Showing 117001 words to 120000 words out of 259198 words
Chapter 40 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
idon ba wayarsa ta ɗauke.
A hankali ya lumshe idanun nasa, hawaye na cigaba da zirarowa daga idonsa, wanda shi kansa be san takaimaimai na menene ba.
Ya ajiye wayar, ba tare da ya buɗe idon ba, yana jin yadda zuciyar sa ta cunkushe, ga matsanancin shauƙin son kasamcewa da Farhan da yake bijiro masa.
A hankali ya janyo pillown da ke gefensa, ya rungume shi gam a ƙirjinsa, yana sauke ajiyar zuciya.
Sunusi ke zaune akan wani buzu, se rubutu yake a jikin wani allo, gabansa wuta naci a jikin wasu ƙananun itace.
"Sunsi wai akanwa kake wannan aikin ne haka?"
Sunusi ya ɗago kansa yai murmushi yace "Haladu kenan, ai tunda ka ga nayi wannan zaman, aikin nayi ne, zazzafan aiki zanyi farraƙu zanyi"
Haladu yace "wa za kaiwa Farraƙun?"
"Wannan yarinyar mana da malam ya tambayar min aurenta, se nema take ta wahalar da ni, ashe wani ɗan tayin yaro take so, yake hure mata kunne, shine nake son in nuna musu ba a ja da ƙolo"
Haladu yace "haba mutumina, a sassauta musu mana, kasan wannan aikin yayi zafi da yawa kai musu wani dai daban ba wannan ba"
Sunusi yace "inaa, ai Wannan ɗin dai zan musu, naga kanta yana rawa ne, gara in saita ta tun da wuri, se tayi dana sanin wulaƙanta ni, kuma aikin da zanyi akan Yaron nan na gaske zanyi, yadda gobe in ance ya ƙara baze ƙara ba, zan kwashi kwanaki ina yi"
Haladu yace "to ai shikenan, Allah ya dafa"
Sunusi yace "Ameen"
Lilly kam likita yace se ta kwana a Asibiti, saboda a cigaba da ƙara mata ruwa.
Da yamma Mummy ta koma gida dan harhaɗo kayan da zasu zauna a Asibiti kafin a sallame su.
Lilly tace a taho mata da wayarta, zata gayawa ƙawayenta dan su sanar ba ta da lafiya a makaranta.
Haka kuwa akayi, koda aka kawo wayar Lilly ta duba, kusan missed calls goma sha na Sir Nazir. Tsaki tai ta ajiye wayar tana ƙunƙuni.
"Dan Allah ni dai in ba zaka iya zuwa ba, ka barni inje da kaina in ɗakko Sadik"
"Saboda kece sarauniyar 'ya'ya ko? Saboda rashin ta ido seki je ki cewa sirikan ki su baki ɗanki ko, to bari kiji in gayamiki wallahi Kika je garin nan da sunan ɗakko Sadik, ko kika ke ba tare da izina na ba wallahi a bakin Airenki!"
Ras! Gaban Mother ya faɗi, dan Abba be taɓa makamancin wannan furicin ba, duk laifin da za tai masa, lallai wannan karon he is very serious on what he is saying.
Kuma da ya gama maganar yai tafiyarsa ya barta a gurin, aikuwa ta zauna sosai tana kuka.
Faruk ne ya shigo falon, ya tarar da ita zaune ta ma faman hawaye.
Yasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi, ya taka a hankali yaje kusa da ita ya zauna, ya fara share mata hawaye yace "haba Mother, dan Allah kiyi haƙuri da batun Sadik, ki kwantar da hankalinki ki dena wannan kukan, baze maganin komai ba"
"Haba Faruk, dole in kuka Sadik yarone ƙarami, be taɓa nesa dani na kwanaki masu yawa ba, amma an baro shi a ƙauya, in da be taɓa zuwa ya zauna ba, kuma an hanani magana"
"Hakane ba a kyauta miki ba, amma dan Allah kiyi haƙuri Mother, duk fa kukan nam da kike be canza Komai ba, kiyi haƙuri kukan ba shine magani ba, insha Allah in dai Sadik ne zasu dawo miki da abun ki"
Haka yaita rarrashin Mother, yana cikin rarrashin nata sega Khairat ta zo Gidan, dan ta cigaba da taya Mother zama, dan ta ɗebe mata kewa.
Da daddare bayan magariba tuni 'yan dubiya sun fara zuwa duba Lilly, ta samu Mummy ta tafi rakiya ta ɗaga wayarta ta kira Haseena a wayar mamansu.
Maman Haseena na ganin Lilly ce ta bata wayar.
