Showing 90001 words to 93000 words out of 259198 words
Chapter 31 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
zata wuce, ya tsallako ya biyota yana "waini kwanan nan me nai miki ne? Ko gaisheni kin dena yi?"
Kallonsa tai take taji wani takaici ya mamayeta, se tsamin rana yake ga wani Mugun warin hammata da yake.
Cigaba da tafiya tai ba ta da niyyar saurarar sa, harta shige gida, ya tsaya saroro yana mamakin yadda Farhan ɗin ta canza, da duk in da ta ganshi seta gaishe shi, amma yanzu ta canza.
Yau ne dr. Ze dawo daga tafiyar da yayi seminar Abuja, Jidda tayi duk iya ƙoƙarin ta tai gyare-gyaren tarbarsa tana Addu'a Allah yasa ta burgeshi.
Ƙarfe huɗu na yamma ya shigo, fitowa tai daga ɗaki tana masa murmushi, binta yai da kallo ganinta cikin rigar buba ta leshi, ta ɗaura ɗan kwali se ya ganta yau daban sosai, kamar ba ita ba.
Ƙarasowa tai ta karɓi jakarsa, ya rungumarsa yace "You look so beautiful"
Murmushi tai tace "Sannu da zuwa Ranka ya daɗe"
"Yawwa uwargida"
Suka ƙarasa tai masa jagora yai wanka, ta kawo masa Abinci, se kallonta yake, dan sosai tayi masa kyau yau ɗin nan.
Dagewa tai iya ƙoƙarinta, take masa magana da girmamawa saɓanin da da take yaɓa ta yadda take so.
Aikam taga yaita nan nan da ita, yana koɗa yadda tai masa kyau, ya saki jiki sosai suna hira, kamar lokacin aka kawota a amarya.
A hankali ta nustu tana tunani, Usman yana matuƙar son girma, yana son yaga ana girmama shi, an girmama decisions ɗinsa.
A zigar ƙawaye na school da blogs ɗin da take following a social media, ta yadda da Aƙidar cewa idan ka fiye yiwa namiji biyayya ze raina ka ne, ko ya dinga wulaƙanta ka, da ta nustu se taga itama akwai abubuwan da ta tsiro da su na yace ayi abu kaza ta nuna ita ba za tai ba, sedai yabi abunda take so.
Shi kuwa idan yace ai abu sau ɗaya tace a'a, baze kuma zancen abun ba seya ƙyaleta da fari gani take ita ke galaba, seda taga yadda yake watsi da ita yana sabgarsa, ya nuna mata ko da ita ko ba ita ze iya rayuwarsa.
Tana matuƙar son dr. Dan haka ta fara gano kura kuranta, tai ɗamarar gyarasu tun kan tafiyarsu tai nisa a haka.
Nazir yana gidansa da yake zaune, ya gyara katifarsa ya kwanta message ya shigo wayarsa
"Hi"
Ganij baƙuwar lamba yasa yai reply da "wake magana?"
"Nice" aka bashi amsa.
"Ke wa?"
"Fatima Hakeem"
"Ina kika samu lambar wayata?"
Yana mata reply ta kirashi, ba tunanin Komai Ya ɗaga yace "ina kika samu lambata kike damuna?"
"Au hakama zakace ko?"
Yace "Ya akayi?"
"Ƙara na kawo maka"
"Wace irin ƙara ce haka, baki kawota tun a makaranta ba, se yanzu?"
"Ai ƙarar ka na kawo maka"
"Hmmm"
Cikin shagwaɓa tace "Shine ɗazu ka cemin daƙiƙiya, wai meyasa ka tsane ni?"
"Ba daƙiƙiyar bace? Ba kya son karatu sam, shiyasa nake miki haka kyayi zuciya"
"To kuma seka dinga dizgani a gaban 'yan ajinmu wallahi seda nai kuka ɗazu"
"Haba dagaske"
"Uhmm, uhmm wallahi dagaske nake, dan Allah ka dena min haka Please"
"In dai ba zaki dinga karatu ba, nima ba zan dena ba"
"Ina yi fa"
"A'a banga alama ba"
Shiru tai ba ta kuma cewa komai ba yace "Hello"
Kawai ta sa kukan ƙarya, yace "Subhanallah meye na kuka kuma?"
"Ba kaine kace ba zaka dena cemin daƙiƙiya ba"
"Kinga ya isa haka, kar wani abun ya sameki ace nine"
"To zaka dena?" ta faɗa a shagwaɓe.
