Showing 192001 words to 195000 words out of 259198 words
Chapter 65 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
mata fyaɗe tana maye, wannan wane irin bala'i ne, gurin wa za ta kai ƙara bayan ita ta kai kanta?.
"Duk kai ka janyo min Sadik, tarayya ta da kai ba ta amfana min Komai ba se zunzurutun bala'i, ka sanya ciwo a zuciyata, da fari nayi zaton Alkhairi ne shigowar ka rayuwata, amma yanzu na tabattar da kai ƙaddara ne, insha Allah daga rana me kamar irin ta yau zan shafe ka a tarihin rayuwata, ko a lahira bana fatan sake yin ido biyu da kai, na tsaneka Sadik, na tsane ka Tsana me tsananin gaske.
Zan shiga bariki in tara kuɗin da zan kawo ƙarshen Iskanci da tsageranci na Mubarak babba da tawagar sa.
Ba ni ba Aure, sedai se na rama yaudarar da Sadik da yai min akan sauran maza!.
Da irin wannan maganganun ta nufi hanyar fita daga Hotel ɗin, zuciyarta kamar ta tarwatse.
Nana ta gama fushin ta ta sakko, dan ba za ta iya dogon fushi da Sadik ba, dan ta fuskanci idan ta biye masa, haukata ta zeyi, dan ba shi da aiki se tsokanar ta, da takura mata be kuma gigin cewa ze mata wani abu ba, hakan ya sa ta ɗan sakko daga fushin da take, amma haryanzu idan ya so ganin ɓacin ranta, se ya kwanta a jikinta, nan za tai ta mita tana cewa wallahi ba ze sake lalata ba.
Yau sun gama cin Abincin dare, Nana tace "Friend nifa gaskiya Islamiyya nake son shiga, dan Allah ka sani a Islamiyya mana"
Sadik yace "ke kinga wata Islamiyya a nan ne, to ni makarantar addinin Musulunci ɗaya na sani a garin nan, kuma tana da nisa sosai daga nan gidan, sedai in biya miki ta online ki dinga yi a system ɗina"
Tace "yawwa, amma fa nagode Sosai, Allah ya saka da Alkhairi Autan Mother" yai murmushi kawai ba tare da yace mata Komai ba.
Tana nam zaune ya ɗakko System ɗin sa, yai mata registration na Online islamic classes, hatta kuɗin da ake buƙata ya biya mata, nan Nana ta dinga murna tana masa godiya, tare da yi masa Addu'oi kala kala.
**********
"Khairat, wai meke damunki ne? Kullum kina ɗaki kamar me jego"
Khairat ta ɗan ɓata fuska tace "ba Komai fa"
"A'a ban yadda bakomai ba, ke kenan kullum a ɗaki, Mother ta kirani a waya ba a dadi, akan kije amma kin ƙi, kwata kwata kin ɗauke ƙafarki daga gidansu"
Ta tura baki gaba tace "to ni Mummy me zanje Gidan in yi?"
"Kamar ya me zaki je ki yi, da me ki ke zuwa yi?"
"Mummy gidan fa ba kowa, daga ni se ita da 'yan aiki, gidan is boring wallahi"
"To amma duk da haka, zaman ki a gidan ma ɗebe mata kewa, kinga ita kaɗai ce a gidan"
Khairat tace "hmm Allah sarki, gidan b kowa yanzu, Sadik yana can, ni shi nake son in ga yadda ya zam, gashi tun da ya tafi ko a waya, be taɓa kirana ba, Mother tace min ya canza layin da yake amfani da shi a can, na karɓi sabuwar lambar ta sa amma ba ta shiga, tace min lokuta da dama idan ba shi ya kiraka ba, wayarsa ba ta shiga"
Mummy tace "hakane, amma mahaifinsa ne ya sama sa takunkumi, ya ƙayyade masa iya wanda ze dinga kira da layin, an saita layin na sa da iya lambobin da ake so ya dinga ta'amalli da su, haka HAUWA tace min"
"Taɓ, gaskiya an matsan ta masa da yawa, gashi an haɗa shi da 'yar ƙaiye haka ze ta fama"
Mummy tace "yawwa, ni se da ki kai wannan maganar ma, sannan na tuna da batun Yaron nan Abdul, ɗan Gidan Hajiya Azumi, dan ubanki Khairat meye aibun yaron nan da yace yana sonki? Kike wa ɗan mutane wulaƙanci lafiyar ki ƙalau kuwa?"
