana ba, shi Abba ya saka ai mata, kaya na gani na faɗa.
Gefe guda Jairi na ta shan wuya a gurin yarinyar uwarsa, tana son yaron amma idan ya isheta da kuka, zama take ta taya shi kukan, idan yaa isheta da tsotso ma haka take dire shi, ta cigaba da sabgogin ta, ai tai mata faɗa amma ko a jikinta, ba abunda yake bata haushi irin cikin dare yaita tsala kuka, Kamar ana cire masa ido, ta juya ta shige bargo ta bar mutan gidan da rarrashin sa.
Har magariba sannan Farhan ta farka daga mayen da take, tai alwala ta rama sallolin da ba tai ba, tana kwance a ɗakinta Amir yai sallama yace "Yaya, Doctor yana sallama da ke"
"Kaje ka ce masa ba zan zo ba"
Mamaki ya kama Amir, ze yi Magana amma tai masa tsawa tace "kace ba zan zo ba"
Yaron yaji maganar tai nauyi yaje ya gayawa Doctor, dan haka ya wuce yaje ya gayawa Abba abunda Farhan tace.
Abba ya tashi da kansa ya je har ƙofar ɗakin Farhan ya ƙwanƙwasa, amma tai shiru.
Ya ɗaga labulen, amma kasancewar da wuta ya ga fuskarta a kumbure, ta dunƙule guri ɗaya.
"Meya sameki ne haka? Kukan me kike? Har kika ce acewa yaron nan ba zaki zo ba?"
Aikuwa ta kuma fashewa da kuka tace "Abba, da yawa maza ba sa tsoron Allah, Ba zan Auri Doctor ba dan Allah ni a ƙyaleni, wallahi Abba na gaji da Komai gani nake kamar a duniya ni ka ɗai aka tsana"
Abba ya ƙarasa cikin ɗakin ya zauna a kusa da ita yace 'ki dena irin wannan maganar, Allah ya jarrabi dubunki da abunda ya ninninka naki, ki godewa Allah ya baki rai ya baki lafiya, ki dena wannan maganar"
Gaba ɗaya ta manta tare da Abba take magana, neman in da zata amayar da abunda ke ranta kawai take, cikin kuka tace "Yayi Aure fa Abba, har an masa haihuwa"
"Shi wa?" Abba ya tambaya cike da rashin fahimta.
"Abba Sadik mana, Sadik Abdullahi Rano, na so shi na so shi, ya kyautata min ya sa na fara son shi, amma ya yaudare ni Abba, kuma na kasa mantawa da shi" tai maganar tana wata irin whalalliyar ajiyar zuciya.
Abba ya jinjina sunan nasa, wato matashin nan da ya taɓa kawo mata invitation na bikin yayansa, tabbas ba ze manta yaron ba.
Wato shine silar duk wannan wahalar da Yarinyar tasa take sha, shine Yaron da take faɗa dama? Wanda ya dinga hure mata kunne?
Abba ya haɗiye wani abu me ɗaci a maƙogwaronsa sannan yace "banda abunki dama Farhan, ina ke ina wannan yaron, ai kyan ƙwarya tabi ƙwarya dama, idan ta bi Akushi fashewa za tai, wannan yaron ba sa'an Aurenki bane, yaro ne ƙarami kuma ɗan masu kuɗi ina ke ina shi?"
"Abba, da Umma ta ja ni a jiki kamar sauran 'ya'ya da Sadik beyi galaba a kaina na fara son shi ba, Astagfirullah, Astagfirullah Abba da Sadik da Sunusi, zan iya yafewa Sadik amma ba zan iya yafewa Sunusi ba, shine mutum na farko da ya fara ɓatani a gurin iyayena, da kuma mutanen unguwa, Abba ta yaya zan kuma yadda da wata Soyayya a gurin maza, Sunusi ba da'awar yana sona yake ba? Amma hakan be hana shi yi min wannan sakayya ba".
Shi kansa Abba daga baya yake godewa Allah, da yasa aka fasa Auren nan, dan yanzu idan Sunusi ya ganshi ɗauke kai ya ke, koma ya fara yada masa maganganu da habaici.
"Na sani Farhan, Amma cikar kimarki, da abunda ze goge miki wannan tabon shine Aure, ba duka maza ne suke haka ba, Kamar yadda kuma wasu matan ba ku da kirki, kar laifin wasu ya shafi Abbas.
Na so ki koma Makaranta, amma a yanayin da kike ɗin nan ba zan so ki cigaba da zuwa Makaranta ba, kiyi haƙuri kinji Farhan"
A sanyaye tace "to Abba" ya dinga rarrashin ta yana mata Nasiha, har hankalinta ya ɗan kwanta.
Abba da kansa yaje ya samu Abbas yace masa yayi haƙuri yau bata jin daɗi, sedai ya dawo ko zuwa gobe ne in Allah ya kai rai.
Abbas yace ai mata sannu daga nan ya tafi.
