Showing 54001 words to 57000 words out of 259198 words
Chapter 19 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ta zaci ɗan fita falo tai zuwa harab zata dawo, amma taji shiru ba taga motsinta ba, Nan da nan ta fita nemanta da kanta, sedai ba Nana ba alamarta a gidan nan.
Hankalin Inna ya ɗaga ta shiga tanbayr masu gadi, da masu aikin gidan amma suka ce ba su ga Nana ba.
Da hanzari Inna ta koma babban falo, wanda yai daidai da fitowar Alhaji Abdullahi, kallo ɗaya yaiwa mahaifiyar ta sa ya fuskanci akwai matsala.
Cikin damuwa yace "Hajiya Inna, lafiya kuwa?"
"Yarinyar nan ce ban gani ba, tunda na farka ban ganta ba, bata gidan nan"
Yace "Subhanallah, garin yaya babu kuma wanda ya aiketa?"
"Bana tunanin hakan, dan ba in da ta sani"
Mother ce ta fito ita da Sadik, daga sashen ta, tai tozali fa su a tsaye cirko cirko.
"Lafiya kuwa?" Mother ta tanbaya.
Alhaji Abdullahi yace "Nana ce ba'a gani ba, tun ɗazu ba ta gidan nan an tambayi masu gadi sunce ba su ganta ba, ka ga Sadik ka fita ka ɗan zazzaga layu kan nan ko wani gurin ta fita.
Ɗan buɗe baki Sadik yai yace "Abba ni ta ina zan fara neman ta? Ina zan nufa?"
"Koma ina ne ka nufa, kaje ka zazzaga ko Allah ze sa ka ganta"
Ran Sadik yai matuƙar ɓaci, ya bar falon yana ƙunƙuni, wai ya fita nemanta se kace wata Akuya.
Mother kamar za tai magana, amma ta fasa dan ta kula kamar kwanan nan Inna zuga Alhaji Abdullahi ta ke, da ta ɗanyi masa kuskure kaɗan se ya fara mata masifa.
Nana kuwa tare suka shiga Kitchen da Jidda su kai girkin rana, suna yi Jidda na cin dariyar Nana, babban abunda ke ƙara bata mamaki da burgeta game da Nana be wuce yadda Nanan ke magana da manyance ba, a shekarunta wasu abubuwan tayi ƙanƙanta da faɗinsu, amma ba abun mamaki bane, tunda a hannun tsofaffi take.
Yayin da ita kuma Nanan ke manakin yadda Gaba ɗaya suke magana da iyayi, magana ɗaya biyu se anyi turanci, turancin ma me wuyar ganewa irin na turawa, ga yadda Jiddan ke zubawa Dr. Shagwaɓa a gabansu ba kunya.
Se bayan azahar, sanan Faruk yace Nana ta tashi su tafi.
Jidda tace "gaskiya uncle ka barmin Nana, idan zasu koma se ka zo ka tafi da ita"
Faruk yace "taɓ, ai wallahi kakarta ba zata yadda ba, ki bari in kin tambayi izinin Hajiya Inna, shikenan"
Nana ta shiga ran Jidda sosai, ta haɗa mata sha tara ta arziki, su kai hotuna sannan suka nufi komawa gida.
Sadik kuwa yana tafe yana masifa ya koma gida yace shi be ga Nana ba, gaba ɗaya aka dinga jimamin in da Nana ta shiga, hankalin Inna ya gama tashi, Alhaji Abdullahi yana ko report za'a kai gun 'yan sanda.
Turo ƙofar ɗakin Nana tayi, hannunta rungume da kaya ta shigo da Sallama, gaba suka waigo suna kallonta.
Se yanzu ta sha jinin jikinta, ta tuna ba ta sanarwa da Inna zata fita ba.
A fusace Inna tace "daga ina kike?" Kafin ta amsa, sega Faruk ya shigo falon shima.
Ya kalli su Abba yace "Abba lafiya na ganku a nan?"
Abba yace "Nana ake ta nema, kuma se gaku tare"
Faruk yace "ai ni ne nace ta rakani gidan dr. Mu ka kai musu Abinci, daga nan kuma muka zauna se yanzu, laifina ne ayi haƙuri please".