"Haba Mummy ni fa Yarinya ce, kalleni 'yar Yarinya da ni kawai kuma se in fara wata Soyayya?"
"To meye a ciki, so kike se kin tsofe tukuna, abunda wasu ke rububin nema ido rufe, shi fa Dagaske yake Aurenki yake son yi"
Khairat tace "Wallahi Mummy baƙi ne"
"To baƙin a wuyanki zaki rataya shi? Ina ruwanki da baƙinsa, dan kina fara akace dole se kin Auri fari?"
"Mummy wallhi shi na sa baƙin yai yawa, bana son shi ne ma wallahi"
"Haba Khairat, ina wani baƙi a nan gurin, yaro da sana'arsa da rufin Asirinsa da komai, ai ba kala ake dubawa ba, in da za'a samu kwanciyar hankali"
Ji tai kamar ta gaywa Mummy, ita fa Faruk take so, amma se ta kasa, tai shiru tana sauraran Mummy da ke tai mata nasiha akan Abdul, nasihar da ke shiga ta hagu ta fita ta dama, dan sam ba taji wata alama na za ta iya son Abdul ba, dan ita Faruk kawai take so.
Nana ƙarfe takwas na dare, ake fara musu karatun Islamiyya na online, mutum ze iya ajiyewa ya saurari lecture idan an gama in ba shi da lokaci, amma ita Nana tafi son ƙarfe takwas ɗin nan ya zamana anyi karatu da ita.
Idan Sadik yana nan, yana kusa da ita yana kallon yadda take tattara nutsuwarta akan abunda ake koyawa, da littafin ta da bironta, amma shi ba ruwansa, yana gefen ta yana aikin game a waya, ko a talabijin.
Sam harkar Addini ba ta wani damu Sadik ba, iya wuya da shagala ba ya wasa da salla, wannan ze yi ta akan lokaci amma ba lallai yaje masallaci, se dai yayi a gida, dama batun wani tasbihi da Addu'a ba yi yake ba, da ya idar da salla yake shafawa ya tashi.
Nana tana lura da shi, sedai ba ta son tayi Magana, yai fushi su hau faɗa, dan haka bayan ta kammala karatun Ranar ta kalleshi tace "Friend, kayi sallar isha'i ne?"
Yace "No, yanzu dai zan yi"
Tace "ok, to bari im yi Alwala seka jamu sallar, yau a nasihar ƙarshe da Sheikh yake mana kullum, yai jan hankali akan sallar jam'i, ka ga gara mu dinga yi tare muna samun lada da yawa ko?"
Yai murmushi yace hakane.
Taje tai alwala, ta saka hijjabi ta bi bayan Sadik.
Normal ya ja su salla, suka idar ta ga ya yunƙura ze miƙe tace "A'a, Friend na ga ba kai tasbihi ba"
"Wane tasbihin?" Ya tambaye ta.
Tace "Subhanallah, Alhamdilillah, Allahu Akbar, da akeyi ƙafa talatin da uku, da sauran Addu'a"
Sadik yace "Ai ba farilla ba ne"
"Amma ai Sunna ce me ƙarfi, ya zaka ji idan na baka dafaffiyar shinkafa ziryan babu mahaɗi, Astagfirullah kar in yi saɓo, baka san ladanka yai yawa sosai? Idan fa mutum yai ibada ba shi da tabbacin an karɓa, dole se mutum yana haɗawa da Addu'oi.
Gashi kai da kake shirin zama salamburuti, na 'yan ƙwallo ai dole mu dinga Addu'a Allah ya ɗaukaka ka, da kuma Allah ya tsare ka"
Komawa yai ya zauna, ya shiga yin tasbihi, wanda rabonsa da yayi bar ya manta.
Duk da ƙuruciya da shirirta irin ta Nana, amma a haka ta hilaci Sadik, yai tasbihin sa gaba ɗaya, da Addu'oin da ake bayan idar da salla, da azkar ɗin maraice"
Tace "yau za kai bacci me daɗin gaske, saboda kai Addu'oin nan, zakaji kamar ba ka da damuwa, ba ka ji ana Addu'a takobin mumuni ba?"
"Hakane, Thank you for the reminder"
Tai masa murmushi daga nan, sukai sallama kowa ya nufi makwancin sa.
