Showing 228001 words to 231000 words out of 259198 words

Chapter 77 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13375

yadda rana ɗaya duk tai wani iri ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba, ya sake tabbatar da kishi bala'i ne, sedai hanyar da ze bi ya wanke kansa a gurin Nana yake.
A falo ya fito ya sami Nana ta na shayar da Sahal, ya samu guri ya zauna a kusa da ita ya kira sunanta "Husna" banza tai masa Kamar ba da ita yake ba.

"Magana fa nake miki, dan Allah ki tsaya in miki bayani"

"Ba ka da wani bayani da za kai min, ai bayani na gama jinsa kawai ka ƙyaleni, ka rubutan takarda sakina, ka Auri matar so wadda kake so, idan na yaye Sahal ma zan kawo maka ka bata, in ya so se in koma makaranta wataƙila a gaba, in samu wanda ze so ni saboda Allah"

"Dan Allah Besty ki saurareni"

Cikin kuka tace "ba wata Besty, dama ka sha gayamin ni ba komai bace face me aikin ka, ka cutar da ni baka sona ka bari na haihu da kai, ka kashemin rayuwa, Allah ya bani ladan biyayya amma na gama zama da kai, ƙauye zan koma na gama Auren"

Be taɓa zaton Nana mafaɗaciya ce haka ba, ya dai santa da tsiwar tsiya amma tana da matuƙar sauƙin kai sosai da sosai, amma a wannan karon kam ba ya tunanin za ta fahimce shi.

Ta shirya tai tafiyarta cikin gida, ɗakin da tai jego taje tai kwanciyar ta.

Haka Sadik ya wanzu cikin tsananin damuwa, Besty ta caza masa kai, ga ɓangaren guda na zuciyar sa na son ganin Princess.

Da azahar ya shirya ya tafi gidansu Farhan, sedai zuciyarsa ba daɗi, abun ya zame masa biyu, da idan Farhan ta caza masa kai, rarrashinsa da Nana ke yi, ba ƙaramin nutsuwa yake samu ba, to gashi Yanzu ma Nana ta juya masa baya.

Tun da Motar Sadik ta shigo layin Farhan ta sha jinin jikinta, dan tana tare da Abbas, ya dawo da ita daga makaranta.

Abbas ya kalli Farhan yace "ya dai na ga kin canza?"

Sadik yai parking ya fito babu walwala, kai tsaye ya tunkaro in da su Farhan ke tsaye, ko kallon in da Abbas yake be ba, ya kalli Farhan yace "Farhan me nace miki ne wai? Bance ki sallami mutumin nan ba?"

Abbas ya kalleshi yace "bawan Allah ya dai?"

Sadik yace "ba da kai nake ba, da matata nake"

"Ya akai ta zama matarka? Nine nake shirin Aurenta ai"

"Ni kuma nine mijinta, ka tambayeta kaji" Sadik yai maganar yana maida idonsa kan Farhan.

"Sadik meye haka kake min ne? Meyasa kake min haka? Na gaya maka wannan shine wanda zan Aura, meyasa kake son ta ƙarfin tsiya se ka dawo rayuwata, nace maka bana buƙatar ka, bana sonka Sadik ka fita daga rayuwata, ka jefa rayuwata cikin bala'i kuma kana cigaba da bibiyata meya haka Sadik?"

Sadik ya kalleta ya jinjina kai yace "Nagode Farhan, amma ba gudu ba ja da baya, nine mijinki ki rubuta ki ajiye, idan ba ni ba Wallahi ko wa kika aura tare muka aureki" yana gama maganar ya nufi motarsa cikin hanzari.

Abbas yace "wannan ne Sadik ɗin naki dama?"

Farhan kamar za tai kuka tace "Shine amma.....

Abbas yace "Shhhhh, no need to hear anything from you, se anjima" shima ya nufi tasa motar.

Farhan ba ta gane wani hali Abbas ya shiga ba, fushi ko akasin haka?.

Sadik kuwa ikon Allah ne kawai ya kai shi gida, dan ba a hayyacinsa yake tuƙin nam ba saboda damuwa.

Yana zuwa gida BQ ya wuce sedai ya tarar Nana ba ta nan, ga wardrobe ɗin Sahal duk an watso kayansa ƙasa.

Cikin hanzari ya fito har da haɗawa da gudu, ya shiga cikin gida yana ƙwalawa Mother kira.

