Showing 153001 words to 156000 words out of 259198 words
Chapter 52 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
yai yace "ai sekin fi missing Sadik, shine abokin shirirtarki"
"Ai na saba da rashinsa a gidan nan yanzu, amma gaskiya sena fi missing ɗin ka"
Faruk yace "ba wani, faɗi gaskiya ni a wa zaki missing ɗi na?"
"Kai a big Lovely brother na"
Murmushi ya kuma yi me ƙayatarwa yace "wannan yabo haka? Ko dai wani abun kike buƙata ne?"
"Shikenan ba zan yabe ka se ina buƙatar wani abu?"
"Hmm, to ai shikenan godiya nake Lil Sisy"
"Kai ba za kai missing ɗina ba?"
"Mmm to, gani nan dai ban sani ba ko zanyi ko ba zan ba"
Ɗan shiru tai ta zuba masa ido tana kallonsa.
Miƙewa yai ya na murmushi yace "don't mind dear, i will so much Miss you"
Yai Maganar tare da ficewa daga falon yana murmushi, tabi bayansa da kallo.
Ji take tamkar ta sanar da Faruk cewa son shi take, amma ba ta san ta in da Yakamata ta fara ba, gashi yana ta shirin tafiya, ta rasa yadda zata ɓullowa lamarin.
Kusan duk bayan sati biyu Steve yake zuwar wa Nana visiting, ya kawo mata provision saboda Ba Komai na Abinci ake bata ba, ba a bata abunda ya wuce tea, fruit ko chips se bredi, saboda suna amfani da Naman alade, ita Nana ba ta san dalili ba, ba ta damuwa da yadda ake bambanta su gurin Abinci, da safe ta sha tea da ƙwai ko dankali, ga kayan siyayyar tarkacen madara da kayan ciye ciye da Steve yake kawo mata yace inji Abba.
Nana tana karatu sosai, duk da idan rigimar ta ta motsa zata zauna tai ta kuka, babu wanda yake takura mata komai gashi nan a wadace ba takura, amma ita hankalinta ya na kan gida Nigeria, dan tafi sakewa a nan.
Tayi ƙalau da ita kamar ba ita ba, fatarta tayi fresh saboda zama guri ɗaya, shi kansa Steve yai mamakin ganin yadda Nana ta ƙara kyau a cikin ƙanƙanin lokaci, gashi har harshen ta ya fara sauyawa, babban abunda yai masa daɗi yadda malaman suka yabeta academically and morally.
Ya kira Abba ya gaya masa cigaban da aka samu game da karatun Nana, Sannan ya bata Wayar.
"Abba ina wuni"
Abba yace "A'a turancin dai za'ai min, ya Makaranta Nana"
"Lafiya ƙalau Abba, ya su Faruk da Mother da su Anty Jidda"
"Duk suna nan lafiya, ai last week naje gidan, Inna na ta gaishe ki"
Nan da nan ƙwalla ta taru a idon Nana tace "ya jikin Alhaji?"
"Ahh jikinsa yai kyau sosai Alhamdilillah, kun kusa hutun session ko?"
"Eh mun kusa, ai zan dawo ko?"
"No, kuyi zamanku ku cigaba da karatu, zamu zo ai, zamu shigo muku visting insha Allah, ga kilishinki kayan guda Hakimi ya bani, zan zo miki da shi"
Nana tace "to Abba nagode, in kunyi waya kace ina gaishe su, nayi missing ɗin su sosai"
"Bakomai kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki kinji, kiyi karatunki da kyau, Steve ai yana kawo miki kayan buƙatunki ko?"
"Eh yana kawo min, duk sati biyu se ya zo"
"To Alhamdilillah, ya ɓangaren addinin ki, ba wata matsala da kike fuskanta ko?"
"Ba wata matsala, ina addini na ba ruwansu da ni"
"To Alhamdilillah, ki kwantar da hankalinki kiyi karatunki, wataran se labari"
"To Abba, Nagode sosai a gaida su Mother"
"Zata ji insha Allah, Faruk ma ya kusa tafiya matsers ɗin sa, gidan ze zama se mu kaɗai"
"Allah sarki Yaya Faruk, ace ina gaishe shi Allah ya bada sa'a"
"Ameen ya hayyu ya ƙayyum, se anjima"
Sukayi Sallama, Mother da ta shigo tun ɗazu ta kalleshi tace "wao da wa kake waya haka ne? Se murmushi ka ke?"