"Hamshaƙiya, ina kika shiga ne yau kika ƙi zuwa school bayan kin san exams ake?"
"Bani da lafiya ne" Lilly ta bata amsa.
"Subhanallah, meya sameki ko Asmar ce ta ta shi?"
"A'a zazzaɓi ne ina Asibiti anyi admitting ɗina, dan Allah ku sanar a school, duk da ma dai Mummy zata turo uncle ya sanar"
"Eyya Allah ya baki lafiya, se munzo dubiya habibin naki kuma ya sani?"
'ke dalla ƙyaleni da wannan mutumin se anjima" Lilly ta katse wayar.
Gaba ɗaya Sadik ya koma salihin ƙarfi da yaji, ba sawa ba fitarwa daga masallaci se ɗaki se zaman fada.
Nana kam tausayi yake bata yanzu sosai da sosai, duk ranar da ta tabattar za a girka abunda ba ze iya ci ba, se ta nemo wani abun da zata bashi a ɓoye yaci, ze karɓa ya cinye amma baze iya godiya ba.
Nana na cikin turakar Hakimi tana masa surutu, yace "je ki kiramin wancan Yayan naki"
Nana ta miƙe tana faɗin "ni ba Yayana bane" tai waje zuwa ɗakin Sadik.
Yana zaune yayi shiru yana zancen zuci Nana tace "kai ka zo ana kiranka"
Ya ɗago ya kalleta ya maida kansa ya sunkuyar.
"Da kai fa nake"
"Ki ka kuma cemin kai sena ɓarar da ke a gurin nan"
"An faɗa, kai kai kai ƙaton kai"
Sadik ya tsani tsiwa, shiyasa Farhan ke burgeshi akwai girmama mutum ba wannan tsigaggaiyar ba.
Yasan yanzu in beje kiran ba se ya janyowa kansa wata damuwar, haka ya miƙe ya biyo bayan Nana.
A tsakar gida ya tarar da Nana, ta kamo kunnen wannan muzurun da take cewa Autan Mother.
Ta riƙe kunnensa tana cewa "kai dai jarabarka tayi yawa, ga masifa ga ba'a maka gwaninta sena cillar da kai a waje, ɗan bantan uban me dogon kunne"
Sarai Sadik ya san da shi take, Sedai ganin ba kowa a tsakar gidan, yasa ya ƙarasa in da take ya danƙota ya miƙar da ita tsaye.
"Wayyo Allah na Inna!" Ta faɗa tana rarraba ido
Sadik ya tsare gida sosai, ya ƙare mata kallo yace "Ni sa'anki ne? Ko na miki kama da abokin wasanki?"
"Dallacan ni ka cikani, meye haka Inna wallahi ya taɓa ni"
"Uban me zan taɓa a jikin naki? Shashasha ƙwailar banza da ta wofi, mara Kunya wallahi kika kuma cemin kai, ko na taho kika ɗau wannan magen kina zagi sena miki rashin mutunci sena kikkifa miki mari"
Inna Kuwa a tare suka fito da Hakimi suna kallon ikon Allah, Sadik ya riƙe hannayen Nana, shi kam ko a jikinsa ya cigaba da yiwa Nanan warning.
"To ni ka sakarmin hannu, ni ba 'yar Iska bace da zaka riƙen hannu"
"To waye ɗan iskan? Wallahi idan ba ki kiyaye ni ba sena zubar miki da haƙora, stupid girl"
"Wallahi ni ba stupid bace" bakin Nana yaƙi mutuwa, se zubo masa rashin kunya kawai take.
Hakimi ya sake jinjin tsantsar fitsara irin ta Sadik, ganin idonsu ko a jikinsa balle ya cika Nana ko ya dena zaginta.
Inna kam riƙe haɓa tai tana ganin ikon rabbi.
Sannu a hankali Hakimi ya tako zuwa in da suke tsaye, ya cire hannun Sadik a na Nana.
"Kai yanzu ka rasa da wa za kai faɗa se ƙanwarka? Kai ba abun kunya bane a gurinka?"
"Allah ya rufan Asiri wannan ta zama ƙanwata, ni ba ƙanwata bace"
"To mecece ita a gurin ka?"
Hakimi yai maganar yana kallon ƙwayar idon Sadik.
Sadik ya sunkuyar da kai, saboda tsananin kwarjini da dattijon yai masa.