"Kiran me kake min haka?"

Sadik yace "Mother ina Besty? Naga bata BQ"

Mother tace "ta je gidan dr."

Sadik yace "Ya salam, Mother meyasa kika barta, Wallahi ƙauye zata tafi"

Mother tace "yo ni na sani ne? Na zaci ta da saninka, kuma koma mene banga laifinta ba, tunda kai ne baka da hankali, ba zaka kashe 'yar mutane da ƙuruciyarta ba"

"Mother yanzu kin goyi bayan ta tafi ta barni, Wallahi ina sonta Mother"

"Na goyi bayanta ɗin, ko ni kaiwa abunda kai mata na gama zama da kai, mara hankali kawai!!!
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680







Sadik ya zauna akan kujera jiki babu ƙwari, yana murza goshinsa saboda wani irin zafi da kansa yake masa, gaba ɗaya ya rasa ina ma ze dafa yaji daɗi, Mother kuwa tai tafiyarta ta bar shi a gurin a zaune.

Ya tashi ya shiga ɗakinsa na nan falon ya nemi guri ya kwanta, yanzu azahar ta wuce, idan yaje ƙauye yanzu ba ze samu damar dawowa akan lokaci ba.



Nana kuwa tana ɗakin Inna, se uban kuka take kamar wadda aka tsinewa, idanunta duk sun kumbure, fuskarta tai jawur.

Inna ta kalleta tace "to yanzu Nana ke yaji kika yo ko me?"

Nana tace '"Ni ba zan cigaba da zama da shi ba, kawai ya sakeni ya zauna da wadda yake so"

Inna tace "ba shakka sarauniyar marasa hankali, shi kuma ɗan naki ya zaki da shi?".

"Ba shi abunsa zanyi, ba ze ƙara shan Nono a jikina ba, yaje ya san yadda ze yi da shi"

Inna tai murmushi irin nasu na manya tace "Yarinya ƙuruciya na ɗawainiya da ke, kin ban kunya Nana, kin ganni ban taɓa yaji ba duk zamana a gidan kakanki tsawon wannan shekaru ba dan kuma ba ma samun saɓani bax

Ba kunya Nana tace "kema dan bece ze miki kishiya bane, kuma ai ke sonki yake ya Aureki ni kuwa fa, aka cusa masa ni ya Aureni, dama ya sha yi min gorin sadakata aka ba shi bana damuwa, ashe da gaske yake, dan kunnena naji yana faɗar ba sona yake ba" ta ƙarasa maganar tana kuka.

Inna tace "sannu mara kunya, ni kike cewa dan ba ai min kishiya bane ba ko?"

"Inna kiyi haƙuri raina ne a ɓace wallahi"

Inna tace "kin kyauta, ki dena wannan kukan ki ɗau ɗanki ki shayar da shi yanzun nan kan in ɓata miki rai"

Haka nan Nana tana kuka, ta ɗau Sahal tana rarrashinsa, ta fara shayar da shi.

Inna tace "ki kwana da shirin gobe in Allah ya kaimu da safe zaki wanke ƙafarki ki koma ɗakinki" Nana ta sake fashewa da kuka, gaba ɗaya Inna kamar ma ta tsanete ne duk wannan abun ko guri ɗaya ba ta ga alamar za su bawa Sadik laifi ba.

Taƙi cin abinci se aikin kuka, daga salla se kuka, har ta fara ji a ranta da iyayenta na da rai ba za'a nuna ba ta da amfani ba s gurin Sadik, sunfi son Sadik Yanzu a kanta.

"Ki ta so kakanki na kiranki" taji muryar Inna, kamar ba zata motasa ba se kuma ta tashi, ta nufi turakar Hakimi, ta tarar yana kashingiɗe gefensa ga Sahal a kwance yana shan hannunsa.

Nana ta shiga ta zauna ba tace komai ba, tana ta goge hawaye.

Hakimi yace "matso kusa dani abar sona"

Nana ta girgiza kai tace "Allah Alhaji ka dena sona, Sadik kuke so tun da kuka fifita farincikinsa kun dena sona"

Hakimi yai murmushi yace "haba Nana, ya kike tunani irin haka? Tun daga tasowarki muke riƙe da ke, ba mu taɓa zaɓa miki abunda ze cutar da ke ba, dan haka yanzu ma ba zamu zaɓa miki abunda ze cutar da ke ɗin ba, ki kwantar da hankalinki ki zauna a gudanki, ki rungumi mijinki da yaronki, dama shi namiji mijin mace huɗu ne, kiyi haƙuri na san an miki laifi amma kiyi haƙuri"

"Cewa fa yai ba ya sona, da kunne na naji, zaman me zanyi kenan?"

