Showing 165001 words to 168000 words out of 259198 words

Chapter 56 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13262

kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, wallahi duk kin rame Farhan"

Farhan a ranta tace 'da za a ƙyaleni da Auren Sunusi, a barni da tunanin Sadik kawai, da na samu sassauci a raina'

Amma a fili ta kasa Magana sam, se ƙoƙarin mai da hawaye kawai da take yi.

Lilly tace "Farhan, ke naki me sauƙi ne, Soyayya shu'umar a bace, mussaman idan ta kama ka a lokacin da baka shirya mata ba, Sadik be kyauta ba, dan babu wanda be san Soyayyar ku ba, amma ni dai roƙona a gareki kiyi haƙuri ki manta da shi"

Se da ƙirjin Farhan ya buga, kowa seyace ta manta da Sadik, how could this be possible, ya tabatta Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kenan?.

A zahiri ta jinjinawa Lilly kai, dan zuwa yanzu surutan Lillyn sun cika mata kunne, sam ba ta son hayaniya ko yaya take yanzu.





Sam Nana ba ta ji ta ƙoshi ba, saboda yunwa take ji sosai da sosai, amma Sadik ya haɗata da fruit, har gara madarar ta temaka mata, saboda maiƙon da ke jikin madarar.

Yau ma a falon ta kwana, kwanciyar ƙasa da ta kan kujera ta sa, haƙarƙarinta da wuyanta se ciwo suke mata.

Yau bayan tai sallar Asuba, taƙi komawa bacci ta nemi guri ta zauna, Har ƙarfe bakwai, Sadik ya shirya ze tafi makaranta, miƙewa tai tsaye ya zo ze wuce ta kalleshi tace "Nifa yunwa bake ji wallahi"

"Se ki cinye ni ai, bani hanya ni zan wuce"

"Dan Allah ka bani abun da zan sawa cikina, wallahi yunwa za ta kashe ni"

"In da zata kashe kin ai da na huta"

Hawaye ya taru a idon Nana, dan karma tai kuka yaji tausayinta, ya raɓata ya fice.

Nana ta zauna ta ci uban kuka, har wajen ƙarfe tara, sannan ta gaji ta tashi, ga wanka ta na son yi, ga yunwa ta addabeta.

Ta tashi ta dinga leƙe leƙe, har ta gano Kitchen, ta shiga tana duba Kitchen ɗin, kayan da ke Kitchen ɗin, sun sha banban da irin namu na Nigeria, wasu abun akwai a Nigeria wasu babu ba ta sansu ba, mussaman ita da take ƙauye.

Ta buɗe fridge ɗin da ke Kitchen ɗin, amma bakomai a ciki se wani sauran yoghurt.

A kitchen ɗin ta zauna ta shanye shi tsaf, ta ajiye kwalbar amma ba ta ji alamar ƙoshi ba.

Ga shi wanka take son yi, amma babu sabulu a banɗakin da take Alwala.

Daga baya ta yanke shawarar shiga ɗakin da Sadik yake, aikuwa ta samu kayan wanka a ciki, ta samu tai wanka, ta canza kaya ta shafa creams ɗin sa, ta haye gadonsa tai kwanciyarta.

Se bayan azahar Sannan ta tashi, tai salla ta ɗakko Akwatinan ta ta ajiye su a cikin ɗakinsa.

Yau a kai sa'a da la'asar ya dawo, amma ya tarar da ita a falo, duk tai wuri wuri saboda yunwa.

Ta na kallonsa ta shareshi ba ta kula shi ba, shima kuma be kulata ba, ya shiga ɗakinsa yai wanka ya canza kaya, Sannan ya dawo falon ya sameta ya ajiye mata wani ƙaramin pack a gabanta.

Cikin sauri ta buɗe park ɗin, farfesun wata ƙatuwar kaza ce a ciki, se ƙamshi take.

Ba ta san lokacin da tai murmushi ba, taje ta wanke hannunta, ta sa kazar na a gaba ta dinga ci saboda ba ƙaramar yunwa take ji.

"Ke! Ke! Kina ina?!"ta jiyo Sadik yana ƙwala mata kira.

"Kut, nice ma ke ɗin, wallahi ba zan amsa ba" ta cigaba da cin kazarta.

A fusace Sadik ya fito yace "kina ji ina miki Magana kika shareni, uban waye yace ki ajiyemin Akwatin ki a ɗakina?"

"To ni a ina zan ajiye?"

"A kaina zaki ajiye" ya bata amsa yana huci.