Wani uban tsaki Sadik ya ja yace "wallahi wannan Yarinyar ba tayi ba, ta sa aka wahal da ni ina zaga layuka nemanta kamar ɓarawo"
Murguɗa baki tai tana hararar Sadik, ya ƙara harzuƙa yace "wallahi nazo gurin nan sena tataka ki, na tsani yarinyar nan tunda ta zo gidan nan take wahalar da mutane'
"Seka kasheni ai tunda ka tsaneni, masu gida na ga ma kunkuru da yake yawo da gidansa a ka, se ka naɗa gammi ka ɗau gidan naku a bayan ka ai"
Inna tace "rufemin baki kan in zo in gurza wannan shegen bakin naki, kai kuma kayi haƙuri kaji zamu bar muku gida, ba kai kaɗai ba naga alamar matar gidan kanta mun isheta, zamu tafi Insha Allah, gara mu tafi ka dena ganinta kana ƙara tsanarta"
Mother tace "to ni kuma meye nawa a ciki?"
Faruk yace "dan Allah kuyi haƙuri, dul laifina ne wallahi"
Abba kam ya fusata sosai da abunda Sadik yayi, ya tabatta abunda Inna ke faɗa yaransa ba su da tarbiyya, dan haka yace "Sadik faɗan da nai maka ta dama ya shiga ya fita ta hagu ko? A gabana ka ke cewa ka tsani Nana ko, duk da matsayin ta a gurina, Nagode amma ka sani nafi ƙaunarta fiye da kai ɗan da na haifa a cikina, shashasha mara ɗa'a"
Da sauri Sadik ya ɗaga kai ya kalli Abba, jin Abba yace wai ya fi son Nana da shi.
Nana kam sumsusm ta wuce masaukin su, Inna ma ba ta sake cewa komai ba ta bi bayan Nana, taje ta sameta a ɗaki, ta dinga mata faɗa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, dan seda Nana tai kuka.
A lokacin Inna ta saka Nana ta fara haɗa musu kaya, dan ta ƙudirce a gobe in Allah ya kaimu zasu bar gidan.
Da daddare Sadik ya buɗe ɗakinsa na cikin ƙaton falon da ke daf da ƙofar sashin Mother, saboda yanzu gidan ba kowa.
Ƙofar ɗakinsu Inna a buɗe tana jiyo hirar da Mother take da Sadik.
Sadik yace "Mother, nifa banji kin yaba sirikar taki ba"
Mother tace "ai sirikata son kowace ƙin wanda ya rasa, ga ilimi ga kyau ga gayu, ai Jidda tayi ta ko ina"
Sadik yace "Mother ba wannan ba, yarinyar da na kawo ku gaisa da ita Ranar Mother's evening fa"
Mother ta ɗanyi shiru tace "wace yarinyar ce? Namanta wallahi"
"Mother, wata Fulani girl da na kawo miki, har kuka gaisa kina magana da su Anty Naja lokacin"
Mother tace "to ai Mutanen da yawa ba lallai in tuna ba"
"Please Mother ki tuna ta mana"
"Kai ka ƙyaleni, ni ban tuna ba, ya ma akai ta zama surikata?"
Ɗan sosa kai yai yace "eh, in law ɗinki ce to be in the next couple's of year's, not year's ma in next year Insha Allah"
"Wai tsaya, ba dai budurwar Faruk bace, aikuwa zeci ƙaniyarsa ze gamu dani, he better concentrate in his studies, karma ya ɓatawa 'yar mutane lokaci, shine y turoka da ita?"
Sadik yace "Ohhh my God, Mother she's my fiance, budurwata ce fa"
"What! Me kace?"
"Mother you heard me fa, and you are still asking me"
"Ai dole in sake tambaya, wace irin maganar banza ce wannan? Ina kai ina wata budurwa, ko secondary School ba ka gama ba"
Ɗan kwaɓe fuska yai yace "Mother, am finishing secondary School this year insha Allah, zan kammala secondary School a wannan shekarar, Abba yace in zaɓi kowace school nake so a duniya ze kaini, kan in gama degree ta kammala secondary ita, ni da ze yuwu ma, da se mu tafi can in da zanyi karatun ni da ita"
Wani banzan kallo Mother ta watsawa Sadik, ta ja tsaki ta maida hankali kan TV.