"A'a ba kiji dai dai bane, Ya tabbatar min da yana sonki sosai, kar ki bari sheɗan yai tasiri a rayuwar Aurenki, kiyi haƙuri, na san kinyi biyayya amma kiyi haƙuri ki ƙara kinji yarinyar kirki"

Nana a ranta tace dama idan akace kayi haƙuri an so cutarka ne, ba ta sake cewa uffan ba ta koma ɗakin Inna, ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta take mata.

Washegari tun da wuri Inna ta saka Nana ta fara kintsawa wai ta koma, abun kunya ta fito be sani ba kuma a ga ta koma da ƙafafuwan ta, ta rasa abunda yake mata daɗi gaba ɗaya.







Tunds Abbasa ya tafi Farhan take kiran wayarsa, amma a kashe har wayewar gari, wayarsa ba ta shiga sam, kasa daurewa tai, ta tabbatar da tabbas Abbas yayi fushi ne, abunda tun haɗuwarsu be taɓa yi ba, duk irin girman laifin da zatai masa ba ya taɓs kai ya duba balle ya nuna yayi fushi, shiryawa tai ta bishi Asibiti.

Sedai da taje baya cikin office ɗinsa, wata Staff ta tambaya, ta sanar mata baya jin daɗi yana office ɗin sa na saman bene ya kwanta.

Da hanzari Farhan ta bi matattakalar bene zuwa office ɗin saman, ta tura ƙofar tare da yin sallama.

Yana kwance akan aboservation bed ɗin da ke office ɗin, yana ganinta ya tashi zaune tare da ƙaƙalo fara'a yace "Madam yau da kanki?"
Da sauri ta ƙarasa gaban gadon tana faɗin "doctor, na ganka a kwance ba ka da lafiya ne?"

Abbas yace "A'a hutawa nake yi kawai"

Farhan tace "Amma na ganka duk wani iri?"

Yace "bakomai fa, kar ki damu"

Farhan tace "dole in damu doctor, tun abunda ya faru jiya wayarka a kashe, doctor dan Allah ka fahimceni, Wallahi bakomai a tsakanina da Sadik a yanzu"

Ya ɗanyi murmushi sannan yace "meyasa kika ɓoyemin dawowarsa gareki?"

Tace "saboda ba abune me muhimmanci da zan sa a gaba har ya zama topic ɗin tattanawa ba, babu amfani dawowarsa ratuwar tawa, dan haka babu dalilin da ze sa in gayamaka, hakan ka iya ɓata maka rai"

"To ai ni rashin gayamin ɗin yafi ɓatamin rai Farhan, amma bakomai dai ya kike?"

Kamar za tai kuka tace "doctor bana son zama, butulu dan girman Allah kayi hsƙuri, nayi laifi amma kayi haƙuri Please"

"No,ba kya laifi Farhan naji daɗin dawowarsa rayuwar ki"

Farhan ta kalleshi da mamaki tace "saboda me?"

"Saboda shine jigon matsalar ki, dawowarsa tamkar yaye fiye da rabin damuwarki ne"

"Doctor dan Allah ka dena wannan maganar, me zanyi da Sadik for God sake? Kalli irin rayuwar da na faɗa saboda soyayyarsa, me dawowarsa ze amfana min? Ni dai ba kuma gangancin komawa soyayyarsa zan ba, dan haka dawowarsa rayuwat ba amfani"

"Idan ke kin dena son shi ai shi haryanzu yana sonki, kuma yana kishinki"

"Dan Allah doctor ka bar Wannan maganar ka ji, kayi haƙuri Please"

"Ai ba ki min laifi ba"

"No, na maka laifi mana, gashi har ka faɗa min. ina neman afuwarka Please"

"Farhan kenan, to naji shikenan ya wuce, yanzu me kike so ayi?"

"Ina son kaje ka karya, ka zauna a office ka duba marasa lafiya"

Abbas yai murmushi yace "ya akai kika san ban karya ba?"

"Doctor saboda na san damuwa farin sani, na san wahalarta da ƙalubalenta"

Murmushi kawai yai ya sakko daga kan gadon, ya biyo Farhan suka fito.