"Ni da Nana ne, naji daɗin yadda ake yabonta tana ƙoƙari Sosai a makarantar, na jinjinawa ƙoƙarin ta sosai da sosai, a 'yan watannin nan ace tana capturing abunda suke gaskiya tayi ƙoƙari"
Taɓa baki Mother tai, tai masa shiru ta cigaba da abunds take, dan ko sunan Nana ba ta son ji.
Sadik ya zama famous a Makarantar su, yana da abokai da ƙawaye kala kala, gashi yai suna a team ɗin su na ƙwallon ƙafa na makaranta, ga competition da suke na gyming, gaba ɗaya ya canza kamar baƙin bature, ya tara uban gashi kullum cikin kashewa gashin nan kuɗi yake.
Amin har baya son ya haɗu da Farhan, dan da sun haɗu take expecting samun wani information daga gare shi akan Sadik, yaje gidan su Sadik sau biyu amma tun a gate ake sanar da shi baya nan, kuma baam wanda ya taɓa gaya masa ga in da ya tafi.
Duk da Farhan ɗin ba tambayar sa take in da Sadik yake ba, amma ya san yai mata alƙawarin ze bincika mata in da Sadik ɗin yake.
Yau ma a Library suka haɗu, duk da ba karatu ne ya kaita Library ɗin ba, taje ne dan ta keɓe kanta daga mutane, ta zauna a in da suka saba zama ita da Sadik tayi tunaninsa sosai ba tare da wani ya takura mata ba.
Amin ya zauna a kujerar gaban Farhan yace "sannu ina fatan ban takura miki ba"
Tace "A'a bakomai"
Yace "Na san na miki alƙawari, akan bincika miki in da Sadik yake, wallahi zuwa na biyu gidan su, amma tun a gate ake cemin baya nan, naga an canza musu megadi da wancan ne mun saba sosai ze bari in shiga ciki ko lambarsa in samo, amma wannan bama ya bari a shiga gidan nasu, amma dai ba zan gaji ba zan cigaba da bincikawar"
Farhan tace "bakomai kar ka damu, hakan ma Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"
Yace "bakomai karki damu, ki kwantar da hankalinki nasan duk in da yake shima kina nan a ransa, kuma ze dawo gare ki"
"To shikenan, Allah ya sa"
Yace "insha Allah"
Tana Library, har aka tashi daga Makaranta ta tashi ta tafi gida, taje ta tarar Umma ta dawo daga kasuwa, ta yo siyayyar kayan Kitchen, ga Adda Maryam ta zo suna ta dudduba kayan da Umma ta siyo.
Adda Maryam na ganin Farhan ta fara rangaɗa guɗa, wai ga Amaryar su.
Murmushin yaƙen ma kasa ƙaƙalo shi tai balle taiwa Adda Maryam, kawai ta shige ɗakinta ba tare da ko gaishe ta tayi ba.
Shirye shiryen su kawai suke na biki, yayin da hakan ke baƙantawa Farhan ɗin rai, babu wani karsashi ko ɗoki na amare a tare da ita.
Duk da adda Maryam ta san Farhan ba ta da magana, amma tayi mamakin yadda Farhan taƙi kulata sam, duk rashin son maganar Farhan tana hira da Adda Maryam, ko ita ko Adda Hafsatu, amma wannan karon Farhan taƙi kulata.
Farhan haushin Adda Maryam take ji, dan tana ɗaya daga cikin wanda suka taka muhimmiyar rawa, akan lallai se an aurar da ita, suka dinga bugo waya suna cewa lallai ai mata Aure, sekace ance musu lalacewa tayi.
Bayan magariba Farhan na kwance a ɗakinta, yau ba Islamiyya, sedai wata irin kewar Sadik tana damunta, ga wani irin feelings from no where da ya dameta, wanda hakan kan faru a duk lokacin da ta kusa yin period.
Juyi kawai take akan katifar ta, wasu hawaye masu ɗumi suna bin gefen idonta, Babu abunda take buri banda ta ji ta a jikin Sadik, haka kurum take jin kamar ƙamshin turarensa take ji.
"Yasalam kar in haukace" ta furta lokacin da wasu hawayen ke zuba daga idonta Kamar an kunna famfo, ko ba komai zubar hawayen ma samun sassauci ne a gareta.
