Showing 138001 words to 141000 words out of 259198 words

Chapter 47 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

kawota ba.

A hankali ya ga ta fara motsawa, dan haka ya tsaya ya zuba mata ido.

Ƙoƙarin ta da kabbarar salla take, a cikin yanayin da take, harta fara ƙoƙarin tashi zaune.

Abbas ya maida ita ya gyara mata kwanciya yace "Sannu"

A hankali ta fara buɗe idonta, dishi dishi take gani, ba ta gane a ina take, ta kalli Abbas amma taga fuskar Sadik.

A hankali ta kai hannu, ta riƙo hannunsa ta fara Magana "Sadik, Sadik dan Allah, dan Allah ka dena min haka, you are the only.. only...Sadik I need you....." Allurar da yai mata da ya shigo ce ta cigaba da ɗibarta, dan haka a cikin magagi take.

Abbas yai shiru yana Nazarin ta, da abunda take faɗa.

Ganin ta fara bacci, yasa ya fara ƙoƙarin zare hannunsa daga nata, amma ta riƙe gam tana tura baki.

"Kowane Sadik ɗin nan ya na da alaƙa da damuwarta, wanda ya kai ta ga wannan rashin lafiya"

Wata Nurse ce ta shigo za tai masa Magana, amma ya girgiza mata kai da alamar tai shiru, baya son mara lafiyarsa ta tashi.

A hankali ya zare hannunsa daga na Farhan, ya fice daga Office ɗin.



Nana tana ji ta na gani, da daddare Inna ta haɗa mata kayanta, ta na yai tana mata nasiha akan tayi haƙuri da abunda Allah ya hukunta akanta.
Nana taiwa Inna banza, ta cigaba da sharɓar kukanta.

Inna ta kalleta tace "Nana ba zaki dena kukan nan ba ko?"

Cikin kuka Nana tace "Inna ya za ai in da ne kuka, bayan ba kwa sona, kun Auramin wannan Yaron, wanda a gabanki yake cewa ya tsaneni ni"

"To Nana, Allah ya riga ya hukunta lamarinsa, ba yadda kika iya, sannan karki sake ce masa yaro, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kiyi masa biyayya, duk abunda yakamata in gayamiki na sha gaya miki a baya, bake ba fito na fito da shi, matsayinsa a gurinki a baya daban, a yanzu ma daban, dan haka ki nutsu kiyi haƙuri"

Ƙara rushewa da kuka Nana tayi, tana "Innalillahi wa innalillahi raji'un, nikam na shiga uku wallahi bana sonsa"

Tun Inna tana rarrashin Nana, se data zageta tsaf a daren nan.

Ita kanta Inna ba ta so Auren Nana ya zo mata a haka ba, taso Nanan ta ɗan tasa tai gagarumin bikin aurar da jikarta ɗaya mace da aka mutu aka bari, sedai wannan Auren da a kai na gaggawa shine mafita, akan samuwar abunda ze rusa farincikin ahalin gaba ɗaya.

Sadik kuwa tunda aka ai ɗaurin Auren nan yaƙi magana, se ajiyar zuciya da yake tayi, wadda take nuna yana cikin damuwa.
Sedai ta gefe ɗaya yana ji a jikinsa, babu inda Auren ne zeje, dan baze taɓa iya zama da Nana a matsayin matarsa ba, wannan kudahumar 'yar ƙauyen mara kunya, ya san ba yadda za ai Mother ta yadda da Auren nan ba. Dan haka dole ne a raba shi.




Da safe da Abban Farhan ya zo, ya tarar Farhan ta tashi, har an taimaka mata tai wanka, sedai ta ƙi cin Abinci.

Abba ya kalleta yace "sannu Farhan, ya jiki"

Farhan tace "da sauƙi Alhamdilillah, Abba ina Umma?"

Abba yace "tana nan Lafiya, tace a gaishe ki"

Farhan tace "ba zata zo ta dubani ba?

"Kinga Farhan, mu bar wannan maganar, Anty Uwani da Hauzaifa suna nan tafe tazo ta zauna da ke, amma haryanzu likitan be gayamana meke damunki ba"

Farhan ta ɗan gyaɗa kai.

Abba yace "Farhan Hajiyar nan tana da kirki, duk wannan ɗawsiniyar babu ko kwabon mu a ciki, Allah ya biyata da Gidan Aljanna".

"Ameen" Farhan ta amsa.

Suna cikin Magana ne sega Abbas ya shigo, da flask ɗin Abinci a hannunsa, suka gaisa da Abba.

