Showing 108001 words to 111000 words out of 259198 words
Chapter 37 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
nan, kusan kullum seta gota lokacin dawowa daga Makarantar dare, yau se goma da rabi ta dawo, na tambayeta tace wai sunje dubiya, gaba ɗaya alamu sun nuna ƙarya take, nifa gaskiya tsoro nake ji"
Abban Farhan ya numfasa yace "to yanzu meye abunyi? Ke ba wani matsarta kike ba balle ki tabattar da abunda kike zargi, amma meye abunyi a naki ganin?"
"Abunyi ɗaya a haƙura da wannan bokon, wannan Yaron ya turo ayi Auren nan, yanzu har an fara yarmin da magana a dangi, na bar Yarinya a gida muna haɗa kafaɗa, dan Allah kayi wani abu a kai"
"Banƙi ta taki ba akan Yarinyar nan, amma ni a jikina na yadda da ita, duk da ba'a shedar ɗan yau, tana da burin yin karatu a Rayuwar ta, dan haka bana fatan tauye ta, shiyasa nake son in bata dama, amma zan ga abunyi, idan Auren ne masalaha se ace ya fito ayi, amma nima kin jefa tsoro a raina, amma zanga abunyi insha Allah"
Umman Farhan tace "Aikam dai ya kamata a gaggauta sanin abunyi, tun kan ta jawo mana magana, kwanan nan duk ta canza gaba ɗaya"
*****
Se gefin Asuba sannan Sadik ya samu bacci ya kwashe shi, da ƙyar ya tashi sallar Asuba, itama a ɗakinsa yai sallarsa, ko azkar be ba ya haye gado ya cigaba da baccinsa.
Ƙarfe takwas da rabi, Abba ya kintsa ya kalli Mother yace "Ina Auta ne?"
Mother tace "ina ga be tashi ba"
"Wane irin be tashi ba, ba shekaranjiya na gaya masa tare da shi zamu duba Hakimi ba? Faruk je ka taso min shi dan ƙaniyarsa"
Cikin bacci yake jin maganar Faruk a kamsa "kai Sadik ka tashi fa, Abba yana jiranmu wai ka manta yau da kai zamu tafi ƙauye?"
Wani uban tsaki Sadik ya ja, ya sake juyi ya cigaba da baccinsa.
"Wai ba zaka tashi ba, Abba fa ya shirya kai kawai ake jira"
Ai Sadik ko gezau beba, ya cigaba da baccinsa hankali kwance.
Faruk ya ƙyale shi, ya koma falo in da ya bar su Abba.
"Ina Sadik ɗin?"
"Wallahi nayi nayi yaƙi tashi"
Abba yace "yaƙi tashi, bari inje da kaina ina taso shi, ko daga shi se gajeren wando ne haka zamu tafi"
Da sauri Mother tace "No baza'ai haka ba, yi hakuri bari inje in taso shi, yi haƙuri"
Mother ta fita ta nufi BQ, aikuwa tana zuwa ta tarar da Sadik a kwance abunsa yayi ɗai ɗai, yana kwasar bacci.
Ɗan ƙura masa ido Mother tayi, ganinsa take kamar jaririn da ta haifa jiya, haryanzu kallon abunta take wani ɗan ƙaramin yaro, da be wuce idan yana kuka ta rungume abunta ta rarrashe shi ba.
Ta ƙarasa gaban gadon nasa ta fara bubbuga filonsa.
Tura baki yai ze sake juyi.
Mother tace "dan ubanka ka tashi, in ba haka ba Abbanku yace ko daga kai se gajeren wando ne haka ze tafi da kai ƙauye"
A hankali ya buɗe idanunsa akan Mother, ya tura baki yace "ni wallahi Mother bana son Zuwa garin nan"
Mother ta sassauta murya tace "to ya zakayi, tashi za kai ka rufan Asiri kar Ya ce ni nake zigaka, tashi maza kaje kai wanka"
Sadik na tura baki haka ya shiga wanka, kan ya fito tuni Mother ta haɗa masa breakfast.
