Showing 3001 words to 6000 words out of 259198 words

Chapter 2 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

nan ne fa" yai maganar yana sake kafeta da idanunsa kamar wani babban saurayi.

"Toni me zance?"  Tai maganar a shagwaɓe.

Kasa magana yay, se ido da yake binta dashi, a hankali yace "koma meye kice kawai my wife"

"Thank you my Love" ta faɗa cike da jin kunya, kamar wadda tai saɓo, kasancewar shine mutum na farko data furtawa kalma me girma haka.

Ya lumshe idanunsa Yace  "ina sonki my Farhan, jeki gida kar ayi miki faɗa, idan aka yi miki faɗa bazanji daɗi ba"

Tai murmushi ta buɗe motar, ta fita har direban zeja motar, Sadik Yace  "tsaya inga ta shiga gida mana"

Direban ya tsaya yana mamakin, wannan taɓara da ƙarfin hali  gami da tsaurin ido na wannan Yaro, ko secondary school be kammala ba, amma yasan ya tsara yarinya ta soshi, itama kuma ta biye masa maimakon ta maida hankali akan karatunta, Koda yake duk RUƊIN ƘURICIYA ke damunsu.

Sadik kuwa bin bayan Farhan yayi da kallo, duk da ta ɗora ƙaton hijjabi akan uniform ɗin nata, seda ya dena hangota sannan Yace  "mu tafi gida"

Direba yaja mota suka nufi gida.

Suna zuwa tangamemen gidan, direban ya kutsa da motar yai parking, Sadik ya buɗe motar ya fito, kai tsaye cikin gidan ya shiga, sakamakon shriye shiryen bikin Yayansu da ake, mutane suna ta shige da fice a gidan nasu.

Yana kallon mutane a falo, amma ya hau bene, ba tare da ya kula kowa ba.

Yayar mahaifiyarsa ce ta hangoshi ta shiga kiran sunansa  "Sadik, kana kallon mutane amma ka wuce baka kula kowa ba?"

"Zan kulaku anjima idan kuka ragu, duk kun cika mana gida"

Be jira me zata ce ba ya ƙara gaba, ɗakin mahaifiyarsa ya shiga, ya tarar da ita tana ɗakko kaya a wardrobe ɗinta, ta dubeshi tace  "sweetheart, ka dawo ya school ɗin?"

Cikin shagwaɓa Yace "Am so much tired , gashi duk an wani zo an cika mana gida da hayaniya"

"Sorry, kasan shirye-shiryen bikin yayanka ake yi, dole mutane suzo amma ko zaka ɗakinka na BQ ka kwanta ka huta?"

Girgiza kai yayi Yace  "No, a ɗakin Daddy zan wanka in kwanta, a kawomin Abincina nan"

Ta shafa sumar kansa tace  "considered it done my auta"

Yace  "Mother dan Allah a miƙomin jallabiyata, idan kin sauka ƙasa"

Ta jinjina masa kai, Sukayi murmushi tare, ta fita daga ɗakin.

Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, ya fito daga shi se gajeren wando ya tsaya a gaban mudubi, yana ƙarewa kansa kallo, Farhan ce ta faɗo masa rai, a hankali ya lumshe idonsa, yana saƙawa da warware abubuwa da dama a ransa.

Buɗe ƙofar ɗakin akayi tare da yin sallama, ya amsa ba tare da waiga ba, saboda yaga me shigowar ta mudubi.

"Sadik manya, ashe ka shigo amma ba labari, ko neman mutane baka yi"

Murmushi yayi Yace "ai ban san kina gidan nan ba, na dawo kawai na tarar an wani cika falon, babu ma hanyar da zanbi in wuce ɗakina, shiyasa kawai na taho nan"

Ta ƙarasa inda yake tsaye, ta ajiye kayan Abincin, sannan ta ɗora masa ash ɗin Jallabiyarsa a kafaɗarsa tace "gashi nan, Mother ce tace in kawo maka, sarkin rashin son Mutane"

Yai murmushi, yana ƙoƙarin zira jallabiyarsa, ta ƙura masa ido sannan tace  "Semi finalist, next year by now insha Allah an kusa grad, kaima ka wuce Dubai"

"Waye yace miki zanyi SS3, this year zan gama makaranta ni"

Tace  "meyasa zaka gama this year? Jumping zakayi kenan?"