Adda Maryam ta ɗaga labulen ɗakin Farhan tace "ke 'yar Fulani ban san me nai miki ba kin ƙi kulani, ko duk kunyar ce? Kije ana Magana da ke a waje, ina ga ko angon namu ne?"
Farhan tace "to zanje"
"Naji Muryar ki a shaƙe, ko baki da lafiya ne?"
"A'a" ta bata amsa a taƙaice.
Bayan fitar Adda Maryam, Farhan ta zura hijjabin ta da niyyar tana zuwa, ta huce abunda ke damunta akan Sunusi, sedai tun daga soro ta fara jin ƙamshin turare, tana zuwa ta ga Abbas maimakon Sunusi.
Ya kalleta yai murmushi yace "muje Hajiya ke neman ki dama"
Tace "to bari in faɗa a gida"
Ta koma gida ta sanar da Umma, sannan ta fito suka jera da Abbas zuwa gidan Hajiya, ba tare da wani ya furta komai ba.
A kai sa'a akan idon Sunusi suka nufi Gidan Hajiyar sa.
Farhan ta zauna a falon Hajiya, Abbas ma ya nemi guri ya zauna ya kalli Farhan yace "ba Hajiya ce ke kiranki ba, dama ni nake neman ki"
Ta ɗago ta kalleshi ta sunkuyar da kanta.
"Bana son mu tsaya a ƙofar Gidan ku ne, wannan shashashan, sorry in dena zaginsa shi zaki aura, bana son yazo ya samu gaba da masifa shiyasa na janyo ki nan"
"Amma ina Hajiyar?"
Yai murmushi yace "Hajiya tana nan, tana ɗakinta tana salla, na gaya mata zanje in taho da ke muyi Sallama, je ki duba ɗakinta in baki yadda tana nan ba"
Ta girgiza kai tace "na yadda"
Ya gyara zama yace "gobe in Allah ya kaimu zan tafi, tafiyar tawa ce nayi ba nayi ba, se yau Allah ya nufa gobe in Allah ya kaimu zan tafi, na zo in sake ganinki ne, sedai haryanzu ba wani cigaba se ramewa kike kuma yi"
Farhan tai shiru ba tace komai ba.
"Farhan, kowane bawa da kika gani a rayuwarsa, da irin ta sa ƙaddarar kiyi haƙuri ki karɓi taki, tun ranar da na fara ganinki zuwa haɗuwar mu ta ƙarshe, da naga wanda zaki aura, naji ina matuƙar tausayinki, kina cikin hatsari Sosai da sosai sedai dan Allah duk abunda ze faru, You have to maintain your diginity, kar kije garin nemawa kanki mafita ki faɗa wata hanyar daban kiyi haƙuri"
Farhan bata gama gane inda maganganun Abbas suka nufa ba, ita dai tana jinsa ne kawai.
Tana cikin nazarin maganganun sa taji ya riƙo hannunta cikin hanzari ta kalleshi, a hankali tai ƙoƙarin zame hannunta amma taji ya riƙe gam.
Wata irin fargaba ta shige ta, ya kai hannunsa ze cire zoben hannunta, wanda Sadik ne ya bata a lokacin birthday ɗin ta.
Da hanzari ta miƙe tace "ka sakarmin hannu tafiya zanyi"
"Nima ba wani abun zan miki ba, ba mutumin banza bane ni, mahaifiyata tana nan, ya za'ai in yi wani mummunan kuskure, nima ina da 'ya'ya, na san irreplaceable Sadik ne ya baki wannan zoben, so I want substitute him from your life".
"Dan Allah ka bari" ta faɗa a raunane.
"Ba kya son ki manta da shi ko? Bayan shi ya manta da ke?"
"Be manta dani ba"
"Meyasa zuciyar ki ba ta son Gaskiya ne? Farhan?"
Shiru tai tana goge hawaye da hannu ɗaya.
"Shikenan muje in rakaki gida, nasan kan in dawo daga karatu kinyi Aure, ina fatan Allah ya baku zaman lafiya, ina kuma yi miki nasiha akan kiyi haƙuri na bawa Hajiya gift ɗina na Aurenki ta baki, kiyi haƙuri kinji?"
Ta jinjina kai alamar to.
