Showing 141001 words to 144000 words out of 259198 words

Chapter 48 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

haƙuri Auta, nasan ba a kyauta maka ba, amma ba yadda ban ba Abbanka ya ɗakkomin kai amma yaƙi, nace zanje in ganka nan ma ya hanani, dama nasan ba jin daɗin zaman garin nan kai ba, amma kayi haƙuri kai wanka ka fito, zan kawo maka Abinci in baka da kaina"

Har Mother ta gama surutunta, Sadik be tanka ba sema kunna shower da yai, dan ya dena jiyo sautin Maganar Mother, ya lumshe idonsa hawaye na zirarowa daga idonsa.

Da tsananin Mamaki Mother ta nufi part ɗin Abba, ta tarar ya cire Babbar rigarsa yana waya, ta kalli bedside taga ya ajiye uban goro da alawa, ɗan taɓa baki tayi, ta shiga kawo masa Abinci.

Be ce mata uffan ba ya fara cin abincin sa, ta kalleshi tace "Dan Allah Yallaɓai meke faruwa ne?"

"Wai me kika gani ne?"

"Ganinku nai gaba ɗaya wani iri, kamar wani abu na faruwa"

"Ba abunda yake faruwa se Alkhairi" ya bata amsa.

Can ya ɗago yaga yadda ta zuba masa ido yace "yawwa ina fatan an bawa Nana Abinci?"

Ta ɗan yatsuna fuska tace "namanta ne, bari in magana a bata"

Ta miƙe ta fita, tana zuwa falo Khairat ta dawo daga Makaranta, tace "Mother na dawo"

"Sannu da zuwa, Sadik dai ya dawo"

Cikin murna Khairat tace "Allah sarki bestyna, yana ina?"

"No, karki je in da yake yanzu ban san me akai masa ba, naga baya walwala"

"Amma dai lafiyarsa ƙalau ko?"

"To gashi nan dai ban gane masa ba"

Khairat tace "ina ga fushi yake, bari in bari zuwa anjima na je gurinsa"

Mother ta manta da abunda ya fito da ita, ta ɗakko kwanukan Abinci ta shiga ɗakin Sadik, amma ta tarar da shi a kwance, ya lumshe ido ksmsr me bacci.
Mamaki ya kuma kamata, yana jik motsinta, amma ya rufe ido kamar yana bacci, ta ajiye masa Abincin ta fita daga ɗakin.
ta koma gurin Abba, ta tarar ya gama cin Abinci, ya kwanta.

So take ta kuma masa magana, amma yaƙi bata fuska sam.

Rabon Nana da Abinci tun jiya da safe, Inna tayi tayi tai kurarin amma Nana taƙi cin Abinci, har zuwa yanzu ba ta ci Komai ba, ga yunwa ga damuwa nan da nan kanta ya hau ciwo, har da zazzaɓi.

Se bayan Abba ya idar da sallar la'asar ya shirya ze fita, sannan ya zauna a gefen gado, ya kalli Mother yace "Hauwa"

Tace "Na'am"

Yace "Na sani kin sani, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yacewa Sahabban sa, shin bana sanar da ku manya-manyan zunubai ba, Sahabbai sukace gayamana ya ma'aikin Allah, yace da su 'Shirka da Allah, saɓawa iyaye, da kuma shedar zur, Kin sani saɓawa iyaye laifi ne me girman gaske a gurin Allah, sannan kowane mumini ba ya zama mummuni se ya yadda da ƙaddara, me kyau ko akasinta, ɗa baya taɓa girma a gurin iyaye, kamar yadda haryanzu mukewa Usman kallon yaro ƙanƙani har muke zaɓa masa wasu abubuwan game da rayuwarsa, to muma haryanzu hakane, ba'a girma a gurin iyaye, kuma duk hukuncin da suka yanke akan ɗa, in dai be saɓawa mahalicci ba to tabbas be dace ga ɗa na gari ya bijire ba, dan Iyaye ba zasu Cutar da ɗan da suka haifa ba.
Dan haka nake son ki tayani yiwa iyayena biyayya, Kamar yadda ban taɓa yunƙurin ganin kin saɓawa naki iyayen ba, nima ina so ki bani ƙwarin gwiwar da zan bi nawa iyayen, tunda iyayena naki ne.
A dawowar mu kinga abubuwa da kike buƙatar bayani, na zo da Yarinya ba tare da na gaya miki meyasa na taho da ita ba, duk da hakan ba abun damuwa bane, dan ina da hurumin ɗakko duk wanda nake so ya zauna a gidana.
Wannan goron da kike gani, na ɗaurin Auren ɗanki ne!!!"