A ƙasan zuciyar Inna tana jin tausayin Nana, amma ta danne dan da Nana ta gano hakan za ta cigaba da taɓara, da iya shege kala kala, dan haka ta danne ta ƙi nunawa Nana tana tausayinta.

Tana zaune tana ta uban kuka, Sahal ma kukan yake ta tsalawa, Inna tai faɗan tai faɗan amma Nana tai burus tana ta kukanta.
Sallamar Sadik da ta ji se da ta tsagaita, dan tabbatar da in Sadik ɗin ne da gaske.
Sallama ya sake yi, Inna ta amsa masa, Sadik ya shiga cikin ɗakin, yana shiga su kai ido huɗu da Nana, da idanunta su ka kumbure saboda azabar kuka da kishi.
Ya gaida Inna ta amsa masa cike da kulawa, ta tashi ta ba shi guri, ya nufi in da Sahal yake tsala kuka, ya ɗauke shi jikinsa duk a sanyaye, ya rungume Sahal a jikinsa yana rarrashinsa, Nana ko kallon in da yake ba tai ba, ta ɗauke kanta.
Sadik ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya zauna amma ta ɗauke kanta.

"Besty" ya kira sunanta.

Wata uwar harara ta wurga masa, cike da tsiwa tace "Nana dai kamar yadda kowa ke kirana, ba wata Besty ba sunan yaudara"

"Nana nine nake yaudarar ta ki?"

"Au to da me kake? Tun da nake da kai ka taɓa gayamin kai ka na da wadda kake so? Ka dinga cewa kana sona ashe kai da wadda kake so rainamin hankali kawai kake"

Sadik yai ajiyar zuciya yace "Husna, meyasa kika taho ba izini na?"

"Saboda ba zan koma in cigaba da zama da kai ba, daga nan sakina za kai ka ɗau ɗanka ka kaiwa wadda kake so ta riƙe maka"

"Nine zan sake kin?"

"Eh ka sakeni"

"Haba Nana, ina ilimin naki na addini, Wallahi baki ƙarasa jin abunda zan faɗa bane ranar, ina sonki Nana, ƙara Auren da nake son yi, ba dan in cuzguna miki bane dalili ya kawo hakan, kar ki manta gidan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam mata goma sha ɗaya ne".

"Eh mana, tunda nake da kai ba ka taɓa cemin Annabi yace ba, se yanzu da yake Aure zaka ƙara, zaka wani fara cemin meye meye, waima ta yaya zaka iya riƙe mu mu biyu? Gaba ɗaya shekarunmu nawa ne, ni Wallahi ka gama dani ka gama raina min hankali, kawai kaje ka bawa Hakimi takarda ta"

Sadik yace "haka kike so?"

Tace "eh, haka nake so"

"Shikenan, tashi muje gurin Hakimin ki gaya masa, abunda yace shikenan"

"Ni ba zan wani je gurin Hakimi in gaya masa ba, kai ne zakaje ka gaya masa"

"Malama, ba sakin kike so ba tashi mu tafi gida"

"Wallahi ba zan tafi ba, ai ba asararriya ce ni ba, da zaka ce ba ka sona ba, kuma in koma in cigaba da zama da kai ba"

"Nana, da ba na sonki ba zan biyo ki nan ba, dan Allah kizo mu koma gidanmu, Please".

Se kuma kayi, tai maganar tana juya masa ƙeya.

"Ke Nana ku hanzarta, ku zo kuyi sallama da kakanku kuzo ku wuce ku tafi" cewar Inna da ke tsakar gida.

Ai take Nana ta sake fashewa da kuka, Inna taga abun Nana nayi ne, dan haka ta dinga zaginta ta sa ta a gaba, ta shirya suka shiga gurin Hakimi, ya daɗe yana musu nasiha, Sannan suka nufi tafiya.

Ta ajiyewa Sadik Sahal a gaban mota, ta koma bayan mota, tai zamanta.

Sadik ya fara jinjina yadda ze fara zama da Nana da Farhan, kowacce be san halinta ba se yanzu da wannan Magana ta taso.

Har suka je gida Nana ba ta kula Sadik ba, yai surutun harya gaji tai masa banza, ta ma yi kwanciyarta a bayan mota ta bar shi da ɗansa.