Farhan ta dinga kallonsa, tana tunanin a in da ta sanshi.

"Gawa taƙi rami, ba magana?" Abbas yai maganar yana kallon Farhan.

Babu Uniform a jikin Abbas, dan haka ba ta gane likita bane.

Ya kalli Abba yace "Baba babu wata damuwa, zaka iya tafiya gurin Aikin ka, zamuyi ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai, Hajiya tana nan tafe"

Abba yace "eh ƙanwata ma tana nan tafe anjima zata zo ta zauna da ita"

Abbas yace "babu laifi"

Ya Ajiye kular Abincin ya fita.

Abba be jima ba sosai ya tafi, saboda shima yana jin kunyar azo a samu shike jinyarta a matsayin ta na babbar 'yar sa.

Wata Nurse ce ta shigo, ta zubawa Farhan Abincin kular da Abbas ya zo da shi, ta takurata taci Amma ƙememe Farhan taƙi.

Ana cikin haka zega Abbas ya sake shigowa ɗakin da Farhan take.

Wannan karon da lap court ya shigo ɗakin nata, se a yanzu ta gano shine likitan, kuma taga kamanninsa da Hajiyar sa.

Nurse ɗin ta miƙe tsaye cikin girmamawa tace "sannu da zuwa doctor"

Yace "Yawwa ya patient ɗina?"

"Patient gata nan, anma taƙi cin Abinci"

Abbas yace "bakomai, jeki kawai"

Nurse ta Ajiye Abincin ta fita, ya zauna akan kujerar, ya ɗakko plate ɗin me ɗauke da faten wake ya sha Alayyahu da kifi, ya kalli Farhan yace "Hajiya ce ta bani tace in kawo miki kan ta zo, ki karɓa kici"

Ta girgiza kai tace "Na ƙoshi"

"Ki daure kici ko ba yawa saboda ki samu ƙwarin jikinki"

"Naƙoshi" ta faɗa a raunane.

"Hey, karɓi kici nace" ya faɗa cikin tsawa.

A gigice ta karɓa hannunta na rawa, ta fara kokawar cin Abincin, amma kunya take ji, saboda a iya gaban Sadik take iya cin Abinci.

Abbas yace "Sorry kin sa na miki tsawa, daure kici kinji"

A hankali ta fara cakalar Abincin, kamar ba ta so.

Abbas ya ɗan kalleta yace "Mhmm hira nake so muyi"

Haushi ne ya fara kama Farhan, dan mutumin nan ya takurata sosai.

"Zan tambayeki wani abu, ina son ki gayamin gaskiya kinji?"

Farhan ta jinjina masa Kai.

"Waye Sadik?".

Wata irin ƙwarewa Farhan tai, wadda ta haddasa sakin plate ɗin hannunta!


(Me ze faru idan aka jewa Mother da Nana a matsayin sirikarta? Wace irin rawa Abbas ze taka a rayuwar Farhan, Ya Sunusi ze kaya da sauran al'amura keep following my pen Ayshercool)


Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.





Abbas ya ƙurawa Farhan ido, ya miƙe yaje fridge ɗin dake ɗakin, ya ɗakko ruwan roba, ya miƙa mata.

Ta karɓa ta ɗan sha kaɗan ta ajiye, ya ɗakko flask ɗin Abincin nan, ya ajiye mata a gabanta yace "oya, ɗau spoon ki cigaba da ci"

Jikinta na rawa, saboda wani irin kwarjini da yai mata, haka ta dinga cakalar Abincin nan tana ci.

Gani yai idonta ya cika da hawaye, da alama dai kamar ya takura mata, ya kalleta yace "ajiye in kin ƙoshi"

Aikuwa kamar jira take, ta ajiye kwanon Abincin.

Ya sake kallonta yace "Oya, gayamin waye Sadik?"

Mamaki ne ya cikata, a ina ya san Sadik? Ya a kai ya san shi?.

"Mhmmm ke fa nake jira"

Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta, tana kokawar maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.

Yace "shikenan, tunda ba zaki gayamin ba, bari idan Abbanki ya zo na tambaye shi, ko in gaya masa Shi Sadik ɗin yana da Alaƙa da rashin lafiyar ki"

Cikin sauri ta ɗago kai, hawaye na bin fuskarta tace "A'a, dan Allah kar ka gaya masa"

"Meyasa kar in gaya masa?"

"Bakomai"

"Ban yadda bakomai ba, ki gayamin gaskiya ba wanda zan gayawa"

Tai ajiyar zuciya tace "ɗan makarantar mu ne" se kuma tai shiru.