A zabure ta kalli Abba tace "ban fahimce ka ba, wanne daga cikin 'ya'yan nawa?"

"Abubakar Sadik!"

"What! Sadik ɗin akaiwa Aure?"

"Eh shi ɗin, tun wancan Zuwan da nayi, Hakimi yace lallai in nemawa Nana karatu a ƙasar da Sadik zeje karatu, jiya kuma bayan sallar juma'a ya ɗaura masa Aure da Nana, ban san dalilin Hakimi na yin haka ba, amma koma dai menene nasan dalili ne me ƙarfin gaske, dan haka ina fatan ni da ku mu karɓi hakan a matsayin ƙaddara mu riƙe yarinyar nan kamar tamu, danni 'yata ce kin sani, Hakimi ya gindayamin hatsari me girman gaske, akan idan wani abu ya samu Auren nam be yafemin ba"

Miƙewa Mother tai tace "Ya isa haka, wannan kai kanka ka san ba abune me yuwuwa ba, shikenan ni bani da iko ko martabar da za'a tuntuɓe ni kan a yankewa ɗa na hukunci? Wane irin abune wannan za'aiwa yaron da be san komai ba Aure? Me Sadik ya sani dudu guda nawa Sadik ɗin yake da za ai masa Aure, kuma a rasa wadda za'a aura masa se wannan yarinyar? Shikenan ni bani da iko akan yarana? Sedai ai duk hukuncin da ake so akansu, ko hakan yaimin ko be min ba? Da sake a wannan karon baze yuwu ba"

Dama Abba ya san hakan zata faru, dan haka Abba yace "na biyo miki ta laluma amma naga baki gane yaron rarrashi, kiyi abunda kike ganin shine daidai, nima zan abunda ya dace"

Fuuuu tai waje daga ɗakin, ta wuce ɗakin Sadik ta tarar da shi akan sallaya alamar salla ya idar, yai shiru yana tunani.

"Kai dama abunda aka ƙullo kenen? Har nake tambayar ka menene kace min bakomai, wato kana sane kaje kace musu Aure kake so ko? Me ka sani a game da Aure? Shikenan ka gurgunta rayuwarka, kazo matsaloli su addabeka ka bi ka tsofe"

"Haba Mother, tayaya kike Tunanin zance sumin Aure, in ma hakane ya za'ai ince A auramin wannan baƙauyiyar, tausyawarki nake buƙata ba wannan faɗan da kike min ba"

Se kuma jikin Mother yai sanyi, ta zauna a kusa da shi tace "kana nufin baka son Auren nan?"
."Mother ya za ai ince ina so, na tsani Yarinyar nan ko ganinta bana ƙaunar yi"

"Shikenan, ka kwantar da hankalinka, in dai wannan ne an gama, dole Auren nan ya mutu"

"Amma Mother, Hakimi yace be yafe ba idan wani abu ya samu Auren"

"Kana son Auren kenan?"

"Mother dan Allah ki dena faɗan haka, wallahi bana so"

Tace "in dai baka so ai shieknan, shi Hakimin ai ba ubanka bane da Allah ya isansa zata bika, tsabar son zuciya ne irin nasu, da kuma tasanar da suke min ta shafeku shiyasa aka maka wannan Auren, dan a cusan takaici, zan nuna musu nima 'yar yauce, dan an gaji da wannan abun nasu, ka kwantar da hankalinka kaci Abinci"

Sadik ya jinjina kai cike da jin ƙwarin gwiwa, akan kalaman mahaifiyarsa.






Da Yamma Abba yazo sake duba jikin Farhan, yaga da sauƙi sosai dan har hira sukayi.

Abbas ya shigo ɗakin, yana ganin Abba yai murmushi yace "Baba sannu da zuwa"

Abba yace "Yawwa, Sannu da ƙoƙari, muna ta godiya fa Allah ya saka da Alkhairi"

"Ai bakomai, insha Allah zuwa gobe in Allah ya kaimu zamu iya sallamarta, muna monitoring ɗin hawa da saukar jininta ne, amma in ba zaka damu ba, ina son muyi magana da kai a Office ɗina"

Abba yace "badamuwa"

Kallon Abbas take, tana fatan Allah ya sa ba zancen Sadik zewa Abba ba.

