Showing 225001 words to 228000 words out of 259198 words

Chapter 76 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13282

yace "wai Aure ze ƙara"

"What?" Mother tai Maganar cikin ɗaga murya.

"Wallahi abunda yace min kenan"

"Amma ka tsinka masa mari ko, dan ya dawo hayyaccinsa"

Abba yace "ba wani marinsa da nai ni, sedai kawai na koreshi ne"

Mother tace "lallai yaron nan ba shi da hankali, gaba ɗaya yaushe yai Auren farin, da har ze ɗakko wannan maganar, da ya a kai masa Auren farkon ma?"

"Rigima mana, irin tasa ai Sadik halinsa se Addu'a, ya zo ya tattara ya koma makaranta, Ya bar su a nan ita na nema mata wata makarantar ta cigaba da zuwa, in ya so ko me raino se a samo mata, wadda zata dinga riƙe mata takwarana"

Mother tace "base an wani samo me raino ba, ta dinga bar min shi zan riƙe"

Abba yace "to shikenan, Allah yayi jagora, amma dan ubansa makaranta ze zo ya koma bana son rigima".



A falon BQ ya tarar da Nana, ta saka Abinci a gaba tana son ta ci, amma Sahal se rigima yake ya hanata cin abinci, kuma da alama tana jin yunwa sosai, se haɗe rai take gashi baya gajiya da tsotso.

Sadik ya ƙarasa ya karɓi Sahal, yana rarrashinsa, ita kuna ta fara cin abincin, ya ɗan zuba mata ido sannan yace "wato yanzu kin dena damuwa da ni ko? Ko ki min tayin Abincin?"

Cikin ko in kula tace "am tired ne, dole in zubawa sarautar Allah ido"

Jikinsa ya ɗanyi sanyi, tabbas Nana duk da tarin shiriritar ta, tayi iya yinta taga Ya dawo da walwalarsa, amma abu yaƙi yiwuwa.

"Husna" ya kira sunanta, ta ɗago ido tana kallonsa.

Yace "am so sorry, na san gaba ɗaya ba kya jin daɗin yanayin zaman mu a yanzu, amma kiyi haƙuri komai ze wuce insha Allah".

Shiru tai ba tace komai ba ta cigaba da cin abincin dake gabanta, se ganin hawaye yai yana ɗiga akan hannunta daga idonta.

Ya ɗan lumshe idanunsa ya kwantar da Sahal da yai shiru, yana cin hannunsa, ya zauna a kusa da ita sannan yace "tuba nake my wife, kiyi haƙuri dan Allah, zan canza insha Allah, zamu koma normal yadda muke, ki dena kuka bana son hawayenki Besty" yai maganar cike da kulawa yana share mata hawaye, ita dai ba tace masa komai ba, ya cigaba da rarrashinta.

Bayan sallar isha'i Sadik yai kwalliya cikin manyan kaya, ya tafi gidansu Farhan, amma ya tarar da ita tana zance acikin motar Abbas, ransa ya ɓaci sosai amma be ce komai ba, ya fito daga motar yaje ƙofar gidansu ya samu guri yai zamansa.

Farhan ta ƙi fitowa daga motar Abbas, ta dinga jansa da hira daban daban, har mamaki abun ya bawa Abbas, yace "ya dai na fuskanci hira kike ji sosai, Allah ya kaimu bikin nan a raƙashe babyna"

Farhan tace "hmm ba wani raƙashewa, ai ɗaurin Aure da wuni rana ɗaya kawai"

Abbas yace "A'a, dole ki shirya wani ɗan reception ke da ƙawayenki"

"Ai ni bani da ƙawaye"

"Ahha haba dai, to suwaye zasu raka ki gidana?"

"Dagaske bani da ƙawaye, 'yan uwanmu ne zasu kai ni"

Yai murmushi yace "ke dai abun mamakin ki baya ƙarewa Farhan" haka suka cigaba da hira, daga bisani su kai sallama Ta fito daga motar, ya ja ya tafi.

Ta zo zata shiga gida, ta share Sadik kamar ba ta ganshi ba, ya miƙe ya tare mata hanyar shiga ta dube shi tace "meye haka kuma? Bani hanya zan wuce"

Sadik yace "ba zan matsa ɗin ba, me nace miki akan shiga motar mutumin nan?"

