Showing 216001 words to 219000 words out of 259198 words
Chapter 73 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
hamshaƙan manyan mutane ne ke kama irin wannan ɗakin.
Sadik ya sa hannunsa a jikin handle ɗin ƙofar ɗakin, zuciyrsa na wani irin harbawa, cike da Zullumi da fargaba ya buɗe ƙofar yaji a buɗe take, ya shiga ɗakin, ba ya fargabar koma ba ɗakin ya shigo ba, babban burinsa kawai ya sa Farhan a idonsa.
Ɗakin ba kowa, ya ƙarewa ɗakin kallo, ya kuma kiran lambar Farhan, ai kuwa yaji ringing ɗin wayar a ɗakin, yana ɗaga kai ya kalli in da sautin ke tashi, idonsa ya sauka akan wayar da ke kan side bed, ga manyan kwalaben magani da wasu tablets a akai.
Jikinsa ya ɗau rawa ya ƙarasa gaban side bed ɗin, Sadik ya shiga jujjuya magunan zuciyarsa na wani irin zafi, irin ƙwayoyin da Mubarak ke ta'amalli da su ne, na saka maye.
Ƙofar banɗaki yaji an buɗe, ya ɗaga idonsa ya zubawa ƙofar.
Sanye take da wata matatsiyar riga doguwa iya gwiwar ta, sosai rigar ta fitar da shape ɗin jikinta, kanta ba ɗan kwali, tana ɗan dafa kanta alamar ko yana mata ciwo, ko haryanzu tana maye.
Ƙamshin turaren da ya daki hancinta ne yasa kanta ya sara, ta san babu wanda take irin wannan ƙamshin se Sadik, tun da ya bar duniyarta ba ta sake jin sa ba, ta ɗago manya manyan idanunta da suka ɗan yi ja.
Wani irin ƙuuuu cikinta ya bayar, ta shiga ƙifta idanuwa, dan ta tabattar da ƙwayar da ta sha ta saketa, ko kuma gizo ne abunda take gani.
Sadik ya zuba mata ido, ko ƙiftawa ba yayi, ta tabbata Farhan ɗin sa ta sauka daga turbar da ya santa a kai.
Jiki a sanyaye Ya fara tunkararata, wata irin ƙaunarta na fizagarsa.
"Stop their!" Ta daka masa tsawa.
Ƙoƙarin tunkararta yake amma ta kuma cewa "kar ka zo in da nake, i said you should Stop their".
"Farhan, nine fa Sadik ɗinki ne"
"Shut up, bad lier ko suna in dai da kai ake ba na ƙaunar jinsa, azzalumi mayaudari leave my room now, get out from sight".
Kamar Sadik ze kuka yace "Farhan dan Allah ki saurareni"
"Wallahi ka zo in da nake se na caka maka abu, bana sonka bana son ganinka na tsaneka, na tsani me sonka ka fita ka bani guri" ta ƙarasa maganar kanta na juyawa, da son tabattar da mafarki take ba, dan yana yawan yi mata gizo a cikin mayenta.
Ya ƙaraso in da take, amma ta ja da baya ta ɗago fuskarta da tai jawur, kamar mayunwaciyar kura ta cigaba da Magana "nace maka ka fita ka barmin ɗaki na, nan gurin sana'ata ne, bana buƙatar mutum irinka a nan"
Sadik yace "Farhan ko sau ɗaya ki saurareni"
"Ba zan taɓa saurarar ƙarya da yaudar ba, daga bakin maƙaryaci, kalli halin da nake ciki duk sanadiyyar ka, ka fita nace maka kan in maka illa da kwalba yanzun nan"
Daskarewa Sadik yai yana kallon Farhan ɗin sa, me tsananin kunya da bin unarninsa yau ita ke masa tsawa haka.
Ai be Aune ba ta dinga hankaɗashi, gudun kar taiwa kanta illa yasa ya ƙyaleta ta hankaɗashi har waje, ta rufe ƙofarta ta zauna a bayan ƙofar tana rera kuka.
Sadik ya jingina da jikin ƙofar, yana sauraron sautin kukanta, dake ƙona zuciyar sa.
Wani baƙin ciki ne ya tasowa Farhan, jin yadda ƙasan zuciyarta ya ƙawata mata girma da kyan da Sadik ya ƙara yi, ta tabattar wa da kanta zahiri ne abunda ya faru ba Sharrin ƙwaya ba.
Sautin fasa kwalba Sadik yaji, daga nan yaji ta ƙwala ƙara, a gigice ya jinjina ƙofar amma yaji ta rufeta gam.
