Showing 132001 words to 135000 words out of 259198 words
Chapter 45 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
fita ya bata Guri ta cigaba da sharar tana ƙunƙuni.
Ya zamana kusan kullum se sunyi faɗa, da abun nasa ya lafa amma yanzu kamar kaji, ko wasu abokan gaba haka suke yi.
Da ne Inna take shiga ta tsawatar musu, amma yanzu kam ta ƙyale su. In zasu kashe kansu ko a jikinta, suyi tayi, sedai in ta gaji ta ƙarewa Nana zagi.
Lilly ta rasa ta in da zata ɓullowa lamarin da ke tsakanin ta da Nazir, Sosai take sake jinsa a ranta, kuma ba iya Soyayyarsa ce ke damunta ba, har da muradin sake kasancewa da shi.
Abu kamar wasa ko Abinci da baccin kirki suka gagari Lilly, kamar yadda take karantawa a Novels, haka ta auri shan Lipton da lemon tsami, dan samawa kanta rangwame.
Abun ya fara damunta psychologically, gaba ɗaya ta koma wata irin shiru shiru, kusan kullum ta na ɗaki, se in waya take da Nazir, shine take rage damuwa, shima kasamcewar ita kaɗaice a ɗakinta, wasu lokutan wayar tasu ta kan zarce ƙa'idar Addini, su shiga wani fage daban.
Kusan kullum se ya tambayeta, ya ake ciki tai maganar Aurensu kuwa a gidan su, amma tace a'a ita tsoro take ji.
Yau da ita da Mamanta da Daddynta kasancewar yana gida hutu, suna Dinner da daddare, amma sam ya lura da yadda ba ta iya cin Abinci, se juya cokali da take, tai shiru tana zancen zuci.
"Hey what are you thinking of?"
Maganar mahaifinta ce ta dawo da ita daga tunanin da take, firgigit ta kalleshi tace "Nothing"
Yace "No, akwai wani abu, ba kiga yadda ta rame ba? Gaba ɗaya kamar bata walwala" yai maganar yana kallon maman Lilly.
Tace "Na gani wallahi, i even ask her tace min bakomai, shiyasa na ƙyaleta kawai.
Yace "ko dai haryanzu jikin ne?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
Yace "to meke damunki, Gayamin kinji Babyn Daddy"
Ji tai kamar ta gaya masa, amma yai mata wani irin kwarjini da ta kasa ko ɗaga ido ta kalleshi, tace "bakomai fa Daddy"
Yace "oya, maza ɗauki Abinci ki ci, ko in baki da kaina ne?"
Ta girgiza kai tace "zan ci da kaina Daddy"
Yace "oya maza ɗau spoon ki ci ina kallon ki"
Haka nam ta ɗau cokali tana cin Abincin, ba dan tana jin daɗin sa ba.
Farhan tunda su kai wayar nan ta ƙarshe da Sadik, ba su sake waya ba, ta kira wayarsa in ta shiga ma baya ɗagawa, jikinta gaba ɗaya yayi sanyi da lamarin, ga lokacin da za a kawo kuɗin Auren ta da Sunusi se ƙaratowa yake yi.
Ta rame tayi duhu, amma hakan be sa Ummanta saurararta ba balle taji abunda yake damunta ba.
Duk da lokuta da dama ko Abinci aka bar mata a Kitchen haka za'aje a tarar da shi ba ta ci ba, in kuma ita ta girka haka zata raba ga bawa kowa, amma ita ba zata ci ba, dan ɗaci Abincin yake mata a baki, mussaman idan yaje maƙogwaronta.
Wata irin matsananciyar soyayyar sa ce take cigaba da nuƙurƙusa zuciyarta, mussaman lokuta masu hatsari da suka faru a rayuwar soyayyar su, her first kiss with Sadik, his romantic actions towards her, how supportive and protective he is, wata karaya ce ta sake baibaye Farhan, da tunanin idan ta rasa Sadik waye ze maye mata gurbinsa, Sadik ya koyar da ita abubuwa masu ruɗani, da tsayawa a zuciya, ba ta tunanin za ta so wani kamarsa.
Sadik ya cire layikan wayoyinsa gaba ɗaya, ya ƙulle su ya saka a ƙarƙashin kilisan ɗakin, dan sam baya son wani ma ya kirashi a waya, sam ji yake wayoyin ma sun fita daga ransa, yaita ƙoƙarin tuna wani abu, amma ya kasa se dai ya haƙura.
Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana, yana kwance yai rigingine, kamar wanda aka tsikara, ya tashi ya fito ya nufi turakar Hakimi, abun mamaki yana zuwa ya tarar da Abba da Faruk.