"Ni dai a ja mata kunne ta dena shiga sabgata, in ba haka ba sena ji mata ciwo"
"Ahh kasheni za kai, ji min ciwo ai ba kai da yawa ba"
Inna tace "dan ubanki ki biye masa yai miki illa, uwar marasa kunya"
Nana ta tura baki tace "dama ai yace ya tsaneni, seya kashe ni ya huta kawai"
"Eh na tsane ki" ya maimaita jijiyoyin kansa suna miƙewa, alamar ya zuciya ƙwarai.
Hakimi ya kama hannun Sadik suka fita waje daga gidan.
Suna fita Inna ta dirarwa Nana da faɗa "ki cigaba da masa rashin kunya, idan yai miki illa ke kila jiyo, kuma wallahi kika kuma bari ya taɓa jikinki sena miki dukan tsiya, 'yar banza shashasha"
"Inna fa shine kawai ya riƙen....."
"Zakimin shiru ko sena zo na tura kanki a cikin murhun nan" Nana tai shiru tana zumɓura baki.
Wani ɗaki Hakimi ya kai Sadik, ya sa Sadik ɗin ya zauna yana ta huci, ya kalli Sadik yace "meyasa ba ka da ta ido ne? Kasa ƙanwarka ta raina ka, kuma a Gabanmu babu ko ta ido, su baka san mata haƙuri ake da su ba?"
Hakimi yai maganar yana monitoring moves ɗin Sadik.
Sadik yaƙi magana ya sunkuyar da kai yana huci.
Yace "shikenan, ka zauna a nan ka baro musu cikin gidan, ka dena ganinta kana jin haushinta, idan ka huce zaɓi ya rage naka, ko ka zauna a nan ko kuma ka koma ciki.
Amma kai baka san a cikin horon da nai niyyar yi maka, wani ƙasurgumin ƙauye na so kai ajiyarka ba, amma ta dage ta dinga bani haƙuri? Ita rayuwa ka kiyayi furta ka tsani mutum, mussaman a gaban makusantan sa in ba haka ba wataran za kai nadama"
Sadik be ko gezau ba, har Hakimi ya gama nasihar sa ya baro shi a ɗakin.
Baban Lilly da sassafe ya dira, dan an sanar masa Lillyn ba lafiya harda ƙarin jini.
Dogo ne sosai, giant baƙi ne ga idanunsa jawur kamar gauta, alamun girma sun bayyana a tare da shi, dan lokacin retire ɗin sa ya kusa, kallo ɗaya za kai masa ka ga tsagwaron kwarjini a tare da shi.
Yana zaune a bakin gadon Lilly, ya riƙe ɗan ƙaramin hannunta a nasa, hannu ɗaya yana shafa kanta yace "Sannu Mamana, ya kike jin jikin naki?"
Cikin shagwaɓa tace "Daddy na warke ai, ni sonake a sallame ni mu koma gida, am tired na gajinda zaman Asibitin nan"
"Ohhh sorry, amma idan ya kamata a sallame ki za'a sallameki ai, haryanzu jikinki ba ƙwari"
Lilly tace "Daddy na gaji ne"
Uace "ok shikenan, bari likitan ya shigo in masa magana"
Ana haka se ga likitan ya shigo hannunsa ɗauke da file ɗinta yana dubawa.
Baban Lilly yace "yawwa Doctor dama nemanka nake"
Doctor yai murmushi yace "Ai gani nazo"
"Doctor jaririyata fa ta gaji da zaman nan, ai discharging ɗin ta Please"
Doctor yai murmushi yace "wannan ƙatuwar budurwar ce jaririya?"
"Jaririya ce mana, aka ban zani ai goya abata zanyi, fifteen to sixteen years ai jaririya ce haryanzu"
Doctor yai murmushi yace "in ba zaka damu ba yallaɓai ina son ganinka a office ɗina"
Baban Lilly yace "ba damuwa muje"
Gaban Lilly yai mummunar faɗuwa, saboda fargabar kar likita ya gano abunda ya sameta ya gayawa Babanta, ai take wasu irin hawayen tsoro suka fara zubo mata.
Wayar ta ce ta hau ruri ta duba taga Nazir ne, a fusace ta ɗaga wayar tace "wai meye ne?"
"Ban gane meye ba? Ina ta kiranki ba kya ɗagawa, ashe kina Asibiti harda ƙarin jini!"
"Tabbas ina Asibiti harda ƙarin jini, babana ya dawo likita ya gayyace shi Office ɗin sa, dan haka ka shirya komai ze iya faruwa!!!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Jikin sir Nazir ne ya ɗau rawa jin abunda Lilly ta faɗa.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Lilly yanzun meye abun yi?"
"Nima ban sani ba, sedai kawai muyi ta Addu'a, ni kaina a tashin hankali nake wallahi".
