Showing 135001 words to 138000 words out of 259198 words
Chapter 46 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
me tana shawowa kwanar gidan, ta tarar da cincirindon mutane a gurin, sunyi cirko cirko, duk da juma'a ce anyi sallar juma'a amma yanayin yadda taga mutanen hankalimta ya sake tashi.
Nan take gabanta yai mummunar faɗuwa, jikinta ya ɗau rawa numfashinta ya shiga barazanar tsayawa.
Da gudu ta nufi gidan tana ture mutane, hawaye na bin fuskarta.
(RIP ALHAJI ALIYU MAMMAN RANO (HAKIMI)
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Kutsawa kawai Nana take tana kuka, yayin da dandazon mutanen ke binta da kallo, kamar wadda ta zare.
Da gudu ta kutsa ta shiga, sedai tai turus saboda kasa banbance Alhini mutanen ke yi ko kuma farinciki.
Turakar Hakimi ta nufa, ta shiga da sauri.
Hango shi tai a zaune, ya sha fararen kaya da naɗi, sedai kana ganinsa ka san yana jin jiki ne.
Runhumeshi taje tayi tana kuka tana faɗin Alhamdilillah, Ka ji sauƙi? Ka warke?"
Yayi tari yace "Da sauƙi Alhamdilillah" ajiyar zuciya ta dinga saukewa, ta ɗaga kai ta kalli jama'ar da ke ɗakin.
Se a yanzu ta kula da Abba, da Faruk a zaune, gefe ga Inna se Sadik dake zaune, idonsa yai ja kamar garwashi.
Se da gabanta yai mummunar faɗuwa ganin idanun Sadik ɗin, kamar ba idon bil adama ba.
Wani irin matsiyacin kallo Sadik yaiwa Nana, wanda ya hadda sa mata ƙullewar ciki saboda razana.
Cikin ƙullewar kai Nana tace "Inna wai me ake a gidan nan?"
Inna tace "ba zaki gaida baban naki bane"
Jiki a sanyaye Nana ta kalli Abba tace "Ina kwana"
Jiki ba kuzari Abba yace "ina wuni dai ko"
Nana tace "eh ina wuni"
Yace "lafiya ƙalau Alhamdilillah"
Hakimi yai tari, sannan yai gyaran murya yace "Alhamdilillah ala kulli halin, dukkan godiya ta tabatta ga Allah, Abdullahi" ya kira sunan Abba.
"Na'am ranka ya daɗe" Abba ya amsa yana risinawa.
"Ka sani ban yanke wannan hukuncin ba, se da na nasan ina da ƙwararan dalilai na, kar ka kalli abunda nayi a matsayin cin zarafi ko nuna maka baka isa da iyalinka ba, Komai nayi nayi shine da dalili, ko bayan raina ban yadda wani abu ya samu Auren nan ba, Nana amana ce itama 'yarka ce, kuma marainiyar Allah, dan Allah a kula da Amana, sannan ka jawa ɗanka kunne a kanta"
Ya kuma yin tari sannan ya kalli Sadik da ke ta ajiyar zuciya yace "Abubakar, na san na maka ba daidai ba, amma ka sani duk abunda babba ya hango ko yaro ya hau rimi ba ze hango ba, ban ɗau wannan hukuncin dan cuzgunawa rayuwarku ba, sedai ba zan zuba ido wani abu ya ratsa ta cikin iyalina mara daɗi ba, nasan ko bayan raina nan gaba zakayi Alfahari da hukuncin da na yanke, kaga kamar yadda kuke iƙrarin kun tsani juna, kaga se ku kashe kanku in kun ga dama, duk wanda ya ƙoƙarin raba abunda na ƙulla, ban yafe masa ba, Allah ya baka damar Auren mata huɗu, nan gaba in kana buƙata ka iya ƙarawa, amma ban yadda ka wulaƙanta 'yar uwakka ba"
Zare ido Nana tai ta miƙe daga jikin Hakimi tace "Wai Auren wa akayi? Wa kaiwa Auren?"
Inna ta daka mata tsawa tace "rufe mana baki ki, nemi guri ki zauna"
"Inna a ina zan zauna, wai meyafaru ne?"
Duk da jikin Hakimi ba ƙwari, haka ya janyo Nana ya zaunar da ita a kusa da shi, yace "kalli cikin idona"
Ba musu ta kalli idonsa, take taga yai mata wani irin kwarjini, jikinta ya hau tsuma, Hakimi yace "Zaki bi Abubakar turai karatu, kema a can zaki ƙarasa naki karatun"
Cikin rashin fahimta tace "Alhaji meyasa, ni fa bance maka zani ba"
"Saboda na yanke hukunci, na Aurar da ke ga Abubakar Abdullahi Rano, ɗan uwanki"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un! Alhaji laifin me nai maka, meyasa zaka ce haka?, in bishi turai banda uwa banda uba se Allah se ku, idan ya cutar dani fa?"