Turus yai yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Abba ya kalli Sadik ya ganshi so calm, yai ƙiba yai haske saboda babu yawo, sedai kana kallon fuskar sa kasan a cikin damuwa yake, dan samu babu walwala a tare da shi.
Tsayawa yana binsu da kallo, kamar be sansu ba, in lissafin sa daidai ne, yau watansa uku da kwana Ashirin da biyu kenan a garin nan, ba tare da ya ga wani daga gidan su ba, kuma ba tare da ya saka ƙafarsa a waje ba.
Abba yace "to ba zaka ƙaraso ciki mu gaisa ba kenan?"
Jiki a sanyaye Sadik ya shiga ɗakin ya zauna a kusa da Abba, amma be ce Komai ba.
Faruk ya taɓa shi yace "meye hakan kake yi kamar wani ƙaramin Yaro?"
Ɗagowar da Sadik ze yi sega hawaye a fuskar sa, take Abba yaji yana neman ya karaya, wani tausayin Sadik ya shige shi, ya san zaman ƙauye baze zama abu me sauƙi ga Sadik ba, tunda tun haihuwar sa a cikin gata yake, amma an ajiye shi a nan tsawon kwanaki ba tare da ganin kowa daga gida ba.
Cikin dakiya Abba yace "meye kuma na kukan? Sekace wani ƙaramin Yaro?"
Faruk ne ya rungume Sadik a jikinsa, yana duddukan bayansa alamar rarrashi yace "we Miss You Brother"
Sadik yace "don't lie to me, you don't Miss me at all"
"Who told you so? Zo muje waje kaji"
Sadik ya yunƙura ze tashi, amma Hakimi yace "Uban naka ma ba zaka gaishe shi ba?"
Ya kalli Abba yana son yai Magana, amma ya kasa se kuka.
Abba yace "Ranka ya daɗe ƙyaleshi ma gaisa an jima"
Faruk ya ja hannunsa suka fita daga turakar, Inna ta taɓe baki, banda sangarta kamar Sadik ya zauna yana wannan uban kuka haka kamar wani ɗan yaye.
Hakimi ya maida hankalinsa kan Abba yace 'Amma Bawan Allah, nace ya batun tafiyar Yaron nan nemx
Abba yace "muna ta shiri ranka ya daɗe, nan da abunda be fi sati uku ba insha Allah ze tafi, ana ta shirye shirye"
Hakimi yace "yayi kyau, abunda nake so da kai shine, a sati ukun nan ina son a nemawa 'yar uwarsa Makaranta a inda ze karatu"
Abba yace "Nana?"
"Eh ita"
Abba yace "Amma ranka ya daɗe, ai shi jami'a ze shiga ita kuma tana aji biyu a ƙaramar Sakandire"
"Eh, ai ba a jami'ar nake nufi ba, Makaranta nake son a sakata daidai da karatunta"
Inna tace "Amma Allah ya baka yawan rai, Nanan za'a kai turai karatu a wannan shekarun nata?"
Hakimi yace "haka nace, umarni nake bayarwa ba shawara ba"
Abba yace "shikenan, ai hakan baze gagara ba, insh Allah za'a nema mata"
Gaba ɗaya kan Inna ya kulle, me Hakimi yake nufi da yin haka? Wannan wane irin hukunci ne? Yarinyar da ke kan ganiyar tashen balaga ita za'a kai ƙasar waje karatu? To waye ze kula da ita a can?'
Sadik kam Faruk ne ke ta rarrashin sa, Sadik yace "Yanzu meyasa baku taho min da Mother ba? Shikenan an tsaneni an kawoni nan an ajiye kamar wani ɓarawo?"
"Kayi haƙuri Sadik, yama za'ai ace ba'a sonka, Abba ne yace Mother ba zata biyo mu ba, amma ita ma tayi kewarka sosai, kai kasan kukan da tai saboda an bar mata kai a nan, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe Insha Allah"
"Amma tare zamu tafi ko?"
Faruk yace "wallahi ban sani ba, amma bari muga zuwa mu tafi me zece"
Shi kansa Faruk yai mamakin yadda Sadik ya zama wani shiru shiru.
A hankali ya dinga ɗaukar Sadik da hira, har Sadik ya manta da damuwar da yake ciki suka cigaba da hira.
Sedai ga mamakin Sadik yaji Abba yace Faruk ya tashi su tafi, gaba ɗaya zuwansu basu fi awa ɗaya da rabi ba zasu tafi.