Yace "ina jinki, se kuma akai yaya daga nan?"

Ta sunkuyar da kai taƙi magana.

"Ko dai yana takura miki ne a makarantar, yana miki abunda ba kya so?"

Tace "A'a"

"To gayamin, Why you don't want him to leave you?"

Ta ɗaga kai ta kalli Abbas, tana mamakin yadda akai yasan wannan abubuwan haka.

Yace "Anyway, tunda ba kya son maganarsa, Yaushe kika fara rashin lafiya?"

"I don't know" ta bashi amsa.

"As how? I mean Yaushe kika fara jin wasu alamu na rashin lafiya"

"Ba zan iya tunawa ba, kawai ina yawan jin faɗuwar gaba ne, bana kuma iya cin Abinci, and i thinks am having cancer"

Zaro ido yai yace "how do you know that? Ke kin san meye Cancer kuwa?"

Ta share hawayen fuskarta tace  'ban sani ba amma ina tunanin ina da tabbacin haka"

"Asibiti kika je aka gaya miki haka?" Yai maganar yana kallon ta.

Tace "No, ina gani a tv, ana faɗar symptoms ɗin, and am having some of the symptoms"

Yace "Well, a ina kike jin Symptoms ɗin? And wace irin Cancer kike tunani?"

Tai shiru ba tace komai ba, sema sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.

Yace "na gane, but for how long kika fara jin Symptoms ɗin?"

"Almost a year" ta faɗa cike da kunya.

"Karki kuma jawa kanki wannan masifar, is not a cancer, ba yadda zaki zauna da wannan ciwon tsawon shekara guda ba tare da kin fara shan magani ba, ace bata nuna ba, what You Are feeling is just a homonal activities, ki kanji ciwon a lokacin da kika kusa fara al'ada ko bayan kin gama da wasu 'yan kwanaki, is normal, Da kinyi Aure zaki dena ji, da zarar Sadik ɗin ya fito a kai Aure zaki nemi ciwon ki rasa, alamu sun nuna kina buƙatar Aure ne, da zarar kimyi Aure zaki dena ji, sedai maybe when you are pregnant in the first trimester zaki ji ciwon, ko makamancin haka"

Farhan ji tai kamar ƙasa ta tsage ta shige, saboda tsananin kunya, kuma hankali kwance yake mata bayani.

"Ko akwai wani abu da yake damunki deep down inside your heart bayan wannan?, a shekarun ki be kamata jininki ya hau Sosai ba"

Ta girgiza kai alamar bakomai.

Yace "Mhmm Yaushe Sadik ɗin ze zo dubaki ne?"

Jin tambayar da yai mata yasa Ta ɗauke kai daga kallonsa, tana hawaye.

A take ya fara gano matsalar Farhan, yace "he broke your heart ko?"

Tace "No"

Ya ɗan ƙura mata ido, tayi yarinta da Love Crises, she's very young, koma dai menene, akwai depression a tare da ita, Kuma da alaƙa me ƙarfi a tsakanin ta da Sadik.

Yace "ajin ki nawa yanzu?"

"Jss3" ta bashi amsa.

Ya ɗanyi shiru, gaba ɗaya ba ta fi Shekara goma sha huɗu zuwa sha biyar ba, amma tana ɗauke da damuwa,
Yace "Shikenan, bari in bari ki sake samun nutsuwa, ma cigaba da maganar, amma tabbas ina son jin a gayamin waye Sadik ɗin nan"

Ba tace masa komai ba har ya fita daga ɗakin.




Nana kam an haɗa mata akwatinta cif, dan har an kai akwatin mota, ta ƙanƙame Inna tana kuka tace "Inna meyasa zaku turani in da ban san kowa ba? Wallahi Inna bana son yaron nan, Inna ya akai kika dena sona, da kula dani kika yarda a tafi dani in da babu idonki a kaina? Haba Inna ta, da wa zan rayu babu ke a in da nake"

Ai duk yadda Inna take dakewa se kuka, tace "kiyi haƙuri Nana, Allah ya baku zaman lafiya, ki bi mijinki ki samu aljannar ki, na so in samu isashen lokaci tare da ke, amma baze yuwu ba, kiyi haƙuri kiyi karatu da kyau Allah yai miki Albarka, ki kula da tarbiyyar da muka ɗoraki a kai"

Nana tana turjewa tana kuka, aka kaita Mota, se kuka take kamar wadda aka gayawa ranar mutuwarta.