Ya juyo ya fuskanceta sosai sannan Yace  'Khairat, jumping zanyi in kammala secondary School this year insha Allah, saboda Aure nakeso, Aure zanyi nan kusa"

Kwashewa Khairat tayi da dariya tace  'look at you, dan kaga kana da girman jiki? Secondary school fa zaka gama, Yaya Usman ma daza'ayi Aurensa Yanzu, seda yayi PHD, wakake tunanin ze maka wani aure yanzu?"

Ƙurawa khairat ido yayi sannan Yace "kina ganin nayi ƙanƙanta inyi auren ne?"

'ƙwarai kuwa, guda nawa kake zakayi zancen wani aure? Better build your future my friend, and stop talking this rubbish"

Tai maganar tana dariya, ta bar ɗakin.

Sadik ya daɗe a tsaye a gurin yana tunani, sannan ya ɗakko sallaya ya tada salla, bayan ya idar yaci Abincinsa ya kwanta.

Farhan ma harta koma gida, ta shirya ta tafi islamiyya, tunanin Sadik ɗinta ne a zuciyarta, tana tuna yadda yake yawan kyautata mata, amma abun tambayar anan shine, zasu iyayin aure kuwa ita da Sadik? Ita dai tana jin ƙaunarsa sosai a cikin ranta.

Se yamma sosai Sadik ya tashi, yai sallar la'asar sannan ya sakko ƙasa, har yanzu gidan da mutane sedai sun ragu ba kamar ɗazu ba, Yayyansa ne maza zaune tare da Yayar mahaifiyarsu, suna shirya atamfofi a cikin akwati, wanda za'a kaiwa Usman na lefe.

Sadik ya nemi guri ya zauna, yana bin kayan da kallo.

Mamansu Khairat ta kalli Sadik tace "dan ƙaniyarka ina maka magana ɗazu, amma kamin banza ko?"

Yai murmushi Yace 'na gajine, kaina na ciwo, gashi kuma an cika falon, shiyasa ban tsaya ba, wai wannan kayan duk na lefen ne?"

Maman Khairat tace  'eh gasu nan, jibi zamuje mu kai masa insha Allah"

Usman Yace "Autan mother Babu ko kara, ko 'yar sarƙa baka siya ka bani ba, a matsayin gudunmuwa"

Sadik Yace  "gaba ɗaya fa siyayyar nan kaɗan ce akayi maka a Nigeria, duk a waje aka yota, kowa yazo baka kuɗi kawai yake kaida Mummy, kuma kace Sena saimaka abu na  baka duk kuɗinka Bross"

Faruk Yace  'ji ɗan rainin hankali yaron nan dan Allah, duk gidan nan babu wanda ake sakarwa kuɗaɗe kamar ka fa"

Usman yace  "wallahi kuwa, yaron nan kuɗine dashi kamar banza a account bema san me zeyi dashi ba"

Sadik ya karkace ya gyara zamansa akan kujera yace  "aini na dena cin kuɗina, nima lefe zan fara tarawa, next year by now za'a kamin nawa lefen"

Maman khairat tace "Usman, dan Allah makemin mara Kunyan yaron nan"

Sadik yace "Nifa Mummy dagaske nake, aure zanyi nima, zamu yi magana da Daddy idan ya dawo gari, nifa banƙi a haɗa bikina dana Yaya Usman ba"

Umar ne ya kai masa duka Yace "yi mana shiru dan ubanka, mara kunya kawai, ubanwa ze maka auren? Ko dan kana ganinka ƙato haka? Better concentrate on your study, shikansa Bross Usy seda ya haɗa PHD ze aure balle Kai, da yanzu Balagar ta zo maka "

Harar Usman Sadik yayi Yace  "meye wani PHD?  Aure ze hanani karatune? Ai da sauƙi tunda balagara ta zo, Zan baku mamaki kwanan nan.

Ya miƙe yana zumɓura baki ya bar falon.




Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_



                            Page2

Sadik na fita harabar gida, ya tarar abokansa sunzo wai zasu snuka, ya bisu suka fice dan yaje ya sarara.

Corper Nazir kuwa ya sha faɗa a gurin director, saboda ƙararsa da Sadik ya kai, ya dinga mamakin wannan lamari, shikenan dan yaran masu kuɗine baza'a basu tarbiyya ba? Yara duk ba ɗa'a? Ai makaranta ba iya gurin koyon karatu bane, hadda tarbiyya shikenan se a zuba musu ido su lalace, baza'a tsawatar musu ba dan kar iyayensu suji haushi?

Abun ya dameshi sosai, Tare da ganin rashin ma'anar wannan lamari akwai buƙatar a duba, idan bahaka ba rayuwar yaran zata ɓaci a banza.