Sadik yace "Abba ni fa?"
"Ban da kai Sadik, a nan zamu barka se lokacin tafiyar ka tukuna"
"Abba saboda me?"
"Saboda haka nace" Abba ya bashi amsa.
"Abba yanzu ma tafiya za kai ka barni?"
"Eh, zama guri ɗaya yasa ka nutsu ka ƙara kyau"
Sadik bece komai ba ya juya ya tafi ɗakinsa ya rufo ƙofa.
Gaba ɗaya jikin Faruk yai sanyi, shi kansa Abba ba haka ya so ba, amma ba yadda ya iya.
Hakimi yace "Bawan Allah, ko baka faɗa ba, nasan zuciyarka da ta matarka babu daɗi na riƙe muku ɗa, amma banyi hakan dan muzguna muku ba, duk abunda kaga inayi da dalili nake yi, wanda base na zauna ina faɗar dalilin ba idan na isa, dan haka in anje gida a bata haƙuri, muna ɗaukar matakin da ya dace ne, Allah ya kiyaye hanya"
Abba yace "babu wani dalili da ze sa ayi abunda za'a cutarmu, muna godiya duk matakin da aka ɗauka akanmu daidai ne, kai da kaya ai mallakar wuya ne"
Hakimi yace "hakane, Allah yayi albarka"
Abba da Faruk suka kama hanyar komawa gida.
Suna tafiya a hanya, Faruk ya lura da yadda Abba yai shiru kamar yana nazarin wani abu.
"Abba meke faruwa ne" Faruk yai maganar cikin ladabi.
Abba yace "Bari kawai Faruk, ban san me Hakimi yake shiryawa ba, yace se an nemawa Nana Makaranta a London, abun tambayar a nan a ina zata zauna? Waze kula da ita? Kaga Sadik yana hostel ni kuma ba zanso ta zauna a cikin turawa ba, saboda addinin ta da tarbiyyar ta, da se ince ko gidan Steve zata zauna, ban san yadda a kai Hakimi ya yanke wannan hukuncin ba, duk da tarin tsantsenin sa akan tarbiyya, abun mamaki naga ita kanta Inna ma ba ta san zacen ba"
Faruk yace "aikuwa duk wani hukunci da Hakimi ze ɗauka, baze ɗauka haka nan ba seda dalili"
"Hakane, na so sanin dalilin amma naga baya son in fiye tambayar dalilin, shiyasa ban tambaye shi ba"
"Amma Abba meyasa baka tambaye shi mu tafi da Sadik ba"
Abba yai murmushi yace "kana son in ja wa kaina ɓacin rai ne? Bari dai in yi abunda yace in gani, samun Admission ɗin nan kusa abune me wuya amma dole zan bincika"
Suka cigaba da tafiya kowa yana saƙe saƙe a zuciyar sa.
Sadik zaman dirshan yayi, zuciyarsa ta bushe gaba ɗaya, ga kansa ya kulle ya rasa abunda yake masa daɗi gaba ɗaya.
Farhan na tafe tana jefa ƙafa, kai kace bata da jini a jiki, tunani kawai take a ranta daban daban, haka kurum zuciyarta ke raya mata, anya Sadik ba Yasmeen ɗin ajinsu ya koma so ba, shiyasa yai watsi da ita ba, in ba haka ba meya kai Yaseen gidansu Sadik harta san yana ƙauye?.
Dummm zuciyarta tayi, taji jiri na nema ya kwasheta ta faɗi ƙasa, da Sauri ta kauda wannan tunanin daga ranta.
" 'yan Makarantar bokoko" da sauri ta waiga jin anyi magana a gefen ta.
Haladu ne, abokin Sunusi, ba ta kulashi ba ta cigaba da ƙoƙarin tafiya, yace mata "Ina wuni"
"Lafiya ƙalau"
"Amm Farhan" ta waigo ta kalleshi.
Ji yai kamar ya gayamata abunda Sunusi yake akanta, amma se ya kasa yaga be dace ya tona masa Asiri ba suna tare.
Dan haka yace "An kusa kawo kuɗi ko?"
Banza tai masa ta cigaba da tafiya, Haladu ya jinjina kai ya ƙara tabattar da Farhan ba ta ƙaunar Sunusi, dama ba su dace ba sam.
Lilly ce zaune a Office ɗin Nazir, yana aiki suna hira ta zubo masa ido.
Yace "ya dai wannan kallon fa?"
"Yaushe zaka zo gidan mu?"
"Lilly haryanzu baki cemin komai game da batun za'a bani ke ko ba za'a ban ba, ya za ai na fara zuwa?"