Farhan kam, shaye shaye da ta fara ya sa ta dena jin shakkar kowa, sedai ba ruwanta da mutane, duk wani wanda ta saba gaisawa ta dena, kullum tana ɗaki.
Ita kanta ba ta jin daɗin shaye shaye da take yi, ko tayi yunƙurin denawa ta taji Soyayyar Sadik na ƙoƙarin dawo mata, se ta nemi abun da za ta sha ta manta Komai.
Abba ya zubawa sarautar Allah ido, banda Addu'a ba abunda yake yi, yayin da abun duniya ya ishi Umma, ta rasa in da za ta saka kanta, duk da halin da Farhan ke ciki, ko da wasa Umma ba tai tunanin jan ta a jiki ba, sema ƙyama da ta shiga nunawa Farhan ɗin, ta hana ƙannen Farhan ma shiga sabgar Farhan ɗin.
Yau juma'a, bayan an sakko daga Masallaci, Huzaifa ya zarce gidan su Farhan dan kai musu ziyara, ya kwana biyu be je gidan ba, saboda yanayin makaranta da yake zuwa.
Ya tarar da Umma, ya zauna suka dinga hira, can yace "Umma wai ina Yaya ne?"
Umma ta kwaɓe baki tace "ba ka san sabuwar rayuwar da ta zaɓawa kanta ba, rayuwar bin duniya, tana ɗaki tana aikin shaye shaye"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Umma wane irin shaye shaye kuma?"
"Shaye shaye dai da ka sani, ai rabonka da Gidan nan ka daɗe, tun ranar ɗaurin Aurenta ba ka sake zuwa ba, a ranar ma shaye shaye tai, tayi mankasa abunta, yanzu kwana a gida ma se ta ga dama, nayi nayi Abbanku ya ɗau mataki a kanta, amma ya ƙi ya zuba mata ido, wai muyi mata Addu'a, addu'a ba tare da ɗaukar mataki ba"
Jikin Huzaifa yai sanyi ƙalau, ko da wasa idan aka ce Farhan za tai shaye shaye ze ƙaryata, yanzu ma ba dan Umma ce ta gaya masa da bakinta ba, cewa ze ƙarya ne.
Mahaddaciyar Alƙur'ani, m Yarinya me tsananin riƙo da Addinin ta, amma ace wai ta na shaye shaye, to me ya janyo hakan?
Jiki a sanyaye ya nufi ƙofar ɗakin Farhan, ya bubbuga.
Cikin sassanyar muryarta tace "shigo"
Huzaifa ya shiga ya tarar da ita a zaune, duk ta rame tai wani iri.
Yace "Yaya, dagaske abunda Umma ta gayamin hakane? Wai kina shaye shaye?"
Ta jinjinawa Huzaifa kai alamar eh.
"Kenan yanzu da gaske ne?"
Farahan tace "hakane Huzaifa"
Huzaifa yace "innalillahi wa innalillahi raji'un, Yaya me yai zafi haka? Meyasa kika zaɓi ɓata Rayuwar ki?"
"Huzaifa, idan nai shaye shaye ne kawai nake samun mafita, ina da damuwa Huzaifa, damuwa ce ke barazana ga rayuwata, Huzaifa se in kwana uku a jere ban rintsa ba ko na awa guda, ƙwaƙwalwa ta zata iya bindiga"
"Amma Yaya ina Alqur'ani? Kika ajiye shi kika kama wannan mummunar rayuwa?"
Cikin hawaye Farhan tace "bana iya karantawa yanzu, ko na buɗe kasawa nake,idan nace zan biya haddata nan ma bana iyawa, hadda ta duk ta zube, ji nake kamar zan mutu"
Huzaifa cike da tausaywa yace "Yaya, meye damuwar ta ki? Me kike buƙata ina Auren Sunusi ne kuma gashi an fasa?"
Girgiza masa kai tayi tace "faɗa maka damuwa ta ba shi da wani amfani, amma daga cikin sashin abunda yake haifar min da damuwa, shine ɓata min suna da Sunusi yai, wanda hakan yake bibiyar rayuwa ta" ta dafe kai tace "subhanallah, Huzaifa ba na son tuna Komai dan Allah ka tafi in samu in huta"
"Amma Far....
"Dan Allah ka tashi ka tafi, ba na son ganin kowa a kusa da ni"
Jiki a sanyaye Huzaifa ya tashi, ya bar ɗakin ya fito ya tarar da Umman Farhan na wanke wanke a tsakar gida, ya kalli Umma yace "Umma, Amma babu wani mataki da za'a ɗauka akan wannan lamarin?"