Da wannan damuwar ya koma gidan daya kama, da yake ba'a camp yake a zaune ba, gida ya kama yake zaune a ciki.

Washegari ya shirya Domin zuwa makaranta, kamar kullum anyi assembly an gama, Farhan nata rarraba ido taga ta ina zata hango Sadik, sedai bata samu ganin nasa ba, ta duba inda yake tsayawa amma baya nan, duk setaji ta damu, haka aka sallamesu suka tafi azuzuwansu.

Sadik kam yau makara yayi sosai, corper Nazir yana harabar makarantar a tsaye yana zazzagawa, dan tabbatar da komai ya tafi daidai.

Motar gidansu Sadik ce ta kunno kai cikin makarantar, har Corper Nazir ze shiga cikin makaranta, yaga zuwan Sadik, dan haka ya tsaya.

Sadik ya fito daga mota, ya rufe motar ya saɓa jakarsa, ze shiga cikin makarantar.

Cikin shouting corper Nazir yace "hey come here'

Sadik ya juyo ya kalleshi, sama da ƙasa kamar kar yaje, sukuma yaje kiran, yana wani bossy walking yaje inda Nazir yake tsaye, Nazir ya kalleshi yace  "why are you just coming?"

Sadik ya kalleshi ya ɗauke kai.

"Check your watch, what's the time now?"

Sadik ya ɗauke kai kamar ba dashi ake magana ba, principal ne ya taho inda suke tsaye, yana faɗin"what's going on here?"

Nazir Yace  'Sir, wai Babu wani penalty na makara kowani laifi, idan yaran nan sun karya doka? Kalli lokacin da yazo makaranta, kuma na yiwa director magana akan haka amma ya nuna min is like you don't punish them"

Principal ya kalli Sadik yace  Yace  "Sadik, why are you late? Baka san lokacin da Yakamata kazo school bane?"

Tura baki Sadik ya shiga yi, yana hararar Nazir.

PC yace  "idan ka sake makara, sena baka punishment me wahala, ɗau jakarka ka bar gurin nan kafin in ci mutuncin ka"

Sadik ya ɗau jakarsa fuuu yai cikin makarantar, yana tunanin yadda ze koyawa Nazir hankali.

Principal ya kalli Nazir yace  "ka manta da director, duk abunda yakama na hukunci a hukuntasu, shi yana la'akari da yadda ze samu kuɗine kawai, shiyasa baya goyon bayan hukuntasu, kuma wasu daga yaran iyayensu nada kuɗi yanzun nan se su ɗaureka, amma dan dai punishment wanda zasu iya, in sunyi laifi kar a saurara musu"

Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin yaran.

Koda Sadik yaje ajinsu da malami a ciki Yana lesson, amma babu neman izinin shiga ko makamancin haka, ya kunna kai cikin ajin nasu, yaje gurin zamansa ya zauna, Tare da ajiye jakarsa, fuskar nan tasa a ɗaure yana ta jan tsaki.
Duk ajin suka waigo suna kallonsa, daga bisani malamin ya cigaba da Koyarwarsa.

Sadik be saurari me Malamin ke koyarwa ba, ya kifa kansa akan benci, zuciyarsa cike da jin haushn irin yadda Nazir ke zaƙewa da son cusawa hukumar makaranta wani ra'ayi na daban akansu, dole yayi maganin Nazir.

Malamin na fita su Amin suka zo inda Sadik yake, Nasir Yace"babban yaro ya dai? Meyafaru ne mun ganka Wani iri"

Sadik yayi tsaki Yace  "dan Allah ku rabu dani"

Amin yace "haba Sadik, Ya hakane? Mun tambayeka meyafaru kana wani cin magani"

Banza Sadik yayi musu, suka gama surutunsu 'yan matan class ɗin ma sukazo kan Sadik suna nasu surutun

"Babban yaro waye ya taɓo mana kaine?"

Kamar da Dutse suke Magana, yai musu shiru ƙarshe se haƙura suka yi suka ƙyaleshi.

Farhan kuwa gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, ta kasa samun kwanciyar hankali saboda rashin ganin Sadik, ɗalibai kowa yana harkokinsa amma banda Farhan.

Ganin da tayi zaman baze fishsheta ba, yasa ta miƙe ta nufi hanyar ajinsu Sadik.

Tana zuwa gaba ɗaya ta kasa shiga, ta tsaya a waje tana leƙa ajin, ba zata iya shiga ajin ba, saboda na Seniors ɗintane, gashi bata san kowa a ajinba se Sadik, dan haka tana jin nauyi sosai.