Mother tayi mamakin yadda Nana ta dawo, amma ba abun mamaki bane dama ta san Inna ba zata barta ba, tun da Nana ta dawo, ta bawa banza ajiyar Sadik, dama ba girki take ba, daga cikin gida ake kawo musu, sedai idan tana son ta girka masa wani abu, ko kuma yace yana son ta dafa masa wani abu, idan tai wankanta ta gyara ɗanta se tai tafiyarta ɗakin da ke sashin Mother tai zamanta.

Sadik be taɓa zaton son da yake wa Nana ya kai haka ba, se da ta dena shiga sabgarsa gaba ɗaya, lokacin da suke normal in dai yana nan tana jikinsa, tana zuba masa shirirta suyi ta ƙuruciyarsu tare, ga uwa uba ba shi girmasa da take yi, duk da Nana akwai lafiyar tsiwa amma ba ta raina Sadik ba, ba shi girma da take yasa take ƙara burge shi, sam ta manta da miyagun maganganu da yake mata a baya, saboda ba sa jituwa in sun tuna ma sedai kawai tayi dariya.
Amma yanzu gaba ɗaya ta buntsure ya kasa gane kanta, yai missing ɗinta over, ko gurin kwana ba ta haɗawa da shi.

Yanzu ma ya dawo daga gidansu Farhan, amma be samu ganin Farhan ɗin ba, ga wata irin yunwa da take addabar cikinsa, ya tarar ta tsuke a cikin wando da vest, sabgar gabanta kawai take kamar ba ta ganshi ba, ga gashin kanta da tai parking ya sha gyara, da da ne idan be yaba ba da ya sha mita da haɗe rai, ta dinga binsa kenan tana wai ba ka ganni bane? Amma yau ko kallo be ishe ta ba.

Kamar me jin tsoronta yace "Husna dan Allah zan sha tea"

Ba ta amsa masa ba, ta shiga kitchen ta dafa ta kawo masa, daga nan ta wuce ɗaki tai kwanciyar ta.

Har bacci ya fara ɗaukarta, taji yana shafa gashin kanta, da yake ta ƙamshin man gashi.

"Meye haka wai?" Tai maganar tana ture hannun Sadik.

"Nana, nine fa"

"Kai ɗin fa lafiya?"

"Tambayata kike lafiya dan na zo in da kike? Kina ganin abunda ki kai na watsar da ni kin kyauta dan kawai nace zan ƙara Aure, gaba ɗaya kin ƙaurace min?"

"Kai da za kai sabon Aure a kawo maka amaraya, me kuma za kai da ni? Dama amfanina gurinka kenan, ka biya buƙatar ka in samu ciki in haihu, matar so tana nan tafe za'a kawo maka"

"Yasalam, Wallahi Nana ba dan wani abu nake son yin Auren nan ba, kuma ni ba don abunda nake sonki kenan ba, ina sonki ne saboda Allah, amma kiyi haƙuri".

Daga haka ya juya mata baya, yai shiru yana tunanin meye mafita a gare shi, dan ya rasa mema Yakamata yayi akan wannan al'amarin.

Can dare Nana tai juyi, ta zata bacci yake, gari yayi sanyi sosai sedai Sadik be rufa ba, saboda a yanzu ko sanyin ba ya ji, ta janyo bargo ta lulluɓe shi, ta dafa goshinsa taji ya ɗau zafi, ba ta sauke hannunta ba ta shiga karanto masa adduoin bacci, da sauran adduoin da suka sawwaƙa a bakinta, dan ita ce take sa shi a gaba yayi dama kan su kwanta, se suyi tare dan haka yanzu ta san ba lallai yayi Adduoin bacci ya ɗauke shi.
Ta idar ta tofa masa, ta sake rufeshi sanann ta kuma juya masa baya.

Sadik ya sauke ajiyar zuciya a ransa yace "You love me too Husna, kishi ke damunki, amma ta ya zan wulaƙantaki, zan yi haƙuri da duk abunda zakiyi, Allah ya kawomin mafita"
Saukar numfashinta ya fara ji, alamar bacci ya kwasheta, ya matsa kusa da ita, ya rungumota jikinsa yana shaƙar sassanyan ƙamshin da take, yana jin yadda yai kewarta, amma Yanzu da yai yunƙurin wani abu, ko za ta yadda se sunyi faɗa, shi kuma baya son ya takurata sam.


Usman takanas ya zo gidan, da Mother ta ba shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login