"Wane mataki, babanta yace a ƙyaleta ai mata Addu'a"
"Amma Umma, kamar za'a iya shawo kan matsalar, akwai abunda yake damunta in aka zauna da ita aka ji matsalar ta wataƙila a shawo kanta ta dena"
Umma tace "koma meyake damunta Allah yai mata magani, ni ba zan iya ba taje tai abunda ta ga ya dace da ita"
Shikansa Huzaifa yana mamakin hali irin na Umman Farhan, kawaicinta akan Farhan yai yawa.
Tabbas da Malam Zakari, wato mahaifinsa yana gari, da yaje ya sameshi yai masa magana, wataƙila shi ya iya shawo kan matsalar Farhan.
Ɓangaren Lilly kuwa, se abunda yai gaba, Nazir ya maida ita tamkar matar da ya ba da sadaki ya aura, wasu lokutan taje har gida ta same shi, su sheƙe ayarsu, ba tare da iyayen ta sun san me take aikatawa ba.
Sannu a hankali Nana ke ribatar Sadik, ta ke sanya shi kula da addini, mussaman Addu'oi, dan sam ba su dame shi ba ba yinsu yake ba.
Wataran idan ya na jin mutunci, se aita abun arziki, idan kuma akasin hakane se su yita faɗa ba ze yi ba.
Zuwa yanzu Sadik ya zama popular Sosai a cikin makaranta ba bu wanda be san shi ba, saboda harkar ƙwallon ƙafan da yake yi.
4months later.
*******************
Tsaye yake a jikin mota, ya zuba mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi.
"Dan Allah ka dena kallona" tai maganar tana haɗe rai.
"Dole in kalleki Farhan, na rasa yadda zan yi da ke, kin ƙi yadda da wancan lamarin, nace miki muyi Aure amma shima kin ƙi yadda, na rasa in da kika sa gaba, ki tausayamin haka mana"
Ta ɗago idanunta da su kai mata nauyi, ta zuba masa Sannan tai wani irin ƙasaitaccen murmushi, tare da ɗan tura baki tace "ka bani dariya, wai ka rasa gane in da na sa gaba, ni nace maka zan aure ne? Ai ban isa Aure ba ni"
"Haba Farhan, ya zaki ce haka? Wannan wace irin Magana ce, ba ki isa Aure ba amma kike yawo?"
Ta ɗan tsuke fuska tace "Wannan kuma wani dalili ne na daban, da na barwa kai na sani, ka ga If you are tired, juts leave me ni ba zanyi Aure ba, dan babu shi a tsari na"
Yai ajiyar zuciya yace "shikenan, amma ba zan iya rabuwa da ke ba, bari in tura miki kuɗi kya sa kati"
Ba tace Komai ba ta ɗauke kanta zuwa kallon wajen motar da suke ciki.
Wayar hannunta tai vibrating, alamar saƙo ya shigo, ta duba taga kuɗi ya turo mata, dubu hamsin wai ta sa kati.
Murmushin ƙarfin hali tai, ta buɗe motar ta fita ta nufi cikin gidan su.
A ƙofar gida ta tarar da Abba, shi da baƙo, ta gaida baƙon nasa sannan ta wuce cikin gidan.
Ta na kallon Umma a tsakar gida, ko uffan ba tace mata ba ta wuce ɗakinta, ta zauna tana jujjuya kuɗin da Wannan saurayin na ta me suna Nura ya sa mata, ta duba account balance ɗin ta, kuɗi fal a cikin account ɗin, amma ita kanta ƙyamar kuɗin take, ga kuɗi a account ɗin ta amma sun kasa ba ta farinciki.
Babban abunda ke rage mata damuwa shine shaye shaye, yanzu zuwa anjima wani hamshaƙin attajirin ɗan siyasa ne ze zo su fita, shine yake ɓata ta da kuɗi, tun da ta faɗa wannan mummunar harkar take haɗuwa da Samari kala kala, duk da tarin ƙuruciya da ƙarancin shekarunta, amma a haka maza ke binta.
Sallamar Abba da ta ji a ƙofar ɗakinta, ya sa ta dawo hayyacinta, ta amsa masa tare da gyara zamanta.
Abba ya shiga ɗakin, ba tare da ya kalleta ba yace "nace a cikin manemanki wa kika turo gurina?"