AYI HAƘURI A LALLAƁA BA EDITING, WAYAR TA SAMU MATSALA.
A gigice Sadik ya shiga jijjiga ƙofar yana kiran Sunan Farhan, Amma ta ƙi buɗe ƙofar, ya nufi reception cikin hanzari ya sanar musu da abunda ke faruwa, aka zo da spare key, aka buɗe ƙofar, tana zaune tana kuka, ta yanka hannunta yana ta zubar da jini.
Sadik ya shiga cikin ɗakin da Sauri ya tunkareta, amma ta miƙe ta ɗau sauran kwalbar, ta saita shi tace "wallahi ka zo in da nake se na caka maka ita"
So makaho ya cigab da nufarta, yana faɗin "ki tsaya Farhan, ba ki ga yadda hannunki ke zubda jini bane? Ki tsaya ki ji"
Ganin ba shi da niyyar dena kusanto in da take, ya sa ta saita cikin ta da tsinin kwalbar, tace "Wallahi ka zo in da nake se na sokawa kaina kowa ya huta".
Receptionist ɗin da suka zo tare da Sadik tace "kaga malam, dan Allah tunda kaine ba ta son gani ka ƙyaleta, kar ta kashe kanta ku janyo mana bala'i"
Jiki a sanyaye Sadik ya juyo ya baro ɗakin, ya fito waje ya zauna, ya dafe kansa yana jin yadda kan ke sara masa, wai yau shi Farhan ke gudu haka, take jifa da miyagun maganganu.
Farhan ba ta damu da yadda jini ke zuba a hannunta ba, sedai yadda take jin haushin zuciyarta da ƙasan zuciyar ke ƙoƙarin shiga cikin farincikin ganin masoyinta.
Ta yanke shawarar barin Hotel ɗin ta canza wani, dan idan ta koma gida ma ze iya binta can, dan haka ta zura doguwar rigar ta, ta zauna a gefen gado ta ɗau wayarta missed calls rututu ta gani, abun ya bata mamaki wannan lambar waye haka?.
Sadik na nan zaune ya ga wani hamshaƙin mutum ya taho, tinkis tinkis ya nufi ƙofar ɗakin da Farhan take, ai a zuciye Sadik ya miƙe, ya rufa masa baya, cikin azama ya sha gabansa ya tare ƙofar ɗakin.
Mutumin ya kalli Sadik yace "kai Samari lafiya kuwa?"
Sadik yace "kai zan tambaya ko lafiya"
"A'a kaga matsa ka bani hanya"
"Wallahi in dai ina motsi a gurin nan ba ka isa ka shiga ɗakin nan ba"
Mutumin yai saroro yana kallon Sadik yace "kai wai meye matsalar ka ne?"
"Matsalata shine ka koma, ba zaka shiga ɗakin nan ba"
"A saboda me?" Mutumin ya tambayi Sadik cikin mamaki.
"A saboda mata ta ce a ciki"
"Ikon Allah, wato Farhan ta fara mu'amala da mahaukata kenan"
Cikin ɗaga murya Sadik yace "kaine mahaukaci, tsohon banza da na wofi, ka zo kana haikewa ƙanƙanuwar yarinya 'yar cikinka dan Allah dube ka mutumin banza da na wofi"
Galala ya buɗe baki yana kallon Sadik, ba'a taɓa baƙanta masa rai aka ci mutuncin sa kamar yadda Sadik yai masa yau ba.
Ya nuna kansa da yatsansa yace "ka san ko ni waye kuwa?"
"Mutumin Banza mana, wanda be san ciwon kansa ba"
"Yayi kyau, dole in sa akawomin ƙarshen rashin kunyarka a yau ba se gobe ba"
Sadik yace "ba irina akewa barazana ba kaji ko"
Jin hayaniya yasa Farhan Fitowa daga ɗakin, sedai ga mamakin ta taga Sadik a tsaye a gurin.
Ta kalli Alhajin tace "ashe ka zo amma ba ka min magana ba"
"Eh na zo, wannan sakaran yaron ne yai min rashin kunya ya hanani shigowa, waya zan azo a tafarmin da shi a koya masa hankali"
Sadik ya tunkaro Farhan yana cewa "dan Allah Farhan ki saurareni, yanzu ki bari ina kai ki a duba hannunki, se muyi Magana"
"Wallahi ka kuma doso in da nake, sena baka mamaki" ta maida Idonta ga mutumin nan tace "Ya ci arzikina, ka ƙyaleshi ba ruwanka da shi, muje kawai"
Cikin hanzari Farhan tai gaba, Sadik ya bita yana cigaba da kiran sunanta.