"Se nayi tunani, seda safe zanyi aiki"
Tace "Bari in zo in tayaka"
"No, kika makara gobe a school zaneki zan ba Punishing ɗin ki kawai zan ba"
Kamar me raɗa tace "good night Sir"
Ta katse wayar tana murnar yadda ya amsa mata waya da dukkan attention ɗin sa. Da alama ds wuri tarkonta ze Kama Nazir da wuri.
Abu kamar wasa Farhan kusan kullum idan Farhan taje ajinsu Sadik, su Taslim kullum cikin sauraron Audion Novels suke, idan ba taji a can ba ma 'yan ajinsu su Yasmin koda Yaushe aikinsu kenan.
Kan wani lokaci tunani ya fara yiwa ƙwaƙwalwar Fahan yawa, wannan litattafai suka fara tasiri a ƙwaƙwalwarta.
Gashi a duk lokacin da ta kasance a kusa da Sadik, se taji wani baƙon lamari yana bijiro mata, ko kuma yayin da yaje gurin kwanciya, se tunaninsa ya addabi zuciyarta fiye da yadda take ji a farko.
Gefe guda Lilly na ta ƙara shigewa Sir Nazir, ya zaman kullum lokacin break za taje Office ɗinsa suyi hira, tun yana korarta har ya zama idan ba taje ba ze aika a kirata.
Farhan ta rasa abunda yake mata daɗi, ta tashi da ƙullewar gefen mara, kuma gashi ba lokacin period ɗinta ba, babban abunda yake ƙara tsoratar da ita be wuce yadda in ta je fitsari take ganin wani yana fita daga jikinta ba, wasu lokutan kan tai fitsari, wasu lokutan bayan tayi fitsari, mussaman idan gefen mararta ya ƙulle, sedai babu wanda zata tunkara tai masa bayanin abubuwan da ke damunta ɗin, a haka ta lallaɓa ta tafi Makaranta.
(Akwai ruwa kala kala da suke fita daga jikin mace, a duka cycle ɗin ta daga zuwan ala'ada zuwa wata.
Mata na mistake da zarar sunga abu na fita a jikinsu se suce infection ne, ba kowane ne infection ba.
Ruwa da yake fita kwana 11,12,13-14 bayan gama al'ada me kama da zare ana jawoshi, wannan yana nuni ne da ovulation period, wato mahaifa ta shirya karɓar jariri. A wannan tsukin lokacin mace zata idan tai tarayya da namiji za ta iya samun ciki. Shine wasu lokutan gefen marar mace har ƙullewa yake, wani ma ya dinga fita da ɗan sirkin jini.
Akwai wanda yake fita, normal kamar ruwa ya kan jiƙa pant wasu lokutan, wannan normal lubrication ne na vagina, shi wannan ruwan yana bawa gurin kariya, a hausance ana ce masa Ni'ima, wanda ya kan ƙaru lokacin feelings Wannan duk normal ne.
Discharge kamar dusar awara, me wari da ƙuraje, wannan shi ne na cuta, wanda za'a nemi magani.A kiyayi shan magunguna barkatai, saboda lafiyar kayan cikin da ke tace magungunan, bayanin da yawa amma zan taƙaita a nan)
Babu me zaunar da Farhan yai mata bayanin wannan, balle ta san takamaimai meke damunta.
Da break ta tashi ta tafi gurin Sadik, dan ajinsu se hayaniya suke, a ganinta ko zata samu nutsuwa a can.
Baya ajin sun fita ball, se matan ajin su, amma ba Tunanin komai taje gurin zamansa ta zauna, a hankali tana cigaba da jin mararta na ƙullewa, ƙarshe suma su Taslim suka bar ajin suka tafi nasu guri.
Kamar an jefo Sadik se gashi ya shigo ajin, yana ganin Farhan yace "yaushe kika zo? Da kin zo filin ball ina can kallon ƙwallo, yanzu su Tasliysuka cemin kina nan kina jirana"
Shiru tai ba tace komai ba, ya ƙaraso ya kalleta yace "ya dai ko ba lafiya?"
Ta girgiza masa kai tace A'a ni dai ka zauna.
Yace "to shikenan" ya nemi guri ya zauna a kusa da ita.
Ba tace masa komai ba, ya tsaya yana kallonta, fuskarta ta nuna ta na da damuwa, amma yasan in dai ba ita tai niyya ba, ba zata gaya masa ba.
Ya gaji da zaman shirun, ya ɗakko wayarsa yana dannawa, a hankali ta ɗora hannunta akan nasa.
Can kuma ta tashi zaune ta kwanta akan kafaɗarsa.
