Showing 93001 words to 96000 words out of 259198 words
Chapter 32 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
a tsakar gida.
Hajiya tace "Maman Farhan, wani shishshsigi na zo nai miki, amma lamari na 'ya'ya shi ɗa na kowa ne ko ba haka ba?"
Umma tace "hakane"
Tace "yawwa, Magana ce game ds Farhan, duk da na ga ku al'adar ku ce ba'a bawa ɗan fari kulawa, amma 'ya'yan da a kaiwa wannan ban da na yanzu, Farhan ta zama budurwa ba ta da ƙawar da ta wuce ki.
Ki duba yanayin jikinta, Allah ya bata garin jiki yakamata ace ta fara saka brezia saboda yanayin jikinta, Yakamata ta san mahimmancin kula da jikinta, duk da naga 'yar ta mu nutsatsiyya ce Alhamdilillah, amma saboda yanayin al'adar taku nace ni bari in zo da kaina in adana 'ya ta, da na kirata na mata magana ni da ita, amma naga ba haka yakamata ba, yanzu ina Farhan ɗin?"
Umma tace "tana ɗakinta" taiwa ƙanin Farhan ɗin umarnin ya kira Farhan.
Farhan ta fito tsakar gida, duk da takaicin da ke cunkushe a zuciyar Farhan, a haka ta gaida Hajiya.
Hajiya ta miƙowa Farhan ledar viva tace "Farhan ga brezia nan ni na siyo miki da kaina, a adana wannan baiwat da Allah ya bayar, dan ba kowa yake bawa ba, a adana yadda yakamata Allah ya fito da danƙareren miji na gani na faɗa"
Kasa ɗaukar ledar Farhan tayi, ta ɗaga kai tana kallon Ummanta, amma taga Umma na kallon wani gurin daban.
Hajiya tace "Au ba zaki ɗauka ba, jira kike se ta baki umarnin ki ɗauka, maza ɗauki kije, idan Allah ya haɗaki da 'yan banzan samarin nan na zamanin, sukai miki ba daidai ba, ko wani ya taɓa kya nutsu ai tashi kije"
Gaba ɗaya wat irin kunya ta mamaye Farhan da Umma, sam Umma ba ta ji daɗin maganganu nan da Hajiya ta faɗawa Farhan ba, wata irin kunya ta lulluɓe ta.
Farhan tace "Nagode" ta ɗau ledar ta tafi.
Tan zuwa ɗakinta ta zazzage ledar, taga brezia ce guda bakwai, sababbi ga turaren humra hadda su hoda da jambaki.
Da sauri ta miƙe ta fara gwadawa, ta saka sannan ta kawo rigarta ta mayar se ta ga rigar ta ƙara zama a jikinta.
Se kuma kawai taji kunyar kanta ta kamata, wai yau ita ce da saka brezia, farin cikin samun wannan kayan, yasa duk ta manta da wasu damu wowi da suka dameta.
Washegari da taje school kuwa, Sadik ya dinga cewa "wani abu ya canza a tare da ke Farhan, amma na kasa gane ko meye"
Ta bagarar da zancen, dan da sa idonsa ze iya ganowa, sedai tana ta so ta bashi labarin jiya Sunusi ya zo, amma ba ta son ta sa shi a damuwa.
Amarya Jidda kam, tuni ta fara dawowa daga rakiyar ƙawaye, dan ta fara fuskantar wannan Aƙidar ta su hadda baƙi ciki a ciki, dan su basu samu damar yin Auren ba, amma duk lokacin da aka haɗu a group ko get together ana hira, suna nuna cewa yiwa namiji biyayya yana kawo raini da wulaƙanci.
Tabbas namiji ya cancanci yabo da biyayya, duba da irin tarin ɗawainiya da ke kansa, duk dan ganin farincikin iyalnsa.
Ganin ta fara dawowa daga rakiyar su ne yasa suke ta faman zunɗenta yayin da wasu ke zigata wai daga yin Aure duk ta canza.
Yanzu ma chatting take, a group wata Friend ɗin su ta turo, yiwa miji girki ba dole bane, anayi ne dan kyautatawa, kuma ai cewa a kai miji ya ciyar da mata.
Nan da nan topic ya ɗau zafi, yayin da wasu ke ta supporting ɗin topic ɗin.
Jidda tai murmushi tace "haba ku kuwa, ya fita ya nemo rana, zafi, sanyi ya fita ya nemo sannan kuce girki ba dole bane, ai kuma ku gayawa kanku gaskiya"
"Ke Jidda wai ko dai dr. Naki ya jiƙa wani abu ya baki ne yasa duk kika zama haka?"