"Baze cutar da ke ba, muma kuma ba zamuyi abunda ze cutar da ku ba"
Fizgewa tai daga jikin Hakimi jikinta na tsuma tai hanyar waje, Inna tace "ku riƙeta karta fita" ai kan ta gama Magana Nana ta kasa da gudu tai waje, Faruk yabi bayanta, tana zuwa babban soro ta faɗi ba tare da sanin in da kanta yake ba.
Tunda garin Allah ya waye, Farhan ke wani irin matsanancin faɗuwar gaba, har idan zuciyarta ta buga seta dafe ƙirjinta, ta koma fizgo numfashi da ƙyar.
A hankali take shirin Makaranta, tana yi tana jin wani irin tsoro da fargaba suna shigarta.
A makare ta isa makaranta, gaba ɗaya har aka gama lesson ba ta fahimci komai ba.
Sannu a hankali take tafiya, tana tafiya tana jin Kamar numfashinta ze ɗauke har ta isa gida, Umma sarai ta lura da yadda Farhan take komai sanyi sanyi, amma ba ta tambaye ta meya sameta ba.
Farhan Ta ɗauro Alwala, ta zo ta tada salla, ta kai raka'ar farko da kyar, ta miƙe zata kawo ta biyu ta faɗi a gurin.
Kasancewar duk ƙannenta sun tafi Islamiyya, Umma kuma tana cikin ɗakinta, dan haka babu wanda ya san meyafaru.
Ko motsi ba tayi balle numfashi, tana ƙasa kawai a kwance.
Su Amira ƙannenta suka dawo daga Masallaci, suka ci Abinci amma ba su ji motsin Farhan ba, kasancewar sun sa ba me son hayaniya ba ce, ga ta da son bacci dan hala suka ƙaddara bacci kawai take.
Wajen la'asar Huzaifa ya zo gidan, a tsakar gida ya tarar da Umma suka gaisa, yace "Umma Ina Yaya, ta zo taga sabuwar wayar da na siya, ta sa mun Albarka"
Umma tai murmushi tace "tana ɗaki"
Hauzaifa ya shiga ƙwala mata kira yana "Waliyya zo kiga sabuwar wayata" amma yaji shiru.
Yai knocking ƙofar ɗakinta yace "in shigo?" Amma shiru.
Ya ɗaga labulen ɗakin, ya ganta a kwance akan sallaya kamar ba rai a jikinta.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Umman Farhan zo ki ga" yai maganar yana nufar in da Farhan ke kwance.
Da Sauri Umman ta tashi tana faɗin lafiya.
Tana zuwa ta tarar da Farhan a kwance, tazo ta taɓa ta taɓata amma babu alamar motsi a tare da ita.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Huzaifa kamar fa ta rasu ne"
"A'a Umma ba ta mutu ba, tana da rai"
Umma ta girgiza kai tace "kalli fa ba in da yake motsi a jikinta"
Huzaifa ya fita da gudu, ya ɗebo ruwa yazo ya shiga shafa mata a gishinta zuwa fuskar ta.
Tai yunƙuri Kamar za tai numfashi, amma ta kasa.
Yace "Umma kin gani, mu kaita Asibiti"
"Ni ina naga abun hawa, kawai ka kira baban ta a waya ka sanar masa"
"Umma idan akace se Abba ya dawo ai abun ze zama worst, bari in fita neman abun hawa, kiyi tai mata fifita.
Ƙannen Farhan suka kewaye ta suna kuka, Amira na mata fifita, Umar na karanta mata Alqur'ani.
Kai tsaye gidan Hajiyar nan Huzaifa ya nufa, saboda yana fita yaga mota a tsaye a ƙofar Gidan.
Sallama ya shiga kwaɗawa, ta amsa ta bashi iznin shiga.
Tana ganinsa ta gane shi, ya tarar da ita da babban ɗanta, shine ya zo da mota Gidan.
Nan Huzaifa ya gayamata abunda ke faruwa, nan da nan hankalinta ya tashi, ta ɗau hijjabi tabi Huzaifa.
Tana zuwa ta tarar da Farhan, a mawuyacin hali.
