Showing 51001 words to 54000 words out of 259198 words
Chapter 18 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
tsokanar sa akan Farhan, su kai ta iya shegen su san ran su.
Sedai gaba ɗaya jikin Prince ɗin a sanyaye yake, ya dake ya ɓoye halin da ke damunsa, ya dinga biye musu.
Nas yace "Prince, wai ya batun movies ɗin da aka tura maka ne, ka kalla kuwa, kaga yadda ake madarar Love, ba irin wanda ku keyi ba, sekace masu wasan yara, dan Allah kai ba ka ji kunyar ka dinga nuna wannan Yarinyar kace budurwarka ce ba? Kalli kayan jikinta ta jibga uban mayafi kamar wadda zata ja salla....
Wani irin warning glance Prince yaiwa Nas, hakan ya sa Nas ɗin yin shiru.
Daf da magariba amma har a lokacin zuwa ake, har 'yan ajin su Farhan ma sun halarci taron bikin.
Sedai gaba ɗaya Haseena ta kasa sukuni, saboda kyan da Sadik yai a idonta, babban abunda yasa ta tsani Farhan bakomai bane illa kishi, gashi Sadik ɗin ba shi da fuskar da za tai masa shishshsigi, amma harga Allah yana matuƙar burgeta.
Yau ta ƙara tabattar da Sadik ƙyakyawa ne na gaske, dan ba ƙaramin cika ido da kwarjini yai a cikin manyan kaya ba, duk da ƙarancin shekarunsa, Allah yai masa ƙirar manya, dogo ne ga shi da jiki, wannan jikin ne ke ɓoye ainihin ƙuruciyar sa.
Yauma Inna ta ga taɓara kala kala, da rashin ta ido, wanda suka ƙara tsaye mata a zuciya.
Se wajen ƙarfe goma na dare, Sannan aka watse daga gurin bikin.
Farhan da ta koma gida, tayi zaton Umma za tai mata faɗan ta daɗe, amma ga mamakin ta ba abunda Umman tace mata.
Nan ta baje uban kayan da Sadik ya bata, ta bawa Umma, amma Umman taƙi ko kallon in da kayan yake, ƙarshe se bari tai da Abba ya dawo, ta kai masa ya sa albarka, yace suje su raba ita da ƙanen ta.
Ta rasa yadda za tai da ranta da wannan halin ko in kula da mahaifiyarta ke mata, kawai saboda tana 'yar fari, ita tafi danganta wannan abun da kawai ba ta santa ne, dan wannan abun ya wuce kawaici.
Tun da suka taho da Sadik, ta kasa gane me ke damunta, gaba ɗaya jinta take wani iri kamar ba ta da lafiya, ta rasa takaimeme meke damunta, ga Wani yanayi da ta tsinci kanta, tun shigarta motar Sadik duk da ba yau ta fara hawa ba, amma ta kasa tantance yanayin da ta shiga.
Ga shi ƙasan cikinta yana mata ciwo kaɗan kaɗan, amma babu wanda ta gayawa, to wa ma zata gayawa? Ummanta da ba ta son taje in da take? Ko kuma ƙannenta maza?.
Jin ciwon be takura mata bane, yasa ta cigaba da sabgogin ta.
Tun bayan sallar isha'i da tai, ta samu guri ta zauna ta shiga tunani daban daban, a baya ko bisa kuskure Sadik ya taɓa jikinta, se ta nuna masa taji haushi, amma haka nan yau ba ta ji haushin hakan ba, sema kasa manta hannun sa da tayi, da irin ƙamshin turarensa.
Nan ta lalace a gurin da Tunanin Sadik,ba ta taɓa sanin haka akeji a soyaya ba, Sadik ya koya mata son sa.
Ji tai tana son yi masa bangajiya, amma da wace wayar?
Nan ta shiga tunani, can wata dabar ta faɗo mata, ta tashi ta tafi ɗakin Umma, ta tarar da Umman na shirin kwanciya.
Cikin sanyin jiki tace "Umma, dan Allah aron waya nake so ki bani, zan duba wani abu a internet"
Nuni tai mata da in da wayar take, ta juya ta kwanta.
Cikin farinciki taje ta ɗau wayar Umman, ta koma ɗakinta zuciyarta cike da farinciki.
A gajiye sosai Sadik ya koma gida, sallar isha'i kawai yai, ya haye gadon sa, dan ya gaji sosai.
Cikin sa'a bacci yai awon gaba da shi.
Cikin baccin yaji wayarsa na ringing, a fusace ya ɗago wayar, amma yaga Farhan ke kiransa da layin.
Murmushi yai, ya katse kiran ya kirata.
