Showing 45001 words to 48000 words out of 259198 words

Chapter 16 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13313

Baby Princess, naji kinyi shiru"

"Ba ka cemin ƙanwarka ce ba?"

"Ai cousin ɗina ce, akwai Aure a tsakanin mu"

Take Farhan taji zuciyarta na tafasa, jiki a sanyaye tace "se anjima"

Sadik yace "Malama kar ki kashemin waya, ban gama Magana ba"

A ɗan hasale tace "to ai aiki zanyi"

Rungume pillow yayi yace "na so ace am with you right now, in ga kishi na a kyakykyawar fuskar nan taki Baby, da wasa nake miki wallahi, tsokanar ki kawai nake"

Tura baki tai kamar yana ganin ta tace "to ni ina ruwana in ma dagaske kake"

"Ke ko kike da ruwa Yarinya, ba zaki tabattar da hakan ba, se kin ganni da wata, amma bana fatan hakan, ke kaɗai kin ishi Prince, am sorry kinji Babyna wasa nake miki"

Motsi ta jiyo a tsakar gida, dan haka da sauri tace "se anjima"

Ta kashe wayar, kallon wayar yayi, tare da yin murmushi, ji yai duk damuwarsa ta gushe, ya ji daɗin yadda yanzu take sakin jiki harta faɗa masa abunda yake ranta, a hankali yana sake gane halayenta.

Sauka yai daga kan gadon yana murmushi, da jin daɗin yadda kishinta ya kasa ɓoyuwa.

Ita kam Farhan shiru tayi, tana sauraren wanda ke motsi a tsakar gida, Huzaifa ya leƙo ɗakinta yace "kin gama wayar?"

Tace "eh na gama, ga ta Nagode sosai"

Ya sa hannu ya karɓi wayar yace "ba batun godiya, kuɗin kati kawai zaki kawo"

Ba tace komai ba se murmushi da tai masa.

Shiru tai ta na nazarin maganganun Prince, yanzu idan dagaske yake mata fa, Khairat ma budurwarsa ce!.

Da ma ana ta masa gorin yana Soyayya da ita, tana abu kamar 'yar ƙauye, amma da gani dama Khairat wayayyiace kamar Prince, dan yakan yi mata hirar Khairat ɗin, amma ba ta taɓa kawo komai a ranta ba, saboda cewa yake ƙanwarsa ce.
Gefe guda kuma ga batun Sunusi, da ta tuno zancen Sunusin nan, se taji gabanta ya faɗi gaba ɗaya se ta rasa sukuni.
Ba ta san da wani idon zata fara kallon tsabar idon Abbanta, idan lokaci yayi tace masa ba ta son Sunusi ba ita da wanda take so.

A hankali ta zame jikinta ta kwanta, ta lumshe idanunta tana sauraron yadda bugun zuciyarta ya ƙaru saboda damuwa.

Shikam Prince zuwa yamma tuni ya manta da batun wandon sa da Khairat tai masa asara, sema nemanta da yake suje taga gurin da ya kama, za suyi party da abokan sa.

Sedai ya nemi Khairat ya rasa, Mother ta sanar masa, ko ɗinkin ba taje ta karɓo ba, tunda yai mata tijara da safen nan, ba ta kuma fitowa ba.

Ɗan girgiza kai yai yace "lallai ma yarinyar nan ba ta da kunya, tai min laifi kuma ta hau fushi, Allah ya temaketa Princess ta bani haƙuri, fa sena tattaka ta"

Mother tace "wacece kuma Princess"

Ba kunya Sadik yace "sirikar ki ce" yai maganar yana nufar part ɗin Mother.

Ɗan girgiza kai tayi ta cigaba da sabgoginta, dan bata ɗaukar maganganun Sadik ɗin da mahimmanci, tana barinsu ne a mazaunin ƙuruciya, Ina Sadik ina wata budurwa.

Duk wani shirye shirye Sadik ya kammala, daga kama guri kuɗin Abincin da zasu ci shi da abokansa duk ya kammala biya.

Ranar Laraba ya kama ranar da Sadik ɗin zeyi tasa walimar, shida abokansa saboda ranar Alhamis za'a fara bikin.