Da kanta ta zauna tana bawa Sadik ɗin Abinci a baki, yana ci yana zuba taɓararsa son ransa harya ƙoashi.
Ya saka ƙanan kaya, ya shafe sumarsa da mai sannan ya fito shi da Mother.
Abba na ganinsu ya ƙurawa Sadik ido daga bisani yace "Sannu ko"
Sadik ya sunkuyar da kai.
"Nace sannu, barka da warhaka ranka ya daɗe, ka shanyani ina jiranka ko? Harna aika amma kaƙi tasowa, da nazo kanka da zaneka zanyi"
Sadik dai bece komai ba ya koma gefe yana sosa ƙeya.
Wata jaka Mother ta samu, ta zubawa Sadik ruwan roba, da tarkacen cookies a ciki, wai ta san ba iya cin Abinci zeyi a can ba.
Sukai sallama suka kama hanyar tafiya.
Suna tafe a hanya suna hira da Farhan, yana tura mata messages.
"Beb kika hanani bacci jiya"
"Ta yaya na hanaka bacci kuma?"
"Through out the night am dreaming of you, gaba ɗaya na kasa bacci, gashi da sassafiyar nan Abba ya sa an tasoni mu tafi ƙauye"
"Eyya sorry, Allah ya kaiku Lafiya ya tsare ku, ka kulamin da kanka Please"
Murmushi Sadik yai ya tura mata "An gama Amaryar Sadik, Allah ya mallaka min ke Farhan"
"That's my prayer always"
"Dagaske kina mana Addu'a?"
"Hmmm, ni gani nake ma kamar nafi sonka"
"Ke 'yar Fulani Yaushe mu kai haka dake, kufa rigima ce da ku ga rinto, banda rinto ta ya kika fi sona?"
"Nice me rinto ko?"
"Eh mana kece, Yarinya dan baki san halin da nake ciki akan ki bane, ina sonki da yawa fa"
"Ya kai cikin kofi son da kake min?"
Kawai Sadik ya fara dariya, Faruk ya kalleshi yace "kai lafiyar ka kuwa?"
Sadik yace "Meka gani?"
"Gani nai kana dariya kai ka ɗai"
"No wata beb ce ke bani dariya"
Faruk ya girgiza kai yace "Allah ya shirye ka Sadik"
Sadik yace "meye kuma Allah ya shiryeni? Haram na aikata?"
"A'a ba haram ka aikata ba, amma gaskiyar Inna da tace be dace a kaika ƙasar waje karatu ba, zuwa za kai kai ta abunda Allah ya nufeka dayi, baka da wani zance sena mata da kuma Aure"
Sadik ya waiwaya baya, dan yaga Abba na jin hirar ta su, amma yaga Abba sam hankalinsa baya kansu, waya ma yake.
Sadik ya dawo da kallonsa kan Faruk yace "eh ɗin anyi zancen Auren, lafiya ce ta kawo hakan"
Faruk yai murmushi yace "Ruɗin ƙuruciya kenan"
"Kaga ka kiyayeni da wannan zancen RUƊIN ƘURUCIYA"
Faruk yace "Allah ya ƙara lafiya Yariman Hausawa"
Sadik ya cigaba da hira da Farhan, ta hanyar musayar saƙonni, yana nishaɗi.
Da wuri suka ƙarasa garin, rabon da Sadik yaje garin nan harya manta Tsawon lokacin, dan gaba ɗaya garin nan be masa ba.
Ranar Asabar ne, ya kama ba Makaranta dan haka Nana tana gida ba in da taje.
Ta dawo daga aike taga motar su Sadik, fara'arta ce ta faɗaɗa, da taga Faruk ya sakko daga Motar.
Ya zaga ya buɗewa Abba shima ya sakko, har ƙasa Nana ta durƙusa ta gaida Abba, ya amsa mata cikin sakin fuska.