Seda suka fito tsakar gida, sega Hajiya ta fito daga ɗakin ta tace "Farhan, seda yaje ya tattago ki ko? Wa shi me 'ya, salla nake ne, nace in so yake sedai ya haƙura kin zama rabon wani, amma na kasa gane inda ya dosa, wai ai ke 'yarsa ce"
Abbas yace "Hajiya kenan, bari in rakata gida"
"To shikenan, ki gaida Ummanki"
Farhan tace "to zan gayamata insha Allah seda safe"
Suna fitowa daga gate ɗin gidan su Abbas, suka ga Sunusi da wasu abokansa a ƙofar Gidan yace "kun gani ko? Yanzu kun yadda da abunda na gaya maku? Sun kusa awa guda cikin gidan nan, daga ita se shi ba kowa a gidan, yanzu da nai magana ace sharri nake mata.
Haladu ne yace "haba Sunusi, ya za ka dinga zargin matar da zaka aura? Baka da tabbas fa akan maganar da kake"
"Kamar ya bani da tabbas? A gaban idona fa ta fito daga gida, suka shiga gidan nan tare, saboda sheda shiyasa na kiraku"
Abbas ya kalli Farhan yace "muje"
Hawaye wani na bin wani ta cewa Abbas "kalli irin mutumin da zan aura? Kullum ƙoƙari yake yabi diddigi na ya wulaƙanta ni, Hajiya fa tana cikin gidan nan amma kalli abunda ya tara mutane yake faɗa"
Abbas ne kaɗai yake iya jin me take faɗa.
Yace "bakomai, ki barwa Allah, muje kawai"
Har ƙofar gida ya raka Farhan, yayin da Sunusi ke ta zazzaga bala'i.
Farhan na shiga gida, gurin Abba ta shiga tana kuka, hankali a tashe yace "Lafiya kukan me kike haka?"
"Abba Sunusi ne"
"Me Sunusin yai miki?"
Nan ta kwashe Abinda ya faru ta gaya masa, Abune mawuyaci Farhan ta kai ƙara tace gashi an mata laifi, ko lokacin yarinta sosai, ba ta zuwa ta kawo ƙara duk girman laifin da akai mata ko cutarwa kuwa.
Shi kansa Abba yaji babu daɗi abun da Sunusin yai, dan haka yace "ki dena kuka, tashi ki tafi ɗakinki zan masa Magana"
Farhan ta tashi ta fita tana kuka.
Aikuwa tana shiga ɗaki aka turo ana sallama da Abba, Abba ya miƙe ya fita yana zuwa ya tarar da Malam Labaran da kuma Sunusi.
Abba suka gaisa da su, Sannan Malam Labaran yace "to ina zaune Sunusi ya zo min da wata Magana akan matarsa, to nace ban sani ba ko kana da masaniya a kai"
Abba yace "Malam Labaran, girma da mutuncinka na gani ya sa zan bawa Sunusi yarinyar nan, da kuma nustuwar sa da addininsa da yadda yake girmama mutane, daga fara neman Auren nan zuwa yanzu ba zan iya faɗar adadin sau nawa ya kawo min ƙarar ta ba, shi fa lamarin Aure ɗan haƙuri ne, yarinyar nan baka Aureta ba tukuna dole wataran samari zasu biyo ta tun da yanzu take kan ganiyar ƙuruciya yanzu take girma, idan ka kawo min ƙararta ina ɗaukar mataki bata taɓa nuna damuwarta akan haka ba, ba fa dan bana sonta nake mata haka ba, yau da bakinta ta kawomin ƙarar ka akan abinda kai mata, ka tara mutane a waje kace wai ta keɓe da namiji a cikin gida, ƙaddara ma hakane ai kai me rufa mata Asiri ne,balle seda ta shigo ta faɗa a cikin gida, Hajiya ta turo ɗanta wane tace taje tana nemanta, ba'a Aure da zargi fa in ka san kana zarginta to a haƙura da lamarin nan kawai"
Da sauri Malam Labaran yace "A'a ba za ai haka ba, dan Allah ayi haƙuri insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, kai kuma Sunusi kar ka sake haka, zaka ɓata mata suna a unguwa, ba a haka baka kyauta ba"
Cikin ikon Allah suna cikin maganar sega Hajiya da Abbas, ta ƙara so suka gaisa da su Abba Sannan ta kalli Abba tace "Malam Ali banji daɗin abunda ya faru yanzu ba, Ina cikin gidan da izini na Abbas ya kira Farhan, ba zan taɓa bari ayi ɓarna a gaban idona ba, saboda nima ina da baya, Abbas shine likitan da ya duba Farhan, ze tafiya ƙaro karatu, yace min yana son suyi sallama, ya kuma bata abunda ze bata ance za tai Aure, amma an tara min jama'a a ƙofar gida wai ɗana ya keɓe da 'yar wajenka a cikin gida ne, wanda maganar ba haka take ba"
Abba yace "dan Allah kiyi haƙuri, kinga yanzu haka zancen da muke kenan"
Nan suka taru suka ƙarewa Sunusi ta tas, suka nuna masa ba a haka.