"Mother i meant what I said, Aure nake so inyi please, ki sa baki dan Allah, kinga ko da kuɗin plazar mu zan iya riƙeta, se Abba ya suponsoring karatunmu, ina son Yarinyar ne Please Mother ki sa baki, dan...
"Shut up Sadik!" Mother ta faɗa a tsawace.
"Kasan me kake faɗa kuwa, haryanzu ba ka cika shekaru goma sha takwas ba, uban waye ze maka Aure, me kai achiveing a rayuwar ka da har zaka fara tunanin wani Aure? Get out from my side, kaje ka kama litattafanka, kayi karatu ka zama wani abu kafin ka fara wata maganar aure, Allah ya ƙara nunamin kayi Wannan zancen"
Sadik ya ƙulu da jin zancen Mother, dan gani yake kamar kalaman nata na nisanta shi da mallakar Farhan ɗin.
Fuuuuu ya tashi ya bar falon a fusace, ya fasa kwana a ɗakinsa na cikin gida da yai niyya.
Inna kam duk da taji hirar ta su girgiza kai tayi, da jinjina gaɓunta irin na wasu iyayen na wannan zamani,kamata yai yadda yaran suka zama na zamani, iyaye ma su zama na zamani a gurin tarbiyya.
Suna ta ihun ilimi ilimin zamani, amma takasa amfani da hikima da ilimin akan ɗanta.
A fakaice yana wa mahaifiyarsa nuni da waye shi ne? Da kuma abunda yake so amma ta kasa ganewa, hakan yana faruwa a farkon a ƙuruciya, wanda wasu yaran kan zo musu da RUƊANI, idan ba su samu kyakykyawar kulawa da shawarwari ba se a samu matsala.
Yanayin Sadik, da abunda suka dinga yi shida abokansa a gurin bikin nan kawai, ya isa ya nuna maka waye shi, a ɗan zaman nan nata tana ankare da halayyar yaron.
Ba dan gudun shiga abunda be shafe ta ba, da tayi abunda ya dace akan Sadik, amma tayi alƙawarin fita daga sabgar su gaba ɗaya, idan lokaci yayi iyayen Sadik zasu hankalta, da maida hankali akan yaransu, sedai zata taya su da addu'a Allah ya shirya mata zuriya ya tsaresu da taɓarɓarewar ƙarshen zamani da RUƊIN ƘURUCIYA!
Domin gyara Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.
Kar a manta a garzaya shafin Arewabooks, domin cigaba da samun littafai na, kuyi following ɗina @Ayshercool.
https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
RUƊIN ƘURUCIYA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Writer of
WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)
_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_
⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️
SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.
Sadik a fusace ya koma BQ, ya shiga ɗakinsa ransa na masa ƙuna.
"Wannan wace irin rayuwa ce? Boko boko boko! Kamar bokon nan ce tikitin jin daɗin duniya, shikenan dan mutum zeyi boko baze aure ba?"
Wani tsakin ya kuma yi, tare da fesar da iska daga bakinsa.
Meyasa Mother taƙi goya masa baya a wannan karon? Meyasa ita kullum take kallon shekarunsa da ƙanƙantarsa?
Ɗan gajeren tsaki ya kuma ja, ya haye gadonsa ya kwanta yai rigingine, take Farhan ta kuma faɗo masa, wani irin shauƙin sonta na ƙara ratsa shi sannu a hankali tabbas son da yake mata ba RUƊIN ƘURUCIYA ba ne, soyayya ce da ba ruwanta da girma ko yarinta.
Wayarsa ya ɗakko yana kallon hotunan ta da yake wayarsa, she's cool and Beautiful, uwa uba ta na da tarbiyya da ɗa'a a nutse take.
Ya shafi screen ɗin wayar ta sa, ya lumshe ido yace "I love You Farhan" yai Maganar a hankali, yana sauke ajiyar zuciya.
Kamar wanda aka tsikara, ya tashi zaune, ya janyo system ɗin sa, ya kunna, Series ɗin nan da yake kallo ya nemo, ya kunna ya cigaba da kallon sa ba tare da fargabar Komai ba, a tunaninsa hakan ze ɗauke masa hankali da rage masa damuwa.