Ɗan maidaidacin hall ne ya kama, yayi kyau sosai gurin, ƙarfe biyar motoci suka fara parking a harabar gurin.

Kallo ɗaya za kaiwa matasan yaran, masu ji da tashen balaga kasan 'ya'yan gata ne.

'yan secondary, Mazansu da matan suna sanye cikin crazy jeans, da riguna me ɗauke da sunan Amarya da Ango a gaba, baya kuma sunan mamammalakin rigar.

'yan makarantar sun wa Sadik kara, dan harda 'yan primary a cikin wanda suka zo partyn.

Shikansa uban gayyar duk da Asarar da Khairat tai masa, amma ya saka wani wandon, yayi kyau ya fito a ainihin ajebon sa, sumar nan tasa afro style ta sha wanki da mayuka, se wani irin ƙyalli take.

'yan mata sangan sangan se yawo suke a cikin maza da matsastun riguna da wanduna, duk sun matse halittun Jikinsu.

Tamkar jinsi ɗaya suke, haka suke shiga suna fita a cikin mazan nan, ba ruwansu da wannan namiji ne waccan mace ce.

Ita kanta Khairat da taje gurin, seda ta sarawa rashin ji irin na 'yan makarantar su Sadik, duk itama ta su makarantar suna nasu rashin jin, amma su Sadik sun damesu sun shanye.

Nan aka fara raye-raye, da ɗaukar hotuna, su Nas suna ta zuba rashin mutunci, da tanka 'yan matan in anjima su rungumo waccan, ko su kamo waccan suna rawa.

Shikansa uban gayyar haka 'yan mata suka baibaye shi, da sunan ɗaukar hoto suna rungumarsa, dan duk taƙadirancin Sadik a school, ba ruwansa da rungume rumgumen mata.

Kan stage suka janyo shi, suka dinga juyashi da sunan rawa.

Mubarak ne yace "mutumin nifa banga Farhan ba"

Haɗe rai Sadik yai yace "in ka ganta me za tai maka?"

"A'a bakomai, ai gani nai Yakamata ace tana gurin nan dan tayaka murna"

A taƙaice Sadik yace "ba ta zo ba"

Ba'a tashi daga gurin nan ba se goma na dare, amma anci an sha yadda yakamata, wanda aka gayyata da wanda ba'a gayyata ba duk sunci sun ƙoshi.

Wasu sukaiwa Sadik keyholders da Manyan kofuna na cas, da sunan couple's ɗin a jiki, kowa da abunda ya bayar na gudunmawa saboda shima Sadik ɗin meyi ne.

Seda aka watse za su taho gida sannan hankalin Sadik ya dawo jikinsa, Mother tai masa missed calls ba adadi.

Haka ma Khairat, itama wayarta kira ne rututu a ciki.

Khairat tace "Sadik kaga kiran wayar Mother, ga na Mummy bari in kira su inji ko lafiya?"

"No ƙyalesu in muje Gidan ayi duk wadda za'ayi"

Haka ya cigaba da driving, suka tafi gida.

Sedai suna zuwa gidan, a harabar gidan suka tarar da su Mother a tsaitsaye suna kiran layinsu, dan babu wanda yasan in da suka tafi, Sadik be gaywa kowa party ya shirya ba, dan karma asa wasu su bisu suje su hana su rawar gaban hantsi.

Ganin su Mother harda shi kansa angon a harabar gidan be dameshi ba, dan ko a jikinsa, amma idonsa na sauka a na Inna yaji gabansa yai wata irin mummunar faɗuwa!


Domin sauke manhajar AREWA BOOKS, Danna wannan link ɗin.

https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f

Domin gyara, Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.



https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f






21-22






Jikin Sadik yai sanyi da kallon da Inna take masa, wani irin kallo take ƙare musu tun daga sama har ƙasa.

Mother tace "Auta ina kuka tafi haka? Tun wajen goma na safe rabonku da gidan nan, ba irin kiran wayar da ba'ai muku ba amma ba kwa ɗauka, ina kuka shiga ne?"

Tsuke fuska Sadik yai yace "mun shirya party ne da abokaina, 'yan makarantar mu, shine muka je da Khairat"

Usman yace "Amm ai seka sanar, duk ka ɗaga mana hankali kun sa mutane a damuwa"

Khairat dai tai tsit tana rarraba ido.