Hakimi ya ƙarewa Nana kallo yace "zanyi kewarki jikata, ko a 'ya'yan da na haifa, babu wanda nakewa son da nake miki, sedai ba yadda na iya".

Ya kalli Sadik yace "ga ta nan, Amana a hannunka, Nana Yarinya ce me tarbiyya, da muka raina nasan wa na aura maka, nasan na maka laifi, amma nan gaba zaka gane gata nai maka, ka kula da Amana, idan kaci Amana Allah yana kallonka, Abdullahi kar a bari inji wani abu mara daɗi game da Amanata, kuje Allah ya sauke ku lafiya"

Nana tana kuka, haka aka ja motar nan suka tafi, yayinda zuciyar Sadik kamar wutar ƙira, saboda wata irin wuta dake ruruwa a cikin zuciyarsa, jin Hakimi kawai yake, amma wannan Amanar kam ba abar karɓa bace a gurinsa.

Ganin kukan na Nana a ta da niyyar denawa yasa Abba yace "haba Nana, kukan ya isa haka, kar kanki yai ciwo kinji, ki dena kukan nan haka ya isa"

Faruk yace "hakane, ki dena kukan nan kar kanki yai kafin muje can gida" ya ƙarasa maganar tare da miƙa mata hankici, dan ta goge hawayenta.

Wani uban tsaki Sadik ya ja, dan ko motsin Nana baya ƙaunar ji, duk da yau ce kusan zece ranar 'yanci a gareshi, bayan takure shi da akai tsawon lokaci, aka hanashi walwala kamar wanda ya karya dokar ƙasa, sedai sam baya farinciki da hakan, dan da ya tuna yadda aka katse masa hanzari aka aura masa baƙauyiya, se yaji wani marurun takaici ya tokare masa zuciya.

Nana ba ta sake tsinkewa da al'amarin ba, se da suka shigo gari Sosai, wata fargaba ta lulluɓeta, dan bata san wace irin karɓa Mother za tai mata ba, dan tun ainihi dama Mother ba ƙaunarta take ba, balle yanzu da aka aurawa ɗanta 'yar ƙauye da ta ke ƙyama, kuma ɗan da take ganin be isa Aure ba.







Wajen ƙarfe tara da rabi, Hajiya ta zo Asibitin, tai murna sosai da ganin cigaban da aka samu akan jikin Farhan, dan ta farfaɗo sosai, sedai tayi rama sosai da sosai, ga leɓenta da ya bushe.

Hajiya tace "Sannu Farhan, ya jikin naki?"

Farhan tace "Jiki da sauƙi Alhamdilillah, Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi yasa kifi haka"

"Ameen, bakomai Farhan Allah ya ƙara miki lafiya, Ummanki tace a gaishe ki"

Shiru Farhan tai ta sunkuyar da kai, yanzu idan ma mutuwa tai shikenan, sedai ta mutu ba tare da Umman ta zo ta ga halin da take ciki ba.

Zuwan Hajiya babu daɗewa, sega Anty Uwani, wato babar Huzaifa ta zo.

Nan suka gaisa da Hajiya, ta kalli Farhan tace "Sannu Farhan, gaba ɗaya kin rame lokaci ɗaya, Allah yasa kaffara ne, ya ƙara afuwa".

Kasancewar Anty Uwani mace ce me faran faran, hakan ya sa suka saki jiki da juna ita da Hajiya suke ta hirar su.

Farhan tai farinciki sosai, jin Abbas ya gaya mata ba ta ɗauke da sanƙaran mama (Cancer), wanda ta daɗe a cikin matsananciyar damuwa, da kokwanton ciwon ne ya kamata.

Amma idan har dagaske doctor Abbas yake, da yace idan tai Aure zata dena jin Symptoms ɗin, sannan ta dena damuwa idan har dagaske yake Aure take so, meyasa ba ta farinciki da ɗokin Aurenta da Sunusi? Tabbas ba Aure take buƙata a yanzu ba soyayya da farinciki take buƙata, sedai gashi me samar mata da su ɗin yai nesa da ita, nisan da bata san a wani hali yake ba, balle soyayyarta.
Kenan ta rasa Sadik ne? Kokuwa haryanzu matsalar ƙauyene na rashin network ya hanashi nemanta?
Wata zuciyar tace "ko dai gidansu zanje in tambaya in ji?'

Da sauri ta kauda wannan tunanin, ita a wa, za taje gidan su ta tambayi in da yake?

To ko dai abokansa zata tambaya, su Amin?.

"Ke Farhan, tunanin me kike hakane?"