"Assalamu alaikum" ta faɗa cikin sassanyar muryarta.
Shiru yai yaƙi amsawa, ta sake maimaita sallamar amma yai shiru.
"Hello ba ka ji na?"
Murmushi yai cikin muryar bacci yace "Ina jinki fa"
Dariya tayi tace "ji shi kamar wani Baby"
"Ummmm ai Babyn ne, dan na tashi daga Babyn Mother Babyn Princess ne"
Wata kunya ce ta lulluɓe ta, har mamakin Sadik take idan yana wani abun, ta rasa ina yake koyo manyance, da iya soyayya.
"Ya naji kinyi shiru? Ina fatan ba ai miki faɗan kin daɗe ba?"
Tai ajiyar zuciya tace "ba aimin ba"
"To Alhamdilillah, a ina kika samu waya?"
"Wayar Umma ce, nace mata zanyi abu a internet ne"
Wani murmushi Sadik yai wanda shikaɗai yasan ma'anarsa.
"Ya naji kana dariya?"
"Dole inyi dariya mana, 'yar budurwata ta faller sona sosai, tunda zata iya ƙarya ta karɓi waya dan taji muryata"
"Nice nake ƙarya ko?"
"No, ba haka nake nufi ba, sorry bugun zuciyata, the only Moon in the sky, My little angel, my diamond Baby"
Dariya tayi tace "to ya isa haka, wai a ina kake koyo wannan abubuwan?"
Gyara kwanciyarsa yai yace "to ta ya bazan koya ba? A gabana Yayana ke ta sa soyayyar, lokacin muna tsohon gidanmu a ɗaki ɗaya muke kwana, a gabana yake soyayya, ga fina finai da nake kallo, ƙarewa ma Daddy da Mother ba sa ɓoye yadda suke son junansu ko a gabanmu ne, to meyasa ba zan iya soyayya ba"
Zare ido Farhan tai tace "kai! Mother kuma?"
Sadik yace "eh mana Mother, a gabanmu suke cewa suna son juna, basa ɓoye soyayyar su duk da sun tsufa maimakon su barmana" ya ƙarasa Maganar yana murmushi.
Shiru Farhan tai, ta ɗan tafi tunani anya tunda take ta taɓa ganin wani abu makamancin soyayya a tsakanin iyayenta? Iya abunda take gani shine law and order, biyayya da hidima amma ba ta ganin wani abu makamancin na so a tsakanin su.
"Kin tasheni daga bacci, kin ƙimin hira kinyi shiru"
Dawowa tai daga tunanin tace "au ka fara bacci ne?"
"Eh, na fara bacci wayarki ta shigo"
"To ba yanzu zaka koma baccin ba, cigaba da yi min hira"
Yanzu Sadik ke ƙara tabattar da Farhan ta iya hira, samun wanda za tai hirar ne babu.
A shagwaɓe yace "ni bacci nakeji"
"Ni kuma bana jin baccin"
"Ke gobe in Allah Ya kaimu za'a ɗaura Aure, da wuri zan tashi ki ƙyaleni"
"Aushhh" ta faɗa a raunane.
Da sauri yace "lafiya kuwa?"
"Cikina ne yake ciwo"
Sadik yace "ya salam, ko kinci wani abun ne?"
"A'a seda safe kawai"
Cikin damuwa yace "wait, ki sha magani karki kwanta kina jin ciwo kinji Babyna"
Da hmmm kawai ta amsa masa.
Ta katse kiran, cikin sanɗa ta je ɗakin Umma, ta tarar tuni Umman tayi bacci ta ajiye mata wayarta ta fito.
Haka cikinta ya cigaba da yi mata ciwo, wanda ta rasa ina ne ma yake ciwon.
Sadik yai rigingine, a hankali ya furta ya rabbil izzati ka tsareni faɗawa halaka, Allah kasa iyayenmu su yadda su Auran yarinyar nan, ina sonta Sosai, Allah ka aurar dani da wuri.
Ya ƙarasa yana lumshe idon sa.
Inna kuwa bacci ɓarawo ne ya ɗauke ta, ƙarshe cikin dare ta tashi tai Alwala tai salla, ta dinga addu'oi tana nemawa zuriyarta da al'ummar Musulmi shiriya, amma ta girgiza da yanayin rashin tarbiyyar da ta gani a tsakanin yaran ƙarshen zamani, masu ji da RUƊIN ƘURUCIYA!
Sadik ya kwana da begen Masoyiyyarsa, cike da mafarkai masu tabattar da lafiya da nuna alamun girma ga ɗan Autan na Alhaji Abdullahi.