Faruk ya kalleta yace "Ina wuni"
Nana tace "A'a ai zan gaisheka, ina wuni"
"Ba zan amsa ba, tunda ni na fara gaisheki" yai maganar yana murmushi.
Abba yace "ƙyale wannan yayan naki, ya me jiki?"
A ɗan Sanyaye tace "jikinsa da sauƙi Alhamdilillah"
Abba yace "lafiya dai ko?"
Nana tace "eh Lafiya ƙalau"
Duk wannan maganar da suke, se yanzu Sadik ya buɗe motar ya fito.
Sumar nan se sheƙi take kamar gashin mace, ya ƙara fresh da shi kamar baya shiga rana.
Yana sanye cikin ƙanan kaya, wando jeans da baƙar T shirt, ya ƙara kyau sosai.
Ya ɗaga kai yana ƙarewa harabar in da suken kallo, ya ɗan kalli inda Nana take ya ɗauke kai.
Itama wata uwar harara ta wurga masa, irin ko da wacce ka zo daidai nake da kai ɗin nan.
Suka ɗunguma suka shiga gidan, Kai tsaye turakar Hakimi suka tafi dake cikin gidan.
Suka sameshi a kwance, hannunsa riƙe da carbi yayin da Inna ke sallar walha.
Hakimi ya yunƙura ze tashi zaune, Faruk da Abba sukai hanzarin zuwa suka ɗago shi.
Ya kalle su yace "Masha Allah, sannunku da zuwa kun sha hanya, Bawan Allah ka sai hanya kana ta zarya, Yakamata ka dinga hutawa"
Abba yace "Alhaji taya zan huta, ai duk inda nake hankalina yana nan baze kwanta ba, ka ƙi bari in tafi da kai"
"A'a bakomai barni a nan ɗin, ina samun kulawa sosai"
Alhaji ya kalli in da Sadik ya ƙame a tsaye yana binsu da ido, yace "Yarima, yau an zo da kai kenan, manya gatan wasa"
Sadik ya ɗanyi murmushin gefen baki yace "ina wuni, ya jiki"
"Jiki Alhamdilillah, ana dai yi mana addu'a ko?"
Sadik yace "eh ana yi"
"To madalla"
Inna ta idar da sallarta, ta shafa Addu'a tace "Sannun ku da hanya"
Abba yace "yawwa, yame jikin kuma?"
"Jiki Alhamdilillah da sauƙi"
Inna ta ɗaga kai tana ƙarewa Sadik kallo, irin kallon da ya tsana dan a haka take gano abunda za tai ta masifa a kai.
Ya ɗan risina yace "Ina wuni?"
Inna taja wasu seconds tana kallonsa sannan tace "hala kashi ne a gurin da baza ka zauna ba, ka ƙame a tsaye?"
Hakimi yace "kin san saraki, ƙil shimfiɗar gurin ce ba ta masa ba, a samo masa Matashi"
Inna tace "Sarakin wa? Wannan sarautar ba dashi ta dace ba, aka bashi ita, ba wani matashi da za'a bashi, im baze zauna ba yaita tsaiwa, soja"
Sadik dai bece komai ba ya nemi guri ya zauna akan tattausar daddumar da ke gurin.
Nana ta fita tsakar gida, ta samu Jug ta zubo ruwan randa, ta haɗo da kofuna, bisa ga koyarwar Inna, ta kawo Musu.
Ta shiga zuzzuba musu ruwan tana miƙa musu, sedai taƙi zubawa ta bawa Sadik.
Hakimi yace "shi wannan laifin me yayi miki da baki zuba kin bashi ba?"
Sadik yace "No, am not thirsty bana sha"
Ɗan ƙaramin tsaki Nana tai, tana hararsa.