Jidda tace "ya jiƙa ya bani zumar soyaya mana"
"Ke, mu zaki gayawa magana dan kin san Namiji, to muma muna hanya" cewar Abida.
Jidda tace "dole in gaya muku magana mana, seku jira ku san namijin kuma kwayi bayani"
Maryam tai Voice message tace "ba shakka kin shahara, ke gaki kin san daɗin miji, muma muna hanya dan ubanki amma batun sakarwa miji wannan maganar babu ita"
Jidda tace "ki bari ki san daɗin mijin, se mu tabattar da hakan"
Maryam tace "ɗan labarta mana meye daɗin mijin"
Bestyn Jidda ce wato Sajida, tabi Jidda private tace "besty, a beg close that Chapter, ki rabu da wannan shashashan, suna bugun cikin ki suji sirrin Aurenki, dan Allah basar da su"
Jidda tace "kuma fa hakane besty, kai shiyasa nake yinki tawa ta amana, bari in ƙyale su kawai"
Kwana biyu Lilly ba taje office ɗin sir Nazir ba, kuma ya shishshiga ajin su, amma yaga bata zuwa kwana biyun nan.
Abun seya ɗan dameshi, ya koma gida da daddare ya ɗau wayarsa ya kira ta.
Ya kira ya kai sau uku, se a na huɗu ta ɗauka, da ta ɗauka ɗin kuma taƙi magana.
"Baki ga kiran wayata bane kika ƙi ɗagawa?"
"Na gani" ta bashi amsa.
"Amma meya hana ki ɗagawa?"
"Bani da lafiya" ta faɗa a taƙaice.
"Meya same ki?"
"Allah baby gani nake kamar ba sona kake ba, daga wannan incident ya faru, shikenan kake fushi dani duk na rame ko iya cin Abinci ba nayi, kuma ko a waya ka kasa kirana, ni wallahi ba ka sona" ta ƙarasa maganar cikin kuka.
Ya kwantar da murya yace "haba Babyna, ke in wani ya gayamiki bana sonki zaki yadda? Kawai banji daɗin yadda Farhan ta samemu bane, kuma kika nuna baki damu ba shiyasa naji ba daɗi but am sorry please"
Shiru tai taƙi Magana.
"My Lilly kina jina?"
Kukan shagwaɓa ta kuma sa masa, ya shafi gemunsa ya lunshe ido, ya furzar da iskar bakinsa yace "Babyna nace kiyi haƙuri dan Allah, ko nima so kike in fara Rashin lafiya ne?"
"A'a bana son kayi rashin lafiya"
"To shikenan, ki dawo school please, duk ranar da ban ganki ba bana jin daɗi"
"Ai da ka damu dani, da in da nake zaka zo"
"A'a Lilly ina jin tsoro ne, amma kiyi haƙuri ki dawo kinji tawan"
"To shikenan, Zan dawo insha Allah"
"Yawwa i love You so much"
Tace "Ummmm I love you too"
Haka ya zage ya cigaba da zaro manya manyan kalaman Soyayya ga Yarinyar da ta kasance ɗalibar sa, wadda ba ta fi sa'ar Autar su ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cike da ƙalubale, wataran farinciki wataran akasin haka.
Lilly ta koma Makaranta suka shirya, ita da Nazir suka cigaba da rayuwar su kamar da.
Mubarak Babba duk in da yaga Farhan se ya mata kallon warning, kallon zamu gauraya, dan ya tabattar mata da se ya rama marin da tai masa, kuma ko da tsiya ko da tsiya tsiya se ya keta alfarmar rayuwar ta.
Kasancewar Farhan ta fara gogewa Sosai, duk da rashin maganar ta amma tana da ƙwarin gwiwar mayar masa da martani ta hanayar cewa "Allah ya fika, kuma ba ka isa kaimin abunda be min ba".
Sunusi ya cigaba da zuwa gurin Farhan, sedai fa ba wata hirar kirki, shikaɗai yake surutunsa ya gama ya tafi, kanzil ba zata ce masa ba, sedai yayi ya gaji ya tafi, ƙarshe Ya kai ƙararta gurin Abba, Abba yace yayi haƙuri rashin sabo ne da ba suyi ba.
MASOMIN RIKICI!