Farhan kuwa da ƙyar tai bacci, gefe guda ciki na ciwo ga kuma tunanin soyayya.
Bayan sallar Asuba, Sadik ya koma bacci, kaɗe kaɗe da bushe bushen da suka cika gidan ne, suka sa ya farka.
Windown ɗakin sa ya buɗe ya leƙa, yaga manyan motoci anyi parking ɗinsu, ga maroƙa da manyan mutane sun cika harabar gidan, alamar ana shirin tafiya gurin ɗaurin Aure, kuma masu bushe bushen ya tabattar masa da Hakimi ya ƙara so.
Cikin hanzari ya shiga ya watsa ruwa ya fara nasa shirin shima, dan tuni hayaniya ta cika BQ ɗin, abokan Dr. Sun cika part ɗin suna shiryawa.
Rufe ɗakinsa Sadik yai, ya cigaba da shirinsa cikin nutsuwa.
A babban falon gidan Hakimi ya zauna, ya sha kayan sarauta se zuwa ake ana kwasar gaisuwa, ana ta gaggaisawa cikin girmamawa kasancewar sa mutum me barkwanci.
Nana kam ta dinga murna, fa zuwan Hakimi taje ta maƙalƙale shi, ta zauna a inda yake, tana nuna yadda tai kewarsa.
Ƙarfe goma shaɗaya aka kammala haɗuwa, aka nufi babban masallacin unguwarsu Amarya Jidda in da za'a ɗaura Auren.
Nan ma Mother ta sha ado, tai kyau kamar itace Amarya se zuba ƙamshi take, ta sha shadda hannunta da wuyanta duk gwal, da ka ganta ka ga matar manya.
Ƙarfe ɗaya aka dawo daga ɗaurin Aure, aka dinga shigowa ana Allah ya Sanya Alkhairi ana ɗaukar hotuna.
Hakimi ne ya fara shiga falon, se Alhaji Abdullahi da 'ya'yansa, abun da yafi ƙayatarwa shine, duk sun ɗora farar Alkyabba me aikin blue, akan fararen shaddojin su, ga naɗi da akayi musu, sunyi kyau matuƙa gaya.
Inna ta kalle su tai murmushi tace "Allah ya shirya mana zuri'a" dan ganin su cikin wannan kamalar ba ƙaramin burgeta yai ba.
Nan aka zauna Hakimi ya dinga addu'oi, tare da Nasiha ga angon da kuma iyayensa, tare da yi musu gargaɗi akan shiga sabgar ɗan da matarsa idan ba aka abunda ya zama dole ba.
Daga ƙarshe yace "Nagode Allah, sannan nai farinciki da Allah ya aramin rai na ga Auran jikana na fari, idan ina da rabo Allah ya nunan na sauran, na Faruku da na wannan abokin nawa, mara son mutane"
Yai maganar yana kallon Sadik, ba kunya Sadik ya gyara Alkyabbarsa yace "zama ka gani insha Allah, dan nawa za'a fara wata shekarar sannan nan wannan" yai maganar yana nuna Faruk.
Hakimi yai murmushi yace "Allah yasa"
Abba kuwa daƙuwa yaiwa Sadik yace "Ƙaniyar ka, mara kunya wayake ta taka, kaida ko sakandiren baka gama ba, next year by now insha Allah kana Amurka ko jamus kana karatu"
Ɗan tura baki Sadik yayi, yayin da Inna take bin su da ido tana nazartar, duk wani motsi na Sadik ɗin.
Da Yamma Hakimi ya ja tawagar sa ya koma, yayin da Inna tace ba zata bisu ba, za ta koma daga baya akwai abunda za tayi kan ta taho, ƙila se bayan sati da bikin.
Nana tace ita kuma za ta bi Hakimi ta koma ƙauye, Inna tace ba in da zata yadda suka zo tare za su koma.
Nana ba taji daɗin hakan ba, dan harga Allah ta gaji da zaman Gidan nan dan ba ta ga zaman me zasu yi ba bayan an gama biki.
Bayan sallar isha'i, 'yan uwan Amarya suka kawota gidan su ango gaida surikai, kan a kaita nata gidan.
Aka dinga mata Nasiha da Addu'oi, sedai kana kallonta kasan itama 'yar boko ce, ba wani kuka da take yi, gashi a ƙalla ta kai shekaru ashirin da bakwai.