Ba ta tsaya ko ina ba se jikin motar mutumin nan, cikin takaici mutumin yace "wai ke ina kika samo wannan mayen yaron ne mara hankali"?
Abun takaici se taji Maganar da Alhajin yai ta ɓata mata rai, amma ta basar tace "buɗe min ni in shiga mu tafi"
A zafafe Sadik ya ƙaraso gurin, dai dai lokacin ya buɗe mata motar za ta shiga, amma Sadik ya ture shi ya sa ƙafa ya daki murfin motar, ya juya kan Farhan yana huci, amma ya gaza furta komai.
Tuni hankalin mutane ya fara dawowa kansu, Sadik ya kalli mutumin nan yace "wallahi idan ba ka fasa bibiyarta ba, se na tona maka Asiri a garin nan, se nayi maganinka kan ka kayi maganina tsohon banza da na wofi"
Kan Sadik ya waiga tuni Farhan ta kak gate ɗin Hotel ɗin, ya zura da gudu ya bita sedai kan ya cin mata ta haye Napep tai gaba, ya juya kamar mahaukaci ya hau motarsa ya bisu, sedai ɓat suka ɓace masa.
Duk da haka be karaya ba haka ya cigaba da bulayi a tsakanin unguwar nan, amma be ga Farhan ba balle alamarta.
Be koma gida ba se bayan ƙarfe tara na dare, haka ya koma wujiga wujiga kamar wanda ya dawo daga filin yaƙi.
Already yayi Sallah isha'i a waje, bq ya wuce dan kar ma Mother ta ganshi ta sa shi a gaba da tambayoyi.
Ya ɗau wayarsa ya fara kiran wayar Farhan, sedai ya jita a kashe.
Inna ce ta shigo ɗakin da Nana, take tana ta jijjiga Sahal da hannu ɗaya, yana ta uban kuka, hannu ɗaya kuma tana riƙe da wayarta tana dannawa, hasken wayar ya haska fuskar Nana tana zubar da hawaye.
"Ke lafiyar ki kuwa?" Firgigit Nana ta shiga goge hawayenta, tace "bakomai"
"Kamar ya bakomai kina kuka?"
Aikuwa ta sake fashewa da kuka tace "Inna yau fa kwana takwas Besty be kirani ba, kuma ni na kira tasa wayar ba ta shiga"
"Ikon Allah, saboda mijin naki kika zauna kina kuka haka? Ke da kika ce ba kya son sa da"
Nana ta tura baki tana ci-gaba da share hawaye.
"To ki kula da yaron hannunki, ki rarrashe shi, seki kira uwarsa kiji ko yana lafiya"
"Inna Kunya nake ji, ba zan iya kiranta ba"
"To ni ki kira, se ki bani in mata Magana"
Cikin Sauri Nana ta nemo lambar Mother, ta kira ta miƙawa Inna.
Mother taga baƙuwar lamba, dan ba ta da lambar Nana, amma jin muryar Inna ta ɗan sake suka gaisa.
Inna tace "dama matar Sadik ce tace ko lafiya, yau kusa kwana takwas be kira su ba, duk tabi ta ɗaga hankalinta, kuma shi tasa wayar ba ta shiga"
Mother tace "ai Sadik ɗin ne gaba ɗaya na kasa gane kansa kwanan nan, ban san meke damunsa ba amma bari in bashi wayar"
Mother ta katse kiran, ta wuce BQ ta tarar da shi a kwance akan kujera, yai shiru ya dulmiya cikin tunani.
Mother tace "Allah yai maka maganin ko ma mene yake damunka, na rasa gane kanka gaba ɗaya kwanan nan, kuma kaƙi gayamin meke damunka"
Sadik yai shiru bece komai ba, se gyara kwanciyarsa da yai.
Mother ta kira layin Nana, Nana ta gaisheta, ta amsa mata tace ya suke ya Sahal, Nana tace suna lafiya, daga haka ta miƙawa Sadik wayar.
"Assalamu alaikum" Sadik ya faɗa a Sanyaye.
"Besty, laifin me mu kai maka haka, ka manta damu gaba ɗaya, na kiraka wayarka a kashe me mu kai maka ne?"
Jikin Sadik yau sanyi ƙalau, cikin rashin ƙwarin jiki yace "Am sorry Nana, bana jin daɗi ne"
"Shine kake faɗan sunana ko? Me nai maka dan Allah" ta ƙarasa maganar tana kuka sosai.