Sadik kam ƙara haɗe rai ya fara takawa, ze nufi sashin su.

"Kai zo nan" Inna ta kira shi cikin bada umarni.

Ɗan tsayawa yai yayi jim, se kuma ya juyo ya tako in da suke ya tsaya.

Inna ta kalli Khairat ta kalli Sadik, sannan ta kalli in da Mother ke tsaye tace "yanzu ke Hauwa tsakanin ki da Allah, Laifin da yaran nan sukai ba su isa hukunci me tsauri ba? Kalli shigar jikinsu, kalli jikin wannan Yarinyar, ta bishi cikin maza, tun safe ba sa gida se ƙarfe goma na dare suka dawo, maimakon ku tsananta bincikar su, ku san matakin da zaku ɗauka, kawai iya abunda zaku ce musu kenan? Kalli wandon jikinsa kamar mahaukaci duk a yayyage kamar wanda ya zare, kalli uwar sumar kansa kamar ɗan daudu, ita wannan Yarinyar kalli suturar jikinta.
Wannan wane irin riƙo kuke wa yaran nan? 'ya'yayenku fa se Allah ya tambayeku akan rainon su, suna shekarun su ne na RUƊIN ƘURUCIYA, Komai ze iya faruwa, amma har suje su shirya abu isu isu babu sa idonku a kai, wannan wace irin rayuwa ce, a tunanin ku wannan wayewa ce? Babu sa ido akan yaranku kun bar su suyi abunda suke so? Wallahi idan baku kiyaye kun kula da tarbiyyar yaranku ba watarn za kuga abun da ba kwa so"

Cike da ƙosawa Mother tace "Allah ya kiyaye ya tsare, dan Allah kima dena wannan maganar, kar ki musu baki yara idan ba'a bar su sun huta ba ya za'ai, a kirshe su, shima  yawan takura yana lalata yara, kuma naga yaran nan sun saba da rayuwa da turawa ne, in Allah ya yadda ba abunda ze faru, yawan yi musu faɗa ma raini yake kawowa, kuma party a tsakanin su yara ba yanzu suka fara ba, kuma ba abunda ya taɓa faruwa, sunyi ne kawai dan taya ɗan uwan su murnar Auren da ze"

Inna ta jinjina kai tace "ba shakka, 'ya'yan turawa ko, shikenan Allah ya temaki turawa, Allah ya shirya"

Tana gama faɗin haka ta juya ta koma cikin gidan.

Shi kam Sadik kamar ya fashe, saboda yadda ya kumbura baki yana wani irin huci.

Mother tace "kaga abunda ka janyo min ko? Na gayamaka tunda Allah yasa tsohuwar nan ta tare a gidan nan kayi komai a hankali, in ba haka ba ido zata samana komai ta gani taita masifa"

Usman yace "Mother, dan Allah duk kuyi haƙuri dan Allah komai ya wuce, karki kuma yin wani lafin, kuma dan Allah idan ta ɗau zafi ki dena tanka mata, hakan yana tunzurata, Yanzu dai duk kuyi haƙuri"

Sadik bece komai ba ya wuce ɓangaren su, Khairat ma ta shiga cikin gidan tana sunkuyar da kai kamar munafuka.

Mother kuwa tana zuwa ɗakinta, cikin 'yan uwanta ta hau masifa tana mitar Wai Inna tana ja wa 'ya'yansu masifa tana musu baki, ita Alla alla takema ayi bikin nan tabar mata gida duk tabi ta isheta.

Suka haɗu suka dinga yi da Inna suna zagin ta.

Ita kam Inna tunda ta koma ɗakin da suke, tai shiru tana tunani al'amuran Sadik na bata tsoro da mamaki, tabbas idan aka cigaba da tafiya a haka da wannan sakacin ko sakarcin na uwarsa tabbas Yaron ze lalace.

Dan ta lura halayyar sa daban da ta sauran yayyen sa, tarbiyyar Sadik na buƙatar jajircewa da kuma sa ido, saboda kansa yana rawa fiye da shekarun sa.