Hajiya ta hau faɗa tace "ni tun ba yau ba na fuskanci yarinyar nan ba ta da lafiya, tayi rama sosai ba ta da kuzari"
Ta kalli Amir tace "maza jeka gida ka kiramin Daddyn Arham kace nace ya taho da motarsa ƙofar Gidan nan.
Nan suka fara ƙoƙarin ɗaga Farhan, amma abu ya gagara saboda Farhan na da jiki, kuma gaba ɗaya jikin nata ya saki.
Hajiya da kanta ta leƙa, tacewa ɗanta ya zo ya temaka musu.
Yana zuwa ya ɗaga Farhan, Kamar ya ɗau karauni haka yai waje da Ita.
Hakan yai daidai da zuwan Sunusi, dan ganin meke faruwa yaga mutane a ƙofar Gidan su Farhan.
Yaga an fito da Farhan, hijjabin ta ya ɗage sam bata hayyacinta, amma babban abunda ya dame shi ba rashin lafiyar bane, illa ɗakkota da ya ga wani ƙato yayi.
Maimakon Umma tabi su Hajiya, tace ba zata bisu ba, ta bawa Huzaifa kuɗi tace ko za'a buƙaci wani abun, ga kuɗi nan kan babanta ya dawo.
Da sauri Sunusi ya ƙaraso, sedai kafin ya ƙaraso tuni sun ja motar sun tafi cikin hanzari.
Amir ya samu a tsaye yana kuka a ƙofar gida, ya kalleshi yace "Kai meya samu yayarka?"
Amir yace "ba ta da lafiya, suma tayi an tafi Kaita Asibiti"
"To waye wancan da ya ɗakkota?"
Amir yace "nima ban sani ba" daga nan ya jiya ya shige cikin gida.
Sunusi yai shiru yace "ko dai shine Sadik ɗin?" Se kuma ya tuna Sadik be kai wannan jiki da tsayi ba, kuma a Muryar Sadik da ya ta ɓa ji, akwai yarinta a muryarsa, amma wannan babba ne sosai.
Umman Farhan kuwa tai zuguum a gida, tana tunanin meya samu Farhan haka.
Suna tafe a mota ɗan Hajiya yace "Hajiya wai meya samu yarinyar haka?"
Hajiya tace "Nima ban sani ba wallahi"
Huzaifa yace "ni a iya sanina ban ga tana rashin lafiya ba"
Hajiya tace "Ai ba kusa ba nesa ga Allah, Allah ya bata lafiya"
Kasancewar ɗan Hajiya wato Abbas likita ne, wani private Hospital ya kaita, Asibitin na abokin Aikinsa ne amma tare suke gudanar da Asibitin.
Suna zuwa aka bawa Farhan gado, aka fara bata taimakon gaggawa, da alluran da zasu taimaka mata.
Aka bar su Hajiya a reception, kusan mintuna Arba'in, sannan Abbas ya fito.
Hajiya tace "Abbas ya jikin nata?"
"Eh ta samu releif, mun ɗora ta akan drip, na rubuta teses an ɗebi jininta an kai lap, za'a duba".
"To Allah ya bata lafiya, meye bill ɗin a biya?"
Abbas yai murmushi yace "lallaima Hajiya, yanzu kawai seki biya"
Tace "eh mana"
Yace "to ni meye amfani na in har zaki biya? Wai ina mamanta ma, ina iyayenta naga wannan yaron ne kawai ya biyo mu, in sunzo se su biya kuɗin, an rage musu 30% saboda ke"
Huzaifa yace "ga kuɗi Umma ta bani, nawa za'a biya"
Hajiya tace "ƙyaleshi Huzaifa"
Ta kalli Abbas tace "Ina tausayin Yarinyar ne, ai ita ce nake cewa da zan maka mata ta biyu da ita, amma a kace an mata miji, ai 'ya ta ce"
Kawai Abbas ya hau dariya yace "wannan 'yar Yarinyar, da da wuri nai Aure ai na haife ta, wannan ai 'ya ta ce"
Hajiya tace "wallahi Yarinyar akwai nutsuwa, ga tarbiyya she's first child of her Fulani parent, so ba kulawa Sosai, yanzu haka in ka bibiya ta daɗe tana rashin lafiya basu sani ba, kuma maybe ba ta faɗa ba, tunda ba ta da magana"
Abbas yace "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, tunda 'yar ki ce shikenan ba se kun biya ba"
Se Wajen magariba, se ga Abba hankali a tashe ya isa Asibitin, ya tarar da Hajiya a Asibitin.