A ransa yace 'wannan shegiyar yarinyar ta fara rainin hankalin nata, in mata wani abun wannan tsohuwar ta ji haushi ta fara min masifa"
Inna Kuwa tana kallonsa, yadda yaƙi shan ruwan nan, da yadda yake ta ƙarewa ɗakin nan kallo, kamar ya ganshi a wata duniyar daban.
A hankali Sadik ya silale ya fita, ya tafi mota ya ɗau ruwansa na roba ya zauna yana sha.
Mother ta kirashi a waya, sedai duk yadda ya so ya ɗaga wayar nan abu ya gagara saboda rashin Network, yai yai ya ɗan zazzaga ko ze samu Network amma abu ya gagara.
Ransa ya ɓaci be san lokacin da yace "wannan banzan ƙauyen, Network ma babu dan masifa"
"Wallahi ƙauyen mu ba banza bane, sedai me maganar ne banza"
Sadik ya waiwaya yaga Nana a tsaye hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano, da alama aikenta a kai.
"Ke kuma nasa dake ne? Zaki fara bibiyata kina min rashin kunya, bar ganin gidanku nazo, wallahi se in tattakaki"
"Wallahi baka da wannan ƙafar, babu ƙafar da zata iya tattakani in gaya maka, kuma wallahi a garinmu kake gidanmu, zan iya sa dogarai su zane min kai, dan nan ba gidanku bane balle ka ɗagamin murya"
"Ni zaki sa dogaran su zane?" Yai maganar yana nuna kansa.
"Eh kai ɗin zan sa su zamemin kai, gara ka shiga hankalinka" ta ƙarasa maganar tana hararsa tai waje.
Binta yai da kallo, wata ƙwaila da ita se rashin mutunci fal cikinta.
Gajiya yai da neman Network, ya koma cikin gidan yana tsaki da ƙanan surutai, shi ya gaji ma so yake su tashi su tafi, amma yaga basu da wannan niyyar.
Lilly ce kwance akan makeken gadonta, se juyi take daga ita se underwear, ta rasa meke mata daɗi gaba ɗaya, wata irin kasala ke damunta, gashi wata irin wuta take ji a jikinta, babban burinta be wuce sake kasancewa da malamin ta b wato Nazir, ta rasa in da zata saka kanta, gashi sunyi nadamar abunda suka aikata, har yana iƙrarin ze Aureta, amma ita kaɗai ta san me take ji.
Wayarta ce ta fara ringing, banza tai da wayar ta cigaba da juyi, daga wannan angle ta koma wancan, ta nayi tana ɗan jan tsaki lokaci lokaci.
Wayarta ce ta sake ɗaukar ruri, a fusace ta kai hannu ta ɗakko wayar, ta duba se taga Nazir ne ke kiranta.
Ɗagawa tai ta sa a kunnenta "hello my nazee"
Ajiyar zuciya yai yace "Baby meyasa ba kya ɗaga wayata ne?"
"Ba gashi na ɗaga ba"
'amma sau nawa na kira baki ɗaga ba?"
"Nifa ban san kai bane shiyasa"
"Shikenan, naji muryar ki wani iri, Lafiya dai ko?"
"Lafiya ƙalau, Am just missing You Babyyyyy"
Yace "Ummm, jiya fa muna tare, har kin fara missing ɗina?"
"Yes, let's do a video call, I want see you"
Yace "ok, as you wish my love"
Ya katse kiran, ya kirata video Call.
Sedai seda yai turus ganinta a screen ɗin wayarsa, cikin wannan shiga.
Ko a jikinta ta fara yi masa magana "fita za kai hakane, naga kayi wannan kwalliyar haka?"
Da ƙyar yace "wani ɗaurin Aure aka gayyace ni"
"Ok, seka dawo, banda kallon mata Please, duk wadda ta ƙyasa kace mata kana da mata kaji Baby"
"Wai ya naga kina wani ƙara fresh, kim ƙara ja kinga kumatunki kuwa?"
