Showing 87001 words to 90000 words out of 259198 words

Chapter 30 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

Abincin kirki.


"My boy, ya akayi ne naga baka cin Abincin ina fatan ba matsala?"

Sadik yai murmushi yace "bakomai Abba"

"Yayi kyau, ya shirye shiryen exams kuma?"


"Alhamdilillah Abba, mun kusa farawa soon Insha Allah"


Abba yace "that's good, Allah ya bada sa'a, and ina nan ana nema maka admission, an duba min nan Lund University a swiden, Alhaji Ayuba yace ; makarantar ta na da kyau sosai, amma se nan da 6_7 months sannan zasu fara bada admission, kaga kan lokacin exams ɗinka ta fito"

Sadik ya kalli Abba kamar yai magana, amma kwarjinin mahaifinsa ya hana shi yin Maganar, ya haɗiye maganar da yake son yi ɗin, yai murmushin fole.

Aka cigaba da cin abinci, ana hira ban da Sadik da abun duniya ya addabe shi.







Lilly na Office ɗin Sir Nazir, tana ta zuba taɓararta son ranta, shi kuma yana binta ido yana murmushin.

"Sir yaushe zaka zo Gidan mu ne?"

Ya ɗan zaro ido yace "kefa kika cemin gidanku akwai sojoji, so kike in zo su zane ni kenan?"

Lilly tai dariya tace "ba abunda za suyi maka fa, kuma ma ba sa nan se guda ɗaya, ni ka ɗaice a gida, idan na koma kaɗaici ne ke damuna"

"Kuma kawai se in zo muku gida?"

Ɗan tsuke fuska tai tace "ba fa ka taɓa zuwa ba sedai muyi waya, ni dai dan Allah ka zo Gidan mu"


"Kai Lilly, ina jin tsoro gaskiya"


Yana son yarinyar nan matuƙar so, sedai yasan ko da wasa be isa ya tunkari gidansu yace yana neman Aurenta ba, dan zaren ba kalar yadin bane.


"Au kenan baka damu dani ba ko? Nika ɗai nake sonka da nice ai zanje in da kake" tai maganar a shagwaɓe.

"Common baby, you know i love you mana, but akwai risk inje gidanku Fatima, ban san wace karɓa za'aimin ba"

"Nace maka fa ba kowa a gidan, kawai ka zo muyi hira ka tafi, amma shikenan"

Ta juya zata tafi ya riƙo hannunta yace "haba Zahrah na, ba haka bane"

"Dan Allah ka zo please" tai Maganar ta na kallon ƙwayar idonsa.

Ajiyar zuciya ya sauke yace "in dai hakan ze saki farinciki, zan zo Insha Allah"


"Yawwa I love You dear" tai Maganar tana kwanciya a jikinsa.

Kamar gunki haka ya ƙame, yana kallon Lillyn.

Ta ɗago ta kalleshi ta kai hannunta kan gemunsa, da ke matuƙar burgeta.


Kasa ko motsi yai daga in da yake.

Cikin wata irin kasalalliyar murya tace "Ban san iya farincikin da zan ba idan ka zo Gidan mu"

Hannunsa ya kai ya ɗora akan nata tattausan hannun, yana jera ajiyar zuciya, tare da lumshe idon sa.



Babu zato babu tsammani aka turo ƙofar, yanayin da suke ciki na kasala be basu damar yin zafin nama, gurin sakin junan su ba.



"Innalillahi wa innalillahi raji'un!"




Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

Dan Allah a biya kan a karanta.

Ayshercool
07063065680.
                                 



Wasa wasa ta cigaba da jin wannan baƙon yanayin yana bijiro mata, yanayi da bata taɓa shigarsa ba, a hankali take juyi akan katifarta, ta janyo pillown ta, ta rungume shi gam tana ajiyar zuciya, ƙasan zuciyarta tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta.

Sannu a hankali bacci ya kwashe ta, sedai baccin nata be je ko ina ba ta fara ganin Sadik a baccinta, yana sumbatar ta kamar yadda ya faru a gurin partyn nan.

Baccin nata be tsayi ba ta sake farkawa, mamakin yanayin da ta shiga takeyi, harta fara tunanin ko wani abu ne ze sameta? Sedai ta kasa mantawa da mafarkin da tai da Sadik ɗin.

Ɓangaren Sadik ma hakan ne ya kasance, juyi yake bacci ya gagari idanunsa, saboda abunda yake damunsa gashi ya rasa yadda ze iyayensa su fahimce shi, ko yanzu yai Aure yana da abun riƙeta, mahaifinsu ya gina ƙatuwar plaza me hawa uku, kowacce tana da shaguna goma sha biyu, kowa yana da hawa ɗaya, wato shaguna goma biyu.