Abbas yace "wallahi ba dan Hajiya ta sa baki ba, se nayi karar Yaron nan hukuma tabi min haƙƙina na yunƙurin ɓatamin suna da yai"
Sukai ta bawa Abbas haƙuri sanann suka bar gurin.
Sunusi be taɓa zaton Abba ze iya iƙrarin hana shi Farhan ba, yaji Abba ya fara cewa ai yanzu take girma dole samari su biyota, dan haka ya fara tunanin abunda ze yi wanda ze hana faruwar hakan.
Maganar Kamar wutar daji, a daren Magana ta fara bazuwa wai an kama Farhan da Abbas a gidan su, alhalin da kuɗin Auren wani a kanta.
Baiwar Allah sam Farhan ba ta san meke faruwa ba, ita abunda ya dameta kadai take tunanin mafita a kai.
Amin yana kwance yana duba waya, ya shiga IG yai posting hotunan sa na friday, daga nan ya cigaba da kallon hotuna.
Yana shirin ya rufe datar yai karatu, kasancewar jarrabawar WAEC na ƙaratowa, kawai yaci karo da hoton Sadik a gym tare da turawa wata baturiya ta ɗora tare da caption of "ma hottest mate dude"
Da sauri ya tashi zaune, ya cigaba da duba hotunan tabbas Sadik ne, kuma wannan hotunan na kwanan nan ne, kenan Sadik ya tafi karatu ba tare da yayi wa kowa sallama ba, kuma ya kashe wayoyin sa gaba ɗaya, to meyasa yai haka sekace wanda ba shi da gaskiya.
Da sauri yai screenshots ɗin hotunan, ya tura group ɗin su na whats app na 'yan ajin su, nan da nan suka fara Sharhi wasu suka ce suka sun gani.
Sunyi mamakin yadda Sadik yai tafiya haka ba labari.
Washegari a school, su Nas da sauran 'yan ajinsu ma, haka suka ci-gaba da tattauna batun tafiyar Sadik ba labari.
Har ajinsu Farhan Amin yaje, ya tarar da ita tai shiru ta zubawa 'yan ajinsu ido, suna ta hirarsu, suna sha'aninsu banda ita da se kallonsu kawai da take.
"Sannu dai" Amin ya faɗa yana zama.
Farhan ta kalleshi tace "yawa sannu"
Amin yace "na zo da labari ne, wanda ban san ya zaki ɗauki abun ba, amma koma dai ya ne ki ɗauki lamarin da sauƙi. Jiya na ci karo da hotunan Sadik a Instagram, da alama ya tafi karatu ne, dan a cikin turawa naga hotunan nasa, hakan na nufin ya tafi karatu ne"
Farhan tai murmushi tace "shikenan, tunda yana lafiya Alhamdilillah, Nagode sosai"
Amin ya dinga binta da ido, dan ganin reaction ɗin ta amma ya kasa gano halin da take ciki.
Gaba ɗaya zuciyar Farhan ta bushe, meyasa Sadik ze tafi ba tare da ya sanar da ita ba?.
Ta rasa tunanin meyakamata tayi, kuka ko farinciki? Sadik yana nan lafiya, amma har ya tafi karatu ƙasar waje be nemeta ba, what does that mean? The relationship is over, he don't want her anymore, he dumps her aside? So Abbas gaskiya yake gayamata kenan, Sadik ya barta kenan?! Ya ilahi.
Idanunta su kai jawur, does she deserves this from him? Tana zamanta lafiya, ya koyar da ita son shi, kuma ya tafi ya barta ba tare da tunanin wani hali zata shiga ba.
'No, he can't do this to me? Sadik yana sona, akwai dalilin da yasa ya tafi be neme ni ba, shikenan Aurena da Sunusi ze tabatta, Ashe doctor gaskiya yake gaya min? Gaba ɗaya ta rasa tunanin meya kamata tayi.
Seda ta ɗaga kai taga ba kowa a ajin, sanann ta gane an tashi kowa ya