Bayan sunje Office ɗin, suka ƙara gaisawa, Abbas ya kalli Abba yace "wato Baba, a yanayin jikinta abunda binciken mu ya tabbatar mana shine, damuwa taiwa Yarinyar nan yawa, ko kai a shekarunka idan jininka ya kai kamar nata, dole a ɗoraka akan magani, tayi ƙanƙanta da fara shan maganin hawan jin"

Abba ya dafe ƙirji yace "hawan jini kuma?"

"Yes of course, hawan jini gashi shikansa jinin be wadaceta ba, saboda bata cin Abinci, abu na farko Baba Al'ada ba addini bace ba, babu in da akace dan ka haifi ɗa shine na fari kai watsi da shi da lamuransa, Yakamata mahaifiyarta ta ajiye wannan al'adar ta ja 'yarta a jiki ta san meye damuwarta, naso in bugi cikinta inji amma na fuskanci tana da tsananin kunya da zurfin ciki, ko kasan ta rayu tsawon shekara guda da tunanin tana ɗauke da ciwon Cancer wanda ba haka bane?"

Abba ya zaro ido cike da Mamaki "Mahaifiyata yakamata ta san wannan, wanda in Asibiti ya kama a kaita a duba a kaita, amma babu wanda ya sani, Mutane masu hali irin na Farhan suna buƙatar ja a jiki da nuna musu soyayya, yadda zasu saki jiki har a dinga jin matsalolin su, idan aka cigab da tafiya a haka sakamakon da ze biyo baya baze daɗi ba, Mutane masu irin personality ɗinta are at risk of having depression, daga lokacin da ta samu depression ƙwaƙwalwata zatai ta gayamata abubuwa ba daidai ba, zata tsame kanta daga Mutane, da tunanin kowama baya sonta, in a kai rashin sa'a za'a iya wayar gari aga ta kashe kanta, ko a ganta a wata mummunar hanya wadda ba'a fata.
Yanzu babban abunda nake ƙoƙarin yi shine, inga ta kwantar da hankalinta, yadda ko bata faɗi meye damuwar tata ba, a samu jininta ya sauka aita sa ido dan Allah"

Abba yai ajiyar zuciya, dan yaji tsoron bayanin doctor Abbas, Abba yace "Nagode sosai da wannan bayanin naka doctor, Insha Allah za'a sa ido a kanta, Allah ya wuce mana gaba"

"Ameen" Abbas ya amsa.

Daga nan Abba ya tashi ya tafi yana tunani daban daban a ransa.

Bayan fitar su Abba kuwa, Anty Uwani ta sa Farhan tai wanka, ta fito tai salla ta bata Abinci, ba wani ci tai ba, Anty Uwani tai mata sallama tace zata gida ta dawo.

Fitar Anty Uwani ba daɗewa, kawai sega Sunusi ya shigo ɗakin da Farhan take shi da Huzaifa, Huzaifa se tuttura baki yake.

Nan da nan Ta haɗe rai kamar ba ta dariya, taƙi ko kallon in da yake, yana shigowa ya turare ɗakin da warin hannatarsa me maƙaƙi a wuya.
Huzaifa kuwa juyawa yai ya bar ɗakin, dan ya tsani Sunusi shima.

Ya ƙarewa ɗakin kallo Sannan yace "Ya jikin naki?"

"Da ssauƙi" ta amsa a ciki.

"Ki dena Wannan cunkusa fuskar, dan ba abunda ze sauya, a satin nan za'a kawo kuɗin Aurenmu"

Ko kallonsa ba tai ba ta ɗauke kanta daga kallonsa.

"Hmm yarinya kenan, ai ranar a idona aka ɗakkoki daga gida, wani shinƙimemen ƙato ya ɗakkoki kamar inje in bazar da shi, ai an san ina unguwar saboda tsabar wulaƙanci ni ba a aika an kirani na ɗakkokin ba, se wani zindiƙin ƙato za a kira ya ɗauke ki ina mijinki, wannan ai ba yi bane"

"Karka ƙara kiranka da mijina, na gayamaka"

"Wallahi ko kinƙi ko kin so, nine nan mijinki ke mallakina ce"

"Ke tawace Farhan, babu wanda ze mallakeki seni, duk wanda yai gangancin yin hakan, zan nuna masa abunda zan iya yi akanki" Maganar Sadik ce ta dawo mata, gaba ɗaya taji jikinta yai sanyi.

A hankali ta furta "come back to me Prince"

"Me kike cewa ne?" Sunusi yai maganar yana zuri kansa daf da ita.