"Ban gane ba, wai kai meye haɗina da kai ne, dan Allah ka ƙyale rayuwata ta huta"

"Ba ke ba hutu, idan har ba ni kika Aura ba, tunda kika zauna tsawon wannan lokacin har na dawo baki Aure ba, to ki sani ke rabona ce Farhan, dan Allah ki zama me yafiya"

"Kaga dan Allah ka bani hanya zan wuce gida"

"Yadda kika bashi lokacin ki, nima dole ki bani lokaci, sannan let me warn you for the last time, kar in sake ganinki a motarsa, kuma kar ya sake zuwa gidan nan gurinki"

"Saboda ubana ne kai? Mutumin da zan Aurane nan da ƙanƙanin lokaci, kai na bawa dama a farko ba kai amfani da ita ba, dan haka yanzu damar wani ce"

"Farhan ba ki yadda da duk abunda na gaya miki bane?"

"Na yadda mana, ka manta dani a rayuwarka saboda rashin mahimmanci na, kai Auren ka har da ɗa, ka ƙyaleni nima in Auri wanda nake so ka dena shiga rayuwa ta"

Sadik yai wani murmushin rainin hankali sannan yace "da alama kina kishi da matata sosai, hakan ya sake tabbatar min da kina sona haryanzu, karki kishi da matata ba ruwanki da ita, ko ki tambayi ya sunan ɗana ko?"

Wani takaici ne ya ƙule zuciyar Farhan, zata bangaje Sadik ta wuce, amma ya riƙeta kasancewar gurin ba haske.

A fusace tace "meye haka, ka dena taɓani"

"Meye na pretending kuma in dena taɓa ki, meye ba muyi ba a baya, duk ki ka lalata ni, na dinga cewa Aure nake so, se da a kaimin Aure na nutsu duk ke kika koyamin, kika saba mun da..... Se kuma yai shiru yana wata shu'umar dariya.

Wani takaici ya cika zuciyar Farhan, tare da dana sanin kuskuren da tai a baya, ta biyewa Soyayar RUƊIN ƘURUCIYA.

Kawai ta fashe da kuka.

"To me nai miki kuma zaki min kuka, daga tuna baya se kuka, mara kunya kalli da ɗan mayafin da kike shiga motar wani, Allah sarki i miss my old Farhan so much".

Kuka take sosai har da sheshsheƙa, yai mata banza kuma yaƙi bata hanya ta wuce, se da tai me isarta Sannan yai ƙasa da murya ya kai bakinsa kunnenta yace "munyi kuskure a baya, wanda nine dalilin hakan, son da kike min da ƙuruciyar da ke kanmu ya sa soyayyar mu da shaƙuwarmu ta kai mataki me wuyar mantawa, Farhan ke yarinya ce me nutsuwa da tarbiyya, a dalilin soyayyata duk kika canza, idan na gujeki Allah baze barni ba, duk wanda zaki Aure nan gaba ze iya yai miki gori, ni kuwa fa nine silar komai, kuma yanzu ba ki ga na ƙara girma ba, har ɗa ne fa dani, kyakykyawa kamar mamansa".

Tsaki Farhan tai, zata raɓashi ta wuce ya sake riƙota yace "to meye na fushin kuma? Matata Tana da kyau sosai kamar ke ɗin nan, ki rage kishi kuma ki yarda haryanzu kina son Sadik ɗinki, ki kulamin da kanki, I love You" ya ƙarasa tare da sumbatar kumatunta.

Ya cikata, ya juya cikin takunsa a nutse ya nufi motarsa, yayinda galala tabi bayansa da kallo.

Seda motarsa ta bar layin, Sannan jiki a sanyaye ta shige gida.



Da safe Sadik yana bacci, wayarsa ta fara ringing, ganin Abba ne ya sa Nana ta ɗaga kiran, suka gaisa ya tambayeta ina Sadik, ta sanar masa bacci yake, yace idan ya tashi su zo duka yana son ganinsu.

Se wajen goma sannan Sadik ya tashi, bayan ya karya Nana ta sanar masa da kiran Abba, suka shirya zuwa cikin gida, kai tsaye part ɗin Abba suka wuce, suka tarar da shi ds Mother a can.

Suna zuwa Mother ta karɓi Sahal a hannun Sadik tana masa rawa.

Suka gaida su Abba, Abba ya kalli Sadik yace "kai me ka shirya ne akan komawarka makaranta?"