Doctor kuwa suna zuwa Office ɗinsa, Daddyn Lilly ya nemi guri ya zauna, ya kalli baban Lilly yace "yallaɓai, ba yau na fara duba iyalinka ba, mun daɗe tare muna wannan al'ammura na kula da rashin lafiyar iyalinka"
Daddy yace "hakane, ina jinka"
"To su dai 'ya'ya amana ce a hannun Iyaye, iya binciken da mukai bamu gano abunda yai dalilin rasa jinin Fatima haka ba, sedai shawarar da zan baku shine a saka ido sosai a kanta, a kula da Abincinta sannan a kula da dukkan motsinta, da abubuwan da take yi"
Daddy be kawo komai a ransa ba yace "dan dai wannan ai bakomai insha Allah za'a kula, tunda ta samu sauƙin jikin nata harta fara complain, a sallame ta haka, kar a takurata da yawa"
Doctor yace "bakomai, yanzu zan sallame ta insha Allah"
Daddy yace "to shikenan, na gama clearing bills ɗin mu ko?"
"Eh, tun ranar ai an biya komai, se fatan Allah ya ƙara lafiya"
Daddy yace "Ameen ya Allah, godiya nake doctor"
Suka sake yin musabiha, sannan Daddy ya koma ɗakin da Lilly ke kwance.
Ya tarar da ita a zaune, tayi zuru zuru, kamar mara gaskiya.
Daddy uace "Baby na ya dai?"
Tace "bakomai"
Yace "nayi magana da Doctor, yanzu ze zo ya sallame ki, mu tafi gida zan kira Maman ki ba se ta dawo Asibitin ba tafiya za muyi"
Lilly tai murmushi tace "Amma Daddy meya ce maka?"
"Ina ruwanki da abunda yacemin? Bari ya zo ya sallame ki mu tafi gida.
Duk da be gayamata abunda likitan ya gaya masa ba, amma ta samu sassauci dan ta sam da an gano abunda ya sameta, to da tabbas zuwa yanzu kashinta ya bushe.
Washegari bayan an sallamo Lilly 'yan ajinsu suka dinga zuwa dubata, kowa yana mamakin abunda ya sameta da harta kaita ga ƙarin jini, ga fuskarta duk tayi wani iri ta kukkumbura.
Kasancewar yau Juma'a, Sunusi yaci ƙarfin aikin da yake akan Sadik da Farahn, kasamcewar aikin ba kaɗan bane, bayan an sakko daga sallar juma'a, zuwa la'sar yasa wani yadinsa ruwan ƙasa, ya tafi zance gurin Farhan.
Farhan kuwa tana ɗaki, tana lissafin yadda kwanaki suke ja, amma babu ɗuriyar Sadik ba ta san a wani hali yake ba, dama ya gayamata wayarsa ba caji.
Cousin ɗinta ne me suna Hauzaifa ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da Farhan ke ciki.
"Waye" ta faɗa cikin sassanyar muryarta.
"Farhan kinyi baƙo"
"Wane baƙon?"
Huzaifa yace "Wannan Almajirin ne, wai in masa sallama da ke, dan ya raina min hankali ma wai ni ya aika"
Tsaki Farhan tai, tayi shiru taƙi ko motsawa.
Umma ce ta fito daga ɗakin ta tana faɗin "Huzaifa, kar ka sake ce masa Almajiri, ai ka san sunansa, kuma kasan shi ze Auri 'yar uwakka idan yaji kana faɗa masa haka baze ji daɗi ba"
"Umma dan girman Allah ku samu mutum nagari ku aurawa Farahn, wallahi basu dace da wannan Sunusin ba, haba dan Allah yaje ƙauyensu ya nemi dai dai shi mana, se wannan masha Allah ga ilimin addini da na zamani ka.."
"Kai Huzaifa ni kake gaywa haka? Shikenan dan mutum be ilimin zamani ba se ku dinga masa kallon be kai ba? Wace ita da ba zata aure shi ba? Masu ilimin bokon nawa ne sukai auren suke wahalar da matan, wannan da iliminsa da sana'arsa amma ka dinga kushe shi, kul kar ka kuskura in sake jin makamanciyar wannan maganar, ke kuma ki fito kije kin barshi a tsaye".
Farhan ta sako hijjabi ta fito, sedai idan har idon Huzaifa daidai ya gano masa, kuka Farhan take yi.