"Dalla meye hakane, karka sake ka sa jikinka a nawa"

Buɗe ƙofar akayi, wanda yasa Sunusi daidiata nustuwar sa.

"Farhan did they serve your medications?"

Abbas ya shigo yana magana.

Ta girgiza kai alamar a'a, sam be lura da wani Sunusi a gurin ba.

Sunusi kuwa ya gane shi, dan ya kan ganshi a layinsu, yazo gidan Hajiya, sedai yaga Abbas ɗin yai masa kwarjini sosai.

Farhan tace "A'a, amma a bari se anjima" ta faɗa a Sanyaye.

"Ni, yanzu ne lokacin yi, nasan allura ce ba kya so, sedai kiyi haƙuri, ba kiga because you are so special yasa nake miki allura da baki magani da kaina ba, bana son Nurses suyi miki me zafi"

Tai murmushi ba tace komai ba, yayin da Sunusi ya cika yai fam.

Abbas ya haɗa allura, ya kamo hannun Farhan, ya buɗe canula yana mata, yanayi yana shafa kan jijiyar da canulan take, saboda kar tai mata zafi, amma shi Sunusi se yaga kamar da Iskanci Abbas yake hakan, kuma tai fusuƙi da kai tana kallonsa.

Ya kalli Fuskar Farhan yace "Ai ba zafi ko?" Tai murmushi tace "eh"

Yace "Yawwa, ai dama na gaya miki ba zafi, saura ta baya se kuma in sa miki drip zan tafi gida".

A ɗan shagwaɓe tace "wayyo Allah"

Abbas yace "to yi kuka kawai mana, kin samu lafiya ne shiyasa kike kuka"

Sunusi ji yake, kamar ya dunƙule hannu yai ta kirɓar Abbas.

Abbas ya kalli in da Sunusi yake, wanda se da ga baya ya lura da shi a ɗakin yace "ɗan bamu guri zamuyi allura ko?"

"Ba inda zani, nace ba in da zani, tunda nine mijinta ayi a gabana mana in ba munafunci ba se lailaye mata jiki kake, Wato in baku guri kaji daɗin yi, to ba zan fita ba"

Abbas ya zare gilashin idonsa yace "Kaine mijin nata ko wa?"

"Eh nine nan, kallon ku ai kawai nake"

"I don't fucking care who so ever you are, kaje waje zan mata Allura, kuma ni babu wanda yacemin matar wani ce, tunda aka kawota mahaifinta nake gani a kanta, dan haka ka bamu guri"

Abbas ya kalli Farhan yace "wai ma waye wannan?" Kuka Farhan ta saka ta kasa magana.

Be kuma cewa komai ba, yai waya gate sega security da bindiga yazo ya fitar da Sunusi.





Har gari ya waye tsakanin Mother da Abba, ba wanda ya kula wani kowa sabgar gabansa yake da saƙa abunda yake ganin shine daidai a gareshi.

Da safen Abba harya shirya ze fita, yaje ɗakin da Nana take dan ganin halin da take ciki, ya tarar da ita a kwance a ƙasa.

Abba ya ƙarasa da sauri, yace "Nana, kwanciyar me kike a ƙasa haka?"

Nana ta tashi zaune tace "Abba ina kwana"

"Lafiya ƙalau, meyasa kika kwanta a ƙasa?"

"Zazzaɓi nake ji shiyasa"

"Meysa baki faɗa ba to, ai da ko maman naki kin gayawa, wannan kukan da ki kai ai dole kiyi zazzaɓi"

Tace "Ai ban ganta bane, shiyasa ban gayamata ba"

Ya kalli idon Nana, ya ga yadda tai wuri wuri kusan kamar ma a galabaice take, yace "kinci Abinci kuwa?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Jiya fa an baki Abinci?"
Tace "eh"

"Gayamin gaskiya, an baki ko ba a baki ba?" Yai maganar cikin razanarwa.

Tai sauri tace "A'a"

Abba ya jinjina kai yace "dole in nunawa yaron nan da uwarsa a ƙarƙashina suke, zasuga matakin da zan ɗauka.



Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.






Abba ya tashi Fuuuu ya fice daga ɗakin da Nana take, an ɗan jima kaɗan sega Talatu ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta kawo wa Nana Abinci.

Tace "Nana, ya akai ki ka zo ban sani ba, baki nemi kowa a gidan nan ba?"

Murmushin ƙarfin hali kawai Nanan tayi, idanunta sunyi jawurr sun kumbura.

Tace "Yallaɓai ne yace a kawo miki Abinci, Ya kike ya Hajiyar?"