Suka gaisa Sannan yace "Naji labarin karamcin da ki kai mana, ubangiji Allah ya saka da Alkhairi yasa ki ɗauka a gidan Aljanna"
Hajiya tace "Ameen bakomai, ai yiwa kaine, bismillah muje ka ganta"
Suka nufi ɗakin da Farhan take, tana kwance an sa mata Oxygen, hannunta ɗauke da drip, harta faɗa Sosai fatar ta tayi wani iri alamar oxygen ba ta wadatar jikinta.
Ga SPO2 machine yana ta reading vitals ɗin ta.
Ganin halin da Farhan ɗin ke ciki, seda Abbanta ya firgita sosai, ya ƙarasa gaban gadonta, ya shafi gashin kanta da yake a hargitse yace "Allah kai ka halicce ta ka ɗora mata, Ubangiji Allah ka tashi kafaɗunta in ciwon na tashi ne, in bana tashi bane Allah kasa ta tafi a sa'a" yai maganar ƙwalla na taruwa a idonsa.
Hajiya tace "ka kwantar da hankalinka, insha Allah zata samu sauƙi"
Abbas ya shigo da file ɗin Farhan, suka gaisa da Abba, Hajiya tace "Abbas ga mahaifinta'
Abbas yace "Allah sarki, ai naga kama, Allah ya bata lafiya"
Abba yace "to nawa ne aka ce kuɗin Asibitin, in biya mu maida ita na gwamnati, naga wannan Asibitin na masu ƙarfi ne"
Hajiya tace "baka da damuwa da wannan, tayi sabon uba ai yace an mata kyauta" tai maganar tana nuna Abbas.
Hajiya tace "sedai batun wanda ze kwana da ita, naga ka taho kai kaɗai ina Umman nata?"
Abba yace "Ai ba zata zo ba, kin san ita ce ta fari, ina ga ni zan kwana a gurinta, zuwa da safe ƙanwata za ta zo se ta cigaba da kula da ita"
Abbas ya jinjina kai yace "Baba ba kai ya dace ka kula da ita ba, a wannan halin da take ciki, tana buƙatar kulawar uwa ne"
Abba yace "Ai da yake ita ce ta fari, kuma dangin uwar ba a garin nan suke ba, da za a samu me kula da ita, amma bakomai zan kula da ita"
Abbas yace "No ba za ai haka ba, muna da Nurses, za suyi mata duk abunda ya dace, zamu kula da ita"
Abba yace"haba ai wahalar se tai yawa, ba a ɗora muku nauyi da yawa bax
Abbas yace "karka damu, aikinmu ne ai, ka bari zuwa an jima ka tafi kawai, zamu kula da ita, Hajiya tai min kyautar ta ai, 'ya tace nima zan kula da ita, muna da ma'aikata wanda aikinsu ne"
Abba yai ta godiya, har seda Abbas yaji godiyar tayi yawa, ko Lafiya suka bawa Farhan iya godiyar kenan.
Nana kuwa ana ta fama amma ta gagara farfaɗowa, se surutai kawai da take da fizge fizge, se da aka dangana da yi mata rubutu da Addu'oi sannan ta dawo hayyacinta, a hankali ta kalli Inna, ta rintse idonta tana faɗin Allah ya sa ba gaskiya bane.
Inna tace "Nana kina jina?" Ta jinjinawa Inna kai alamar eh.
Tace "to ɗago ki kalleni"
Ta ɗaga kai ta kalli Inna, ta kalli ɗakin still ga Hakimi, ga Abba da Faruk sedai ba Sadik.
Ta miƙe zaune ta kalli kayan jikinta, tun Uniform ɗinta ne da ta dawo da su, tai shiru dan tayi tunanin gaske ne ko mafarki tai, amma komai ya dinga dawo mata tiryan tiryan.
Fashewa tai da kuka a gigice tace "dan Allah Inna kice min ba gaske bane mafarki nake, wallahi ban isa Aure ba"
Inna tace "ki saurareni da kyau, kina jina, Kakanki ya riga ya yanke hukunci, An aurar da ke ga Sadik, yanzu Sadik shine mijinki, ina son ki karɓi ƙaddara a yadda ta zo miki, Allah ya riga ya ƙaddara haka zata faru, dan haka kiyi haƙuri ki karɓe shi a matsayin miji, gobe in Allah ya kaimu zaku tafi, wataƙila a satin nan ko na gaba zaku tafi can ƙasar"
Kawai Nana ta fashe da kuka, tana wani irin sheshsheƙa kamar zata shiɗe, amma ta kasa Magana, se wani irin zazzaɓi ma da ya rufeta.
Abunda ya faru shine, Ranar Juma'a Abba da Faruk suka ƙaraso, suka tarar Likita yana duba Hakimi, saboda jikinsa da ya tashi.