Ko kallonsa ba tai ba ta cigaba da cin abunda ke gabanta.

Sadik ya kai matuƙar ƙulewa da haushi, se jinsa tai yana janyo Akwatinan yana shiga wani lungu a falon.

Tashi tai da sauri ta bi shi, dan ganin ina ze kai mata kaya.

Ɗakina babba, da gado da mudubi kamar na Sadik, har da kayan wasa su teddy da komai da komai, ga zane zane masu kyau, da a kai framing ɗin su, aka saka a jikin bango.

Ya waigo ya kalleta, jin takunta a bayansa yace "Nan shine ɗakinki, karki kuskura ki kuma shigarmin ɗaki, na gaya miki"

Nama tace "Amma ka san da nan ɗin, dan mugunta ka barni nake kwana a cikin sanyi, wuyana se ciwo yake"

Tsaki yai ya juya ze fita tace "Amma, naga ɗakin a ƙarshen gida, in abu tsoro ya zo fa, ko kuma gobara ta kama ai har abun ya cinye ni kan in fito"

Sadik ya kalleta da mamaki, wannan yarinyar wasu lokutan Mahaukaciya ce, wai batun gobara take da abun tsoro.

Tsaki ya ja, ya fice daga ɗakin ya barta ta na cigaba da kallon ɗakin.

Ta gama mamakinta ta fito, ta kasa cinye kazar da Sadik ya kawo, ta tashi zata kai sauran Kitchen, ta tarar da Sadik a Kitchen ɗin yana ta shirya kaya a cikin fridge, wanda ba ta san da su ba ma.

Ya ɗakko kwalbar da ta shanye madarar ciki yace "ke kika taɓa wannan kwalbar ko?"

Ta tura baki tace "to ai yunwa nake ji, shiyasa na ɗauka na sha"

Sadik yace "Yawwa, kin kyautawa kanki, a garin tsinannen kwaɗayi kin sha wa kanki"

"Me na sha?" Ta tambaye shi tana zare ido.

"Madarar karnuka ce, Nonon karya ne  a ciki"

Take ta dafe ƙirji tace "la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalumin, dan Allah meya kawo Nonon karya cikin fridge?"

"Ban sani ba, daga yanzu kya dinga kiyaye abunda zaki ci, in ba haka ba wataran naman karen zaki ci"

Ya fice ya barta dafe da ƙirji tan zare ido, take taji cikin ta na juyawa, naman da taci ma yana taso mata.

Sadik ya koma falo kan kujera yai zamansa, ya kunna tv, wanda tun da suka tare a gidan ba'a kunna ba.

Yana kallonta ta fito daga Kitchen ɗin jikinta a sanyaye, da alama ma kuka tayi, Ba wani Nonon karya da ta sha, Sadik yana sane ya gaya nata haka duk cikin salon yadda ze ƙuntatawa Nana.

Ta koma ɗakin da yace shine nata, ta shirya kayanta a wardrobe, ta shiga banɗaki tai ta kakarin amai ko zata amayar da madarar nan, amma abu ya gagara abu da ta ri ga ta sha tun safe.

Ko da ta dawo Falo, Sadik ya fice ba kowa a gidan se ita kaɗai.

Ta koma tana ta ɗaɗɗaga teddies ɗin dake ɗakin, tana jujjuya su sedai abu guda, wata zundumemeiyar 'yar tsana ce take ba ta tsoro.

'yar tsanar tamkar ɗan shekaru shida, se taga Kamar 'yar tsanar zata fara motsi.

Ƙarshe ta kuma komawa falo ta zauna, shima ta na yi tana waige waige, wai kar 'yar tsanar ta biyo ta falon.

Haka tai ta wannan zaman ɗarɗar ɗin, har ƙarfe goma na dare sannan Sadik ya shigo, sallama yai ta amsa ya zo da kaya niƙi niƙi ya wuce Kitchen, se dai tai ta hamdala da ya dawo ɗin, dan a tsorace take sosai.

Ya fito daga Kitchen har ze gota ta, ya jefo mata abu jikinta, wata roba ce a cikin 'yar ƙaramar jaka, ta zaro robar dabino ne a ciki da yawa, irin lubiyar nan.

Ta bi bayansa da kallo dan wulaƙanci maimakon ya bata, shine ya jefata da shi.

Ta girgiza kai ta ɗan ɗaga murya tace "Nagode"

Yana jinta yai banza da ita ya wuce ɗaki.

Nana ba ta yadda za'ai ta iya kwana da wannan 'yar tsanar a ɗaki ɗaya, dan haka a falon yau ma ta kwana.