Sadik kuwa gaba ɗaya ransa a ɓace yake, Alla Alla yake a gama bikin nan wannan tsohuwar ta bar musu gida, ya rasa me ya tare mata take masa wannan abubuwan, ba damar ya motsa se ta haushi da masifa.

Haka yana kumbure kumburen baki, yai wanka ya kwanta, amma bacci yaƙi zuwa.

Can kuma se partyn da su kai suka dinga dawowa kansa, take surorin 'yan matan nan suka dinga dawo masa kansa.

Ƙoƙarin banzatar da tunanin yayi, amma abu ya faskara, zuciyarsa ta dinga raya masa cigaba da kallon series film ɗin nan, amma wata zuciyar ta shiga gargaɗin sa.

Series ɗin yana ƙayatar da shi, amma kusan kaso arba'in na film ɗin yana bayyanar da very hot Romance ne tsakanin masoya.

Runtse idanunsa yai, amma se ya dinga Ganin Farhan a idonsa, da wannan kyakykyawan murmushin nata.

A hankali ya furta "Oh God"

Ya ɗakko wayarsa, ya dinga kallon lambar da ta kirashi da ita, se kuma ya kalli agogo yaga kusan sha ɗaya na dare, jiki a sanyaye ya ajiye wayar, ya nemi guri ya kwanta.

Da tunani barkatai cikin ransa da haka bacci yai awon gaba da shi.

Washegari Alhaji Abdullahi ya dawo daga tafiyar da yayi, wanda ya kasance ranar fara bikin ɗansa Usman.

Da yamma ya shiga gaida Inna, lokacin kusan duk jama'ar gidan sun yo ye sun tafi gurin biki.

Cike da girmamawa suke hira shi da Mahaifiyar sa.

Can Inna ta nisa ta kalli ɗan nata tace "Abdullahi!"

Wani banbarakwai yaji, dan Inna ba ta sba kiransa kai tsaye da sunan sa haka ba, se idan ta na da wata mahimmiyar magana.

Hakan yasa shi tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan ta, yana sauraren me zata ce masa.

Cike da damuwa tace "Kamar yadda ka sani, ni mace ce me son haihuwa, Allah ya bani haihuwa, sedai duk sun koma, kaine ɗana na huɗu, bayanka na hayayyafa amma duk ba su rayu ba, ɗan uwanka Abubakar ya taso ina murna Allah ya barmin, se bayan yayi Aure ya haifi wannan Yarinyar ya karɓe shi ya karɓi mahaifiyarta"

Mamakin maimaita wannan tarihi da ta ɗakko yake yi, wanda duk wannan abun da take faɗa ya riga ya san da shi.

Ta cigaba da cewa "Ni macece me son iyali na, fiye da tunani, duk da irin son da nake maka, Allah ya ɗaga ka, kayi Aure ka dawo birni da zama, sedai ƙawa zucina akan 'ya'ya ya ragu, tun bayan da Kai Aure, nasan dama namiji wataran mijin wata ne, mace ce duk inda take hankalinta na kan mahaifiyarta.

Na ɗora rai akan jikokina, saboda ganin suma duk tsastona ne, na ƙallafa rai akan su, sedai shima sena fuskanci matarka ba ta buƙatar hakan, ba ta son 'ya'yanta su raɓi ƙauyawa jahilai.

Sena maida hankalina kan Abubakar, ba dan zuciya ta ta dena sonka da 'ya'yanka ba, sedan bana son shiga cikin lamarin iyalan ka, saboda gudun matsala da zubewar mutunci.

Ashe Habu ma bame tsawon kwana ba ne, bayan yayi aure, an haifi wannan 'yar, matar tazo sake wata haihuwar Allah ya karɓeta, bayan rasuwarta nai ta fama da shi yai aure, amma be ba, har shima yai hatsari a hanyar dawowa daga gidanka zuwa ƙauye shima Allah ya karɓe shi.

Nasan za kayi mamakin sake maimaita maka abunda ka riga kasan shi, kuma ya wuce ban yi haka dan Komai ba, sedan sake jaddada maka irin so da ƙaunar da nake maka da 'ya'yanka, saboda dukkanin ku tsatsona ne, ba zan so inga wani mummunan abu ya sami zuriyata ba.

Ja da baya da nayi na zura maka ido kai da iyalan ka, baya na nufin na sallamaku bane bana kishinku.