Banda sauran kadarori da yake siya yana ajiye musu, mahaifiyarsa yakamata ta fara fuskantar sa amma taƙi bashi goyon baya, balle ta taya shi neman izni agurin mahaifinsa, kullum zancensu da lissafin su, University ɗin da ya dace su turashi a ƙasar waje yayi karatu.

Yana zuwa nan a tunaninsa yaji tamkar ya ɗora hannu a ka ya fasa ihu, haka wannan dare ya kasancewa Sadik, rabi bacci rabi tunani.


Ƙarfe ɗaya da rabi na dare, amma Fatima Hakeem wato Lilly, tana kwance a kan gadonta, tasa earpiece tana sauraran Audion wani littafi.

Babu wani cikakken ma'ana da littafin ke ɗauke da ita, face zunzurutun batsa yadda ake fayyece abubuwan da a shekarunta sun yiwa ƙwaƙwalwarta girman gaske.
(Sedai yaran na ƙarshen zamani, ko ba a littafi ba sun san komai, yara ƙanana masu ƙananan shekaru, sedai rubuce rubucen mu na ƙara taka muhimmiyar rawa gurin buɗe Musu abunda be kyautu ace sun sani ba)

Shiru tai tana lumshe ido, tana sauraran yadda me karantarwar shima ya ƙware gurin karantowar ba kunya ba tsoron Allah.

Duk abunda take saurarar nan ba wanda yake mata yawo a zuciyarta irin malaminta Sir Nazir, saboda a siffofin zahiri da ake faɗa a littafin yana ɗauke da su.

A hankali ta sake lumshe idanunta, tana ganinsa a cikin idonta lokacin da take zaune a Office ɗin sa, a hankali tai wani tattausan murmushi, tare da ɗan taune leɓɓanta na ƙasa.


A haka gari ya waye, zukatan matasan yaran kowa da abunda yake saƙawa, da tunanin hanyar samawa kansa mafita.

Assembly ground ya cika maƙil, an gama National Anthem, Madam Joy tai wa Prefects Umarnin yin inspection, suka fara kewaya ɗaliban suna duba wanda suka yanke farce da wanda ba suyi ba.

Salma ce ke duba na 'yan ajinsu Farhan, ta zo kan Farhan, Farhan ta miƙa mata yatsunta dan ta duba, sedai Salman ta kama hannun Farhan ta riƙe tana murzawa a hankali tana mata wani irin murmushi.

Mamaki ne ya kama Farhan, ganin abun banbarakwai, ƙoƙarin zame hannunta Farhan take, amma Salma ta riƙe kam, cikin murya ƙasa ƙasa tace "dagaske wancan yaron saurayin ki ne? Sadik yake ko wa?"

Shiru Farhan tai mata ta cigaba da ƙoƙarin ƙwace hannunta.

"Yarinya wancan ba abunda ze tsinana miki, yazo yana min ihu a kanki, ki fita a sabgarsa ni zan baki abunda be ze iya baki ba, Just be my lover"

Wani irin kallon mamaki Farhan ta bita da shi, kamar ya lover tsakanin mace da mace.

Ta sake murza hannun Farhan a nata tace "kina da kyau Baby, ina sonki"

Ta ƙarasa maganar tare da sakin hannun Farhan.

Bayanta Farhan tabi da kallo tana mamakin wannan baƙon lamari haka.

Sir Nazir shima ya cigaba da zazzaga ɗaliban, ya biyo ta layin da su Farhan ke tsaye, yana doso in da suke Lilly ta Soma bin sa da wannan idanun nata, yauma ba ƙaramin kyau yai mata ba, yana cikin kayansa na Bautar ƙasa, wando da farar shirt ɗin nan, se ƙamshin turare yake, kasancewar safiyace yayi wani fresh da shi.

"Face Your front" ya faɗa a hankali lokacin da ya ƙaraso in da Lilly ke tsaye.

"You look good" ta faɗa lokacin da ya ɗan gota ta, ya waigo ya kalleta amma ta maze kamar ba ita tai maganar ba.

Farhan Kuwa abun ya ɗaure mata kai, duk jarabar Sir Nazir da kwarjinin sa, amma Lilly take binsa da wannan kallo haka.

Aka kammala Assembly aka watse, period ɗin farko Sir Nazir ne ze shiga ajinsu Lilly, dan haka kan ya shiga ta samu brush ta taje yalwatacen gashin girarta, ta ƙara mai a leɓenta, kamar me shirin tarbar wani.