Mamaki ne ya cika Sadik ba kaɗan ba, ko matsarta ya fiye yi, se ta zumɓura baki ta hau mita, amma yau ita ce da kanta ta kwanta a jikinsa, a hankali yace "lafiya kuwa Farhan?"
Ta ɗaga masa kai alamar eh.
Ya gyara zamansa sosai ta samu ta kwanta sosai a jikinsa.
Duk da ƙirjinta se bugawa yake da saurin gaske, ita kanta ta san abunda ta aikata ɗin ba halinta bane, kuma ba abune me kyau ba, amma hakan yasa ta ɗanji sassauci akan abunda ke damunta.
Sadik ji yai tana ajiyar zuciya, yana dubawa yaga hawaye na bin fuskarta.
"Subhanallah, Farhan dan Allah ki gayamin damuwarki, menene?"
Kawai ta ƙanƙame Sadik tana kuka, bata san me za tace masa ba, damuwa kam tana da damuwa fal a zuciyarta, amma ya za tai masa bayani, wannan ba abunda za tai masa bayani bane, tunda ba hurumin sa bane, amma wayake bata dukkan lokacinsa da attention ɗinsa in ba shi ba, wa zata tunkara da abubuwan da suke damunta?.
A hankali ya fara share mata hawaye yace "ban san meke damunki ba Farhan, amma ina jin damuwarki a raina fiye da yadda kike jinta, ina fatan Allah ya yaye miki abunda ke damunki, kiyi haƙuri koma mene Allah ze kawo mana mafita.
Ya ƙarasa goge mata hawayen, ya kwantar da ita a jikinsa, ba tai musu ko ƙoƙarin ƙwacewa ba ta kwanta.
Sedai a take Sadik ya fara neman nustuwar sa ya rasa........
07063065680.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Farhan ce tsaye tana kallon su Lilly, ba abunda ya daki zuciyarta irin miyagun maganganun sir Nazir, da ya dinga jifan ta da su a baya, saboda tana tare da Sadik.
Basarwa tai ra ƙaraso gaban teburin sa ta ajiye masa wasu takaddu tace "gashi inji Madam Joy, tace you should review it"
Tana gama faɗin haka ta jiya ta fice daga Office ɗin.
Jiki a sanyaye ya ture Lilly daga jikinsa, yace "kinga abunda ki ka janyo ko? Shikenan mutuncina ya zube a idonta, za taje tai ta yayata abunda ta gani"
Lilly tace "ba zata faɗa ba, kawai kayi kamar ba abunda ya faru"
Yace "ta yaya bayan ta ganmu?"
"Ajinmu ɗaya da ita fa, kaima ka san halinta ba zata faɗa ba"
Banza Nazir yaiwa Lilly, yana jin dana sanin biye wa Lillyn.
A shagwaɓe tace "Dear fushi kayi ne? Am sorry Please kaji"
Tsaki yaja ya tashi ya bar mata Office ɗin Gaba ɗaya.
Abun ba ƙaramin ɗaurewa Farhan kai yayi ba, za ta iya dafa Alqur'ani ta rantse da wani ne ya gayamata, Sir Nazir zeyi haka ba zata yadda ba, saboda yake tsare gida, ga faɗar Allah yace Annabi yace, dan mutum ne me riƙo da Addini sosai, amma ba kunya ba tsoron Allah ta ganshi rungume da ɗalibarsa a cikin Office ɗin sa.
Tunanin take tayi, taji an janyo hannunta, a fusace ta waiwayo dan ganin waye yai mata haka, kawai taga wanda ta tsana wato Babba.
"Meye haka?" Ta faɗa a raunane.
Yace "Ban gane meye haka ba? Kin san komai amma ki dinga mazewa wai ke ta Allah, duk keɓewar da ku ke da Sadik mun san abunda kuke ai"
Wani Mugun kallo tai masa, tai nufin ta wuce ta barshi a gurin, amma ya sha gabanta yace "kin san yadda kike looking so attractive Kuwa? Idan kika taho jikin ki yana wata girgiza, idan kika bada baya ma wani abun kallon ne, dole ki haukata ɗan mutane, muma ko a na bati ai se a bamu mu taɓa"
Wani mummunan ɓacin rai ne ya kama Farhan, wata muguwar tsanar Mubarak Babba ta kuma baibaye ta, ta juya da baya zata tafi, kawai ya taɓa mazaunanta.
Seda ta yanke masa hukuncin mari, Sannan ta dawo hayyacinta tace "Allah ya isa ban yafe maka ba, mugu asararre"
"Ke dan ubanki ni kika mara, 'yar matsiyata da ke?"