Sadik yace "Makaranta kuma Abba?"

"Eh mana Yakamata ka koma"

Sadik yace "dan Allah Abba ka ƙyaleni ba se na koma bs, ai min transfer in dawo Nigeria"

"Saboda ba ka da hankali? Ka koma makaranta ita ma na fara tuntuba in da za'ai mata registration ta koma makaranta a nan, takwarana kuma Kakarsa tace zata dinga riƙe abunta taje makarantar ta dawo"

"Abba dan Allah ka barni a nan, ba zan iya komawa makaranta in bar su ba"

Mother tace "zama ka faɗi gaskiya ne"

Abba yai mata alama da ido, akan karta tonawa Sadik asiri a gaban Nana.

Abba yace "yanzu ka gwammance in asarar kuɗina kenan?"

Sadik yai shiru ya sunkuyar da kai ƙasa, Abba yace "tashi kaje zan nemeka"

Suka fito shi da Nana, cikin damuwa Nana tace "besty, da Sahal ya isa ysye da na yaye shi na bika, naga Abba ya fi son ka koma"

Sadik yai ajiyar zuciya yace "zaman baze min daɗi ba, ba zan iya zuwa in zauna nikaɗai ba, ke kin san meyasa, Abba ba za su fahimce ni ba"

Ƙunshe baki tai tana masa dariya, yace "au dariya ma kike min ko?"

"To Besty kai ɗin ne ai se a hankali, ai gara ma ka tafi ko nayi ƙiba"

"Wallahi duk na damu, kin rame sosai Besty, kin fi ƙiba da muna London"

Nana tace "to ya zanyi? Shayarwa Sahal ba shi da haƙuri gurin ci, gashi kai kuma duk ka canza abun yana damuna sosai"

Sadik yai ajiyar zuciya yace "dan Allah ki dena damuwa masoyiya, Wallahi kin rame dan ki kwantar da hankalinki"

Nana tace "ai kwanciyar hankalinka its ce tawa, hankalina baze kwanta ba idan kana cikin damuwa"

Sosai take bashi tausayi, ta damu da shi sosai be san yadda zataji ba a lokacin da taji batun ze ƙara Aure.

Sadik yace "kije ki shirya, zan zo muje yawo Yanzu, ni zanyi magana da Mother"

Nana tace "to Besty, kuma ga Sahal na gurin Mother"

Yace "bakomai, zamu bar mata shi a gida ne"

"Ok, bari inje in shirya".

Sadik ya samu guri ya zauna, har Mother ta fito daga gurn Abba ta koma sashinta, Sadik yabi bayan Mother, ta waiwayo ta ganshi a bayanta tace "ya dai kake bina?"

Sadik yace "magana nake so muyi Mother"

"To ina jinka"

Sadik yace "Mother, na san Abba ya gaya miki maganar da mu kai da shi, na batun ina son ƙara Aure, kuma kinga dama ke kika ce zaki sake min wani Auren, dan Allah Mother ka bani goyon baya in ƙara Aure"

Mother tace "rufen baki, lokacin da na so ka bani haɗin kai har a kai ga yi maka wani Auren, ba ƙasa ka watsamin a ido ba? Ka bani kunya sega yarinya da ciki, ni yanzu na dena jin haushinta tausayin ta nake ji, yarinya ƙarama ga ɗawainiyar ka ga ta ɗanka kuma dai-dai gwargwado tana kula da kai sosai, kuma kawai yanzu se ka zo da wata maganar banza, dudu guda nawa kake zaka riƙe mata biyu, dama ba kwa tare ne da sauƙi, amma guda nawa kake da za kai batun ƙara Aure?"

Sadik yace "dan Allah Mother ki fahimce ni, na aikata wani kuskure ne a baya, na fara ajiye 'ya'ya, ba zan so hakan ta faru a kansu ba, dan Allah Mother ki bani goyon baya"

"Wallahi ba zan baka ba, tunda ba ka da hankali, fita ka barmin ɗaki"

"Dan Allah Mother"

A fusace tace "zaka fita ko sena zageka, na ɗuɗɗura maka Ashar". Jiki a saɓule Sadik ya fice daga ɗakin Mother yana tunanin mafita.