Gaba ɗaya yaji tausayinta ya mamaye shi, wannan wace irin rayuwa ce haka? Ace ba za'a bawa mutum zaɓin wanda ze rayu da shi ba sedai a zaɓa masa, hakan ba haramun bane amma babu tabbacin an tuntuɓi Farhan anji ta bakinta akan mutumin nan, kawai ake so a ƙaƙaba mata shi"
Farhan ta fita jiki a sanyaye, tana zuwa ta tsaya ta ɗauke kanta daga kallonsa.
Yace "Hmm babu ko gaisuwa 'yan mata?"
Ko kallonsa ba tai ba ta cigaba da kallon Guri ɗaya.
"Ki juyo mana in kalli wannan kyakykyawar fuskar tawa mana"
Wani banzan kallo ta watsa masa, tana ji a ranta wannan kalaman daga bakin Sadik suka dace su fito.
"Lokacin yayi da Yakamata ki kwantar da hankalinki, ki tsaya mu fuskanci juna, duk wannan haɗe ran da kike na ze canza Komai ba"
Hawaye na zuba daga idonta tace "wai dan Allah me kake so dani ne? Me nai maka haka?"
'ban fahimci me kike nufi ba"
"Meye dalilin da yasa kaje neman Aure gurin iyayena ba tare da amincewa ta ba?"
"Saboda haka Shari'a ta ce ayi, in nemi izinin su kan in zo gurin ki"
"Amma ko da shari'ar tace ai haka, ka san ba zan iya yiwa iyayena musu ba, kuma bani da niyyar wulaƙanta ka, amma zan gaya maka gaskiya wallahi Sunusi ka shiga hakkina, ba ka kyauta min ba"
Murmushi yai yace "Allah ko? Aikuwa sedai kiyi yadda zaki, ko ki haƙuri ko karki yi, mahaifinki ya riga ya bani ke, dan haka gara ma ki haƙura, idan ma saboda wannan ɗan yaron kike min wulaƙanci gara tun wuri ki cire shi daga ranki, idan ma baki cire shi ba ni zan cireki daga ransa"
"Ba zaka iya raba Soyayya ta da Sadik ba, saboda haɗin Allah ce, shi ka ɗai ze iya warware ta, idan kuma ka nace seka rabani da shi ka aureni, ni kuma zan barka da Allah yai ma hukunci dai dai da abunda kai mana"
"Wannan kuma iyayenki zaki samu ki gayawa, bani ba"
Wani irin malolon takaici ne ya tokarewa Farhan a zuciyarta, dan ba ta ƙaunar duk wani dalili da ze sa a ci mutuncin iyayenta.
Juyawa tai ta shiga gida, ta samu soro ta zauna ta saka kuka.
Huzaifa ne ya zo ze tafi, yaga Farhan a durƙushe tana kuka.
Cikin tsananin tausayinta Huzaifa yace "Farhan lafiya kuwa? Wani abun yai miki?"
Cikin hanzari ta ɗago, dan bata san Huzaifa ya zo gurin ba, tai saurin goge hawayenta tace "bakomai fa, har zaka tafi?"
Huzaifa cikin damuwa yace "haba Farhan, duk da babu wata tazarar shekaru a tsakanin mu, amma ni ba wanda zaki ɓoyewa damuwa bane"
Kawai ta kuma fashewa da kuka.
"Kiyi haƙuri Farhan, na san ba kya son Sunusi ko?"
Farhan ta jinjina masa kai da sauri.
"Kiyi haƙuri, wallahi ni kaina bana ƙaunar wannan Sunusin, amma dan Allah ki dena kuka, insha Allah ba me miki Auren dole, dan sam baku dace da shi ba, amma ki dena kuka"
Ta share hawayen ta tace "insha Allah na dena, Nagode sosai Huzaifa, ka gaida gida".
Sunusi kuwa harya bar ƙofar Gidan, ya haɗu da Abban Farhan yana dawowa gida.
Yana ganin Abban Farhan, ya zube har ƙasa yana gaishe shi.
Abba yace "A'a Alaramma, kwana biyu ka ɓuya"
Sunusi yace "wallahi Abba ina nan, Yanzu ma daga gidan nake"
"Ahh to Masha Allah, kaje gurin Farhan ɗin kenan?"
"Eh naje" yai maganar yana ɗan sosa ƙeya, alamar da Magana.
Abba yace "ya dai ko akwai matsala ne?"
"Eh to Abba kusan akwai ɗin kenan zance"
"Subhanallah, matsalar menene?"
"Eh wato Abba, ita Farhan ɗin ce na kasa gane kanta gaba ɗaya wallahi, da farko dai ta amince tana sona, to kuma katsam se naga wani ya kawota gida a mota, nai mata Magana amma naga kamar hankalinta yafi karkata kan shi wancan me hannu da shunin, kuma ma dai yarone