Ta window ta tsaya, tana leƙawa dan taga ko zata hango Sadik ɗinta.

"What are you doing here?" Da sauri ta waiga dan ganin me Maganar, Nasir ne abokin Sadik, ya kalleta yace "ko kina Neman Sadik ne?"

Farhan ta ɗan sunkuyar da kai, cike da jin kunya.

Nasir ya ɗan tsaya yana ƙare mata kallo, da jinjinawa mugun jin kunya na Farhan, se dai babu mamaki irin wannan halayyar ga 'ya'yan talakawa, sam basu da wayewa.

Yace "to ki shiga mana, yana ciki ai"

Kamar wadda aka yiwa dole, ta shiga ajin can ta hango Sadik, zaune ya kifa kansa, gabanta ne ya faɗi tai tunanin ko bashi da lafiya ne?

Da ɗan hanzari ta ƙarasa bencin da yake zaune.
Jin mutum a kusa da shi ne yasa ya ɗago da sauri dan yiwa wanda yazo kusa da shi ɗin masifa, sedai kuma yayi tozali da fuskar Farhan.
Ajiyar zuciya ya sauke, bece komai ba.

A hankali tace "baka da lafiya ne?"

"No Farhan, lafiyata ƙalau"

"Amma ban ganka a gurin assembly ba?"

"Nazo a makare ne, kuma wancan corper ɗin ya ɓatamin rai, sena gyara masa zama tukuna"

Farhan tace "me yayi maka?"

"Yana min shishshigine, dan yana saka wannan koɗaɗɗun uniform ɗin na NYSC, idan be kiyayeni ba zan koya masa hankali"

Farhan tace  "kasan meyasa ya sani punishment jiya?"

Sadik ys girgiza mata kai, tace  "wai saboda kaje gurina, ya tambayeni meke tsakanina da kai, shine 'yan ajinmu suka faɗa masa, shine yaita min faɗa ya sani kneeldown"

Sadik ya daki benci yace "har akwai wani sakaran daze sawa soyayya ta ido a makarantar Nan? Wallahi idan mutumin nan be kiyayeni ba sena sa an karairayamin shi"  yai maganar a harzuƙe wanda seda hankalin 'yan ajin ya dawo kansu.

Aminu Yace  "wai kai Sadik meke damunka ne?"

"Wannan Nazirun ne, da gemu kamar soson wanka wallahi ya cigaba da shiga sabgata kota Farhan wallahi sena masa illa"

Farhan ta kwantar da murya tace  "dan Allah kayi haƙuri, dana sani ban gaya maka ba"

Wata cikin 'yan class ɗinsu Sadik me suna Amina amma suna cemata meenal ta taɓo ƙawarta tace  "Taslim, kina ganin wani abu kuwa, wannan budurwar Sadik ɗin akwai iya barikanci, kalleta saliha kuma yarinya amma ta dabaibaye zuciyar ɗan mutane ji yadda take masa magana"

Taslim tace "ke dai Bari, kina gani Tun ɗazu muke tambayarsa meya dameshi, yai banza damu amma tana zuwa ya ɗago kansa, na rasa meya ja ra'ayin Sadik akan yarinyar nan, kaf class ɗin nan Sadik bashi da budurwa,  ya rasa a inda zeyi budurwa se a Jss2, duk wannan iyayin nasa.

Meenal tace  "lallai ma ke ɗin nan, Sadik wayone da shi ya samo yarinya fresh, wadda bata san komai ba ya koya mata sonsa, zeyi tattalin kayarsa kuma ki ƙare mata kallo, yarinya ce amma me ƙirar manya, tana da zubin halitta me jan hankali sosai"

Suka cigaba da gulmarsu a gefe, Sadik kam se banbami yake akan Corper Nazir, Farhan tace  "ni ka dena wannan faɗan ko in tafi"

"Farhan ya bazanyi faɗa ba, yana nema ya kassaramin soyayya, ina ruwansa damu?"

Nasir Yace "Sorry Prince, ai komu ba zamu bari a kassara wannan soyayyar ba, wadda muke saka rana ta shiga kundin tarihi kamar ta su Laila majnun"

Kamar Farhan za tayi kuka tace"dana sani ban gaya maka ba, nace fa kayi haƙuri"

Sadik yai shiru yana cigaba da huci, Farhan tace  "kayi haƙuri mana, dan Allah ka dena fushi Kaji, ka ga malamnmu ne, koba komai ya koyar damu, ka dena zaginsa"

Sadik Yace "ke dalla ƙyaleni, na tsani mutumin nan wallahi"

Miƙewa Farhan tayi zata tafi, jin yadda yayi mata magana a tsawace, ya riƙo hannunta da sauri, wanda hakan ya haddasawa Farhan mummunar faɗuwar gaba, taga kamar kowa suyake kallo.