Daga ƙauye aka kira Abba, wai Hakimi yana son ganinsa, abun ya ba shi mamaki sosai da sosai, da fari yayi tunanin ma ko jikin Hakimin ne ya tashi, seda yaje ya tarar da shi jikinsa da sauƙi sannan hankalinsa ya kwanta.
Hakimi yace da Abba "Na san zaka yi mamakin kiranka da nai, ba wani dalili ne ya sa na kiraka ba, shekaranjiya Sadik ya zo garin nan, Masha Allah ya kawo mana abun arzikinsa fal, Allah yayi albarka"

Abba yace 'ikon Allah, ai bamu san ya zo bama"

Hakimi yace "hakane, ya kawomin ƙara ne, ko ince ya zo neman alfarma ne"

Abba yace "wace Alfarma kenan ranka ya daɗe?"

Hakimi ya ɗanyi tari sannan yace "kan in tafi kai tsaye ga abunda ya sa na kiraka, lokacin da Sadik ya zauna a garin nan, na sha kama shi yana waya da Mace, yana iƙrarin idan har ta Auri wani ba shi ba ze iya hallaka shi, da kunne na naji wannan cikin dare, na fuskanci yana soyayya da wata yarinyar a wannan shekarun nasa, kuma da alama yarinyar Aure za'ai mata, to da ai haka yaje yai mana wannan gangancin da yanayin ɗabi'un sa, da abunda kakarsa ta gayamin ta gani a game da shi, hakan yasa na ɗau Nana na ba shi, a gefe guda na Aura masa Nana dan sanin Nana marainiya ce ina sa ran in suka zauna guri ɗaya, su sassautawa juna wannan ƙiyayyar da suke wa juna, kuma tunda 'yar uwassa ce ina sa ran ya riƙet da amana ko ba ranmu, banji ta bakin kowannensu ba na yanke wannan hukuncin.
Sadik ya zo min da cewar yana son ya ƙara Aure, kuma dama na bashi wannan damar a lokacin da na Aura masa Nana, nace idan yana da buƙata a nan gaba ze iya ƙara Aure, dan haka kar ku kalli yarintarsa tun da yana so, ba ku san dalilinsa na cewa yana son ya ƙara ba, ya min bayanin komai na fuskance shi, kuma na bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, ya gayamin yana ƙaunar Nana yai min alƙawarin baze wulaƙanta ta ba, dan haka dan Allah ku bashi dama, kuyi haƙuri da yadda Allah yayi shi, ku bashi dama yayi, kuma zan bada kuɗi a sai masa isashen gida da ze ishe su, Allah yai musu albarka gaba ɗaya"

Abba be ji daɗin yadda Sadik ya kawo ƙararsa ba, kuma har Hakimi ya bada goyon baya, Abba bece komai ba, Hakimi yai tai masa nasiha, se Yamma sannan ya tafi Kano.

Sam be yiwa Sadik zancen ba, sedai ya fita daga harkarsa gaba ɗaya.

Nana tana shirya Sahal tana masa wasa tace "bari in shiryaka in kaiwa Abba kai, yaga wankan juma'arka, ko ɗan kyakykyawan Babansa"
Se shiriritar ta keyi, dama Talatu ce take zuwa taiwa Sahal wanka, Nana kuma ta shirya abunta tana shirya shi, tana masa hira kamar yasan me take faɗa.

Sadik ya samu Abba a falonsa ya gaishe shi, da ƙyar Abba ya amsa masa, jiki a sanyaye Sadik yace "Abba dan Allah laifin me nai maka?"

Abba yace "tambayata ma kake ko Sadik? Bayan kaje ka kaiwa Hakimi ƙarata na hanaka Aure ko? To shikenan kaje kai abunda ka ga dama"

Sadik yace "dan Allah Abba ka fahimce ni, Wallahi ba dan na ɓata muku rai nayi ba, Abba ina da dalilin da yasa nake son ƙara Auren nan, Farhan na fara so a rayuwata, saboda ita nai jumping na gama secondary School, dan Allah Abba ku amince in Auri Farhan, wallahi muna son juna sosai, Kasan lokacin da na Auri Nana ba sonta nake ba, Farhan na fara so".

Gani yai Abba ya ƙurawa ƙofa ido, Sadik na ɗaga kai yaga Nana a tsaye da Sahal a hannunta, hawaye harya cika mata ido, alamar taji duk abunda ya faɗa, juyawa tai cikin hanzari har tana tuntuɓe, hawaye na zuba daga idonta.
A falo ta haɗu da Mother, Mother tace "ke kula mana zaki yar da yaron hannunki"

Jiki na rawa ta miƙawa Mother Sahal, tai waje da gudu.