Firgigit Farhan ta dawo hayyacinta, ta kalli in da Anty Uwani take mata Magana.

Hajiya tace "tunanin me kike haka, ki kai shiru ba ma kya jin abunda ake faɗa?"

Farhan tace "bakomai"

"A'a da Komai, akwai abunda yake damunki da alama, wanda ya haddasa miki wannan ciwon naki"

Farhan tace "bakomai fa"

"A'a, to ma naji bakomai amma tunanin me kike haka?"

Tai shiru ba tace Komai ba, nan dai dau kai tai mata faɗa akan koma meke damunta, ta cire shi a ranta, ko dan lafiyarta.

Ita dai jinsu kawai take, amma ba ta ji zata iya hakan ba.




Nana na ganin sun shiga layinsu Sadik, ta sake fashewa da kuka, dan ta tabbata shikenan ita da Ƙauyen da ta tashi, nan ta fara saƙawa da warwara akan irin karɓar da zata samu a gidan su Sadik ɗin.

Tana cikin tunanin ne taji an tsaya, Faruk ne ya fito ya buɗe murfin motar, da yake tana baya ita da Abba.

Tuni Sadik ya fita daga motar yai cikin gida, ba tare da ya jira kowa ba.

Faruk ya ɗakko Akwatin Farhan, suna gaba, tana binsu a baya tana share hawaye.

A falo Sadik ya tarar da Mother, ta ƙarasa da sauri ta rungume Sadik, hadda hawayen farinciki, tace "I miss You my son"

Magana Sadik yake son yi, amma ya kasa se murmushi me haɗe da ƙunar zuciya da yake yi.

Ta ɗago ta kalli Sadik tace "Kai sannu Sadik, duk kayi wani iri Allah sa ba rashin lafiya kai ba, naga idonka duk kai zur zuru"

Sadik kawai ya sunkuyar da kai, wata ƙwallar baƙin ciki ta taru a idon sa.

"Sadik meyafaru ne? Ka gayamin mana"

Tana ɗaga kai sega Abba ya shigo, shida Faruk, taga Faruk da ƙatuwar Akwati, ba ta kai ga yin Magana ba sega Nana ta shigo, tana duƙar da kai kamar munafuka.

Wani kallon banza Mother tai mata sannan ta kalli Abba tace "Sannu da zuwa"

Abba yace "Yawwa"

Sadik na ganin Nana, ya saki Mother ya juya ya nufi ɗakinsa da ke Falon Ya shiga ya rufe ƙofa.

Abba ya kalli Nana da ta ke tsaye a bayan kujera tana rarraba ido yace "ya haka, ke da gidanku ƙaraso ki zauna mana"

A ƙasa Nana ta zauna, tana share hawaye.

"Abba ban gane meke faruwa ba, naga Sadik duk yai wani iri"

Abba yace "An gutsuri wani abu a jikinsa ne?"

Tace "A'a"
"To me kike son ji, ba dai gashi nan an dawo da shi ba, ba su cinye shi ba ai"

Tace "Allah ya baka haƙuri"

Abba yace "Nana, ɗau Akwatin kije ɗakin da kuka sauka lokacin bikin dr., In ba a gyare yake ba, kiyi magana a gyara miki"

Nana ta ɗau Akwatinta tai gaba, ita ta manta ma ko Mother ba ta gaisar ba, saboda tsabar tsoro da fargabar karɓar da za tai mata.

Faruk kuwa tuni ya fice, dan baya son ganin dambarwar rikicin da za'ai s Gidan, dan ya san ba ƙaramar rigima za'ai ba a gidan.

Ɗakin Sadik Mother ta fara zuwa, ta tarar da shi a kwance akan gadonsa, ya ƙurawa roofing ɗakin ido.

Mother tace "Wai kai meke faruwa ne?"

Sadik ya girgiza kai yace "bakomai"

"Kamar ya bakomai, nagan ku duk wani iri, kuma me wannan yarinyar ta zo Gidan za tayi?"

"Mother, I don't have answer for all this your questions, allow me to rest please"

Mamaki ne ya cika Mother, musamman ganin hawaye na zubowa daga idon Sadik.

"Sadik, meyafaru haka kake kuka?"

Sadik baya son cigaba da Magana, dan haka ya miƙe ya shige toilet ya rufe ƙofa.

Se kuma tai tunanin ko dan harya gama zamansa a garin ba taje ta ganshi bane, shine yake fushi?.

Ƙofar toilet ɗin taje ta tsaya tace "kayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login