"Haka kowa yake cewa nima kuma na gani"
Nazir yace "kinga se an jima, karki hanani fita, gaba ɗaya kin sauyan yanayi bye bye"
Murmushi tai ta kashe wayar, tace "ai gara yanayin naka ya canza, kaji abinda nake ji nima"
Ajiyar zuciya Sir Nazir ya sauke, yana jin sa a wani yanayi na daban, na son sake kasancewa da ɗalibar tasa.
A gidan Hakimi kuwa, Da Azahar aka yi funkaso da miyar taushe, ta sha naman kaji da man shanu, kallo ɗaya Sadik yaiwa Abincin ya ɗauke kai.
Abba da Faruk suka zauna cin Abinci, amma banda Sadik da yake ta cin magani.
Abba yace "Kai Sadik ka wanko hannu kazo kaci Abinci mana"
Sadik ya girgiza kai.
Abba yace "me kake nufi?"
"Abba na ƙoshi"
"Saboda me ka ƙoshi" Abba yai maganar yana kallonsa.
"Abba ni ban zan iya ci ba, bana son wannan abun"
"Aikuwa zaka zauna da yunwa, dan ban san me za'a nemo maka kaci ba"
Inna tace "Yanzu meye aibun wannan funkason da ba zaka ci ba?"
Sadik ya ɗan tura baki yace "ni ba naci"
Inna tace "madalla, ka hutawa kanka, kuma babu me nemo wani abun ya baka, kar Allah yasa kaci ɗin"
Tashi yai ya fita daga ɗakin, yana ƙunƙuni ya tafi mota ya ɗakko cake, ya dawo harabar babban soro, in da aka ɗure dawakai, ya shiga cin Abincinsa yana kallon dawakai.
Harya gama cin abunda zeci, ya tsyaa yana jiran yaga fitowar su Abba dan su tafi, amma yaji shiru basu fito ba.
Ya koma cikin gidan amma ya tarar da su a ɗakin Hakimin, ba su da niyyar tafiya ma, sedai ya tarar ana ta shashafawa Hakimin ruwa a jikinsa, alamar jikin ne ya ɗau zafi.
Har la'asar ana fama saboda jikin Hakimi, Abba yace zasu tafi da shi yace be yadda ba, sedai a kira masa likitan da yake duba shi yazo har gida ya duba shi, amma su barshi a turakarsa, yafi son in mutuwa zeyi ya mutu cikin sutura a ɗakinsa ba tare da ya wahal da kowa ba.
Inna dauriya kawai take, yayin da Nana ta dinga kuka kamar ance mata Hakimin ya rasu.
Faruk ne ya biyo bayanta, yana rarrashin ta "haba Nana, ya zaki ɗaga mana hankali kema, ki dena kukan nan haka, insha Allah ze samu lafiya"
Nana ta jinjina kai amma ta kasa dena kukan, yaita rarrashin ta.
Shi kuwa goga Sadik ya koma mota yai zamansa, yana jiran a gama abunda za'ai azo a tafi gida.
Likita yazo ya dudduba Hakimi, yai masa allurai ya bashi magunguna sannan ya ɗan samu sauƙi.
Abba yace baze yuwu su tafi a ranar ba, saboda ko sun tafi hankalinsa ba ze kwanta ba, saboda ya tsorata da yanayin jikin mahaifinsa.
Ai da Sadik yaji labarin a garin zasu kwana, ji yai kamar ance ya kwana a wuta, wani irin takaici ya turnuƙe Sadik, ji yake dama be biyo su ba.
Cikin ikon Allah zuwa magariba Jikin Hakimi yai sauƙi, dan har yana iya miƙewa tsaye da kansa.
Inna kuwa duk tana monitoring ɗin Sadik, yadda yake cika yana batsewa saboda zasu kwana a garin, gashi ya ƙi cin abinci, ruwa ma ya ƙi sha se wanda ya zo da shi na jarka ya Ke shan abunsa.
Saboda rashin network, se message Abba yaiwa Mother, ya sanar mata a garin zasu kwana.