Allah yasa zuwa sha biyun rana, aka samu ya ɗan samu sauƙi, Sadik yana ta murna yasan in Allah ya yadda wannan karon ze tafi gida, aka kawo masa sababbun kaya farare, aka ce su zesa, da farko abun ya bashi mamaki se yai zaton dan yau za'a tafi da shi ne.
Bayan idar da sallar juma'a, akace za'ai ɗaurin Aure a Masallacin, Sadik Alla Alla yake ayi a gama abunda za ai, su tafi.
Can aka fara ɗaurin Aure, yaji an ambaci Nana Asma'u, da Abubakar Abdullahi Rano.
Da fari be san wa aka ɗaurawa Auren ba, se daga baya ya fara tunanin wannan ai sunansa ne?.
Seda aka gama ɗaurin Aure, yaga Abba yana zufa, Faruk ya miƙo masa hannu yace ""burinka ya cika Auta, Allah ya Sanya Alkhairi ya baka wuyan ɗauka"
Zaro ido Sadik yai yace "wa aka ɗaurawa Auren?"
"Kai da Nana mana" ya bashi amsa.
A gigice ya nufi in da Abba yake, yace "Abba da gaske ni aka ɗaurawa Aure?"
Abba yace "Eh, kai aka ɗaurawa Aure"
Gigicewa Sadik yai, ya fara zazzaro ido "Abba meyasa? Meyasa za'aimin jaka? Meyasa za'amin Aure ba tare da sanina na?" Ganin ze tada hayaniya yasa aka sa dogarai sukai cikin gida da shi.
Nan da nan aka fara bushe bushe, Hakimi ya miƙe ze tashi, amma ya yanke jiki ya faɗi.
Aka ɗauke shi aka shiga da shi cikin gida, ana tunanin koma ya rasu ne, nan da nan aka dakatar da wannan busar da ake.
Se kuma daga baya cikin ikon Allah ya farka.
Gaba ɗaya Sadik ya fita hayyacinsa, yai kuka yai kuka har idonsa yai jawur, shi a lokacin nan da Hakimi ya mutu ma ba abunda ze ji, ya rasa laifin me yai musu suka tsane shi haka, ko Auren za'ai masa ai a bari ya zaɓi wadda yake so.
Magana ma ta gagari Sadik, se sheshsheƙa da ajiyar zuciya, wata muguwar tsanar Nana ta ƙara baibaye shi, ko ƙaunar jin an ambaci sunanta ba yayi.
Tun saura kwana biyu Abba su zo garin, Hakimi yace masa in ya tashi tahowa, ya taho da Sadakin ɗansa.
Abba sam ya zaci kawai barkwancin Hakimi ne, amma be taɓa zaton Hakimi zewa Sadik Aure da Nana ba.
Ba shi da ikon ja da maganar mahaifinsa, amma sam be ga tsari a wannan Auren ba tsakanin Nana da Sadik waze tsawatarwa wani? Banda shirme da Yarinta babu abunda za'a tsinana a wannan Auren. A haka ma kullum ba su da aiki se faɗa, ina ga zaman Aure?
Shikan sa Auren babu lallai sun san meye Auren balle suyi zaman Aure, ta guri ɗaya yaji sanyi a ransa, kasancewar Nana boarding aka samar mata, kafin dai ta gama Makaranta, su tare ƙil sunyi hankali.
Ga Hakimi yai jan kunne sosai akan Auren, dan yace be yafe ba idan aka sake wani abu ya samu wannan Aure.
Cikin dare kusan ƙarfe biyu da rabi na dare, Aka kaiwa Abbas sakamakon gwaje gwajen da a kaiwa Farhan.
Ya sa aka kawo masa magunguna, ya tafi da kansa yai mata serving medication.
Ulcer tai mata mummunan kamu, peptic Ulcer irin me riƙe numfashin nan, ga jininta yai ƙasa, ga kuma very high BP, nan ya shiga mamakin yadda a kai wannan 'yar ƙaramar Yarinyar ta samu wannan ciwuka haka.
Ba yadda za'ai ace lokaci ɗaya duka wannan ciwukan suka kamata, sannu a hankali suka kaita ƙasa haka.
Se da ya ja gajeren tsaki,da ya tuna yadda Hajiya ta bashi labarin yadda take zaune a gidan su.
A fili yace "Wannan ai shirme ne, Al'ada ai ba Addini bace"
Yai mata Allura ta cikin canula, yana yi yana monitoring vitals ɗinta, duk da an samu improvement ba Kamar lokacin da aka