A yaune ɗaliban SS3 na makarantar su Farhan ke kammala jarrabawar su ta ƙarshe, suna fitowa daga jarrabawar suka shiga yayyaga Uniform ɗinsu, yayin da wasu suka dinga rubutu da maka a Uniform ɗin, da gudu suka dinga tafiya in da aka aje manyan speakers na cashiya kawai saboda murna, wasu kuma litattafansu suka shiga yagawa suna watsawa sama, shakiyanci kala kala.
Yayinda zuciyar Sadik ta cika da damuwa, ta kuma tsananta harbawa, sam ba ya farinciki zuciyarsa a cunkushe take.
Cikin sanyin jiki yake takawa, Yayin da ɗalibai ke ta iface iface, suna tafiya filin rawa, gami da waƙe waƙe, kamar yadda yake bisa al'adar makaranta, duk lokacin da ɗalibai suka kammala jarrabawar ƙarshe ta fita, an dinga raye raye kenan.
Ƙofar ajin su Farhan yaje ya tsaya, ya zuba hannu a aljihunsa, ya tsurawa ƙofar ido, cikin sanyin jiki ya murɗa ƙofar.
Kamar yai tsammani, yana buɗewa sautin kukanta ya daki dodon kunnensa, yai dirar mikiya a zuciyar sa.
Ajin ba kowa se ita kaɗai.
Sannu a hankali ya ƙarasa, ya zauna a kusa da ita, ya ɗago ta ya tsura fuskarta ido yadda tai ja, fuskar duk hawaye.
Cikin sanyin jiki yake share mata hawayen, yana girgiza mata kai, a hankali ya fara Magana "ki zama jaruma mana my wife, hakan ba yana nufin rabuwar mu bane, zan dimga zuwa ganinki kan in tafi fa"
Wani kukan ne ya sake ƙwace mata, dan tana jin yadda zuciyar ta ke tsananta bugu, da wata irin mummunar faɗuwar gaba da ta tashi da ita yau, dan daren jiya ba ta rintsa ba.
Rungumeta yai a jikinsa tsam, kamar ze tsage ta shige jikinsa, ya kwantar da kansaa wuyanta, yana jin yadda take sheshsheƙar kuka.
Kasa jurewa yai, dan yadda Farhan ke jin faɗuwar gaba shima haka yake ji, a hankaliya lumshe idonsa, sega hawaye na zirarowa daga cikin idon nasa, tabbas abunda ze sa Sadik kuka, ba ƙarami bane, Farhan ta nai wani matsayi me girman gaske a zuciyar sa.
"Princess, dan Allah ki dena kukan nan haka Please, zaki karyan zuciya"
Ƙanƙame shi ta sake yi cikin kuka take cewa "ba zan iya denawa ba, gabana faɗuwa yake, ban san me ze faru ba, kuma bana son ka tafi ka barni"
Shafa bayanta ya shiga yi, yace "ba abunda ze faru se Alkhairi, kuma zan dinga zuwa ina ganinki, kina da mahimmanci a gareni Farhan"
"Dan Allah Sadik, ka riƙe alaƙawarin da kaimin Please" tai maganar cikin kuka tana zubar da hawaye.
"Duk wuya duk rintsi, in dai ina raye sena tabattar wa da duniya, Soyayyar mu ba RUƊIN ƘURUCIYA bace, ba abunda ze sauyan ra'ayina insha Allah, ina sonki Farhan"
"Nima ina sonka sosai Sadik, dan Allah karka barni"
Karo na farko tun haɗuwarsu, da ta buɗe baki tace "ta na son sa"
Ya ɗagota daga jikinsa yace "dan Allah ki maimaita abunda kika ce"
Ɗan tura baki tai, sannan ta lumshe ido tace "Ai kaji me nace"
"Dan Allah ki sake faɗa".
"I love You" ta faɗa tana sunkuyar da kai
"I love You too my princess" ya ƙarasa maganar tare da haɗe bakinsa da nata.
Farhan ta kasa hana Sadik, sema riƙe shi da tayi sosai.
Daga Farhan har Sadik ba zasu iya misalta duniyar da suka faɗa ba, sun shafe lokaci a haka, duk da yadda zukatansu ke matuƙar harbawa, saboda rashin sabo, jin Sadik ya kai hannunsa ƙirjinta ne yasa tsoro ya shigeta, da sauri ta zame jikinta tana maida numfashi.
A hankali ya kashingiɗa ya lumshe ido, yana maida numfashi, yana jinsa a wata sabuwar duniyar ta daban.
Ita kanta Farhan jinta tai wani iri, ta shiga wani yanayi na musamman da ya kan bijiro mata lokaci zuwa lokaci.