"Maganar gaskiya nayi attempting faɗa a gida amma na kasa, yanzu shawara ɗaya ce kawai ka fara zuwa gidanmu"
"Lilly se in zo gurinki ba iznin iyayenki?
"Nifa haɗuwar nan da muke a school am not comfortable kawai ka zo gidan"
"Amma idan aka ganni a gidanku hakan ba ze janyo mana matsala ba?"
"Ba wata matsala, ai ina ga next week in Allah Ya kaimu zasu Sakwatto, se kazo Please"
"Shikenan, Allah ya kaimu kin san bana son ɓacin ranki"
Murmushi tai masa ta miƙe ta bar Office ɗin.
Ko da Abba suka koma gida ya sha tuhuma a gurin Mother, dan yana shiga gidan ta miƙe tana faɗin "Ina Autan yake?"
Abba yace "kamar yaya?"
"Ba ɗakko shi kaje yi ba?"
"Ni nace miki ɗakko shi naje yi? Kiran Hakimi naje"
"Amma kasan a can zaka barshi, maimakon mu tafi tare in ganshi"
"Ban niyya ba" ya bata amsa ya wuce ya barta a gurin.
Mother ta fara ƙulewa matuƙar gaske, akan abunda ake mata akan Sadik.
Tunda yaga sunyi haka, be yi gangancin gaya mata batun Nana ba da ita ma Za'a nemawa Makaranta a London ba, ya ƙyaleta.
Cikin fargaba da ɗari ɗari Nazir ya shirya zuwa gidansu Lilly.
Tun bayan sallar azahar tai wanka ta shirya tana jiran zuwansa, tai kwalliya ta sa masu aiki sun shirya masa Abinci.
Daga nesa kaɗan da Gidan ya tsaya, ganin masu kaki a ƙofar Gidan.
Ya kirata a waya, ya gaya mata ya zo.
Mintuna kaɗan ta kuma kiransa a waya tace yaje Zasu buɗe masa ya shiga.
Yana karanta fatiha da salati haka ya ƙarasa gaban gate ɗin, ba su ce masa komai suka bashi hanya ya shiga.
Ƙarewa gidan kallo yake, gida kamar ba za a mutu ba, yanzu wannan gida dan dai rayuwar tsirarin mutane a ciki, da ana tuna mutuwa da ba a gina shi ba.
Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga Wayar.
Lilly tace "ka miƙo hanyar da take facing ɗinka zamu haɗu.
Haka ya bi hanyar yana rarraba ido.
"Oyoyo" ya jiyo Muryar ta, ta taho da gudu ta rungume shi.
Shima rungumeta yayi yace "Kinyi kyau sosai Baby"
"Dama dan kai nayi, tunda ka yaba masha Allah"
Yai murmushi tai masa jagora zuwa cikin wani haɗaɗɗen falo.
Ta gabatar masa da kayan ciye ciye, ta zauna a kusa da shi, Kamar zata shige jikinsa, ga wani irin fitinanne ƙamshi da dukkanin su suke yi.
"Baby a tsorace fa nake"
"Meye abun tsoro kuma? Ba kowa a gidan fa, daga mu se maids da guard ɗin gidan nan"
Ta dinga jansa da hira, yana cin Abinci Kamar wasu miji da mata.
Sosai suke ƙoƙarin sake kauce hanya, da ƙyar Nazir ya aro jarumta ya ture Lilly, yana sauke numfashi.
Yayin da tai shiru tana kallonsa.
"Lilly alƙawari mu kai ba zamu sake ba, Aure zamuyi kar sheɗan yai tasiri akan mu, kuma kinga matsalar da aka samu wancan karon, bari in tafi"
Ba ta ce masa komai ba, yabi hanyar da ya shigo ya fice.
Nana ba ta san su Abba sunzo ba, kasancewar tana makaranta, sedai tunda ta dawo ba taga Sadik ba ko a tsakar gida.
Ta kalli Inna tace "wai Inna ina wannan suƙundumin?"
Inna tace "me kenan?"
Nana ta nuna mata ƙofar ɗakin Sadik.
Inna tace "wallahi idan ya fito ya dake ki, ki kaimin kuka sena ƙara miki" ba shiri ta tsuke bakinta.
Seda daddare Inna take gayamata su Faruk sunzo tana Makaranta, amma ba ta sanar mata da batun tafiyar ta ƙasar waje ba.
Tace "Amma Inna meyasa basu tafi da shi ba?"