Washegari da safe ba Makaranta, Sadik da wuri ya shirya cikin wando 3quater, da 'yar shimi ya wuce Nana a falo tana bacci, ya  fita jogging.

Se da gari yai haske sannan ya dawo, tuni Nana tai wanka ta canza kaya.

Sadik na shigowa kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, duk da ba wani datti a gidan, amma ta gyara ko ina fes, ta ɗau ragowar kazarta ta ci.

Haka su kai sati a gidan nan, in ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba Sadik ba ya kula Nana, duk da Nana akwai rawar kai, ita dan be kulata ba, ba ya hanata yi masa Magana in tana buƙatar wani abu.

Kullum ze zo da Abinci, ya Ajiye Mata.

Ɗakinta kuwa ta samu bargo ta rufe wannan 'yar tsana da ke bata tsoro, amma duk da haka a tsorace take kwana a ɗakin.




Zaune yake a bakin wani ƙaton ruwa, akan fararen kujeru yai shiruuu yana tunani, teburin gabansa ɗauke da tarin littattafai, amma hankalinsa yana gurin.

Ji yai an taɓa shi, hakan ya dawo da shi da ga dogon tunanin da ya tafi.

"Abbas, ka kammala nazarin litattafan ne ka zauna tunani?"

Abbas ya ja wata irin ajiyar zuciya, tare da lumshe idonsa.

"Wai meyake damunka ne? Tunda mu ka zo garin nan naga kamar ba ka sukuni, ko akwai matsala ne?"

Abbas ya ɗanyi miƙa sannan ya gyara zamansa, ya kalli me masa maganar yace "Ahmad, wallahi hankalina yana Nigeria"

"Me kake tunani a Nigeria? In Madam kake tunani, ta biyoka nan ɗin mana"

Abbas yace "Mmm, ita ma ina tunanin nata, se dai gaskiya abunda ya dameni daban ne, wallahi wata yarinya ce ta tsaye min a rai, ina tunanin halin da Yarinyar take ciki yanzu haka"

Ahmad yace "budurwa kai kenan?"

"A'a, ba budurwa ta bace, she's my client amma ina tunanin halin da take ciki".

Nan Abbas ya kwashe labarin Farhan ya gayawa Ahmad.

Ahmad yai murmushi yace "Lallai Yarinyar ta cancanci a tausaya mata, amma sonta kake"

"Kai, rufamin Asiri kar kasa Matata ta sakeni mana, yarinya ce Sosai not more than 14years, but she's deeply in love with someone, ga kuma a halin da iyayenta ke shirin sa ta".

Ahmad yace "Ni ban da lalacewar zamani, ina 'yar shekara huɗu ina wata Soyayya?"

Abbas yace "Ahmad kenan, Soyaya ai gaskiya ce ba ƙarya ba, kuma ka duba yanayin lokacin da muke ciki, akwai banbancin zamani, yanzu yaran yanzu idansu  a buɗe yake, ga kallace kallacen fina finai, dan haka tunaninsu ba iri ɗaya ba ne da yaran da.
Ni babban abunda yake damuna, bagidajen da iyayenta zasu aura mata, wani wawa mara hankali, ga ta she's very calm, ko Magana ba tayi sosai, wallahi tausayinta duk ya cikan zuciya, idan lissafin da nake daidai ne, saura wata guda ya rage a ɗaura mata Aure, ina tsoron kar deprssion ya kama Yarinyar nan, ko ta faɗa mummunan hali"

Ahmad yace "ka gama kewaye kewayenka ka dawo in da Magana take, You love her"

Abbas yai murmushi yace "ka ga, mu fara abunda ya kawo mu, a bar wannan zancen"

Haka kuwa akayi, nan su ka shiga nazarin litattafan da suke gaban Abbas.



Faruk ya samu delay a tafiyarsa, se yanzu Allah yai tafiyar, ya shirya komai tsaf, washegari da sassafe ze tafi.
Khairat ta kasa zaune ta kasa tsaye, duk ta shiga cikin damuwa.
Ƙarfe tara da na dare, har Faruk ya fara shirin kwanciya se ga Khairat.

Da mamaki ya kalleta yace "Khairat, ya dai? Meyafaru na ganki yanzu, bayan yanzu na baro cikin gidan?"

"Magana nake so muyi"

Yace "ok, ina jinki"

Nan ta shiga in da in da, ta rasa ta ina zata fara masa bayani.