Nana tace "tana nan lafiya"

"Madalla, ashe ba da ita kuka zo ba"

Nana ta fara ƙosawa da hirar Talatun, dan haka tai shiru, ta haɗa tea ta fara sha saboda yadda cikinta yake a ƙulle.

Sosai take cin Abincin ba dan tana so ba, sedan azabar ƙullewar da cikinta yai.

Daga Inna har Hakimi babu wanda yai baccin kirki, mussaman Inna da ta dinga kuka cikin dare, akwai shaƙuwa me ƙarfin gaske tsakanin ta da Nana, lokaci ɗaya ba tare da ta shirya ba, an raba su.

Abba kuwa yana zuwa gate, ya kira security.
Cikin hanzari yazo cikin girmamawa yace "gani ranka ya daɗe"

Abna yace "Dan Allah, daga yanzu zuwa lokacin da Sadik ze bar Gidan nan karka kuskura ka barshi ya fita, idan kuwa har yai maka gardama ka harbe shi a ƙafa"

Buɗe baki security yai da mamaki, ɗan Auta kuma shalelen ake cewa a harbe, Abba yace "Umarni nake ba, idan ba kai abunda nace ba ka bari ya fita, to kai zan harbeka"

Jiki na tsuma yace "shikenan, insha Allah baza'a bari ya fita ba"

Daga haka Abba ya fice daga gidan.

Sadik kuwa tun daga ƙwarin gwiwar da ya samu daga gurin Mother yaji zuciyarsa ta ɗanyi masa sanyi.

Wayoyinsa ya ɗakko ze saka a caji, dan yau da Yamma yana son fita ya sha iska, sedai ya tuna ya baro simcards ɗin sa duka a can ƙauye, a ƙulle a ƙasan kilisai.

Wani dogon tsaki ya ja, ya jona wayoyin, sannan ya fita BQ.

Yana zuwa ya tarar da Faruk yana karyawa, Faruk yai masa murmushi yace "Ango Ango, Ango ka sha ƙamshi Allah ya karɓi Addu'ar ka kayi Aure ka barni"

Tsaki Sadik yai yace "Wannan har wani Aure ne? Da shi da babu duk ɗaya dan babu abinda na tsana sama da Yarinyar nan"

Faruk ya Ajiye kofin hannunsa yace "A'a Sadik, koma menene babu laifinta a ciki, ba ita tace tana sinkaiba, yadda a kai maka ba zata ita ma haka a kaimata, dan haka karka cutar da Ita Sadik"

"Ba abunda yai min zafi, yadda kakaninta suka dinga azabtar dani akanta zan rama, kuma da ƙafafuwanta zata koma in da ta fito, zata gane kurenta"

A ɗan hasale Faruk yace "Sadik, ka manta abunda Hakimi yace maka, amana ce a gurinka"

"Mother tace ai ba Ubana bane, dan haka ba abinda ze faru dan ban bi son zuciyarsu ba"

"Sadik! Are You mad? Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, a nan gurin be kamata kaiwa Mother biyayya ba, kakanmu mahaifinmu ne tunda yai silar kawo mahaifinmu duniya, a tunaninka da baffansu Mother yana raye shi ya ɗau wannan hukuncin zata gaya maka haka ne? Mahaifiyarmu ce amma Yakamata mu dimga tunani akan wasu abubuwan"

Sadik yace "Stop it please, babu wani abu da zaka gayamin da ze sa in sauka daga kan bakana, bana ƙaunarta kuma ba zan zauna da ita ba, se ta koma ƙauyensu, dan yadda suka azabtar dani sena rama a kanta"

Be kuma sauraron Faruk ba yai waje, ya bar shi da buɗaɗɗen baki.

A harabar sukai karo da Khairat, cikin fara'a da murna Khairat ta nufi in da Sadik yake, sedai ko kallo ba ta isheshi ba, saboda yadda ransa yake a ɓace.

In da masu aikin Gidan ke hutawa ya nufa, yana zuwa ya kallesu yace "Ina Bala?"

Security yace "ya fita da Alhaji"

Sadik ya kalli security yace "buɗemin ƙofa zan fita"

"Zuwa inam" ya tambayi Sadik.

"Ban gane zuwa ina ba, ka aikeni ne?" Ya faɗa a hasale.

"Am sorry, megida yace kar in yadda in bari ka fita, in kai gaddama a harbeka a ƙafa"

Saroro Sadik yai yana kallon security, tabbas baya wasa da su, balle ace tsokanar sa suke, wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login