"Nima ban sani ba seki tambayi kakanki"
"Ni duk da yana bani haushi, amma wataran tausayi yake bani wallahi, ya gaji da zaman nan, muma fa lokacin da muka zauna a gidansu gajiya nai da zama"
Banza Inna tai mata ta cigaba da sabgarta.
Nazir da ƙyar ya kai kansa gida, saboda halin da ya shiga, ita kanta Lillyn ta daɗe a gurin da ya barta a kwance, sannan ta tashi ta koma ɗakinta.
Babban abunda ya bata mamaki be wuce yadda su Daddy suka dawo a ranar da daddare, bayan sunce zasu kwana uku sannan su dawo.
Tai pretending kamar tayi bacci, taƙi fitowa, balle tai musu sannu da zuwa.
Ta rufe ƙofarta da key, ta shige cikin bargo tana waya da Nazir, tare da nuna masa yadda tai kewarsa ba tare da kunya ko jin nauyin komai ba, shima haka ya saki baki su kai ta waya.
Se Washegari da safe, sannan Lilly ta gaida su Daddy tare da mamakin dawowarsu a jiya, suna tsaka da karyawa Daddy yace "Lilly waye ya zo min gida jiya da bana nan?" Gabanta ya yanke ya faɗi, ta kalleshi tace "Ammm.."
"Kar ki min ƙarya, bayan tafiyar mu jiya wani yazo gidan nan, kuma ya shigo bisa umarnin ki, waye shi?"
"Amm...mmm....Dadd.....
"Karki kuskura ki min ƙarya! Ba a banza na saka masu tsaron gida na ba, uban waye ya shigomin gida jiya?!" Ya faɗa cikin kakkausar muryar sa.
"Daddy saurayina ne" ta faɗa kamar za tai fitsari.
"Whta! Saurayi Lilly?" Mummy ta faɗa tana kallonta.
"Au ke yanzu nan har kin san kiyi saurayi ki kawo min shi cikin gida na? Lilly are you out of your sense? You are only fifteen years har kin san ha'inci"
Lilly ta shiga girgiza kai tana rarraba ido, dan bata san hukuncin da ze ɗauka a kanta ba.
"Waye shi kuma a ina yake!" Yai mata tambayar cikin tsawa.
"Daddy wani corper ne? Cewa yai yana sona ze Aureni"
Yace "good, kema kuma kina son sa?" Yai tambayar yana tsatsare ta da ido.
Tai saurin ɗaga masa kai alamar eh.
"A ina yake?"
Tace "Nima ban san a in da yake ba kawai haɗuwa mu kai"
Mummy tace "ke Aure kike so kenan?"
Ba Kunya Lilly ta ɗaga kai alamar eh.
Daddy yai murmushin takaici, ya kalli Lillyn da yake ganin ba ta fi ya kamata yai mata wanka ba, amma ita ke cewa wai Aure take so, me ta sani game da Auren da harya bata sha'awa take cewa za tayi.
Ya sassauta zuciyarsa yace "shikenan tunda haka kike so, in dai dagaske yakw, kice ina son ganinsa"
Wani irin farinciki ne ya ratsa Lilly ta gyaɗa kai.
Mummy za tai magana amma ya girgiza mata kai, ya kalli Lilly yace ta koma ɗakinta.
Bayan ta tafi Mummy tace, "kana nufin aurar da Lilly zakayi?"
Yace "sekace bani da hankali, ai daga ji hure mata kunne yake, Allah ne kaɗai yasan tun lokacin da suke tare, sonake yazo in ganshi, in wanda zan yiwa warning n Kawai shikenan, in ma casa shi Yakamata in sa ayi zanyi wanda ya dace".
Yau Friday, Nana na shirin tafiya Makaranta, Inna ta bata sallahun in an tashi daga Makaranta, taje ta karɓo mata saƙo a can wata unguwa, Nana ta amsa da to.
Dan da farko ko makarantar ba tai niyyar zuwa ba, saboda yau jikin Hakimi ya motsa, jininsa ya hau ga zazzaɓi da tari yana ta fama da shi. Dan seda aka kira likita ya duba shi, ana tunanin ko Asibiti za'a ka shi.
Amma inna tace Nana ba zata zauna ba ta tafi makaranta, dan in ta zauna koke koke za tai ta musu.
Har aka tashi daga Makaranta, jikin Nana a Sanyaye yake, ji take kamar kan ta koma gida Hakimi ze mutu.
A gurguje taje ta karɓo saƙon nan, tana tafe tana haɗawa da Sauri, saboda ta koma dan hankalinta yaƙi kwanciya sam.
Sedai