Ya cigaba da kallo, daga episode ɗin da ya tsaya a baya, Film ɗin yana cigaba da nuni da tsantsar soyaya me tsuma zuciya, sedai ba ta sauya zani ba, akwai adult content a cikin Film ɗin, kusa kaso arba'in ɗari na film ɗin in da yafi karkata kenan.
Rikicin film ɗin na ƙayatar da shi, rikicin masarauta da na Soyayya.
Amma maimakon hakan ya ɗebe masa kewa daga damuwarsa, sema sake faɗawa wata damuwar da yayi.
Kamar wanda aka mintsuna, haka ya kashe socket ɗin da system ɗin ke jone, ya rufe System ɗin ya ja wani uban tsaki, ya kife akan gadonsa yana sauke numfashi sama sama.
Haka yai ta juyi, tare da jera tsaki ba adadi, kan bacci yayi awon gaba da shi.
Da sassafe Inna ta fito falo, ta tarar da Mother ta fito ta na bada umarni ga masu aikinta, akan abunda za a girka.
Mother ta kalli Inna tace "Ina kwana"
Inna tace "lafiya ƙalau, nace Bawan Allah ya tashi ne?"
"A'a be tashi ba" Mother ta bata amsa.
"Ta so min shi" Inna ta faɗa ta na zama.
Mother tace "ba ya son a tashe shi idan yana bacci, ya hana tashin sa idan ba shine ya tashi ba"
Inna tace "umarni na ne, a tasomin shi"
Mother ta juya tana ɗan hura hanci, dan takurar Inna tayi yawa.
Kusan 10minutes se ga Mother ta fito, ita da Alhaji Abdullahi.
Sedai Inna ba ta falon, Alhaji Abdullahi yace "bari in duba ɗakin su"
Ya nufi ɗakin Inna, yana zuwa ya tarar da ita a gefen katifa a zaune.
Ya rusina yace "barka da safiya"
Inna tace "Yawwa, ka tashi lafiya?"
"Alhamdilillah, amma yana ga Kamar kin tattare komai?"
Inna tace "Ehh, dama nace ai maka magana ne da azahar kasa a maida mu gida, zaman ya isa haka na gama abun da ya zaunar da ni"
Alhaji Abdullahi yace "Amma Inna da wuri haka cikin gaggawa? Ko dai wani abun akai miki a gidan?"
"Babu ɗaya, kawai ina son tafiya ne kawai"
"Amma Inna, ba ki gayan da wuri ba ba'a shirya muku komai na komawa ba"
"Ni ba wani abu da nake buƙata daga gurinka, abu ɗaya ne zan sake maimaitawa shine ka kula da tarbiyyar yaran ka, ka saka ido sosai ka gane meye damuwarsu sannan meye mafita ga damuwar ta su ba wai abunda kai kake so ba"
Shi dai Alhaji Abdullahi be gama fuskantar in da maganganun na Inna suka sa gaba ba, amma yace "Insha Allah za'ai yadda kika ce"
Tace "Yawwa da azahar zamu tafi Insha Allah"
Ya tashi ya fita jikinsa a sanyaye.
Yau sam Sadik yaƙi shiga cikin gidan, ko gurin Mother be je ba, saboda ransa a ɓace yake gaba ɗaya.
Yana zaune a falo yana video game, Faruk ya fito daga ɗakin sa yace "kai Muje Abba yana neman mu"
Sadik ya kalleshi yace "ina fatan dai ba wani abun nai ba?"
Faruk yace "nima ban sani ba, kawai dai ya kirani a waya ne Yanzu".
Sadik yace "ina zuwa"
"Karfa ka ƙi zuwa ace ban gaya maka ba"
"Kayi gaba kawai, zan zo"
Faruk ya fice daga falon nsau.
Yana isa harabar Gidan yaga Alhaji Abdullahi ya yo wa Su Inna rakiya, an saka Akwatin su a Mota.
Da sauri ya ƙaraso yana faɗin "ya naga haka kuma?"
Abba yace "eh za su koma ne, shiyasa na kiraku kuzo kuyi sallama"
Cikin damuwa Faruk yace "tafiya ba sanarwa haka? Inna meyasa zaku tafi?"