Yasmin ta kaalleta tace "ban gane ba wannan gyare-gyaren fa? Naga kina wani ƙara lip gloss"

Lilly tace "tarko zanyi in hana wani nustuwa, kamar yadda......ta hana...... Nutsuwa a littafi......"

Yasmin tace "shegiyar gari, Allah ya shiryeki"

Lilly tai murmushi ta sake gyara zama sosai.

Tun daga waje ta fara jiyo maganarsa, ta sake gyara zama ta nustu.

Ya shigo ajin da sallama kamar yadda ya saba, suka amsa tare da gaishe shi.

Ya amsa a nutse, ya fara ƙoƙarin gabatar da abunda ya kawo shi, sedai da ya ɗaga ido se yaga Lilly na kallonsa, nan da nan yaji yana neman rasa nutsuwarsa, ya rasa meyasa yarinyar nan ke masa haka.

A hankali ya taka gaban White board, yasa blue ɗin marker, ya rubuta sunan subject da kuma kwanan wata, ya rubuta Respiration, ya ja layi, ya waigo ya fuskanci ajin, cikin turancinsa me iyayi yace "before we proceed, can someone Among you briefly remind us what we discussed, in our previous class?"

Class captain ne ya miƙe, yai bayani ya zauna.

Nazir yace "thank you Class rep, you really try, can anyone add something?"

Tsit ajin yai kamar ruwa ya cinyesu.

"Fatima Hakeem, stand up and said something"

Gaban Lilly ya faɗi, dan ba ta da abun cewa, ga turanci ya zauna a bakinta, amma fa batun wani karatu a aji ba yi take na dan be dameta ba, su goma me a ajinsu, ta takwas ko tara take zuwa, ba wani damuwa tai da karatu ba.

"Am talking to you" ya faɗa a ɗan hasale.

Miƙewa tai tana kumbura baki, tai tsit.

Ya sake maimaita tambayar, amma tai masa shiru.

"Get out from my class, daƙiƙiya Kawai baki iya komai ba se ciye ciye da surutu"

Abun ya tsaye wa Lilly a rai, tai ƙwafa ta juya ta fita ba tare da ko bada haƙuri ba.

Seda ya kori Lilly sannan ya samu Nutsuwar gabatar ds lesson ɗin yadda ya kamata, sedai harya kammala lesson ɗin tana ransa.

Seda ya cinye time ɗin sa cif, lokacin dai dai da buga jiniyar fita break, ya tattara litattafansa ya fita.

Yana fita ya ganta a kan barandar Class ɗin.

Ya kalleta yace "idan kika wuce mintuna uku baki zo ba, i will punish you"

Murguɗa masa baki tai, ta juya ta shiga aji, yabi ta da kallon mamaki.

Tana shiga ajin Yasmin ta hau dariya tace 'haba jaruma ya aka ƙarke da korarki?"

"Ƙyaleshi dani yake zancen ai"

Farhan kam se binsu take da kallo.

"Sssssss"

Ko ba a gaya mata ba ta san Sadik ne kuma da ita yake, ɗan murmushi tai amma taƙi waigawa.

Murmushi yai ya shigo ajin ya ƙaraso in da take zaune, amma tai saurin kifa kanta akan benci tana murmushi.

"Tashi ko in ɗago ki"

Da sauri ta ɗago tana murmushi, ya ɗan ƙura mata ido, yace "ina son murmushin ki Farhan"

Sunkuyar da kai tana murmushi.

Sedai me ji tai yadda ya zauna a kusa da ita ɗin nan, wannan yanayin yana bijiro mata, ya zuba mata dukkan idanunsa, ita kuma ta kasa motsawa.

"Tashi muje ajinmu, Yaushe rabon da kike in da nake, kullum sedai in zo"

"Ni bana son Zuwa ajinku"

"Meyasa, nima bana son zuwa nan, 'yan ajinku suyi ta kallona ko haushi ba kya ji, tashi mu tafi"

Ba musu ta miƙe ta bishi.

Suna zuwa ajin su Sadik Amin ya kallesu yace "A'a Amaryar Sadik, an gujemu, amma dai gashi nan ya ɗakkoki"

Wani kallo Sadik yai masa, hakan yasa ya tsuke bakinsa.

Suka zauna a gurin zaman Sadik, yace "me zamu ci ne My dear"

Yadda yai maganar yana binta da kallo yasa taji ta duk wani iri, tace "bakomai"

"A'a da komai ina zuwa, bari inje in dawo, ungo wayata ki game ko kallon hotuna kan in dawo"

Ba musu ta karɓi wayar shi kuma ya fita.