Ka sani na sani, ni mace ce me zafi kuma da haka nai tarbiyyar ku, ba dan na dage da addu'a da jajircewa ba, da baka taso a haka har wani yai sha'awar Aura maka 'yarsa ba.

Abdullahi, kai da yaranka ba turawa bane ba, 'ya'yanka da kai Hausa Fulani ne masu kamala da tarbiyya, dan kayi boko, ko kun zuwa ƙasashen turawa ba shi ke nufin kuma turawa bane ba.

Bari in fito maka a mutum, yaranka ba su da tarbiyya!"

Da sauri Alhaji Abdullahi ya ɗago ya kalli Inna yace "Inna ba su da tarbiyya kuma?"

Cikin ƙwarin gwiwa, da nuna isa Inna tace "Ƙwarai kuwa, 'ya'yanka ba su da tarbiyya, mussaman me sunan Ƙarami ɗan Autan ka.

Allah ya sani ina ƙaunar yaranka fiye da yadda nake sonka, ka san yadda nake son jikokina duk da ba sa zuwa in da nake, amma hakan ba ze hanani faɗin gaskiya akan su ba.

Abdullahi ka sanya idanu akan tarbiyyar yaranka, kuɗi ba hauka bane ba, kafin kai dubun ka sunyi arziki kuma sun shuɗe babu su a duniyar nan, yana daga cikin sadaka me gudana bayan ran bawa, ya haifi ɗa na gari da ze dinga aikata aikin Alkhairi.

Kana tunanin wannan? Ko kuma neman kuɗin kawai ka saka a gaba, yau kana Habuja, gobe kana gurin wancan gwamana, jibi ka na waccan ƙasar, ka bar mace da tarbiyyar gidanka matar da ita kanta tana buƙatar tarbiyya, wannan ganganci ne haihuwa da damuna.

Ba ina kushe maka iyali bane, ko ƙoƙarin haddasa maka husuma a cikin gida ba, bulaliya nake maka, naga shekaranjiya, naga jiya gashi ana damawa da mu a yau, ko kai da kai boko ka zaga duniya, ba zaka gayamin sanin duniya da zamantakewa ba, bar ganina bagidajiya bafullatanar ƙauye, shekarun da nayi a duniya naga abubuwa da dama, kuma ina iya fahimtar abubuwa da dama.

Dan haka ka kula da iyalinka, ka sa ido akansu sosai ka kula da tarbiyyar su, ka barsu da ingantacciyar tarbiyya da kyakykyawar rayuwa yafi wannan kuɗin da kake tara musu, da basu san ciwonsu ba, sedai su ɗiba suyi ta bushasha"

Tun da Inna ta fara faɗan nan, ya sunkuyar da kai, bece uffan ba seda ta kammala, ya ja nannauyar ajiyar zuciya yace "Insha Allah Inna za'a kiyaye, in Allah ya yadda zan kula kamar yadda ki ka ce"

Inna tace "to Allah ya wuce mana gaba, ya kare dukkan zuriyar Annabi daga taɓarɓarewa da sharrin ƙarshen zamani"

Yace "Ameen ya Allah, Inna nagode Sosai"

Har ya miƙe ze fita tace "fita za kayi ne?"

Yace "eh Inna"

Tace "to zo in fesa maka turare"

Yai murmushi yazo gabanta ya durƙusa, ta ɗakko turare ta feffesa masa tace "yawwa duk da naji kana ƙamshin turare ai gara ka ƙara, ai ƙamshi rahama ne"

Yai murmushi yace "hakane Inna nagode"

Tai murmushi ta cigaba da laziminta.

Maganganun Inna sun damu Alhaji Abdullahi Sosai, duk d aba ta fito ta gayamasa ƙarara meyafaru ba, amma maganganun nata sun tsaye masa a rai sosai.

Se dare sannan aka din ga dawowa daga gurin kamun da aka tafi, wanda zasu kwana a gidan duk suka taho nan gidan, dan a tare motocin suka dinga dawowa.

Wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, Mother tayi wanka ta canza kaya, ta nufi sashin Megidanta da coffee.

Tun da taje take zuba masa hira, tana nuna masa hotunan biki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login