"Subhanallah, ya da kuka kuma ke baki san kin zama Mum ba ne, ke ki kuka Daddyna ma yayi"
"To ba kai ne ba, ka manta da mu gaba ɗaya, hankalina duk ya tashi na rasa meke faruwa"
"Tabbas nayi muku laifi, amma kiyi haƙuri bana jin daɗi ne"
Cikin kulawa Nana tace "eyya, meke damunka?"
"Ciwon kai nake fama ne"
"Sannu, ko dai in dawo ne? Nasan ba ka wani kula da kanka, kai in baka da lafiya gaba ɗaya wani iri kake komawa"
Yai murmushi na ƙarfin hali yace "No, kar ki damu ina kula da kaina Sosai, ki zamanki idan kin huta se in zo in ɗakko ku"
"To kaje Asibiti ne?"
"Eh naje, har an bani magani ma"
"Nifa duk hankalina ya tashi, muryarka fa duk tayi wani iri Allah" tai maganar cikin shagwaɓa.
Ya lumshe ido yace "Besty"
"Na'am Besty na" ta amsa masa.
"Dan Allah ki rarrasan min ɗa, ina jin kukan sa fa"
"Bayan ma ka dena kiransa a waya kaji ya yake"
"Kiyi haƙuri, insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, ki tai min Addu'a"
Tace "to shikenan, Allah ya baka lafiya nan ma ana tai mana saukar Alqur'ani Allah ya ƙara mana zaman lafiya ya baka lafiya, kuma kullum a idan nai salla ina maka Addu'a Allah ya yaye maka damuwar ka ya biya maka dukkan buƙatunka na Alkhairi"
Tabbas yasan Nana tana yawan yi masa addu'a, ko ya sani ko be sani ba, wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar Sadik, tabbas yana son Nana, amma baze iya haƙura da Farhan ba, ko me ze faru ze yi duk me yuwuwa ya mallaki Farhan.
"Besty ya kai shiru?"
"Bakomai, anything special for me? Am missing you fa" yai maganar yana son basar da abunda ke ransa.
"We are missing you too, in gaya maka Sahal ya fara dariya"
"Dagaske, Allah ya sa be riga yi miki dariya kafin ni ba"
"Ai se yana bacci yake yi, amma Inna tace ya fara ƙyuya, kallon mutane yake Sosai"
"Ahh gaskiya gara in zo in taho da ku, tun kan ya fara yi min ƙyuya"
Tai murmushi tace "Naji daɗi da naji muryarka, ka kula da kanka sosai kaji Besty na"
Sadik yace "to my Asma, Ummu Sahal, Yarinya ta zama Mummy"
"Hmm ai zama Mummyn nan ma ba sauƙi, daga Sahal na gama"
"Baki isa ba, next year by now insha Allah kin kuma haihuwa"
Nana tace "ba ka san ya ake ji in za'a haihu ba ko?"
"Na sani mana, tunda tare mu kai naƙuda"
Dariya tai tace "besty me, se da na zo ƙauye naji muna missing ɗin ka wallahi"
Ya shafi sumar kansa yace "karki damu, insha Allah zuwa next week zan shigo in ɗakko ku, nima na fi son in jiku a kusa dani"
"To shikenan, have a nice day, Allah ya baka lafiya ingantacciya abu Sahal"
Sadik yace "thank you wifey, ki kulamin da kanki da babyna, a gaida Hakimi da Inna"
"Zasuji insha Allah"
"Kiss me before you quit the call"
Nana tai murmushi tace "i will kiss you when we meet"
"Da kiss da me?" Yai maganar yana murmushi.
"Da kiss da ba ruwana, Inna tana jinka"
Da sauri Sadik ya kashe wayar, ya lumshe ido tare da ajiyar zuciya, yana jin tausayin Nana sosai da sosai, saboda sosai alamu sun nuna ta na son Sa sosai da sosai.
Inna ta shigo ɗakin tace 'ikon Allah, har kin watstsake kin dena kukan?"
Tai murmushi tana sunkuyar da kai cike da jin kunya.
"Hankalinki ya kwanta dai ko? Maman soyayya"
Nana ta rufe fuska tana dariya.
Sadik ya miƙe ya shiga gida, kaiwa Mother wayarta, ya shiga sashinta da Sallama ta amsa masa, ya ƙarasa ya miƙa mata wayar yace "Mother ga shi"
Mother 5a kalleshi tace "zauna za muyi magana ne"
Sadik ya nemi guri ya zauna, Mother ta ɗan ƙare masa kallo sannan tace "Sadik, ka gayamin gaskiya tsakanin ka da Allah, menene yake damunka"
Sadik yace "Mother me kika gani?"