Farhan ta kalli Abba tace "Abba ni ban turo maka kowa ba"
Yace "wani mutum yazo gurina, neman Aurenki, kuma da alamu mutumin kirki ne da gaske yake"
Farhan tace "Abba ban turo kowa ba gaskiya, kuma ni gaskiya Abba bana buƙatar yin Aure a yanzu"
Abba ya dubi Farhan yace "se zuwa Yaushe? Haka zaki cigaba da zama kina zubar min da mutunci a unguwa? Wannan yazo gurinki anjima wancan yazo, in ta raya miki ki bar gida ki kwanaki a waje, kina min adalci kenan?"
Farhan ta miƙe, ta dawo gaban Abba tace "Abbana, da zan tona maka zuciyata na san zaka tausaya min, kai kaɗai kake jin tausayi na, tunda Allah ya saukar min da ƙaddarar nan, ba ka taɓa buɗe baki ka aibata ni ba, saɓanin uwar da ta kawo ni duniya.
Abba ka sani, babu mutumin kirkin da ze bari ɗansa ya Aure ni, na sauka daga turbar da ka ɗorani, na kama wani layi na daban, amma Abba kasani Addu'ar ka tana tasiri a kaina.
Bayan suna na da ya ɓaci a unguwar nan, duk wani mutumin kirki da ya zo neman Aurena, se an hana shi, kuma ba kowa ke min haka ba se Sunusi, ya hana kowa zuwa gurina. Duk wanda suke zuwa gurina ba Mutanen kirki bane ba".
Ta kamo hannnun Abba cikin na ta tace "dan girman Allah Abba kar kai min baki, kar kai min mummunar Addu'a, na sani zuciyarka na cike da takaicin lalacewa ta, Amma dan Allah Abba kar kai min baki, ka cigaba da yi min Addu'a, dan Allah kar ka tsaneni Abba, na rasa soyayyar uwa tun da ƙuruciya, dan Allah kaima kar in rasa taka.
Nasan ina ɓata maka rai, amma kar in mutu kana fushi da ni, Abba dan Allah kayi Magana".
Ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka me ban tausayi.
Abba kasa Magana yai, se hawaye da ke bin fuskarsa, ya ɗora hannunsa akan Farahan yace "Allah yai miki Albarka, Allah ya shirye min ke, da dukkan 'ya'yan musulmi, na ɗau wannan abu a matsayin ƙaddara, dan haka zan cigaba da yi miki Addu'a insha Allah"
Yana gama Maganar, ya fice daga ɗakin nata, yana share hawayen dake bin fuskarsa.
Nana ce kwance a ƙasa, se juyu kawai take yi, ta rasa abunda yake mata daɗi, ita ba zafi take ji ba ita ba sanyi ba, ita dai gata nan gaba ɗaya zaman ƙasar nan ya isheta, shekara ɗaya da wani abu kenan, tana zaune a London, ba tare da taje gida ba, dan haka komai ma ya isheta.
A haka Sadik ya dawo daga Makaranta ya tarar da ita, se cika take tana batsewa.
Ya kalleta yace "Ikon Allah, yau kuma lafiya kike fushi ke kaɗai?"
Ai yana rufe bakinsa se hawaye "Ni wallahi na gaji da zaman garin nan, haba dan Allah ai ko sau ɗaya Yakamata in je in ga gida, amma in ayi hutu ma sedai in zauna a nan gaskiya ni na gaji"
"To yanzu ya kike so ayi?"
Tace "Ni ka gayawa in Abba in anyi hutu dan Allah ya bani dama in koma Nigeria in huta, wallahi na gaji"
Ya kalleta yace "in kunyi hutu, ni kuma ai lokacin ba muyi ba"
Ta kalleshi tace "to kai ba se ka zauna ba, ni wallahi na gaji, idan hutun ya ƙare na dawo, kai ba se ka zauna a nan ɗin ba"
Sadik yai murmushi, ya zauna a kusa da ita, ya rungumeta a jikinsa, yana kwantar da kansa a wuyanta, yai ƙasa da muryar sa yace "an kawoki ƙasar nan ki karatu ne, saboda kar in lalace kuma seki tafi ki barni, ba kya tsoron in lalace ko?"
Nana ta tura baki tace "Lalacewa ta nawa kuma? Tun da nima ban sha ba, ni kawai gida zan koma"
Sadik yace "to ba zaki koma ba, wa ze dinga