"Gidanmu zamu koma, ai mun zaunu a gidan nan, kuma gashi za'a koma makaranta"
Faruk yace "Inna banji daɗi ba, ke ki tafi ki bar mana Nana a nan"
Inna tai murmushi tace "Inaa ai baze yuwu ba, tana katara ta"
Wani Mugun kallo Mother ta watsawa Faruk, wanda ya sashi mamakin me yai ake masa Wannan kallon.
Sadik ne ya ƙaraso in da suke ya gansu a tsaye, ya kalli Abba yace "Abba gani".
"Dama Inna ce za su koma, na kiraku kuzo kuyi musu sallama"
Sadik ji yai kamar yayi tsaki, amma ya maze ya kalli Inna yace "ku gaida gida"
Maimakon Inna ta amsa se kallon sa da take, Tun daga sama har ƙasa.
Ɗan tsuke fuska yai yana basarwa, dan ya rasa dalilin da yasa Inna take masa irin wannan kallon a duk sanda suka haɗu.
Yana ɗaga ido, sukai ido huɗu da Nana aikuwa ta galla masa harara.
Wani Mugun kallo yai mata, ya tsani Yarinyar nan kamar ya shaƙeta.
Kan su gama sallama Faruk yai sauri ya koma BQ, har sun shiga mota da sauri ya ƙaraso, ya sa hannu a Aljihunsa ya ɗakko kuɗi da wata leda, ya miƙawa Nana.
Nana ta kalli Inna sannan ta kalli Faruk.
Yace "karɓi mana"
Inna tace "ta karɓi ledar dai, amma banda kuɗin"
Faruk yace "Inna wai meyasa kike min hakane, ina ruwanki da mu ba zan bawa ƙanwata abu ba?"
Inna tai murmushi tace "Allah ya baka haƙuri me ƙanwa"
Nana ta sa hannu ta karɓa tace "Nagode".
Yace "yawwa Allah ya kai ku lafiya, ban san zaku tafi yau ba da na muku rakiya ai"
Nan suka cigaba da Sallama aka fara jan motar a hankali, Sadik yace "Allah raka taki gona" hakan ya sauka a kunnuwan Inna, amma tai kamar ba taji ba, aka ja motar suna ɗago musu hannu.
Mother ji tai kamar an yaye mata damuwar ta gaba ɗaya, dan tafiyar su Inna ze sa ta sake a gidan ta, dan zaman su ba ƙaramin takura ne a gareta ba.
Sedai ta ƙwafe Faruk a ranta, fan ba ta gane kan wannan rawar kan da yake ba.
Sadik be shiga gidan ba, ya nufi BQ Faruk ya bi bayansa, suna shiga Sadik ya koma kan game ɗinsa, Faruk ya zauna a ɗaya daga kujerun falon Yace "Kai Allah sarki, ɗan zaman su a gidan nan na saba da Yarinyar nan wallahi, zanyi missing jokes ɗin ta, she's so Funny"
"She's crazy dai, yarinya kamar Mahaukaciya bazar bazar ba nustuwa, ga surutu kamar wata parrot, ni wallahi gara da suka tafi, dama ga tsohuwar nan kullum cikin samun ido take, tai ta min wani irin kallo wanda na kasa gane kansa"
Faruk yace "shut up Sadik, mahaifiyar babanmu ce kar ka faɗi abunda be dace akanta b, kome za tai ba dan ta takura mana take ba, yaushe rabonta da gidan ba zuwa take ba fa, kuma batun Nana, she's our blood sister like Khairat ban san meyasa ka tsaneta ba"
"Ni yarinyar ce ba tai min ba sam, ta fiye rawar kai da fitsara"
"Ni kam ba abunda tai min, ina jinta a matsayin ƙanwata"
"Lallai ƙanwa manya" Sadik yai maganar yana ajiye remote ɗin hannunsa ya bar falon.
Yana shiga ɗakin sa, ya cire wayarsa dake caji, ya ga message ya buɗe message ɗin ya duba.
"Assalam Alaikum, ina fatan kana lafiya, am missing You, kar kai min reply wayar Umma ce, idan na samu dama zan kiraka Farhan"
Jujjuya message ɗin ya dinga yi yana murmushi kamar yana gabanta yace "am missing You too Princess"
Ya cigaba da kallon saƙon, mussaman kalmar am missing You, ba ta taɓa furta masa haka ba,