Tace "ka dena taɓani, meye haka?.

Sadik yace "am sorry, na dena amma dan Allah kiyi haƙuri, zauna"

Farhan ta nemi Guri ta zauna, yace "kiyi haƙuri bazan sake ba insha Allah"

Ta zauna tana ɗan tura baki, taƙi kulashi, ya sake kashe murya yace "haba na face kiyi haƙuri"

Tai murmushi tace  "Na haƙura ai"

Suka cigaba da hira ita da Sadik, yama  manta da maganar wani Nazir.

Har aka koma class Farhan bata sani ba, tana zaune tana hira da Sadik cike da nishaɗi, duk da mafi yawan hirar shi yake mata, ita murmushinta yafi yawa akan magana.

"Ke Farhan!" Sukaji muryar Sir Nazir.

A rikice Farhan ta waiga, dan ji tai an kira sunan nata tamakar saukar Aradu, Kamar yadda ta zata sir Nazir ne ba wani ba.

"What are you doing here? Is this your class?" Ya tambayeta yana zazzaro ido.

Cikin tsoro Farhan ta girgiza kai, alamar a'a  yayinda attention ɗin class gaba ɗaya ya dawo kansu, kowa ya zubo ido.

"Me kikeyi a kusa da namiji a zaune? Ajin ku ne nan? Tashi ki bar ajin nan ki koma ajinku"

Sadik ya fusata ze yi magana, Farhan ta girgiza masa kai, ta tashi da sauri ta fita, Sadik ya tsaya yana kallon kallo da Nazir.

Naziru yai ƙwafa ya fice, yana fita Sadik ya daki benci yana muzurai, Nasir Yace  "easy Prince, kayi haƙuri"

"Mutumin nan yana wuce gona da iri fa, zanyi masa kaca kaca a makarantar nan wallahi"

"Kayi haƙuri, zamu san matakin da zamu ɗauka a kai"

Farhan kam da Kusan gudu ta ƙarasa ajinsu, ai kuwa Nazir ya rufa mata baya, a gaban 'yan ajin ya shiga zazzaga mata bala'i.

"Ke wace irin yarinya ce ne? Abunda kike kin kyautawa kanki ko iyayenki? Gurin wannan ɗan iskan yaron aka turoki? Me kike zuwa gurinsa yi?" Yai maganar yana tsatstsareta da ido.

Farhan ta girgiza masa kai, alamar ba komai.

"Wallahi idan baki shiga hankalin ki ba sena haɗa miki assembly, kuma in kira mahaifinki in gaya masa abunda kike aikatawa, gara tun wuri ki fita harkar wannan ɗan iskan yaron, tun be lalata Rayuwar ki ba"

Farhan tana jin zafin cin mutuncin da Nazir yake mata, sedai jinsa kawai take dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik,sum sum taje ta zauna a gurin zamanta tana sunkuyar da kai, Nazir na cigaba da zazzaga Mata cin mutunci.

"Irinku ne masu komawa iyayensu da ciki ,ku lalace tunda ƙuruciyarku, saboda RUƊIN ƘURUCIYA na ɗibarku, sun turo ki kiyi karatu amma kina biyewa 'yan iska, a haka gaki kamar saliha amma baki da hankali, in sake ganin kinje inda yake, sena zaneki a makarantar nan"

Farhan tai shiru, ta sunkuyar da Kai tana jin yadda maganganun nasa ke mata dirar mikiya a ƙirjinta, taji zafin yadda yake cin mutuncin ta a gaban 'yan ajinsu, dan seda tayi kuka, sedai sam maganganun nasa basuyi tasiri a zuciyarta ba, dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik, tun da ita dai bata ga aibun Sadik ba, a barshii da zafin rai dai wasu lokutan da rashin son raini, amma yana da sauƙin kai sosai, sedai ta yanke shawarar zata yi duk me yuwuwa ta nesanta kanta da Sadik ko dan kaucewa cin mutuncin Sir Nazir da dizginsa da kuma gudun kar ya haɗa ta da mahaifinta, dan a duniya tana tsoron Allah, tana tsoron mahaifinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login