Yana fita Taslim da Meena suka shigo, suka samu guri suka zauna.

Meena ta sa hannu a jakarta tace "Taslim Allah yasa wannan ƙwayar tafi wadda nake sha, ina son cakewa Sosai"

"Mubarak baze baki abunda ba yayi ba, amma dai ki kula, dan kar su saki hauka wallahi dan naga baki da wani aiki se wannan"

"To Taslim ya zanyi, kullum gida ba daɗi, baka da ikon ƙwaƙwaran motsi, idan na sha na shige ɗakina nai luf, ba wanda ya sani nikaɗai nake cakewa ta"

Taslim tace "ke dama kince ba kya iya karanta littafi a waya, na samo Audion a gurin su Lilly, bari musa ki fara jin abunda yake wakana"

Meena tace "to sa inji"

Kasancewar daga su se Farhan a ajin yasa da suka kunna kowa yana jin me ake cewa a Audion.

Abunda Farhan ke gujewa kunnuwanta ji a ajinsu, shi ake karantowa a nan, ita da take game a waya amma seta rasa ina ma zata taɓa tai game ɗin.
Wannan karon kasa tashi tai dan tsira da kunnuwanta daga jin wannan Narkakkiyar baɗala, a hankali ta kifa kanta taji yadda tsigar jikinta ke tashi, numfashinta har wani sama yake.

Sadik ya shigo hannunsa da leda, yazo ya zauna, yace "Sorry na daɗe ko?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Ga Abinci juyo in baki a baki fa kaina.

Noƙe masa kafaɗa tayi, yace 'sarkin kunya, ga naki nan in kin koma aji kya ci.

Ya ɗakko wayarsa yasa earpeice ya hau kallon film.

Ya barta da wayarsa ɗaya a hannun ta, sam hankalinsa be kai kan abunda su Taslim suke saurara ba, amma ita kunnuwanta sun jiye mata.

Nan da nan tunanin Farhan ya nemi ya birkice, jin abubuwan da ko kusa ba ta taɓa kawosu ba, kallon Sadik tai taga ko yana jin me suke saurara, amma taga hankalinsa baya kai.

Da ƙyar ta aro jarumta, ta ajiye masa wayarsa tace "zan tafi Class"

Ya kalleta a shagwaɓe yace "haba dai, yanzu fa kika zo"

"Ai karatu zanje inyi" tai maganar tana kallonsa.

"Wai ya naga duk kin wani canza ne? Meyafaru?"

"Bakomai" ta bashi amsa.

"A'a da komai, kalli ƙirjinki yaddada kike numfashi fa"

Hararsa tai tace "Nika matsa in wuce"

"Aikuwa sedai ki tafi ke kaɗai bazan rakaki ba"

"Eh naji ɗin" tai maganar cikin shagwaɓa.

Binta yai da kallo yadda take tafiya jikinta na juyawa.

Murmushi yai yace "i love Your dramas"

A hankali take tafiya, cike da wata irin matsananciyar kasala, da ruɗanin tunani, Tana tafiyar kawai taji an riƙo ƙugunta, a razane ta waiwayo kawai ta ga Mubarak babba.

'beb ya akai ne?"

"Meye haka ka cika ni"

"Anƙi a cika ki ɗin, abunda ki kaiwa wancan banzan a gurin birthday zaki min nima, munafuka kiyi ta nuna ke ta Allah ce, ashe 'yar hannu ce"

Mutsu mutsu ta fara yi "nika cikani bana so"

Ƙoƙari yake ya haɗata da jikinsa kamar yadda yai mata kwanaki.

Sedai dai gaba ɗaya ba ta da wani kuzari a jikinta, da ƙyar ta aro jarumta, ta kai masa yakushi a fuskarsa wajen idonsa, ba shiri ya saketa ta arta a guje zuwa aji tana haki.

Lilly Kuwa yau har taje tana kwafar note ɗinta ba ta kulashi ba, shikam se satar kallonta yake, yadda ta cuna baki ne ma ya bashi dariya.







Kamar yadda ya zamewa Nana jiki, ta fito daga wanka ta tsane jikinta, ta ɗakko humrarta me ɗauke da muski da alumun a ciki, wanda Inna ce take haɗa mata da kanta.
Mudubi ta ɗakko ta tsaya tana haska hammatar ta.

Ta window Inna ta hangota, tai gyaran murya.
Da sauri Nana ta sauke madubin ƙasa.

"Me kike dubawa a hammatar?"

Cike da ƙuruciya Nana tace "Inna wai ni yaushe gashi ze fito min a hammata?"