Tun da Faruk ya zo Nigeria, Khairat take ta ƙoƙarin yin shishshsigi a wajensa, amma ya basar da ita, sedai ya ɗan tsokane ta, ya ƙyaleta sam yaƙi yarda ta shiga jikinsa, tun da ya tafi ko ta waya ba shiga sabgarta yake ba, dan shi sam Faruk be damu da harkar mata ba balle wata Soyayya.
Tun ana i gobe suna aka kawo manyan raguna guda biyu na suna se saniya wadda za'ai hada hadar Abincin suna, Nana ta sha gyaran kai da lallae kamar Amarya.
Ranar suna yaron yaci sunan Abba, wato Abdallah, akai masa inkiya da Sahal.
Anci an sha a gurin taron sunan nan kamar ba gobe, Sadik ya sha shadda Nana kuma wani danƙareren leshi ta saka, sun samu kyaututtuka Sosai, mutane da yawa ba su san anwa Sadik Aure ba, se da a kai wannan haihuwar.
Wuni guda a kai ana cin Abinci daban daban a gurin nan, aka sha hotuna da raye raye, se bayan magariba sannan aka watse daga gurin sunan.
Tunda Abbas yaje gidansu Farhan akace ba ta jin daɗi, ya buga wayarta ya kai sau goma amma ko ɗaya ba ta ɗaga ba, a wannan karon ma ne gaji ba, ya kuma kiran wayar ta ta yai sa'a ta ɗaga tai Sallama cikin sassanyar muryarta.
Yai ajiyar zuciya a sanyaye yace "ranki ya daɗe, yau Allah yayi an ɗaga wayata?"
Tausayin Abbas ne yakamata, babban mutum kamar wannan yai ta wahala akanta, a hankali tace "Doctor kana lafiya?"
"Eh Alhamdilillah, sedai gaba ɗaya bana jin daɗi kwana biyu da banji muryar ki ba kuma bamu haɗu ba"
Farhan tace "Ina cikin damuwa ne, amma yanzu Alhamdilillah"
Abbas yace "damuwa damuwa, Allah ya kawo mana ƙarshen wannan damuwowin naki"
Tace "Ameen, ka san meya sani a damuwa da kuma kokwanto"
Yace "A'a se kin faɗa"
Tace "Hoton Sadik na gani, matarsa ta haihu, se nai tunanin irin soyayyar da mu kai ya juyan baya, Sunusi yai iƙirarin yana sona, amma shima ya tozarta ni, shiyasa nake jin tsoron in saki jiki da kai Doctor, amma nasan kana haƙuri da ni"
"Farhan, duk abunda ya samu bawa a rubuce yake a cikin littafinsa na ƙaddara, haƙiƙa ya cancanci ki guji maza da halayenmu, saboda an ɗanɗan miki maɗaciya a silar Soyayya, amma hakak ba ya nufin duka maza haka muke, ki bani dama Farhan kar ki hukunta ni da laifin da ba nawa ba"
Ta gyara kwanciyarta tace "to Doctor, ya kake ya aikin?"
Yace "Aiki Alhamdilillah, gobe in Allah ya kaimu zan kai ki makaranta fa, fatan baki manta ba?"
"Bance maka ni bana son makarantar nan ba?"
"Dan Allah Farhan, kar Muyi haka da ke, kinga na biya komai dan Allah ki amince ki koma Makaranta, alfarmar da nake nema a gurinki kenan, dan gara kice ba kya sona da ki ƙi cigaba da karatu"
Ta ɗan ja numfashi Sannan tace "shikenan, se ka Zo"
"Kin amince im zo in kai ki?"
Tai murmushi tace "Na amince doctor"
Sukai Sallama sannan ya kashe wayar.
Inna ce zaune akan kujera Abba na ƙasa tana sanar masa da cewar za ta tafi da Nana can ƙauye, dan kula da ita zuwa Arba'in, da Nana taiwa Sadik zancen cewa yai wallahi ba in da zata, Inna dama ba ta bi ta kan wani Sadik ba, Abba takewa bayani.
Abba yace "to Inna, ban ƙi ta taki ba, amma abubuwa za suyi miki yawa sosai, ga jinyar Hakimi, ga mejego da jariri gashi ke ka ɗai ce, ga babu wanda ze dinga taya ki, kinga abun ze miki wahala sosai, amma kinga nan ga Hauwa'u, ga sauran mutane zasu tsaya su kula da ita sosai, ga kai yaro riga-kafi da cigaba da kula da ita Nanan, tunda kinga doguwar naƙuda tai ga ƙanƙantar shekarunta se ana zuwa ana cigaba da kula da lafiyar ta".
"Na san da haka, amma ni nafi ganewa inje in kula da ita a can, a nan ba ta da mataimaki se Allah, matarka ba wani ƙaunar Yarinyar nan take ba, wannan abubuwan da take ma, saboda jikanta takeyi, gara ka bani 'yata inje in kula da ita sosai"
Abba yace "dan Allah Inna, kiyi haƙuri ki barta