Ya zaci Farhan za tai masa mita ko ta haɗe rai, amma ya buɗe idanunsa yaga ita ma ta kashingiɗa tana sauke numfashi. Da alama ta shiga yanayin da ya shiga.
Ya kai hannu ya kuma riƙo nata, yace "Farhan" ta buɗe ido ta kalleshi, amma se taji kunyarsa tai saurin sunkuyar da kai.
Murmushi yai yace "tashi mu tafi gida, wannan kaɗe kaɗen ya cikamin kunne, ina buƙatar hutawa"
Tace "to"
Ta miƙe ta fita, ya zuba nata ido tun daga sama har ƙasa a ransa yace "Allah ka bani yarinyar nan"
Ta kalleshi tace "ka tashi mu tafi"
A kasalance ya tashi, tai gaba yabi bayanta, ta tsaya ta waigo taga yana tafiya a hankali tace "meye hakane?, ka zo mu tafi, kace mu tafi kuma kana tafiya a hankali"
Sadik yace "kece kika ja min ai"
Share shi tayi taƙi kuma cewa komai.
Ya biyota suka fito, 'yan Makaranta nata iface ifacensu da celebrating, su kuma suka tafi.
Suna tafe a mota hannuanta na cikin na Sadik, direba kam yana hangowa ta mudubi, a ransa yace "shikenan yarinyar nan, Allah dai ya tsare yasa me afkuwa bata afku ba"
Nazir ya tashi da matsanancin ciwon ciki da zazzaɓi, harta kaishi ga danganawa da Asibiti, seda aka masa ƙarin ruwa, dan haka ko Makaranta be shiga ba.
Seda aka sallamo shi ya dawo gida, Sannan ya samu ya sanar da Makaranta, ga halin da yake ciki.
Aikuwa malamai sukai tawaga guda duka je duba shi, kasancewar Makaranta na matuƙar ji da shi.
Da labari ya samu Lilly, Nazir ba lafiya ta damu matuƙa, ta shiga tashin hankali.
Ta kirashi a waya tai masa sannu, amma jin yadda yake amsawar yasa ta san yana jin jiki.
Kasancewar Gidan ba kowa se ita kaɗai, yasa ta cewa masu gadi zata gidansu ƙawarta, ta kira Mummynta a waya ta gaya mata, ba musu suka bata hanya ta fice.
Taje ta yo siyayyar kayan marmari, da abubuwan sha'awa ga mara lafiya, ta tafi gidan Sir Nazir, dan in suna hira yana kwatan ta mata gidan da yake zaune.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Da Lilly tabi kwatancen sa ba ta wani sha wahala ba ta gano gidan, ɗan ƙaramin gida ne, kusan shikaɗai ne a tsukin gurin, dan sabuwar unguwa ce duk ba mutane, ba wasu gidajen kirki se tsilla tsilla.
Ƙaramar Ƙofar taje ta fara knocking, ta daɗe a tsaye dan har ta fara fidda ran za'a buɗe ƙofar, kawai taji an buɗe.
Turus yai ya tsaya yana kallonta, kallo ɗaya tai masa taga yayi rama sosai, idanun sa sunyi zuru zuru, sanye yake cikin dogon wando baƙi, da vest fara ƙal.
Duk da halin rashin lafiya da yake ciki, amma a haka ya daure yace "Lilly, me kike a nan?"
Tace "Duba ka na zo yi, na kasa samun nutsuwa tun da aka ce ba ka da lafiya"
"Shikenan, Nagode ki maza ki koma gida kar wani ya ganki a nan kinji"
Kallonsa tai da mamaki tace "meyasa?"
Yace "idan wani ya ganki za'a iya yi mana sharri fa"
Aikuwa ta haɗe rai tace "dama na sani nina damu da kai, har in zo in da kake in duba ka amma ka min haka shikenan nagode" ta juya zata tafi yace "am sorry ba haka bane, ina jin tsoron abunda zeje ya zo ne, amma shikenan shigo kawai"
Ya bata hanya ta wuce, kasancewar jikin sa ba ƙwari a hankali yabi bayan ta, suka shiga ƙaramin falon ya samu guri ya kwanta akan doguwar kujera. Ya lumshe idonsa.
Ƙura masa ido tayi sosai ta na binsa da kallo, duk da yayi rama amma hakan be hana kyawunsa fitowa Sosai ba, wata irin soyayyarsa na sake fizgarta.
"Sannu my love" ta faɗa cike da kulawa.
ya jinjina mata kai ba tare da ya buɗe idonsa ba.