Sadik kuwa dafe kansa yai yace "ya salam, Wallahi ina son Nana ma, ina ƙaunarta sosai amma.....

Abba yace "oho maka dai, ya rage naka"

Mother ta shiga falon Abba tana faɗin "me a kaiwa yarinyar nan ne? Naga ta fito hankali a tashe tana neman ta yar da yaron hannunta?"

Abba yace "tambaye shi, bayan ƙarata da ya kaiwa Hakimi, akan in bar shi yai Aure, shine ya samu ƙwarin gwiwar tsayawa a gabana yana cemin dama wata yake so aka aura masa Nana, shi yana da wadda yake so, ita kuma ta ji, ina sane na ƙyaleka ka cigaba da zuba, kaga gara ka dena munafutarta, duk ta ɗaga hankalinta akan kana cikin damuwa baka walwala, kai kuma ba ta tata kake ba, wata kake so".



Gaba ɗaya Sadik ya rasa in da ze sa kansa, Nana ba taji maganar har ƙarshe ba, ya san da iya abunda taji za tai masa hukunci.

Jiki a sanyaye ya baro part ɗin Abba, ya tafi BQ, sedai ya daɗe a tsaye a bakin ƙofar shiga, be so labarin ƙara Aurensa ya zo wa Nana a haka ba, tabbas ya san za ta ji babu daɗi, jiki babu ƙwari Sadik ya shiga, ya tarar da ita a ɗaki, tana ta aikin kuka.

Jin motsinsa ya sa ta ɗago ido ta kalleshi, abunka da me manyan idanuwa, tuni idonta yai jawurr saboda kuka fuskarta duk ta kumbura.

Sadik ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, yace "dan Allah Nana ki fahimce ni, ki tsaya in miki bayani"
Ɗaga masa hannu tai tace "har akwai wani bayani da za kai min bayan wanda naji? Sadik ba sona kake ba ka dinga gayamin kana sona, har na yadda da kalamanka, ka yaudareni da kyautatawa da tausayawarka, ina tunanin nayi kuskuren ƙoƙarin bijirewa zama da kai a matsayin miji da nai da farko, na ɗauka na Auri mijin marainiya, ka san ba ka sona meyasa ka ɓoyemin kake nuna min soyayya, an tauyeni na Aureka maimakon a shekaruna ace ina makaranta, ka ɗau damuwa ka ɗorawa ranka, nima ka sani a damuwa, ashe duk dan kana son ka ƙara Aure ne, duk da ƙanƙantar shekaruna, da ka min bayani zan fuskance ka, ba ka se shiga damuwa dan kana son ka ƙara Aure ba, Sadik ko matan duniya duka zaka dinga aurar huɗu kana saki kaje ka Aura, amma ka tabbatar ka sakeni, se ka Auro duk wadda ka ke so, dan ba zan zauna da wanda ba ya  so na ba"

Sadik kamar ze kuka yace "Wallahi Nana ina sonki, baki ji ƙarshen zancen bane, meyasa zance ina sonki bayan ƙarya nake"

"Wai meyasa kake son rainamin hankali ne? Sadik da kunne na fa naji abunda kake faɗa, ka nemi wadda zaka rainawa hankali ba ni ba" ta sauka daga kan gadon ta koma ɗaya ɗakin.

Sadik ya dafe kai, ya rasa wani tunanin Yakamata yayi, ai kome za'ai sedai ayi, amma ba ze yadda ya rabu da Nana ba, duk da son da yakewa Farhan, Nana ba abar wulaƙantawa bace, kuma ya cancanci ta nuna fushinta akan abunda taji yana faɗa, ya san zata ji babu daɗi, amma Baze iya haƙura da Farhan ba ma.

Wunin ranar sam Nana bata shiga harkarsa ba, se kuka da take, ba abunda yake dukan zuciyar ta irin yadda da kunnenta taji yana cewa ba sonta yake ba, ko Abinci ba wanda ya iya ci a cikinsu.
Ɗaki ma daban daban kowa ya kwanta, ta bar shi da Sahal, cikin dare ya dinga tsala masa kuka, haka yaita faman rarrashinsa, bacci kam duk ba su rintsa ba.


Da safe ma Nana ba ta saurari Sadik ba, sedai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login