Mother kanta taji haushin batun kwanan nan, dan ba abunda yafi damunta se Autan ta, ta san Sadik ba 'a masa gwaninta, kuma ba komai ne ke burgeshi ba, Abinci ma ba na ko ina yake ci ba.
Da isha'i, Sadik yana alwala Nana ta fito daga banɗaki, ita ma tayo Alwala, tana fitowa ta fara yarfe hannu, aikuwa ruwan alwalar jikinta ya sauka a fuskar Sadik.
"Ke wace irin Mahaukaciya ce ƙazama zaki watsamin ruwa a fuska?"
Nana ta waigo ta kalleshi tace "kaine mahaukaci bani ba, kuma wallahi kar ka sake cemin ƙazama dan ban ma abun ƙazanta ba"
"Wallahi idan baki kiyayeni ba sena tattakaki a gurin nan"
"Kaga ka kiyayeni da batun zaka tattakani ɗin nan, sedai mu tattaka juna banza kawai"
"Nine banzan?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsa.
"Eh kaine banzan, an faɗa banza"
Aikuwa ya ɗaga butar da yake Alwala da ita, da ruwan da komai ya jefo mata.
Aikuwa tai gefe tana kiran "wayyo Allah Inna"
Ba shiri Inna ta sallame sallar da take, ta fito tsakar gida hakan yai daidai da shigowar su Faruk daga masallaci.
Inna tace "lafiya meye haka?"
Nana tace "dukana zeyi"
Abba yace "Sadik wai kai meyasa baka girma ne?"
"Abba rashin kunya fa take min, saboda tsabar wulaƙanci ta shiga banɗaki tai ƙazantar ta ta watsa min sauran ruwan kashi a fuskata"
Nana tace "kut, wallahi ni ba kashi nayi ba, alwala nayi"
Faruk ƙunshe dariya yai, yai waje dan abun nasu ƙuruciya ce da shirme kawai.
Abba yace "kai yanzu ba ka ji kunya ba, idan ma hakane ba sekai haƙuri ba, kuyi ta abu kamar ƙananan yara,in dai zaku haɗu sedai kuyi faɗa"
Inna saboda tsabar takaici, ta koma ta cigaba da sallarta, ba tare da tace uffan ba.
Nana ma da sauri tabi bayan Inna, dan kar Sadik ya kuma yunƙurin dukanta.
Da daddare Sadik yaita tsaki, gashi akan lintsumemiyar katifa, ɗaki irin na gidan sarauta, amma yaita mita da tsaki, wai ɗakin zafi ga ba wuta, ga missing Farhan da yake.
Ƙarshe se message ya tura mata, ya sanar mata a garin ze kwana, yai trying lambarata amma inda yake ba network.
Tun tara na dare ya tura mata message ɗin, amma se sha ɗayan dare ta ga saƙon, tana tsaka da tunaninsa.
Zuwa gari ya waye, jikin Hakimi yai sauƙi sosai, ya samu ƙwarin jikinsa.
Nana ta shiga ɗakin Hakimi ta gaishe shi, ta tarar yana bacci ba kowa a ɗakin se Sadik, yana zaune yana danna waya.
Nana taje ta leƙa fuskar Hakimi ta tarar bacci yake, dan haka ta juya zata fita, ta kalli Sadik tai masa tsaki ba tare da yai mata komai ba.
Kawai ya ɗau murfin kofin dake gefensa, ya jefeta da shi a ƙafarta.
Ta waigo ta kalleshi tace "Allah ya isa na"
Hakimi kam idonsa biyu, ya lumshe idonsa ne kawai yana jinsu, amma bece musu komai ba.
Kunun tsamiya aka dama da wainar gero, Abba yana ta murna, dan yana missing ɗin Abincin gargajiya, yayin da Sadik ya sake cewa shi baze ci wannan abincin ba, shi kunun tsamiya gudawa yake sa shi, wannan baƙar abar kuwa baze iya ci ba.
Tunda