Inna ba tace komai ba, se mamakin yadda ake ajiye 'ya'ya sukai mizani kamar wannan ba aure da sunan boko, bayan mutane ne su ba ƙarafa ba, a haka ake lalacewa Garin zurfafa bokon nam, dan Akwai lokacin da tilas jiki na buƙatar abokin rayuwa, kuma ga uwa uba gurin yin bokon a cakuɗe ake maza da mata, dan itama dangin amaryar da 'yan makarantar ta su ba ƙananan shakiyayyai bane, irin abunda suka dinga yi a gurin bikin.
Da gani baza'ace Jidda miji ta rasa shi yasa ba tai Aure da wuri ba, saboda ta na da kyau sosai, ra'ayin Auren ne kawai ba'aiba se an gama bokon da suka ɗauketa kamar wani tikitun jin daɗin duniya, ba 'a taɓa cewa ba za'a aurar da 'ya se ta sauke Alqur'ani ba, da wasu litattafan addini ba sedai ace se ta gama boko.
Haka Inna tai ta zancen zuci ita kaɗai, aka gama yi wa amarya nasiha aka tafi rakata ɗakin miji.
Shikam Sadik ji yake dama shine yai wannan Auren haka, amma ace ba za'ai wa mutum Aure ba se bayan ya gama boko, idan kuma mutum ya mutu be gama bokon ba kuma beyi Auren ba fa?
Shikenan Allah ya yayewa Dr. An bar shi shida Faruk a wannan wahalar.
Ya dinga tsaki yana juyi, yai ta zuba ido ko Farhan za ta kirashi, amma shiru ba ta kira shi ba, kuma gashi tace idan ba ita ta kira ba karya kirata, gashi tace masa cikin ta na ciwo yana son yaji halinda take ciki.
Ƙarshe dai se haƙura yayi ya kwanta bacci.
Akai biki aka watse, amma Mother ta ga Inna taƙi tafiya, ta na so tai magana ta na jin tsoro, amma ita har ga Allah ta gaji da zaman Inna, dan wajen watan ta guda a gidan, tun da su kai Aure da Alhaji Abdullahi Inna ba ta taɓa zuwa ta kwana a gidan ba, se a wannan karon, kuma ita har ga Allah zaman na Inna ya isheta.
Alhaji Abdullahi na shan cofee ɗinsa da daddare kamar yadda ya saba, Mother na sake gyara masa shimfiɗa, tana saka turaruka tace "D mace ba kuyi magana da Inna yaushe zata tafi bane?"
Ya ajiye kofin hannunsa yace "kina da damuwa da hakane?"
"A'a, naga ba ta taɓa zuwa ta daɗe haka bane"
Yace "to se a kai yaya? Ba ta da ikon yin hakan ne? Ko kin manta gidan ɗanta ne?"
"A'a ban manta ba, kawai na tambaya ne"
Be kuma ce mata komai ba ya cigaba da shan cofee ɗin sa.
Bayan sallar Asuba, gari yai haske sannan Inna ta koma bacci, Nana na ganin Inna ta kwanta bacci ta tashi ta fito, ita gaba ɗaya kamar akan ƙaya take, ta gaji da zaman Gidan nan, ta rasa zaman me suke a gidan suka ƙi tafiya.
Zuwa yanzu ta saba da masu gadi da ma'aikatan gidan, saboda shegen surutun Nana da san gwaninta, gata da shiga rai dan haka duk sun santa.
Faruku ya fito hannunsa riƙe da kwando, da manyan flask na Abinci a kai.
Da sauri ta ƙarasa in da yake tace "ina kwana"
Yai murmushi yace "lafiya ƙalau, kina lafiya"
Maimakon ta amsa seta jinjina masa kai.
Tace "kawo in tayaka ɗauka"
Yace "No ya miki nauyi, gidan amarya zanje kai musu Abinci, ko zaki rakani?"
Da sauri Nana tace "eh zan raka ka, dama banje ba"
Yace "ok let's go"
Ta bishi zuwa mota, ya buɗe mata gaba ta shiga, ya ajiye Abincin a bayan motar, ya kunna suka tafi.
Sun ɗanyi tafiya, kan su ƙarasa gidan Usman, suna tafe suna hira da Nana ta na zuba masa shirme kala kala.
Gidan babba ne, sedai be ka gidan su Girma, buzun da ke gadin gidan yana ganin Motar Faruk ya buɗe musu, suka gaisa da Faruk, ya shiga da motar.
Ta ƙarewa harabar gidan kallo, sannan ta kalli Faruk tace "gaskiya gidan nan me kyau ne, yayi kyau sosai"
Yace "dagaske?"
"Allah yayi kya masha Allah"
"Zan gayawa dr. Ince kin yaba gidansa, kimce yayi kyau"
Ɗan kwaɓe baki Nana tai, dan da Dr. Da Sadik ba suyi mata ba, Dr. Ba shi da fara'a Sadik kuma bashi da mutunci.