"Calm down, nag duk kin ruɗe Kamar wadda taje screening da fake result, Faruk ne fa feel free to tell me"

"Wata Magana nake so in gaya maka, amma ban san yadda zaka ɗauke ta ba"

"Ina jinki Khairat"

Ta ɗan kalleshi sannan tace "Yaya Faruk"

"Na'am sister Khairat"

"I...mm...dama"

"Dama me?"
"Ina son in gaya maka, Yaya ina sonka ne"

Murmushi Faruk yai yace "Nima ina sonki ai Khairat"

"I serious mean it, please keep joke aside, I want you to marry me"

Ɗan Jimm Faruk yai yana kallon Khairat, yai murmushi yace "Khairat, Nifa yayanki ne, ki bar wannan maganar kinji ko, kar ma ki bari wani yaji ta, babu wannan a tsakanin mu, zumunci da 'yan uwanta ka ne a tsakanin mu, you are still young Khairat, kar ki biyewa RUƊIN ƘURUCIYA kin ji, maza je ki ki kwanta kimga dare ya fara yi"

Jiki a sanyaye Khairat ta baro BQ, tana matuƙar son Faruk, ba ta taɓa zaton haka daga gareshi ba, gashi dai be mata wulaƙanci ba, amma dai be karɓi Soyayyar ta bs, wanda hakan ya tssye mata a rai.

Yanzu Nana idan Sadik baya nan, zama take ta kunna Tv dake falo tai kallo, hakan yana ɗebe mata kewa Sosai, duk da akwai tv a ɗakinta amma ba ta san yadda za tai operating ɗin ta ba, dan babu remote ta falon ce dai akwai remote, dan haka kullum cikin kallon cartoon take.

Yau ma ya dawo ya tarar da ita tana kallon cartoon ɗin ta, kamar kullum ba wanda ya kula wani a cikin su.

Da alama a gajiye yake, ya ɗan jima a ɗakinsa sannan ya dawo falo ya zauna, ya kalli Nana yace "kawon ruwa a fridge"

Kamar ba zata tashi ba, se kuma ta tashi tana tafiya a hankali, kamar mara lafiya, ta kawo masa ruwa da kofi.

Sedai tana kawowa ta tarar ya ɗauke remote, ya canzs channel.

Ta dire masa a gabansa, ta koma gefe tana kumbure kumbure, be ko kulata ba ya ɗau ruwansa yana sha.

Kallonsa take, saboda Ruwan da sanyi sosai, ga yanayin garin da sanyi Sosai,
Amma yake shan ruwa me sanyi.

"In kin ga dama, kije ɗaki na kan gafo, ki ɗau Abinci"

Ba musu ta miƙe, taje ta ɗakko wata jaka, wadda ita kaɗai ta gani a ksn gadon ta dawo falo.

Ta zauna ta buɗe, amma gugguru ne a ciki.

Ta kalleshi tace "wannan ne Abinci?"

Be ko kulata ba ya maida hankalinsa kan TV.

"Wannan ai ba Abinci bane, ni wallahi na gaji da cin wannan abubuwan, wannan ai ba Abinci bane, ya mutum ze ƙoshi da wannan, ni Wallahi Abinci nake so na fi ƙoshi, ko wannan bredin da kake siyo min, amma wannan ai dan nishaɗi ake ci ba yunwa ba"

Kamar be existing a ɗakin ba, haka ta fara ci tana mita.

Can ta maida hankali kan abunda Sadik yake kallo, wani horror Film ne me matuƙar razanarwa yake kallo (the conjuring), nan da nan mood ɗin ta ya canza, ta shiga tsoro Sosai, ba ta taɓa ganin bala'i a film kamar wannan ba.

Wani razanannen ihu da Nana tai, seda shi kansa Sadik ɗin ya razana.

"Meye haka, baki da hankali zaki wa mutane irin wannan ihun?"

Kamar za tai kuka tace "tsoro naji fa"

"Kuma se kiwa mutane wannan ihun, saboda hauka da ƙauyanci? Tashi ki bar falon nan kije ki kwanta, dama ai dare yayi"

Ta noƙe kafaɗa tace "bana jin bacci ai"

"Zaki tashi ko sena make ki?"

Ba shiri ta tashi tana tura baki, duk ta ɓata gurin da gugguru, tai tafiyarta ɗakinta tana ƙunƙuni.

Tai wanka, ta sa kayanta na bacci ta ɗora da kayan sanyi, Sannan ta saka hijjabi ta kwanta, se dai tana kashe fitila ta kwanta, se ta ga kamar teddies ɗin ɗakinta na motsi.