"Eh an mare ka ɗin"
"Ki sa a ranki bashi kika ɗauka, wanda se kin biya shi wallahi, kin san ki bar wancan sokon ya taɓa ki, amma ni kika mareni"
"Eh na bashshi ya taɓa ɗin, ina ruwanka da ni, ka ƙyaleni ka fita daga harkata"
Mubarak yai mamakin ƙwarin gwiwar ta, be taɓa tunanin zata mare Shi ba, saboda kallon sokuwa yake mata.
Da sauri ta shige Mubarak, ta cigaba da tafiya, wasu hawayen baƙin ciki na bin fuskarta, wata muguwar tsanar Babba na kuma mamayeta.
Tun daga nesa ya hangota tana tahowa, ya naɗe hannayensa ya zuba mata ido.
Tana zuwa tai karo da shi a tsaye yana kallonta.
"Sarkin kuka me kuma ya faru? Ki tai min asarar hawaye ba dalili"
Ƙara kwaɓe baki tai tana kuka.
"Au abun hadda shagwaɓa, zo ki gaya min menene kuma? Waye ya saki kuka, kowa yana class amma ke kika fito waje"
Yai Maganar yana janyo ta jikinsa, ba musu ta kwanta a jikin nasa, amma ba zata iya gaya masa abunda Mubarak yai mata ba, saboda sanin halinsa, dan haka tace "faɗuwa nayi"
Kawai Sadik ya kama dariya "wallahi kin fiye abun dariya, Garin yaya kika faɗi?"
Tashi tai daga jikinsa tace "dariya ka ke min ko?"
"Haba ba fa dariya nake ba, zo mu tafi muje ki gayamin waye ya taɓa min ke, garin yaya ma a kai matata ta faɗi"
Ba ɓarin da take yake kallo ba, hakan ya bata damar kallon abunta son ranta tana jin son sa na ƙara ratsa zuciyarta, he's so much caring and funny.
Yace "Princess, gaskiya wannan hijjabin da kike sawa yayi ƙanƙanta, wani zamu siya am so Much jealous"
"To ai ka san idan na sa wanda yafi wannan girma ƙwacewa za'ayi"
Ɗan ƙaramin tsaki yayi yace "kwata kwata wannan tsarin be dace da Addinin mu da Al'adar mu ba, kin ganki kuwa idan kina tafiya?"
Kunyace ta kamata, dan ita kanta tasan kayan sun kama jikinta sosai.
Kenan Babba abunda yake faɗa gaskiya ne.
Bin sa take tayi kamar raƙumi da akala, wani ajin ya jata in da ba kowa, da nufin suje yai rarrashi.
Suna zuwa Yasa hannu ya buɗe ƙofar ajin, sedai mummunan ganin da su kai ne ya razanar da su gaba ɗaya.
Dan seda Farhan ta saka ƙara, ya janyo ta da Sauri ya toshe mata baki.
Wata irin kyarma jikin Farhan yake, ba ita kaɗai ba, shi kansa Kamar zuciyarsa ta tsaga ƙirjinsa ta fito haka yake ji, saboda tashin hankali da fargaba.
Duk iya shegen Sadik be taɓa mummunan gani ba kamar na yau ba.
Bakomai suka gani ba face Salma da gangs ɗin ta suna sheƙe ayarsu, wata irin tsuma Farhan take kamar zata shiɗe, wannan wane irin bala'i ne haka?.
Jan hannunta yai suka bar gurin, sedai ya rasa mema ze cewa Farhan ɗin, gaba ɗaya shima kansa ya kulle.
Ya rakata ajinsu ta shiga shi kuma yai gaba, haka jikinta ya cigaba da kyarma, ta kasa mata abunda ta gani, wanda ya danne wanda ta gani a Office ɗin sir Nazir.
Ko da aka tashi, babu fargabar Komai Farhan ta kuma bin Sadik a motar su, zuwa gida sedai ya kasa ce mata komai, ita ma kuma ta kasa ce masa komai har suka kaita gida, sedai yau a titi ta sauka ta shiga hanyar gidan su.
Tun da ta sauka ta fara tafiya kanta yana ƙasa, sedai ta lura da yadda mutane keta binta da kallo, duk da kasancewar babban hijjabi ne akan Uniform ɗin ta.
Sadik kam yana cike da damuwar yadda ze tafi ya bar Farhan a Makarantar nan, me cike da tarin ƙalubale, babu wanda ya damu da harkar kowa, ita Makaranta neman kuɗinsu ne kawai a gabansu, su kuma ɗaliban suna taƙama da kuɗin iyayen su ne ke aiki, dan haka ba wanda ya isa ya taka su, shiyasa kowa yake abunda ya ga dama.