"Kamar ya me na gani, kai baka ga yadda gaba ɗaya ka koma bane? Ba ka walwala kamar mara lafiya duk ka canza, wanda da ba haka kake ba, ka gayamin ko dai har yanzu Auren ne ba ka so?"
Yace "A'a Ina so"
"Ko dai akwai wata matsala ne?"
Yace "Mother wallahia bakomai fa"
Mother tai shiru sannan tace "kaga kuwa yadda ka koma? Da Abba na gari da shi zan haɗaka ban sani ba ko shi ka gaya masa".
"Allah Mother bakomai dagaske nake"
Mother tai ajiyar zuciya tace "shikenan tashi ka je, Allah ya kyauta koma mene yake damunka Allah ya yaye maka"
Jiki a sanyaye ya amsa da Ameen, ya tashi ya fita Mother ta bi bayansa da kallo.
Komawa yai ya cigaba da lissafin ta in da ze ɓullowa Farhan, ko sau ɗaya ta yadda ta saurare shi, taji uzurinsa, yayi mamakin yadda ta rufe ido ta nuna ba ta ko ƙaunar ganinsa, tabbas be kyauta mata ba, amma har ga Allah idan Farhan ta guje shi be san yadda ze yi ba, saboda yana matuƙar ƙaunar ta.
Farhan kuwa suna tafe a hanya tana rera kuka, ga hannunta na ta zubda jini, Asibitin su Abbas ta sa me Napep ya kaita.
Ta sauka ta biya shi kuɗinsa, ta shiga sedai Abbas ɗin baya nan, wata Nurse tace bari suyi attending ɗin ta ai dressing ɗin hannun, amma tace ita Abbas take nema, ga wayarta ta ɗauke ba caji, da wayar Asibiti ta kira shi, ta sanar da shi cewar ga ta a Asibitin su tana jiransa.
Ai cikin hanzari ya kamo hanyar zuwa Asibitin, saboda yadda yai kwanaki yana zuwa gidansu bata nan, kuma taƙi yadda ta gaya masa in da take.
Yana zuwa ya tarar da ita a reception, ta naɗe hannunta da mayafinta.
Da hanzari ya ƙarasa in da take yace "Farhan, ya akayi ne lafiya kuwa?"
Idon ta fal ƙwalla tace "ciwo naji"
Yace "subhanallah, garin yaya? Meyasa baki bari an duba ciwon kan in zo ba?"
Ta share hawayen fuskarata tace "saboda so nake ai min a hankali, kuma na san kai a hankali za kai min"
Yace "ok to shikenan, mu shiga emergency in duba"
Ta miƙe, yana tafe tana binsa a baya, har suka shiga, ta kwance mayafin, ya fara duba ciwon, ya kalleta yace "dame kika ji wannan ciwon?"
"Kwalba" ta ba shi amsa kai tsaye.
"Garin yaya?"
Shiru tai ba tace komai ba, duk yadda yai ta gaya masa amma ta ƙi, ya ƙyaleta yai mata dressing, ya ɗakko mata magani, da jakar kayanta da ta zo da ita, ya kai motarsa tana biye da shi zuwa motar.
Sam Abbas be mata maganar a ina take kwana ba, da rashin ɗaga wayarsa se ma sannu da yake ta jera mata.
Suna tafe amma tai shiru, tana ta saƙawa tana Warwarewa, gani take kamar har yanzu abubuwan da suke faruwa sharrin ƙwayoyin da take sha ne, amma ba Sadik ta gani a zahiri ba.
Har sukaje gida ba ta ce masa uffan ba, ta sauka ta ɗau jakarta ta ta kalleshi tace "Nagode sosai doctor, Allah ya saka da alkhairi" be amsa ba se ɗan tsura mata ido da yayi, sannan yace "ki kula da kanki sosai, ki kula da shan magani"
Ta jinjina masa kai ta wuce, Umma na tsakar gida tana aiki Farhan ta zo tai salama ta wuce, ta amsa mata ba tare da ta kuma ce mata koma ba, ita ma Farhan ba tace koman ba ta wuce ɗakinta, ta samu guri ta zauna a gefen katifarta, ta dafe kanta tai shiruu tana sake tunani tabbas Sadik ɗin ne dai ya ke ƙoƙarin dawowa duniyarta.
Tabbas dawowar Sadik duniyar ta barazana ne a gareta da ka iya jefata cikin wani mawuyacin hali wanda yafi wanda take ciki a yanzu.
Ta miƙa hannu ta janyo