Ƙofar falon Faruk yai knocking, sun ɗan jira, 'yan mintuna sannan aka buɗe.
Dr. ne ya buɗe, da alama bacci suke, Faruk yace "wai haryanzu baku tashi ba?"
Uasman ya ɗan yamutsa fuska yace "kai kullum seka dinga mana sammako haka, ka dena kawo Abincin nan haka Please"
Faruk yace "Ai nima Umarnin Mother nake cikawa, ita zaka cewa a dena kawo muku Abinci"
Usman yasa hannu ze karɓi flasan Abincin, amma Faruk yace "meye haka? Wallahi semun shiga, Nana wants to see your bride, semun shiga"
Ya ture Ussy ya shige, Nana tabi bayansa tana leƙa fuskar Usman, ko zeyi Magana, amma taga beba, se yamutsa fuska da yake alamar an takurashi.
A Falo suka zauna, Usman ya wuce bedroom ya barsu, Faruk ya kunna musu kallo yace "muna nan, ka gama kumburin ka, se Nana ta ga amarya"
Nana tace "naga kamar yaji haushi fa, ko mu tashi mu tafi ai naga gidan, kuma naga amaryar ranar biki"
Faruk yace "ba haushi yaji ba"
"Amma ai naga ya sha kunu fa"
"Ai shi haka yake, ba ya dariya sosai shiyasa ba'a fiye gane ɓacin ransa ba, koma yaji haushin ƙyaleshi kawa, a nan ma zamu karya muci har na rana sedai su fashe shi da amaryar"
Dariya Nana tayi tace "idan zasu fashe semu tafi"
Ya biye mata suka cigaba da hirarsu, kusan mintunansu talatin, sega Jidda ta fito ita da Usman, tana sanye da doguwar riga da hula akanta.
Tana ganin su Faruk, tai murmushi tace "Afuwan uncle, mun barku a falo ban san kunzo ba, be tasheni ba"
Faruk yace "ai dama nasan baze tashe ki ba, nikuma nace muna nan se kin tashi"
Tai murmushi tace "ya gida ya Mother na"
"Tana lafiya ƙalau, tana gaisheku, ima bacci na ta kirani a waya, wai inje Kitchen in ɗakko Abinci in kawo muku, mun kawo kuma mijinki se wani haɗe rai yake yi"
Banza Dr. Yai musu, ya zauna ya ɗau remote yana canza chanel.
Nana ta kalli Jidda tace "Ina kwana"
Jidda tace "Lafiya ƙalau, ya kike?"
Nana a ranta tace "wai su wannan suyi hausa ma se sun mata iyayi" a fili tace "lafiya ƙalau"
Jidda tace "Uncle ina kuka sami wannan ne? Naga dai ba Khairat bace, Khairat ta girmi wannan, kuma gashi tana kama da ku"
"She's our little sister"
"Haba dai, dama Mother na da 'ya mace ne?"
"Cousin sister ɗinmu ce, tana gidan Hakimi ne ita"
Jidda tace "Allah sarki, sannunki kinji"
Nana tai murmushi kawai, Usman yana ta canza tashoshi, ya kamo MBC3 ana film ɗin up, Nana tai farat tace "laaaa cartoon dan Allah a bar mana"
Camzawa yai ba tare da ya kula Nana ba, Jidda cikin shagwaɓa tace "haba Baby, dan Allah ka bar mata mana"
Ba shiri Nana tace "subhanallahi Baby kuma"
Take dariya ta ƙwace mata, ta kalli girman Usman fuska duk gashi, amma ana ce masa Baby.
Dariya Jidda tai tace "it sounds strange to you ne? Yayi girma ince masa baby ko?"
Nana dai dariyarta ta cigaba da yi, dan babyn nan ya bata dariya sosai.
Faruk yace "mu fa gaskiya ba mu karya ba, dan haka a haɗa Abinci mu ci"
Jidda tace "eyya sorry, kar ace ina da rowa ban san ba ku ci Abinci ba ai, bari in ɗakko plates se mu karya tare.
Ta ɗakko kwanuka a Kitchen, ta zuzzuba Abincin ta haɗawa kowa tea ta bashi, suka fara ci, sedai Nana ta kasa sakin jiki taci Abincin se ɗan tsakurar sa da take saboda su Faruk da ke gurin.
Maimakon da suka gama cin Abincin su tashi su tafi, se suka shantake a gidan dan Jidda ba ƙaramin dariya surutun Nana yake bata ba.
Inna kuwa tun bayan farkawarra ba ta ga Nana ba,