Duk da ba shi da lafiya, amma ko ina tsaf da shi,a gidan a share, hadda ƙamshim roomfreshner.
Ta miƙe ta ɗakko ledar da ta zo da ita zuwa gaban sa, ta zauna tace "ka tashi ka duba abunda zaka iya ci ka samu ka ci kaji babyna"
Ya girgiza mata kai yace "bana buƙatar komai, bana son cin komai"
Cikin shagwaɓa tace "haba dan Allah, ka daure ko yaya ne ka ci"
A hankali ya buɗe ido ya kalleta, yaja numfashi yace "tashi daga kusa dani Lilly, ki tafi gida ma kar a nemeki"
"Ni kake kora ko?" Ta faɗa tana nuna kanta.
"Ba korar ki nake ba, kar a nemeki a gida, na san ba'a san nan kika zo ba"
"Mummy ta na Sakwatto, an musu haihuwa fa, daga nan za taje ganin Daddy a Abuja"
"Duk da haka dai" ya faɗa a hankali.
"Idan ba ka ci ba ba zan tafi ba"
Ya tashi zaune yace "bani abunda kike so inci, Nagode sosai da ziyarar nan, amma ki tafi gida"
"Wai se korata kake shikenan, ni idan ka zo gidan mu ba haka zan ma ba"
Nazir yace "Lilly is different ace ni na zo gidan ku, akan ace ke kika zo gidana, kin kasa gane me nake nufi"
Ba tace komai ba ta ɗakko masa madara ta miƙa masa.
Ya girgiza mata kai yace "zata iya sani amai, bani Ayabar in ci"
Ta ɗakko ta miƙa masa, da ganin yadda yake ci ka san yana jin jiki.
A hankali yace mata "miƙo min ruwa a bayan tv stand ɗin can"
Ta tashi kamar yadda yai mata umarni ta kawo masa ruwan roba, sedai yanzu kusancin da ke tsakanin su yafi na ɗazu.
Ya karɓa ya sha, se bin sa take da ido.
Yana ƙoƙarin kwanciya, Amma ta hana shi tace "guda ɗaya fa kaci, baka ci da yawa ba"
Yace "na ƙoshi, zan iya amai"
Ba tsammani taji ya kwanta a jikinta ga jikin sa da zafi sosai saboda zazzaɓi.
Da ƙyar tace "jikin ne?"
Maimakon ya bata amsa se sake ƙanƙameta da yayi a jikinsa, yana ta numfashi da kyar.
A hankali ta dinga shafa bayansa zuwa sumar kansa, tana masa Sannu.
Gefe kuma tana raya abubuwa daban daban a cikin ranta.
Tabbas mace duk ƙanƙantar mace mace ce, Ruɗin ƙuruciya da kururwar sheɗan, silar lalacewar ƙarshen zamani, abunda ake rubutawa a litattafai ya taka rawa a ƙwaƙwalwar Lilly gurin hilatar malamin nata zuwa ga afkawa tarkon sheɗan, shikuma bisa ga jagorancin sheɗan ya biyewa son zuciyarsa, suka afka tarko me matuƙar muni. Ya aikata zina da ɗalibar sa, abunda ko a mafarki be taɓa kawo faruwar hakan ba.
Ya kalli in da Lilly ke kwance, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta iya yi.
Dafe kansa yayi tare da ɗorawa kansa dukkanin laifin, kan sa cigaba da sarawa yai, ya zubawa Lilly ido da hawaye ke bin gefen idonta.
A hankali ya ɗagota yana mata Sannu, amma ta kasa magana se kuka da take.
A hakan ya temaka mata ta kintsa jikinta, sedai ko haɗa ido ya kasa yi da ita, saboda matsananciyar kunya da kuma nadama da suka shige shi.
Duk da yadda take jinta a galabaice, haka ta fice ta bar gidan, zuciyarta a cunkushe da dana sani da kuma zubar da hawaye, shikenan ta rasa abu mafi kima da daraja a tare da ita, duk da yadda ta ɗokanta da son gazgata abunda suke karantawa a littatafai, da yadda zuciyarta ke ƙawata mata malamin na ta, amma ta gane Barno gabas take.
Ta kuma ji nadamar abunda yafaru a tsakanin su da malamin nata.
Ta na zuwa gida tun a falo ta zube, ta dinga rusa kuka kamar ranta ze fita, tayi asarar da ba zata taɓa mayar da ita ba.
Ranar yau Sadik ya kasa bacci, shi kansa ya san jure rashin Farhan a kusa da shi