Yau gaba ɗaya kamar mara lafiya haka ta wuni, ta rasa meke mata daɗi, har zuwa taje Islamiyya ta dawo, tana tunani wato Salma abunda takeyi kenan shiyasa take mata wasu abubuwan da ta kasa gane kansu gab ɗaya ta dinga cewa wai ta na sonta?.
"Farhan" taji an kira sunanta.
Waiwayawa tai, taga wata babbar mace ce, maƙwabciyar su da tare kwanan nan, dan matar ta girmi Ummanta sosai.
Farhan cikin girmamawa tace "Hajiya ina wuni?"
Matar tace "lafiya ƙalau, zo nan Farhan"
Ba musu Farhan ta ƙarasa in da mata ke tsaye a bakin gate ɗin gidanta, matar ta ja ta cikin gidanta ta kalleta tace "Farhan kina saka brezia kuwa?" Turus Farhan tai tana kallon matar, taji maganar ta tata wani iri.
"Kinga ni uwace ba batun jin kunya kowani abu, kin zama budurwa, ba kya ganin yadda maza ke kallon ki? Duk da naga kina da ƙoƙarin saka hannu a hijjabi"
Farhan tai shiru ta sunkuyar da kai, ita kanta abun na damunta, amma tunda ummanta ba ta siya ta bata ba, ba tai mata umarnin sakawa ba, ba ta san ya zata kalli abun ba idan ta fuskanci ta fara sawa ba da izinin ta ba, iya kaci sedai ta saka half vest ta kawo normal vest ta ƙara a kai.
Hajiya ta jinjina kai tace "jeki, zan shigo gidan naku"
Cike da jin kunya Farhan ta fito daga gidan ta tafi gida.
Da daddare bayan ta kammala cin Abincin dare, tana ɗaki tana bitar Alƙur'ani, Abba yazo ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.
Dama sanye take cikin dogon hijjabi, ta fito daga ɗakin tace "Abba gani"
Abba yace "Yawwa, kije ga Sunusi can a ƙofar gida ya zo ku gaisa"
Ji tai kamar Abba ya watsa mata wuta, jiki a sanyaye tace "to Abba"
Abba yana juyawa ya tafi, Farhan ta fara hawaye, haka nan ta zura takalmanta, ta fita.
Tun kan ta ƙarasa ƙofar Gidan, warin hammatar Sunusi yai mata sallama, cikin baƙin ciki da ɓacin rai haka ta ƙarasa guri ɗaya ta tsaya.
Wandon jikinsa ta kai kwana uku tana ganinsa da shi, rigar ce ma ya canza.
Ya ƙaraso in da take tsaye ya washe baki yana "manya manya maganin ƙanana"
Haɗe rai tayi sosai, ta ɗauke kanta.
"Hmm naga alamar miskilanci kike ji yau ɗin nan, dama malam ne su kai shawara da Abbanku, suka ce lokaci yayi da Yakamata in fara zuwa gurinki dan mu fuskanci juna"
Farhan a ranta tace "ai kuwa ba zamu taɓa fuskanta ba har abada"
"Nasan dai an gama gayamiki komai, kusan tun bara Malam yace min 'meze hana ya nema min Aurenki, tunda yaga ke yarinyar kirki ce, kuna haryanzu ba wanda yake zuwa gurinki, yace ko in ba damuwa ni ya nema min Aurenki, kuma cikin ikon Allah Abban yai murna da hakan"
Wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Farhan, wato ma anga ba wanda yake zuwa gurinta shine aka ce ya nemi Aurenta, son da takewa Sadik ne yasa ba ta bawa kowane namiji fuskar yi mata magana, balle yazo gurinta.
Kwata kwata Sunusi be iya Magana ba, sqe wani soki burutsu yake, ya kama nan ya kama can, ga uwar dariya sekace wani kwantacce.
Ita ko malamanta na Islamiyya da suke alarammomi mahaddatan Alqur'ani, a nuste take ganin su, Amma Sunusi ya fita daban gaba ɗaya.
Har ya gama surutun sa, Farhan ba tace masa ci kanka ba, yai surutan harya gaji yai mata sallama, ya tafi.
Wani marurun takaici ne ya ƙule zuciyar Farhan, ga Sadik me za tai da wani Sunusi?
Ta dawo gidan ba daɗewa taji sallamar Hajiya, Umma ta amsa ta bata gurin zama suka zauna