A razane ta tashi zaune, ta kunna fitila tana waige waige.

Sedai ta ga komai normal, har wani gumin wahala ta fara, ta kasa bacci se zazzare ido, sedai da yake bacci ɓarawo ne, ya kwashi Nana tana daga zaune ba tare da ta shirya ba.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un!" shine abunda ta furta lokacin da ta diro da kan gadonta, tai waje da gudu ta nufi ɗakin Sadik, saboda mummunan mafarkin da tai akan film ɗin.


Ya cire kaya, daga shi se gajeren wando ya saka rigar wanka, ze wanka dan ya kwanta se gata kamar an jefota tana haki.
"Ke meye haka?"
Kamar za tai kuka tace "tsoro nake ji"

"Tsoron me?"

"Wani abu ne a ɗakina yake tsorata ni"

"Kuma ni seki zo min nan, fitar min daga ɗaki"

Hawaye ya cika idonta tace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi tsoro nake ji"

Tsaki yai ya gyara rigar wankansa ya nufi hanyar banɗaki ai kuwa ta bishi.

Ya tura ƙofar banɗakin ze shiga, nan ma ta biyo shi.

"Au banɗakin zaki biyo ni? Dama so kike ki ganni tsirara kenan, to bismillah shigo"

A dirirce tace "yi haƙuri, ni ba biyoka zan ba, akan me zan ganka tsirara? Ni tsoro nake ji ne"

Ta nemi guri ta tsaya a waje, se haki take. tsaki Sadik yai, ya shige banɗakin.

A ƙofar banɗakin ta tsuguna, tana ta haki jikinta yana rawa.

Ya gama wankansa ya fito sanye da rigar wanka, ya ga yadda take jujjuya idanu.

Shi dariya ma ta so ta bashi, horror film ne ya sa ta zama haka, ga iya rashin kunya ga uban tsoro.

Ya sa kayan baccin sa, ya nufi kan gado ze kwanta, nan ma ta bishi.

"Ke wai uban me zan miki ne? Ki fita ki koma ɗakinki ba zan kwana ɗaki ɗaya da ke ba"

Har da hawaye tace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ina ga wannan yarinyar ce a ɗakina, ta film ɗin ɗazu"

Sadik yace "Wai wa ya gaya miki film gaske ne?"

"Wallahi motsi naji a ɗakin"

Sadik ya ɗan taɓe baki yace "seki kwanta a ƙasa, dan ba zan baki pillow ba, da pillow biyu nake amfani"

"To ka bani bargonka, se in shimfiɗa a ƙasan"

"Baki da hankali" shine amsar da ya bata ya kwanta.

Haka ta duƙunƙune a cikin hijjabinta, tana karanto duk Addu'ar da ta zo bakinta.

Cikin dare Sadik ya farka ya ganshi ba a cikin bargo ba, yana kunna fitila ya ga ta ɗauke bargon da filillukan ta barshi a haka, yana can yana bacci.

Seda ya kusa zagi, ya sa hannu ze fincike bargonsa daga jikinta, amma hakan ya sa ta farka a matuƙar razane, kamar numfashinta ze ɗauke.

Tunda Sadik yake be taɓa ganin mutum me tsoron tsiya irin Nana ba.

"Dan kin raina min hankali, shine kika janye min bargo da fililluka?"

Se ya lura kamar a gigice take gaba ɗaya, se maida numfashi take, sam ba ta jin me yake cewa, yaga idan ya matsa kar ta zo ta haukace masa, ƙarshe se ƙyaleta yai.





Faruk ana idar da sallar Asuba, yaje ya samu Mother yai mata sallama, sedai a wannan karon ma se da tai kuka, Faruk akwai biyayya tai masa Addu'a ta fatan Alkhairi, Abba ds Usman ne zasu kai Faruk airport, suna shirin tafiya Khairat ta fito, idonta jawur alamar tayi kuka.

Faruk ya sakar mata murmushi yace "Khairat, ko zaki bini ne?"

Ta girgiza masa kai tace "Allah ya tsare"

Yace "Ameen Bloody na, am gonna Miss you my chef, zan missing girkin ki wataran me daɗi wataran jagwalgwalo"

Su Abba su kai dariya, daga nan suka shuka shiga mota suka tafi.

Ta daɗe a gurin a tsaye, tana tunani kan ta koma cikin gida.



Zuciyar Farhan ta kasa gazagata cewar Sadik ya barta, tana ji a jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login