Inna tace "Rai dai 'yar nan wai an fillewa fara kai, ai ba sekin matsu ba, yana nan tafe da gaggawa, duk ga alamomin balaga nan a tare da ke shima yana nan tafe"

"Haba Inna waike ki ta faɗar wannan kalmar dan Allah"

"Au to kar in faɗa? Ke fa kika fara tambaya na baki amsa"

"To shikenan dai a bar maganar"

"Ai ba za'a barta ba, sena kai aya, shi wannan abun da kike burin ya fito idan ya fito ɗin ba kya gyarawa, to za'a samu gagarumar matsala, kinga idan yana fitowa ba kya askewa kina barinsa cunkus a ciki kamar gonar gyaɗa, duk wankan da zaki ba zaki dena wari ba, idan ke ba kya ji na kusa dake zeji, saboda da kinyi gumi ne lamari ze ɓaci, ko kin sa turare zakiji ƙamshin daban warin daban.
Haka shima na ɗaya gurin idan ya fito ba'a kula da shi, abunda ze faru kenan"

Nana ta kalleta tace "na wani ɗayan gurin?"

"Na ƙasan mararki" Inna ta zage ta dinga bayani, seda Nana tai dana sanin ɗakko zancen nan, sam Inna ba ta jin kunya haka take buɗe zance.

Ƙarshe Nana ta miƙe tasa kayan Islamiyyar ta tai sallama zata tafi.

Inna tace "to a kula da kai, banda biyewa ƙawayen banza, kar wani ya tsaida ke a hanya ki tsaya, banda wasan banza da shirirta a makaranta ki kama kanki, karatu kika je yi, ki kula kar inji kar in gani"

"Inna duk fa na haddace wannan karatun naki"

"Ai gara in dinga tisawa, kar ki manta wani abun, Allah ya tsare"

"Ameen" ta miƙa ta fita.




Wasa wasa har zuwa tashi daga Makaranta, Farhan ta kasa sarrafa ƙwaƙwalwarta akan tunanin da Yakamata tayi, yau abubuwa da dama sun ɗaure mata kai, ba dan Soyayyar Sadik da ke da matuƙar tasiri a zuciyarta ba, da barin makarantar nan za tayi ta huta, abubuwa sun sakota a gaba da yawa, kuma ha ba abokin tattaunawa.

Ta rasa meta tsarewa da dama daga cikin 'yan makarantar nan suke takurata haka, ga uwa uba abunda taji a ajinsu Sadik, da shi yafi komai dagula mata lissafi da ɗaga mata hankali.

Da aka tashi jiki a sanyaye ta ɗau jakarta ta fara tafiya, sedai ta kasa sauri saboda wata irin kasala dake nuƙurƙusarta, so take ta tafi tun kan Sadik ya ganta yace sedai su tafi tare.

Sedai me tana tahowa ta hangi Mubarak Babba ya tsaya a hanya, ya zubo mata ido, da gudu ta kasa tai hanyar ajin su Sadik.

Cikin sa'a tai karo da shi a hanya.

"Farhan gudun ne kike?"

"Bakomai" ta bashi amsa.

"A'a da komai, guje guje ba halinki bane, ki gayamin meke faruwa"

"Bakomai fa"

"Shikenan muje" ya sata a gaba suka tafi.

Suna fita taga babba a waje a jikin tasu Motar shi da Taslim.

Ƙura mata ido yai, ta ɗauke kanta daga kallonsa ta shiga Motar su Sadik.

"Nifa na kasa gane kanki beb, what's wrong ne?"

"Na fa ce maka bakomai".

Yace "shikenan" dan baya son cigaba da matsa mata.

Seda suka fara tafiya sannan ta samu nutsuwa sosai, sedai me kasancewar sun zauna daf da juna ita da Sadik, se take jinta wani iri.

Kallonsa take ta ƙurawa fuskarsa ido, wanda seda hakan ya bashi mamaki.

"Why are you acting so strange, me kike kallo a jikina kuma?"

Kallon direban tayi ta kalli Sadik tai murmushi tace "ni ba kallon ka nake ba"

"Ƙarya nake kenan?"

Ta ɗaga masa gira, murmushi yai ya kwanta a jikin seat ɗin motar yana kallonta.

Da haka suka ƙarasa in da take sauka, ko sallama ba tai masa ba ta sauka ta shiga layin gidansu.

"Farhanatuwa 'yan makarantar bokoko"

Waiwayowa Farhan tai ta ga Sunusi a tsallaken wata kwata yana wankin kaya, yasa wani koɗaɗen yadi.

Ɗauke kai tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login